Sashe 54
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A take gaba d’aya hankalinsa ya sake tashi ya yi dan haka ya ga gara ya kira Najeeb..
ko gaisawar kirki bai bari sun yi da Najeeb d’in ba ya ce ‘’ya nema masa adress d’in Manubiya yanzu, gashin nan zuwa wajen sa, idan ya zo zai ji komai’’.
Yana gama fad’in haka ya katse kiran ya bar Najeeb kare da waya a kunne..
Wanda ya shiga lissafin
…ya kamata ace a dai-dai wannan lokacin ya fara yi wa Yash dariyar mugunta, duba da yadda a baya yake zaginsu idan yaga suna abu a kan soyayya dan gashi alhakin su ya kama shi, tunda gashi yana nema ya susuce tun kafin a je ko’ina ma…..da kuma alhakin y’an matan da suka sha yin kuka a gaban sa saboda matsananciyar buƙatar samun kulawar Yash ɗin, amman kuma gaba d’aya tausayin Abokin nasa sai ya hana shi, sakamokon rikici, fargaba hatta da tsoron da ya jiyo k’arara a cikin muryar Yashjub d’in yanzunnan…
A hankali ya fesar da iska kafin ya furta kalmar ‘’so gamon jini’’ a fili. daga haka ya datse ya kira class rep ya ce “ya tura mass number Abbakar yanzunnan”
A ransa yana mai cewa “k’iri k’iri dai Yash sai ya janyo min raini a wajen Yaran nan, dan yanzu kam babu batun kwana kwana saboda ana ji na tambayi kwatancen gida za a fahimci inda muka dosa…”
Gaba d’aya hankalin Abbakar tashi ya yi, tunda Sir Najeeb ya kira sa ya tambayesa kwatancen
gidan su Manu.
ji yake inama bai yi wa sir Najeeb ɗin kwatancen ba…tsabar halinda yake a ciki tashi d’aya idanuwansa suka ka’da su ka yi jajawur.
Ya tsani abunda zuciyarshi ta gama aiyyana masa akan ya yi,
amman kuma bashi da yadda zai yi..
ya san abunda yake shirin aikatawa bai kamata ba amman fa zuwa yanzu ya fahimci hukuncin da ya yanke kwanakin baya ba shi ne mafita ba!
don tun kafin a je koina ya fahimci idan bai d’au mataki ba tou tabbas hakan na iya zamtowa ajalin sa.
Ba ya so! sam baya k’aunar abunda zuciyarsa take gaya masa take saka tunzura sa akan ya aikata dan ya san hakan bai dace ba amma kuma babu yadda ya iya, dan haka ya d’ago wayar tasa ya bi number sir Najeeb wadda ya kira sa da ita yanzun ya danna call….
Najeeb yana zaune a office d’inshi yana duba wasu takardu Yashjub ya shigo tare da sallamar sa…
Murmushi kawai Najeeb ɗin ya yi ya mik’e yana kallon sa kafin ya ce ’’na Manubiya bada kanka a sare’’.
Kallon sa kawai Yashjub ya tsaya yana yi, dukda ya ji dad’in furucin nasa amman kuma yadda ya gansa ba a shirye chap ba ne ya b’ata masa rai!
Dan haka cikin rashin jin dad’i ya ce ‘’Najeeb, ni da nake tunanin zan same ka a parking lot amma shine kalla ko socks babu a k’afarka ballantana takalmi sannan duba suits d’inka a gefe!
Ina wayarka? Itama na san sai ka nemo ta ko??’’.
Dariya Najeeb ya yi, sannan ya yi sauri ya saka socks d’in ya d’auka suit d’in da takalminsa ya rik’e a Hannu tukunna ya d’au wayarsa da makullin office d’in ya na me kashe computer ya ce ‘’muje Oga’’
ya fad’i hakan yana dariya.
Suna fita a office d’in ya samu ya saka takalminsa sannan ya rufe office d’in ya bi bayan Yashjub wanda ya riga ya yi gaba da d’an sauri, yana tafe yana saka suit d’in tasa.
Suna shiga motar, Yashjub yana shirin yi wa motar key kira ya shigo wayar Najeeb….
bai d’auka ba dan baya buk’atar takura a yanzu saboda yana so Yashjub ya bashi labarin mai ya faru tsakanin sa shi da Manubiya da ya rikice ya gigice har yake buk’atar zuwa gidansu da gaggawa haka!…
Ganin an kira har sau biyu bai d’auka ba sannan ga na uku ya shigo ya sanya ya zaro wayar yana mamakin waye ne haka..
ya d’an yi mamakin ganin sunan Abbakar da yayi saving d’azun, dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba.
Daga d’ayan b’angaren Abbakar ya ce “Assalam alaikom, Sir!
Ɗazu na ji ka tambayeni gidan su Manu, shine ban sani ba ko zuwa za ka yi?’’
Sai da Najeeb ya ɗan juya ya kalli Yashjub wanda ya cilla kan motar ga titi tukunna ya d’an jinjina kai kafin ya ce ’’Eh,muna hanya ma’’
Dum!! Haka k’irjin Abbakar ya buga, ya ma kasa magana, ya kasa cewa komai..kafin da kyar ya samu ya ce ‘’yanzunnan su ka tafi k’auye, gaba d’aya y’an gidansu, sai jibi
Za su dawo’’.
Shiruu Sir Najeeb ya yi, yana d’an nazari kafin ya ce ‘’okay shikenan, ma zo jibin idan sun dawo’’
Daga haka ya kashe kiran ya juya ga Yashjub wanda yake tambayar sa “kai da waye ne?”.
Shiruu Najeeb ya ɗan yi, yana so ya fahimci wani abun game da Abbakar…kafin kawai ya kalli Yashjub sosai, sannan ya ce’’ba fa sa nan, yanzunnan suka tafi k’auye’’
K’iiiiii!!!! haka Yashjub ya ja burki, tukunna ya juyo a d’an fusace ya cewa Najeeb d’in ‘’kuma shine ban ji ka tambayi wanne k’auye ne ba?ko ka san k’auyen?’’
Ɗan ƙuraa masa idanu Najeeb ya yi yana kallon shi kafin chan ya ce
‘’idan na tambaya zuwa za mu yi?’’
‘’Ba tare da b’ata lokaci ba ma kuwa’’
Yash d’in ya ba sa amsa ya na me matsar da motar tasa gefen titi dan ya tare hanya har ya fara tara goslow.
Sannan ya sake cewa Najeeb
‘’Wai tunanin mai kake yi ne?, ka kira da wuri mana mu samu mu kama hanya time is against us(bamu da isashshen lokaci)’’ ya fad’i haka yana kammala parking d’in sannan ya juyo ya zubawa Najeeb lumsassun idanuwansa!.
Sai kuma cikin fushi sosai ganin Najeeb d’in still shi yake kallo sannan yak’i ya sake kiran wayar ya ce
‘’Bani number in kira su, bani mana da wuri ‘’
ya fad’i haka yana mik’awa Najeeb hannunsa.
A hankali cikin kwantar da murya Najeeb ya ce ‘’dan Allah, ka d’an nutsu ka sarrafa komai ko da ace na mintuna biyar ne a cikin kwakwalwarka,
saboda ita kanta idan ka wanke k’afa ka bita har k’auyen su a haka tou akwai matsala,
ka tsaya ka fad’a min abunda ya faru sai a san abun yi, dan Allah.’’.
Shiruu Yashjub yayi, kafin kawai ya d’auke kai!
dan in ya biyewa jayayya da Najeeb yaga alamar ransa ne zai sake b’aci…
A hankali ya kwantar da kansa a jikin seat d’in da yake zaune a kai…
sun kusa mintuna talatin a haka kafin Yashjub ya gyara zamansa ya kunna motar ya ja suka koma inda suka fito.
Har ya sauk’e Najeeb bai sake kallon inda yake ba haka nan ya juya ya wuce ko sallamar Najeeb d’in bai tsaya ya amsa ba,
girgiza kai kawai Najeeb yayi daga haka ya nufi tasa motar ya shiga yayi mata key shima yayi gaba yana mamakin Yashjub da zazzafar soyyayar Manubiya wadda ya lura ta d’an fara tab’a masa Aboki…
Zuwa wannan lokacin Najeeb ya fahimci k’arya Abbakar ya yi masa dan sai yanzu ya tuna suna da exams ma yau da safe around 9 yanzu haka ma maybe sun shiga, but baya so Yashjub ya je wa manubiya a haka dukda bai san me ya had’a su ba, zai bari in Allah ya kaimu gobe sai ya je ya lallab’a Abokin nasa ya fad’a masa me ya faru daganan su san abun yi dan a yadda suka rabu da Yashjub ya san ba zai tab’a sauraron sa yau ba.
Lamarin Abbakar kuma akwai sark’ak’iya.. ya lura Manubiyan kanta tana ji da shi, shiyasa yake so ya nemi bakin zaren ya san abunyi dan ya san idan Yashjub ya san wani abun tou abun ba zai yi dad’i ba shi kuma bayaso Yash ya samu matsala da Manubiya saboda wani Abbakar…..
In banda ciwo ba abunda kan Yashjub yake yi, tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi ja,
in da ace zai san inda Manubiyan take to da sai yaje….
Kawai dai ya tabbatar tunda Najeeb ya masa haka to fa ba zai tab’a fad’a masa ba shiyasa kawai ya hak’ura ya yanke shawarar ya tafi gida yayi sabon shiri……
Yau ma kamar kullum haka Manubiya ta tartara Abbakar ta zuba a kwandon shara, tak’i kula shi.
Ya riga ta kammalawa dan haka yana gama submitting ya yi sauri ya d’auke jakarta daga inda ake tara jakankuna ya fice ya tsaya jiran fitowar ta.
A wajen ta same shi yana tsaye yana jiran fitowar tata.
‘’Ba ni jakata’’ shine kawai abunda ta ce da shi cikin tsare gida.
Murmushi ya yi ya k’arasa inda take tsaye kafin ya ce
‘‘Ki yi hkr tou, dan Allah’’
‘’Ba komai ya wuce Abbakar,
kawai dai na ji haushi ne..bai kamata kai, musamman kai ba wai ace ka b’oye min abu irin wannan ba .shiyasa na ji zafin
abun, yanzu kuma na huce
so ba komai ya wuce.’’
A hankali cikin sanyin murya da mutuwar jiki sannan idanunsa a kanta kyam ya ce
‘’Sure?
ba za ki tambaye ni dalilinna na yin hakan ba??’’
Da sauri ta ce ’’komai ya riga ya wuce, in da ace bai wuce ba da ko kallon ka ba zan yi ba kai ka san halina, tunda har ka ga na kula ka tou ya wuce kenan, kuma bana so ka sake yin maganar’’
Ajiyar zuciya ya sauk’e, ahankali yace ‘’Thankyou’’
‘’Um’’
kawai ta ce, daganan ta yi gaba shi kuma ya bita rike da jakartata a hannunsa, suna tafe suna d’an tab’a hira.
Gaba d’aya Abbakar haushin kansa yake ji na k’aryar da ya yi wa sir Najeeb sannan bayaga hakan ga ta nan a gaban sa amman ya kasa fad’a mata abunda yayi, shi sai yanzu ma ya yi tunanin watak’ila fa sir Najeeb d’in zai iya ganin su a cikin makarantar kuma tare dan haka yayita addua Allah yasa har su fita kar su had’u da shi.