Sashe 58
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gigice ta fito ta bi bayan su, kafin ta kai soron ta fara hangensu a ta chan waje su biyu akan mashin d’in Ya Yusuf d’in amman kafin ta kai ga fita tuni Ya Yusuf ya burga mashin d’in nasa sun wuce.
Kasa tab’uka komai ta yi tsabar rikici, kafin kawai ta fashe da kuka, ta durk’ushe a wajen abun tausayi…
Ta dad’e a haka tukunna da kyar ta samu ta tsayar da kukan nata, ta na shirin mik’ewa Manubiya ta shigo…
A rikice ta k’arasa inda take ta shiga tambayar ta “mai ya faru?”
Da kyar Jidda ta iya yi wa Manubiya bayani, aikuwa a take ita ma ta gigice ta fita a hankalinta duk yadda ta so k’in yin kuka kasawa ta yi dan haka ta bar hawayen suka shiga sintiri akan kyakkyawar fuskarta…
da kyar suka rarrashi junan bayan wasu lokuta tukunna suka share hawayen su, gudun kar su shiga su je maybe ko Inna ta farka ta gane sun yi kuka.
suna shiga kuwa suka tarar da ita ta farka, dan haka suka danni kansu suka Bata abinci da maganinta da kyar, duk da sun lura da yadda take ta kallon su ma’snar ta gane suna cikin matsala kuma tana buk’atar k’arin bayani amma cikinsu ba wadda ta ce mata komai, suka nuna kamar basu fahimci me take nufi ba…..
haka nan ta hak’ura ta kyale su.
Har sama da mintuna talatin, amman sun gagara tab’uka komai, dan gaba d’aya a gigice suke ga kuma k’ok’arin b’oyewa Inna damuwar su da suke ta faman yi…
da kyar suka d’an fara sauk’k’o da jakankunan, suna tunanin inda za su ganshi ko su san abunda ya faru, daganan sai a san abun yi.
Ganin bazama su iya had’a kayan bane gashi sun ma kasa yin lissafi mai kyau tsabar rikicewa ya sanya kawai suka yi alwallah suka shiga jero nafilfili suna masu kaiwa ubangiji kukan su…
ahaka har aka shafe kusan awa biyu da rabi!
sai da suka ji sun d’an dawo dai-dai tukunna k’asa-k’asa Manubiya ta ce mata ‘su had’a kayayyakin nasu kamar yadda yace, in ya so sai su san inda za su kai inna daga nan su shiga neman Baba da neman mafita..’
sai da suka gyarawa Inna kwanciya…ta hanyar juyar da ita ta yadda ba za ta ga mai su ke yi ba tukunna suka shiga had’a kayan a hankali gudun kar ta fahimci mai suke yi..
tsaff!! suka had’a komai, suka zauna suka yi jugum!
A haka har aka shafe wata awa biyun babu Baba babu labarin shi, sai a lokacin sukayi lissafin su nemi Ya Musbah dan tsabar yadda suka gigice sam ba su yi wannan tunanin da farko ba!
Manubiya ce ta ce bari ta je ta dubo shi dan wayarta ba kud’i kuma ta ma kashe, Jiddah kuma ta zauna da inna wadda ta fara bacci yanzunnan….
Ganin har kusan mintuna ashirin ba Manubiya ba alamarta ne ya sanya Jidda ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar zuwa kiran Manubiya.
Tana d’aga labulen ɗakin suka yi ido biyu da Ya Yusuf…
bayansa ta kalla sannan ta d’an lek’a wai ko za ta ga Baba amman sai ta ga wayam!!!
ba tare da ta sake kallon sa ba ta dake sannan ta danne tsoron sa, ta fito ta zo za ta wuceshi.
Hijab d’inta ya janyo ya fisgo ta ya dawo da ita gabansa ya tsayar!
Da sauri Jiddah ta sunkuyar da kanta, dan tashi d’aya hawaye suka shiga silalo mata…..
hab’arta ya kama ya d’ago da fuskar tata da k’arfi wanda hakan ya sanya ta yi saurin runtse idanuwanta hawayen suka shiga sintiri da sauri da sauri akan kyakkyawar fuskarta.
Ya jima yana kallonta tana kukan kafin ya ce
‘’Ok,sorry!(ok, yi haƙuri)”
Ya fad’i hakan yana cika hab’ar tata kafin ya d’aura da cewa ‘’Gani na yi kina neman ki nunamin taurin kai, shiyasa ni kuma na dawo da ke seti..wannan kukan da kika yi ya nuna min ke d’in ce dai Jiddahta’’,
sai da ya fesar da iska tukunna ya ce ’’za mu iya yin magana yanzu’’
ba tare da ya jira jin mai zata ce ba ya fara da cewa
‘’Baba bai dawo ba har yanzu,
na ji d’azu yace ku gudu ko??
So a gani na a yanzu gaskiya gudawar itace kad’ai zaɓinku, amman kuma tsaf za ki iya gyara komai dan komai a hannunki yake.
Ga Baba mallan chan a d’akinshi, Babana shima yana nan,
Ki zo mu je kawai a d’aura mana aure, daganan ni kuma na yi alk’awarin zan saki Baba.’’
A rikice ta d’ago ta ce ‘’Ya Yusuf kai ne ka kama sa? mai ka
yi wa Babana?
ta ya akayi ya yarda ya bika?’’.
Ta k’arashe tambayar tata
cikin tsananin rud’ani da tashin hankali.
Murmushi ya yi kafin ya ce
‘’Ba ni na kama sa ba, amma ni na yi silar da aka kama sa…..
Jidda abun takaicin shine
akan naira miliyan d’aya tak za’a kulle Babanki kina ji kina gani!!saboda tsabar taurin kanki, haka nan zai yi ta shan wahala, bayan kina da ikon da za ku taimake sa…
bari in faiyyace miki abunda ya faru….
Ranar chan a masallaci na gan sa yana kuka, sai na nuna masa na ji tausayin sa ne, na ce masa ‘ana bada loan a bankin da nake aiki, idan yana so zai iya k’arba ya yi business da shi, bayan shekara uku ya biya’
na yi masa alk’awarin a k’asan suna na ma zan saka shi!
ta yadda ko da ace ta kwab’e ya kasa biya ba za’a kama sa ba tunda sunana ne a wajen,
kuma ma inshaaAllah kafin nan za mu biya kud’in…’
A take ya ce min ‘akwai business d’in dama da yake da shi a rai, ya ke son yi!
InshaaAllah a cikin shekara biyu ma zai had’a kan kud’in ya cire ribar sa.’
A lokacin alhaji Baba har rungume ni ya yi,
Allah sarki na ji tausayin shi kuwa na so in janye k’udirina da na k’ulla akansa amma kuma da na tuno da kalar cin fuskar da kukayi min
Sannan na riga na fahimci indai ba ta haka na biyo ba to
ba zan tab’a samun ki ba…
Sai na kauda tausayin shi a raina, na d’auke shi muka je ya cike form kala-kala ba tare da ya san mai yake cikewa ba…..wanda a ranar tabbas rashin zuwa makarantar Baba ya taimaka min ya kuma yi min amfani matuk’a!!
saboda dama Inata adduar Allah ya sa kar ya fahimci wani abun amman sai naga ashe…’’
sai da ya d’an guntse dariyarsa yayi k’asa da murya sosai tukunna ya ce ’’ashe Baba ko cikakken sunansa ma bai iya rubutawa ba’’
Ya fad’i hakan yana mai kwashewa da dariya…
Sannan ya ci gaba da cewa
“Ni na dinga yi masa spelling,
na nuna masa inda zai yi tumbprint, shi kuma ya yi ya mik’a.
Bawan Allah har muka dawo gida yana ta yi mini godiya,
Ina ga
Ya san in ya gaya muku za ku tuhume shi shiyasa ya yi shiru dan har d’azu ma sai da na tambaye shi, shi kuma ya ce min ba ku sani ba, ni kuma na ce to zan zo in yi muku bayani ta yadda za ki fahimceni dalla-dalla, dan har ga Allah dama na ji dad’in shirun da yayi saboda dama banaso kowa ya sani sai a yau d’in.
Na san za ki ce min mai naci ko kuma mara zuciya Jidda amma inaso ki san cewa duk abunda na yi na yi sa ne saboda farin cikinki!
sai kin aure ni tukunna za ki fahimci gatan da nake ta k’ok’arin ganin na tsunduma ki a ciki.
Ki taimake mu ki yi abunda nake so, daganan sai mu je mu ceto Baba, dan muddin suka riga suka tafi da shi to ko an biya kud’in tabbas fito dashi ma aiki ne!!!
inada dubu d’ari tara zan bada cash na san ba za’a rasa cikon da zai had’a kan kud’in ba har intrest d’in ma.
Iyakar abunda za ki yi hargitsin nan ya mutu shine ‘kawai ki aminta da ni!’
Daga nan komai zai tafi cikin tsari.
Ya yarda da ni sosai, yanzu haka yana chan yana jirana in je in fitar da shi, dan ce masa na yi zan zo in yi muku bayani in kwantar maku da hankali daganan in tafi neman kud’in da za’a harhad’a a fito da shi.
To ni kuma kinga sai kin yi min abunda nakeso tukunna zan fitar da shi
Dan haka kinga ƴancin Babanku a hannun ku ya ke.
Sannan bayan an tafi da shi,
za’a zo a kama ku dukkanku har sai kun fito da kud’in nan!!
daga nan kuma a fara kiciniyar fito dashi..’’
Wani irin kuka Jidda take yi abun tausayi, da kyar ta samu ta d’ago kenan za ta yi magana idanuwanta suka sauka akan Manubiya wadda ta gama yawon neman Ya Musbah a wajen wankin su da Gidansa amman bata same shi ba.
Da gudu Jidda ta tafi ta fad’a jikinta ta sake fashewa da wani Irin kuka….
Tsabar tsananin mamakin Ya Yusuf da takaicin sa da kuma tsananin tashin hankali sam Manubiya ta ma kasa kuka ta kasa magana…
haka kawai ta kafe Ya Yusuf da idanu kafin ta samu ta janye Jidda daga jikinta a hankali idanunta har zuwa wannan lokacin suna akan Yusuf d’in tukunna ta nufesa…
yadda Yusuf ya ga ta nufosa sai da ta yi masa kwarjini, aikuwa tana k’arasawa inda ya ke bata yi wata wata ba ta d’aga Hannu ta zabga masa wani irin gigiceccen marin da ita kanta bata san tana da k’arfin yin irinshi ba…..
A rikice Ya Musbah wanda suka dinga tafka sab’ani da shi da Manubiya ya iso hanyar d’akin nasu..tun d’azu Baba ya bada numbersa aka kira sa har ma sun yi magana da Baban.
Bai ga marin da Manubiya ta yi wa Ya Yusuf d’in ba sakamokon k’ofar d’akin nasu da take a ta d’an lungu amman fa yana karya kwana ya hango Ya Yusuf ya shak’e Manubiya da dukkanin k’arfin da Allah ya yi masa, ga Jidda a gefe tanata k’ok’arin kwatar Manubiya amma ta kasa.