← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 84

Sashe 74

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai Yahanasu ta yi kafin ta mik’e ta ce “ina zuwa” tukunna ta Isa jikin k’ofa ta bud’e, ta d’an duba tare da sak’ala key..
saboda yadda ta ji jikinta ya bata akwai Mutum a wajen.

Tana dawowa ta zauna sannan ta ce
‘’Yanzu tou ya ake ciki?
Itama ta amince ne? sannan Yash kana ganin ƙin gayawa su Mommy ba zai janyo wata matsalar ba kuwa?
Kar su ga ka b’oye musu sannan ka gaya musu a k’urarren lokaci, Ka san ba za su ji dad’i ba, za su ce bama su san kana da budurwar ba.

Dole na san in suka ji aure kwatsam zasuga kamar ka b’oye musu ne ko wani abu makamancin haka’’

Iska ya fesar kafin ya ce ‘’Yaha, kin san abunda na gaya miki kwanaki akan Kausar..
In ta ji labarin Inada budurwa aiki ne, kuma kin san Mommy bayanta za ta bi!
Dan haka
Pls, ki bar maganar nan, bana so in gaya musu saboda Kausar wadda banaso ma Ina tuna abunda na ji ranar ta fad’a a kaina, wallahi raina b’aci yake yi!!!.
Maganar Manubiya kuma gobe zan gaya mata
dai..
inshaaAllah Ina fatan Allah yasa ta amince da ni,
dan ba zan ma iya tunanin wai bata amince d’in ba.
Ina adduar Allah yasa zargina ya zamo gaskiya dan na ga kamar itama tana so na.

In komai ya kammala za ai auren ciki gaggawa dan ba zan tsaya ɓata lokacin da zai bawa Mommy ko Kausar damar kawo min cikas ba.”

Murmushi yahanasu ta yi, kafin ta ce ’’na fahimceka, kuma inshaaAllah ba za ma a samu matsalar komai ba.
sannan na san dole ma Manubiya ta ce maka yes! goben nan, dan
bana jin a kaf fad’in duniyar nan akwai Macen da za ta ƙi amincewa da lil bro ɗina(ƙanina)’’.

Dariya ya yi kafin ya d’an harare ta cikin sigar wasa, sannan ya ce ’’lil bro kuma? ko cikakkiyar awa d’aya fa ba ki bani ba’’

‘’Amma dai na girme ka! ko da da second d’aya ne, na dai girme ka’’

Dariya duk sukayi kafin Yahanasu ta ce ‘’amma ta ya kake tunanin iyayen ita Manubiyan za su amince su aura maka y’ar su a cikin wata d’aya kamar yadda ka fad’a?
Ko zaka d’an d’aga k’afa ko wata uku hak….’’

Girgiza Kai kawai ya yi kafin ya ce ‘’gaskiya ba zan iya ba,
dukda ban san ta ya za’ayi su yarda da auren a haka ba amma zan yi ta addu’a, kema ki tayani,’’
Yayi mata maganar cikin yin kalar tausayi, har da wani karyar da wuya .

Tausayi da dariya ya bata dan
haka ta ce ‘’inshaaAllah, komai zai tafi yadda kake so’’.

A hankali ya ce ‘‘Allah yasa”
daga nan suka shiga tattaunawa game da lamarin….’’

Yahansu ta san menene so duba da yadda itama ta so first love ɗinta(saurayinta na farko a duniya) kamar ranta,,saurayin da ya fara yin watsi da ita…
Shiyasa yanzu sam bata ganin laifin Yashjub da ya gigice akan Manubiya….
Adduarta d’aya ita ce ‘Allah yasa a bashi ita a yi auren kamar yadda suketa tsarawa yanzun, Allah yasa kar su Mommy su kawo cikas d’in komai.’

Yash yana k’aunar y’ar uwar tasa sosai..ya lura da yadda su Yasira basa janta a jiki..dukda bai ma san wasu daga ciki hantarar da suke yi mata ba
amman yana yawan tsawatar musu da nuna musu gaskiya,
kawai dai ya san tunda suka riga suka nuna basa sonta to ba lalle ya iya gyara tsakaninsu su dawo su k’aunace yadda ya kamata ba. Yanaso ta ji itama ta musamman ce…itama ta ji tanada ɗan uwa me kaunarta a ko da yaushe, shiyasa ya ke bata kulawa ta musamman,
kuma har ga Allah yana ji da itan da gasken gaske kuma ita kad’aice zai yi shawara da ita ya ji dad’i dan sun saba sosai, shiyasa yanzun ma yake ta neman shawarwarin ta…
Ta kuwa ji dad’i
tun ba ma da ya ce ‘itace za ta had’a masa lefe ba!’
bata san lokacin da ta fashe da kuka ba….

Yahanasu….
Ta kan yi kukan rashin jituwa tsakaninta da y’an uwanta mata, amma a duk lokacin da ta tuna tana da Yash sai ta ji duk damuwarta ta Kau.

Bata jin a duniya akwai d’an uwan da ya ke tsananin k’aunar ƴar uwarshi kamar yadda Yash ya ke ƙaunarta ya ke ji da ita, ko shawara ce da ita ya ke yi,
ko menene sai ya gaya mata….
shiyasa har yau har gobe ta kasa yafewa kanta duba da yadda ita ta kasa gaya masa abu mafi mahimmanci na rayuwarsa bayan ta sani, kuma tana da ikon da za ta taimaka mishi wajen samun abunda ta san zai sanya shi farinciki fiye da komai…..

Ta jima tana kuka har sai da ta
d’an fara bawa Yash ɗin tsoro.

Tukunna ya samu ya rarrasheta da kyar,
ya d’an jata da wasa da hira
daga nan suka shiga wata maganar….
Kafin daga baya ya yi mata sallama, ya tafi bayan ya samu ta hak’ura ta karb’i number Manubiya kawai
dan da farko cewa ta yi sai ya kira mata ita sun yi video call,,
da kyar ya lallab’ata ta hanyar ce mata “Manubiyan ta yi bacci by now.’’
daga haka suka yi sallama, ya tafi.

……..2 hours before now………
…….awanni biyun da suka shuɗe(kafin yanzu)..
Ummi bata wani dad’e a wajen su Mommy ba, ta fita ta wuce d’akinta.
Bata dad’e da fita ba, su Yassira suka shigo, suka taru a d’akin har Yasmeen kamar wasu masu meeting.

Mommy ce ta cewa Yasira ‘ita da Kausar, su je su saka mata ido a k’ofar Yahanasu’
dan ta san tunda ya ce yana so yayi magana da Yahanasun yau to komin dare sai ya je sun yi, su kuma ta maganar da za su yin ne kawai za su samu haske akan zargin nasu….

Ba k’aramin tashin hankali ta sake shiga ba lokacin da ta kira shi ta ji yana waya, kawai ita ta yadda ta gama amincewa ta bada amanna akan maganar Baaba Larai!!
Shiyasa kwata-kwata kwakwalwarta bata bata cewa ‘ai waya yake akan business ko wani abun ba!
tashi d’aya ta amince kawai da wannan Yarinyar yake ta waya.’.

Yassira ce ta samu ta ga Yash d’in, dan Kausar ta saman balcony ta tsaya tana jiranshi, ta yadda yana fitowa daga side d’inshi ita kuma zata gani daga nan sai ta jira in ya shige d’akin Yahanasu ta je ta lab’e!!
saboda ta fi kowa k’aguwa da son jin menene asalin gaskiyar maganar amma sai Allah bai bata ikon ganin nashi ba dan lokacin dai-dai ya zo zai wuce sai aka yi mata text dan haka bata ga shigar tasa ba.
…
A kitchen Yasira ta jira har ya gama da wajen Daddy ya sauk’o ya shiga d’akin Yahanasu, tana ganin ya shige ya turo k’ofar ita kuma ta fito ta Isa bakin k’ofar da sauri ta lab’e.

Shiruu Yassirar ta yi tana sauraron su…
Wato dai zargin su ya tabbata kenan, sannan bayaga hakan kuma aure cikin wata d’aya ma yake son yi!!!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta aiyyana hakan a cikin ranta hankalinta a masifar tashe, ta shiga lissafin….
‘Shin ta ya za su iya
cin nasara akan wannan abunda ya taho musu gadan-gadan haka?.
Babu tausayin wadda ya lullub’eta sai Kausar!
Saboda zuwa wannan lokacin idan Kausar ɗin ta yi wani abun har mamaki take bata, kamar
wata wadda ta fara samun taɓin hankali haka so da k’aunar Yash suka maida ita, sam bata ji bata gani aduk abunda ya shafeshi …’
Yasira tana cikin wannan tunanin ta ji Yahanasu za ta bud’e k’ofar
dan haka ta yi sauri ta wuce ta
fad’a kitchen.

…Now…
…yanzu..
Sai da Yassira ta ji fitar Yash, tukunna ta fito, tana ji kamar zuciyarta za ta tarwatse,
ta nufi sama.
*MANNUBIYA*
*44*

Kausar na tsaye, ta saman balcony ta hango fitar Yash..
ta yi mamakin rashin ganin shigar shi ɗin da bata yi ba dan haka ta fito da sauri tana adduar ‘Allah ya sa Yassira ta samu ikon saurarar su.’
Dai dai tana fitowa ta hangi Yassirar ta nufi side d’in Mommy a rikice, dan ko lura da fitowar Kausar d’in ma bata yi ba.

Da k’arfi k’irjin Kausar ya buga! yayinda k’afafuwanta su ka fara karkarwa…
Da kyar ta samu ta tattaro gaba d’aya kuzarinta
ta bi bayan Yassira tana jin kamar zata fad’i a k’asa dan tabbas wannan rikicewar da ta ga Yassira ta yi tou akwai matsala kenan.

Yassira tana shiga d’akin Mommy, duk suka mik’e tsaye!.
Dama gaba d’ayansu sun taru
Yusra da Yadira ne kawai babu.

Yasmeen ce ta matso kusa da ita ta ce
‘’Lafiyan ki kuwa? Me ya faru?’’

Wani k’ululu da ya tokare mata mak’oshi Yasira ta hadiye tukunna da kyar ta ce ’’Ya‘isha, ku d’an fita, Ina son yin magana da Mommy ita kad’ai’’

Cikin d’an b’acin rai Baaba Larai ta ce ’’zancen banza kenan, waye kika gani Bare a cikinmu?’’

A hankali Yasira ta lumshe idanunta ta bud’e ta na jin tsananin tausayin Kausar har ma da Mommy yana sake lullub’eta, kafin ta ce ’’Ba haka bane Baaba, bana son maganar ta yayatu da yawa ne gudun kar wata a cikin ku ta manta ta yi suɓutar Baki a gaban Kausar.’’

Dai-dai nan Kausar wadda ta k’araso bakin k’ofar d’akin Mommy ta jaa ta tsaya…
Tabbas a yadda ta ga Yasira d’azu da kuma yanda ta ji muryarta a yanzu da abunda ta ji ta fad’a, ta san idan ta ganta ba za ta fad’a mata komai ba duk runtsi!.
Dan haka kawai sai ta yanke shawarar lab’ewa a wajen.

A hanakali Mommy wadda gabanta ya fara fad’uwa sosai, ta k’arasa inda Yassira take ta ce
‘’Yi magana Yassira, ko menene ma fad’i, za mu iya fuskanta in sha Allah!.
Me ya faru? Wacce maganar ki ka ji Yash suna yi da Yahanasu?’’.
Chapter 74 · 0% Book details