Sashe 83
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun jiya da suka samu matsala da su Baba Habu hankalinsa yake a tashe dan ya san auren Jiddan da yake gani tana da Miji a Hannu ba mai yiwuwa baneba…
Shiyasa gaba d’aya hankalinsa ya sake tashi, sai gashi da ikon Allah Allah ya kawo Yashjub…..in dai aka yi bincike ya ji komai daidai akansa to inshaaAllah a cikin sati biyu kamar yadda ya fad’a zai aura masa ita.
…..
A cikin kwana biyu Ya Musbah ya yi bincike ya gama, ya so ya ƙi gayawa Baba
amman sai Ya Nafi’u ya soma da yi mishi nasiha, ta inda ya ke cewa
’’ka kalli komai da kyakykyawar fuska, kar ka yi
mummunar zato. Mu bi komai da addua tunda bamu Isa mu hana Baba yin abunda yayi niyya ba, uwa uba idan Ubangiji ya riga ya rubuta matarsa ce to fa ba mu Isa mu hana ba’’
Kamar ya Musbah zai fashe da kuka ya ce ’’Nafi’u ba fa anan ya girma ba,
taya za ayi amfani da shaidar da aka bayar akansa anan Nigeria??’’
Nasiha da fahimtarwa sosai ya Nafi’u yayi masa, sannan ya masa nuni da rashin son tsananta bincike kafin ya k’are da cewa “mu bi komai da addua, za a ga alkhairi inshaaAllah’’.
Ya Musbah bai iya gayawa Baba komai ba
Ya Nafi’u ne ya same shi yayi mishi bayani.
Sai washegari tukunna Baba yana shirin kiran Yashjub d’in shi ya kira sa.
Dan shi Yashjub har ga Allah ya k’agu, abu har kwana uku sun ce za su neme sa amma har yanzu shiru…Ya san ba shi da wani mummunan hali amman ya kasa hana kansa jin fargaba da tsoro.
Dukda ya san za a ga zumud’in sa amman shi fa akan Manubiya aga komai ma bai damu ba.
………Bayan doguwar gaisuwa da tambayar Baba ya jiki da jikin inna kuma sai kuma ya hau kame-kame.
Murmushi Baba yayi yana yaba yanda Yashjub d’in ya ke son Manubiya, shifa tun lokacin da aka bata aiki dama ya fara tunanin wani abun
Shi a zaton sa ma sir Najeeb d’in ne sai da yaga Yashjub da yanda yayi lokacin da ya ga black snake rik’e da hannunta tukunna ya tabbatar Yashjub d’in ne.
Cike da kamala Baba ya ce ’’yanzu nake shirin kiranka’’
Sai da Yashjub ya d’an sosa k’eya tukunna ya ce ’’to Bara inzo yanzun Baba’’…kamar wachchar ranar Baba so yayi kawai su gama a waya tunda ba wata magana mai tsaho bace ba amman sai Yash d’in ya dage akan yana so ya zo d’in….bayan kamar mintina ashirin sai ga shi….
A masallaci yau ma suka sauk’e shi, Baba ya so ace su Uncle sun d’an shiga maganar amman ko da ya je musu ma ko kallo bai ishe su ba dan gaba suke yi da shi k’iri-k’iri, dan haka suka tari Yashjub iya su uku, Baba Ya Nafi’u da Ya Musbah.
Cike da fahimtar juna Baban yace ‘’zuwa ko yaushe ya turo!
In ta shi ne yanaso ayi a cikin sati biyu ma amman ko yaushe suka shirya sai su fad’i lokacin da suka ga ya fi musu’’
Godiya da murnar Yashjub saida ta bawa Baba dariya dan kasa b’oyuwa ta yi, musamman ma da ya ji Baba ya ce a cikin sati biyu!
Abun yayi masa dad’i matuk’a, shiyasa farin cikin sa ya kasa b’oyewa haka yai ta murmushi bayan yayi godiya
kafin daga baya suka yi wa juna sallama tare da fatan alkhairi,ya wuce.
Washe gari …..
Yau ya shirya samun Daddy,
jiya kwana ya yi yana sallah, yau ɗin ma sai addu’o’i yake ta yi
tare da fatan ‘Allah kar ya sa a samu matsala ta ko Ina’
Dukda ya san tunda har hajiya mama ta amince to a rubuce yake Daddy shima ya amince, dan ko jiya sai da ta kira shi suka yi maganar amma
dama shi addu’ar sa ‘Allah yasa su yarda ayi a cikin 2 weeks d’in, sannan Allah ya toshe duk wata matsala da take shirin tasowa.’
Suna gama waya da Manubiya wadda rikicin ta na kwana biyun nan yake basa dariya sosai, ya mik’e ya nufi parlourn Daddy, dan ya san zuwa wannan lokacin Daddyn ya gama duk wasu aikace aikacensa……
A zaune ya same su shi da Ummi kamar wasu mak’iyan juna! Ita ta juya fuska tana kallon makeken aquarium d’in da yake a parlour ta had’e rai, shima Daddyn ya kauda Kai yana daddanna wayarsa fuskar nan tamau!.
Ko isashshiyar gaisuwa Ummi bata tsaya sun yi da Yashjub ba,
ta mik’e ta ce ‘’sai da safen ku’’
daga haka ta yi wuff ta nufi ƙofa kamar wadda take zaune akan k’aya.
Bin ta kawai Daddy yayi da kallo har ta fice ta rufo musu k’ofar….sam ya kasa gane kanta gaba d’ayanta, abun nata kamar wata mai aljanu, tun abun bai dame shi ba har ya zo ya fara damunshi…yanzu haka shi ne ya kirata akan su samu su d’an yi magana su d’an dedeta amma tana shigowa daga gaisuwa ta d’auke Kai ta had’e rai! Shi kuwa wallahi ta yi kad’an ya bita ya rarrasheta!
Idan ma abunda take jira kenan……
Ahankali cikin kwantar da murya Yashjub yace mishi
‘’Daddy, wani lokacin fa muma sai mun d’an sak’k’o tukunna zaman yake yin dad’i, kuma na tabbatar inda ace rikicin na iyakar kai da ita ne to da tuni komai ya wuce na san da bazata d’auka da zafi har haka ba, amman abun ya had’a da Yara shiyasa ta ji ciwo sosai.’’
K’ura masa idanu Daddyn yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ’’Yash!! Ko a gidan giya akwai babba. Ban auri Matar da zan dinga bin ta tana raina ni tana raina min wayo ba, yi haƙuri da abunda zan faɗa a gaban idonka..ba wai cin fuska ba amma Yash ko Macen da na so fiye da kowa batayi min wannan abun ba.
Sannan nan gidansu Yasmeen ne, abu d’aya wanda na sani kuma ba zan tab’a komawa baya akan maganar tawa ba shine
‘Dole a lallab’amin Ƴaƴana a gidan ubansu, kuma babu wanda ya Isa ya zo nan ya ce zai juya min su!’
Idan ta yarda da hakan a zauna lafiya, in kuma ba ta yarda ba
ta je ta yi ta fushi
Itace ita kaɗai……’’.
Ahankali Yashjub ya ce
‘’Amman Daddy…’’
Cikin d’an fushi Daddyn ya katseshi ta hanyar cewa
‘’Yashjub bar maganar Matar nan, banaso!’’
Shiruu Yashjub d’in yayi,
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya, sai kuma ya mik’e daga inda yake ya koma 3seater da Daddyn yake zaune akai shimanya zauna,a hankali ya ce ’’am Daddy’’
Murmushi Daddyn ya yi tukunna
yace “za a yi min wayo kenan’’
Dariya duk sukayi sannan Yashjub ya fara magana ahankali
“am..Daddy, dama
alfarmar ka da rufin asirin ka nake nema.’’
Bai jira komai ba ya ci gaba da cewa
“na san hakan yana iya zama kamar abu mai wuya amman idan ka yi min wannan gatan to ban san wanne irin farin ciki ni kaina zan shiga ba.
A baya ka sha gaya mana cewa
‘ wacece/wanene muke so a matsayin abokiyar/abokin zama, in dai tarbiyyar su ya kwanta maka to ba za ka yi k’asa a guiwa ba wajen ganin mun mallaki juna.
To Daddy ni a yanzu mahaifin Yarinyar da nake so yana buk’atar d’aurin auren nan da sati biyu ne,
shiyasa nake neman alfarmar ka
In ba damuwa a d’aura a cikin sati biyun masu zuwan kamar yadda ya buk’ata.’’
Shiruu Daddy ya yi, har sai da Yashjub ya d’ago dan kalar shirun da Daddyn ya yi ya yi yawa,
had’a ido suka yi kamar an fisgi maganar daga bakin Daddy ya ce ’’yaushe ka yi budurwa ??’’
fuskarsa tana baiyyana mamaki
Sunkuyar da Kai Yashjub ya yi da sauri dan tashi d’aya ya ji wata kunya ta lullub’esa.
Lokaci guda ya ji Daddy ya fara dariya, cikin dariyar ya sake cewa
“Dan Allah dagaske Yashjub ya akayi ka yi budurwa, abun ya bani mamaki ne, Hajiya Mama ta yi min magana tun lokacin dama nake so ka yi min maganr saboda a tunanin na ita ta had’a ka da Yarinyar ashe da gaske kai ka kyallo abarka.’’
Ya fad’i hakan yana dariya….
Kamar Yashjub zai fashe da kuka cikin yin kalar tausayi ya ce
‘’Daddy dan Allah ka daina’’
Ai kuwa ya sha tsokana a wajen Daddy, dan har ga Allah Daddyn ya ji tsananin mamaki,
kafin daga bisani kuma ya yi
gyaran murya ya gyara zama tukunna ya ce ’’Yash ka tabbatar kana sonta, itace zabin ka?’’
Ahankali yace ‘’Eh Daddy, da dukkan Zuciyata.”
‘’Alhamdulillah’’
Daddyn ya ce
kafin ya ci gaba da cewa
‘’Yash, tabbas alk’awarin da na yi muku yana nan, babu abunda ya chanza amma ka san ba zan bari ka cutu ta ko wacce irin hanya ba.
Abu d’aya da na yi mamaki shine ta inda Mahaifinta ya dage akan a yi a cikin sati biyu
wannan shine abunda zan fi sakawa na’urar bincikena akai wanda ina fatan ya kasance ba wata matsala baceba dan nima farin cikin naka nake son gani.
Idan an duba an ga ba matsala sannan aka yi bincike shima akaga ba wata matsala to da yardar Allah sai a d’aura auren a cikin sati biyun kamar yadda suka buk’ata.
Allah ya yi maka albarka.”
Ahankali Yashjub ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai jin wani farin ciki mara misaltuwa kafin a hankali a fili ya ce ’’Alhamdulillah’’
Muryar Daddy ce ta katse shi jin yana cewa “Ka bani adress d’in da wuri, saboda ina gama binciken nake so zan aikawa su Hajiya mama, dan a samu su taho da wuri suma.’’
D’an b’ata fuska Yash yayi ya d’ago ya ce ’’Daddy yanzu wannan tsohuwar itama sai ta zo?’’
Dak’uwa Daddyn ya yi masa kafin ya ce ’’Dole ta zo, kuma in ka yi mata abunda bata ji dad’i ba tsaf sai ta ce a fasa,
kasan kuma daga ni
har uncle d’in naka dole abunda tace shi za mu yi,
daganan sai in ga k’arshen soyayya’’