Sashe 68
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna fita Baba ya saki hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa…
Dama baya so ya yi kuka a gaban su gudun kar ya karya musu guiwa ya d’aga musu hankali..shiyasa yace su tafi gaba d’ayansu.
Da ace yana da yadda zai yi to da ba zai tab’a aurar da su Jidda yanzu ba,
ya so ƴaƴansa su yi karatu, yaso ace Jidda ta gama ko da level one ne tukunna, amma yanzu kam sai dai ya bita da addu’a da fatan alkhairi tare da rok’on Allah ubangiji ‘ya had’a Manubiya har ma da Jiddan da surukai na gari, ya sa su so
su’
Dan kasancewar ya san mahaifin Yusuf ba shi zai sa ya k’i yiwa y’ar sa wannan addu’ar ba!
yana rok’on Allah ya sa su jata a jiki bayan auren, Manubiya kuma Allah ya bata na gari, a samu kowacce ta zauna lafiya a gidan ta, dan tabbas abunda su maman Baraka sukayi musu yau a asibiti ya tab’a shi sosai, ya ji zafin abun.
A k’ofar gidajen nasu biyu motar Ya Nafi’u ta yi parking, dan haka suka fara firfitowa…..
Ya Musbah ne ya fara shiga cikin gidan nasa, su kuma suna biye da shi a baya.
A k’arshen soro kafin ya k’arasa shigewa cikin gidan sukaga ya ja ya tsaya chak! Ya ƙi yayi gaba sannan yak’i yayi baya.
K’arasawa kusa da shi ya Nafi’u yayi yana mai cewa
‘’Ya dai? kar ka…’’
A take maganarsa ta tsaya chak sakamakon hango Inna da shima yayi a yashe a tsakar gidan.
Da farko tunanin su basu ya yi
’watak’ila ko ta yi k’ok’arin tashi ne sai Allah ya bata iko,
shine da ta fito kuma sai ta fad’i a wajen’…
amman kuma yadda suka ga an shimfid’a mata zani sannan aka d’aura kanta akan pillow ne ya basu tabbacin wannan aikin Baraka ne.
Cikin d’aga muryar Ya Nafi’u ya hau kwala kiran ‘’Aisha! Aisha!!’’
Sai kuma ya juya zai fita dai-dai suka yi kicib’is da Aishar
dan tana jin tsayuwar motar tasa a k’ofar gidan ta d’auko kular da ta gama juye abinci a ciki ta janyo hannun y’arta suka yo gidan.
Cikin fushi ya ce ’’ya akayi kika barta kika fita? ina Muhsin??’’
Inda-inda ta fara yi, tana shirin yin magana ta ga su Manubiya sun yi cikin gidan da gudu, wanda yadda ya Nafi’u ya d’an gota suka wuce ne ya bata damar hango Innar itama dan haka ta yi ciki da sauri tana salati.
A take
Jidda da Manubiya suka fashe da kuka saboda yadda suka ji jikin Innar ya d’au zafi sosai! hatta kayan jikinta ya d’au zafi! ga ranar la’asar da ta kusan fad’uwa ta haske mata fuska sosai gashi babu damar motsawa…….
Dishi-dishi ya Musbah ya fara gani tsabar tsananin b’acin rai da tashin hankali…da kyar ya samu ya iya cewa
‘’Baraka!!’’
Da d’an k’arfi, dan jikinsa wani irin karkarwa yake yi, hatta muryar tasa rawa takeyi.
Tun lokacin da suka shigo ta jiyo su…..dan ta gama watsa ruwa a jikinta kenan sakamokon zafin da akeyi
ta ji tsayuwar motar ya Nafi’u.
Dan haka ta d’auro zaninta, ta yafo mayafinta ta rik’o kayanta a Hannu ta fito fuskarta a had’e tamau!.
…
Tana fitowa Ya Musbah ya k’arasa inda take ya tsaya..so
ya ke yayi magana amman sam sai ya gagara, in banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, dan haka kawai sai ya kafeta da idanu, ya shiga karanto addu’o’i a chan k’asan ransa yana mai neman tsari daga shaid’an saboda a yadda yake jin zuciyarsa a halin da ake ciki ya san muddin ya ce zai ɗauki mataki ko ya yi wani abun to ya san wallahi kashe Baraka zai yi!
sai ya kaita har lahira.
Tunda Baraka take a rayuwarta bata tab’a ganin Ya Musbah a irin wannan yanayin ba, babu abunda ya fi tsoratata irin yadda taga idanuwansa sun yi jajawur hatta farar fuskarsa ta yi jaa!
gashi jikinsa sai wani irin karkarwa yake yi…
Shiyasa gaba d’aya duk sai ta ji tsoro ya lullub’eta, abunda bata tab’a tunanin za ta ji ba kenan dan ko a mafarki bata tab’a kawowa akwai ranar da zata zo ace wai’ta ji tsoro ko shakkar Ya Musbah a rayuwar ta ba’.
A lokacin da suke soyayya
soyayyarshi kawai ta sani, da suka yi aure kuma..hak’uri juriya da lallashin sa kawai ta sani. Shiyasa a yanzu da ta ga asalin fushinsa abun sai ya bata tsoro matuk’a.
Sai da ta d’an yi k’asa da kanta tukunna ta ce
‘’feshi na yi a d’akin, shine na fito da ita waje…..’’
Basu ga k’arasowar Ya Nafi’u ba, sai sauk’ar gigitaccen marin da ya d’auke Baraka da shi kawai suga gani.
Da sauri ta d’ago ta kallesa sai kuma ta kasa cewa komai kafin hawaye sharr ya wanke mata fuska, tama kasa maganar.
Dakyar da mugun kyar Ya Nafi’u ya yi k’ok’ari ya danne zuciyar da take tunzura sa akan ya rufe Baraka da duka, yana wani irin huci ya
juya ya kalli Ya Musbah
Ya ce
‘’Yi hak’uri Musbahu’’
Daga haka ya wuce ya fice daga cikin gidan da sauri, dan ya san in ya cigaba da tsayuwa to tabbas sai an samu matsala.
Yana fita Baraka ta juya tana kallon Ya Musbah wanda yake nan tsaye ya kafeta da idanuwa…
A ranta tana mamakin yadda yana gani Nafi’u ya d’aga hannu ya zabga mata mari amman bai tab’uka uwar komai ba, sannan ba shi da alamar yin komai a kan hakan har yanzun, dan haka ta bud’e Baki zatayi magana kenan shi kuma ya riga ta ta hanyar cewa “ki tafi na sake ki! saki biyu’’
Dede nan Manubiya wadda suka gama kai inna cikin d’aki ta fito ta yo kan Barakar da niyyar ko dai ta illatata ko kuma su illata juna.
Da sauri Aisha wadda dama ta lura da abunda Manubiyan take shirin yi ta taho da gudu ta rik’e ta.
Sai yanzu Baraka ta samu ta goge hawayen da suke zubo mata babu k’ak’k’autawa tukunna da kyar ta ce
‘’Cika ta, cikata ta dakeni tunda ita mahaukaciya ce, nace muku
Feshi na yi amman hakan bai ishe ku ba, uwar taku gwal ce?’’
Cikin fushi Aisha ta ce
‘’Mahaukaciya! Jahila! Dak’ik’iya!
Idan baki saniba to yau ki sani Baraka
‘uwa ta fi gwal’.
Da bata haife shi ba to da baki same shi ba, dak’ik’iya kawai.
Ya Musbah ya ce ya sakeki, dan haka za ki iya tafiya.
ki tartara kayanki ki koma gida a sake yi miki tarbiyya wataƙil in kin gyaru ya dawo dake, dan tabbas ko ni ba zan bada goyon bayan
aci gaba da zama da ke da wannan halin da wannan zuciyar taki ba.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ita da Jidda suka ja Manubiya da kyar suka shige d’aki dukkan su Manubiya tana kuka sosai kamar ranta zai fita! dan ji takeyi idan bata daki Baraka ba yau tou sai ta mutu!.
Ita kanta Aisha ta san
tabbas in ta tsaya tsaf za su kwashi y’an kallo ita da Baraka kuma a ganinta in bata kwantar da husuma ba to bai kamata ta iza wutar ba, dan haka ta zaɓi su zauna a ɗaki sannan ta duk’ufa tausar Manubiya.
Duk bakin Baraka yau kasa cewa ko yin komai ta yi
daga k’arshe kawai sai ta juya
Fuuuuuu ta wuce d’akinta….
Ya Musbah ma bai ci gaba da zama a gidan ba!
Baraka
tana wucewa d’aki ya lek’a ya cewa su Manu “kar wanda ya kulata a cikin su,su barta da duniya’’
daga haka ya juya ya fita.
Baraka tana shiga d’aki ta fashe da kuka marar sauti mai
tsananin cin rai!
Bata tab’a
tunani ba bata tab’a kawowa a ranta Ya Musbah zai iya sakinta ba!!
“to me ya faru, ya akayi har ya iya sakinta! Yanzu ya za ta yi kenan???”
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsar ba.
Ta jima tana kuka tana tunani kafin ta share hawayenta a ranta ta shiga aiyyana
“Tabbas sai ta nunawa Musbahu kuskurensa wallahi!
sai ta jaa shi a k’asa.Kallifa kalar cin mutuncin da suka taru sukayi mata,inaa!bazaiyiu ba wallahi da sake dole ta sake shiri zai ga ikon Allah, bama shi kaɗai ba gaba d’ayan su sai ta nuna musu wacece Baraka’’.
Da farko da ta yanke ne akan babu inda zataje, sai kuma ta bawa kanta shawarar ta je ta samu su mamanta itama, a yadda su Ya Musbah suka hayayyak’o sukayi mata wannan aika aikar
tabbas bai kamata ta yanke shawara ita kad’ai ba….
Tana wannan tunanin ta had’a kayanta kaf, ko d’an kunne bata bari ba a ganinta in tayi haka Ya Musbah zai ji tsoro ya zo biko da wuri.
Su Manubiya suna d’aki sun zagaye inna suna yi mata fiffita sukaji fitowarta tana ta jidar kaya.
Babu wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu,haka suna
jinta ta dinga kwasar kayanta
tana fitarwa one by one
har ta gama……
Ya Musbah yana fita direct wajen Baba ya nufa, dan ya gama rayawa a ransa
‘Idan ma za su maida Inna gida tou sai dare, dan so yake yi ya nunawa Baraka iyakar ta! Ta yadda tana ji tana gani sai dai ita ta fita ta barwa Inna gidan Wallahi’.
A hanya ya had’u da Muhsin da mai sunan baba sun dawo daga siyo madara, dan haka suka wuce wajen Baban da su…
Dama bayaso Baraka ta tafi akan idon me sunan Baba gudun kar yayi ta kuka ya ce sai ya bita.
Sun d’an jima a wajen Baba bayan ya ce mishi
‘’Sunje sun tarar Aisha tana bawa innar abinci ne shine aka tsaya ta gama tukunna a kawo ta’’
Sai da suka kuma d’aukar lokaci tukunna ya bar Muhsin anan, shi kuma ya kama Hannun me sunan Baba suka nufi gidan nasa…
bai yi tunanin tarar da Baraka har zuwa wannan lokacin a gidan ba amma yana karya kwana ya tarar da ita da adaidaita sahun ta har uku tanata loda kayayyakinta ita da masu napep d’in a ciki.