← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 84

Sashe 19

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga bakin k’ofa ake kallon su, ga security ya biyo su yanata faman yi wa Baraka magana
Yana cewa “ta sakar mata Hannu”
amman sam Baraka bata da niyyar sauraren sa,
ita kuma Manubiya taso yin tirjiya ko kuma ta fisge Hannun nata amman kuma a ranta sai ta ce ‘bara kawai ta barta’ gudun kar su yi kokawa ta sake tada wani case d’in a tsakiyar asibitin..
Ta fahimci d’akin da Inna take take shirin kaita shiyasa ta gama rayawa a ranta ‘suna shiga d’akin in ta cika ta ita kuma zata fice ta barta’ dan ta lura burin Baraka tabbas bai wuce ta ga gawar Inna ba…

Da k’arfi ta tura k’ofar suka shiga tare ita da Manubiyan.
Da sauri su Jidda su ka mik’e tsaye saboda a yadda Baraka ta shigo kamar wata mahaukaciya sun yi zaton wani gagarumin abu ne ya faru.
Duk yadda Manubiya ta so ta cika mata Hannun sai ta kiya,
ta rik’eta gam!
Sai a sannan Manubiya ta yi dana sanin k’in kwace Hannunta tun a waje su yi ta ta k’are dan tana shigowa d’akin da Inna ta fara tozali ta bud’e idanuwanta sab’anin ɗazu da ta barta tana bacci.

Da kyar Ya Musbah ya samu ya had’iye wani k’ululun takaici wanda ya tokare masa maƙoshi tukunna ya k’arasa wajen su.
Ba tare da ya kalli Baraka ba ya cewa Manubiya
‘’D’auki jakarki ki wuce gida’’
Dan ya fahimci akan maganar da Manubiyan ta ji suna yi ne shi da Baraka, ta yi wa
Barakan magana
shine ita kuma ta janyo ta nan domin ta d’agawa Inna hankali.

Cikin d’aga murya, hargowa da hayagaga Baraka ta ce
‘‘Ka san me ta yi mini ne
da za ka ce ta tafi haka kawai,
wato ta zagi banza ma kenan ko?.

Allah na tuba in banda k’addarar aure da ta kanainaye ni a gidanka
Manubiya ta isa ta taka inda na taka?
Ballantana har ta kalle ni ta fad’a min maganar banza?

A hankali Ya Musbah ya lumshe Idanuwansa waenda su ka yi jazirrr!! Kafin ya bud’e su ya zubawa Baraka ya ce
‘’Baraka saki Hannun Manubiya ta wuce gida.
Zan yi mata magana.’’

Cikin gurb’atacciyar Hausa security d’in da ya biyosu shima ya matso ya ce
‘’Madam, cika mishi Hannu, ki bar fad’a, ba’a hayaniya, kalle patient fa”
Ya yi maganar yana nuna Inna wadda ta kafesu da Idanuwa.

A hankali Ya Musbah wanda ya ke ji kamar ya nutse a cikin ƙasa ya ɗan waiga ya kalli Innar
kafin ya juya da ɗan zafi ya ce
‘’Baraka ki sake ta, ta wuce nace, ko?’’

Cikin tsananin tsiwa rashin kunya sannan da ƙarfi ta ce
‘’Kaga rufe Bakinka, tunda ba za ka yi adalci ba!
Ƙanwarka ta zage ta zuba mini rashin kunya sannan ko bin ba’asi ma baka yi ba kace kawai in cika ta ta tafi?
wato ban isa bama kenan ko?
To Bari ka ji
bayan cin kashin da kake yi mini da azabtar dani ɗin da kake yi wallahi ban shirya sake d’aukar rashin kunyar k’annenka ba, dan haka ba zan cika ta ba kuma sai ta bani hak’uri yanzu ba sai anjima ba sannan ka kora mata zazzafan warning idan kuma ba haka ba to wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da ita’’

Da mamaki Manubiya ta ke kallon Baraka…
ba abunda ya fi bata mamaki irin yadda Barakar ta ke ihu bayan ga Inna a kwance sannan ta bi ta wani dage akan wai an yi mata rashin kunya
bayan ita Manubiyan ta bata wata biyu a duniya!
Yanzu haka ita ta cika shekaru ashirin da biyu
ita kuma Barakar sai watan gobe….

Security ya yunk’uro kenan zai yi magana
Maman Abbakar ta mik’e ta ce masa
‘’Yi hak’uri, je ka.
Za su yi shiru, bara in yi musu magana’’

Ba dan ya so ba ya juya ya fita dan ya k’ule sosai da Baraka.

Yana fita Baba yana shigowa rik’e da Hannun takwaransa, Muhsin na biye a bayan su.
Dama tun kafin ya k’arasa ya ke jiyo hayaniya gashi kuma ya tadda su cirko-cirko
dan haka ya hau tambayar su ko lafiya….

Maman Abbakar ce ta ce
‘’Tou Baba Musa, ka san dai Manu da Baki da kuma rashin kunya!
To inaga yau abun nata ya biyo ta kan yayar tata ne,
dan gashi har janyo ta ta yi ta kawo k’ara shi kuma Musbahu ya ma k’i ya bari a yi maganar, sai cewa yake ta yi Manubiya ta wuce ta tafi kawai zai yi mata magana’’.

A cikin ransa Baba ya shiga karanto sunayen Allah.

Tsit haka d’akin ya d’auka.

Sai da Baba ya ji ya d’an dedeta tukunna
Ya ce
‘’Musbahu ya ce Manubiya ta tafi za su yi magana saboda nan d’in d’akin mai jinya ne wadda take fama da kumburin zuciya, hawan jin, k’oda da kuma mutuwar b’arin jiki.
Ina fatan kun fahimci dalilin da ya sanya ba ya so a yi wata rigimar a gaban Idanunta kar ku yi masa mummunar fahimta,
ba wai son kai yake shirin gwadawa ba ….’’
A hankali
ya juya ya kalli Baraka tukunna ya ce
‘’Me kike so Manubiya ta yi miki yanzu?’’

A hankali ta sunkuyar da kanta ta cika Hannun Manubiya tukunna ta ce
‘’Baba ta bani hak’uri, karta sake kuma’’

‘’InshaaAllah” Baban ya ce
Sannan ya juya ga Manubiya har
Idanuwansa sun yi jajir suna kyalli tsabar ɓacin rai,
zai yi magana da sauri Manubiyan ta ce
‘’Ki yi hak’uri, sharrin Zuciya ne, ba zan sake ba, inshaaAllah’’

Ajiyar zuciya Maman Baraka ta sauk’e sannan ta mik’e,
Baba kawai ta cewa
‘’Allah ya k’ara sauk’i’’ daganan ta taho kamar zata bangaje Manubiya
ganin haka yasa tayi sauri ta matsa
Itakuma ta bud’e k’ofar ta fice.
Baraka ma Hannun Baba k’arami kawai ta kama suka fita bata cewa kowa uffan ba.
Maman Abbakar ce ta d’an tsaya ta yi musu sallama daga nan ta saka kai ta fice
Jidda da Baba suna masu ce mata sun gode.

A hankali Baba ya ga wasu hawaye suna tsilalalowa Inna ta ido d’aya

da sauri ya k’arasa ya sunkuya dai dai fuskarta ya shiga share mata hawayen nata yana girgiza mata kai alamun ta yi shiru….
Sun jima a haka kafin
ba tare da ya juyo ba
ya ce
‘’Manubiya ki kwashi duk Kayanki da suke anan,
Ki wuce gida.’’

Fashewa ta yi da kuka
Cikin kukan ta ce
‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri,
wallahi ban yi tunanin Baraka za ta yi haka ba’’

Still bai d’ago ya kalle ta ba
ya ce
‘’Ni kuma ban yi tunanin har yanzu ba ki yi hankali ba, ban yi tunanin har yanzu ba za ki iya barin abu d’an k’ank’ani ya wuce ba tare da kin yi magana ba’’

Cikin fushi Ya Musbah ya ce
‘’Ko ma menene ki ka ji tsakanina ne ni da ita!
Dan mai yasa za ki shiga ciki har ki yi mata magana?”

A hankali tana kuka ta ce
‘’ku yi hak’uri’’

Ya d’an jima yana kallon ta kafin ya ce
‘’Ki kwashe Kayanki ki wuce gida, ki je ki fara karatu
Jidda za ta ci gaba da zama anan,
Ke kuma kya dinga yin girki daga gida.’’

Za ta yi magana
ya ce
‘’Manubiya ki je a ka ce ko?’’

A hankali ta d’aga kanta alamun ‘to’ tukunna ta k’arasa ta je ta shiga had’a kayanta, har ta gama bata yarda ta d’ago sun had’a ido da Inna ba
dan ta san ita take kallo,
sai da ta zo tafiya tukunna ta je ta rungumeta ta ce’’Inna Allah ya baki lafiya’’
Still bata yarda ta kalle ta ba.
Daganan ta yi wa su Jidda sallama, Baba ya bata kudi’n mota ta sa kai ta fita.

Ya Musbah ji yake kamar ya fashe da kuka, tabbas Baraka ta kai shi bango!!! k’iri-k’iri duba fa yadda ta disga shi ta wulak’anta shi a gaban jama’a harda wani cewa ‘k’addarar aure’!!
babban takaicin sa shine idan ya d’au mataki a wannan gaɓar ya san sai ya had’u da fushin Baba saboda cewa zai yi dan mai yasa zai biye mata a case d’in da ya had’a da su Manubiya, tunda wani abun yana faruwa kowa cewa zai yi ya bi bayan k’anwarsa sam baza’a duba rashin d’a ‘a da furucin da ta yi a gaban iyayensa ba……….
…
Chaaan yamma.
Jidda na zaune ita kad’ai gashi lokacin zuwan Al’ameen ya yi
ta rasa yadda za ta yi ta fita.
Sai da Innar ta yi bacci tukunna ta samu ta fita, tana ta sauri.

A cikin mota ta same shi yana ta jiran ta

Ba tare da b’ata lokaci ba ta ce ‘’ya zo su je d’akin,
Adda Manu bata nan yau, ta bar Inna ita kad’ai’’

Murmushi yayi
Daganan ya fito suka jera suka nufi d’akin gwanin ban sha’awa.

Sun jima kuwa suna hira,
tukunna ya yi mata sallama ya wuce.

Allah da ya taimaki Jidda sam Ya Yusuf bai had’u da Al’ameen ba dan tana dawowa daga raka Al’ameen d’in ta tarar da shi a d’akin,
ko waye ma yayi masa kwatance, sai Allah .

Tunda ta shigo ta gan sa sai ta tamke fuska, daga gaisuwa bata yarda sun yi wata hirar kirki ba.

Ita sai da ya fad’a mata ma tukunna ta gane wai ashe fushi ya yi tun ranar da ta gudu
shiyasa shi kuma ya ƙi zuwa ya duba Innar sai yanzu….

Ganin dai duk yadda ya yi fad’a, fushi da rarrashi sam ya gagara samun fuska a wajen Jiddan ne ya sanya kawai ya tashi ya tafi dan ya riga ya gama tsara yadda zai yi da ita next tunda ya lura bata san a bita ta sauk’i ba.
Katamau!! Haka shima ya wani tamke fuskar nan tukunna ya fice bayan ya ajjiye musu dubu d’aya akan gadon, wai su sayi abun da basu da shi…..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*10*

Ko da Baba ya koma gida da daddare sai da Manubiya ta sake roƙon sa akan ‘ya barta ta je asibitin washegari’ amman furr ya
ƙi amincewa illa ya ce mata’’ta yi karatu ta dinga zuwa makaranta akai-akai” kawai.
Chapter 19 · 0% Book details