← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 84

Sashe 11

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai Yasira ta yi sannan ta ce
‘’Kausar, inda ace zan ji haushin ki akan issue ɗin Yasir, tou da tuni tun farko da kika gaya mini yadda feelings ɗinki sukayi bouncing (tsuntsuwa) daga kan Yasir zuwa kan Ya Yashjub, da tun anan zan ji haushinki!
Amma banji ba, saboda
You are my best friend (ke babbar ƙawata ce) hakan ne ya sanya na goyi bayanki dan kasancewar Yasir twin brother ɗina ba shi zai sanya in zuba ido Inaji Ina gani ki cuce sa sannan ki cuci kanki ba, domin kuwa na san tunda har
kika iya kallon Idanuna kika ce mini ba kya son Yasir tou tabbas bakya son nasa kenan, dan haka idan na bari kuka yi auren a haka akwai babbar matsala.
wannan dalili ya sanya ko da ace baki samu Ya yashjub ba,
ba zan so ki auri Yasir ba ….’’

A hankali
Kausar ɗin tace
‘’InshaaAllah ma zan samu Ya Yash,
da izinin Allah.
I just need your support (goyon bayanki kawai nake buƙata)
Yasira.’’
Ta ƙarashe maganar a hankali tana kallon Yasirar abun tausayi.

Murmushi Yasira ta yi
kafin ta sanya Hannu ta kamo na Kausar ɗin
tana Murmushin ta ce
‘’Zan taimake ki har sai inda ƙarfi na ya ƙare InshaaAllah,
tun muna Yara kin kasance ƙawata kuma ƴar uwata wadda take tsaya mini tsayin daka akan komai!.
Idan na ƙi yi miki wannan taimakon kwaya ɗaya wanda na san shine farin cikin ki Ƙausar ai na zama butulu.’’

Cike da jin daɗi
Kausar ta ce ‘’Thankyou’’
tana Murmushi.

Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda za su yi da Yasir, saboda sun fahimci sai sun yi da wayo, dabara sannan da gaske tukunna za su ci nasara!
Dan sai yanzun ne suka fahimci
ashe su sun raina adadin yawan ƙaunar da yake yi wa Ƙausar ɗin, basu yi
Tunanin ya yi zurfi a sonta har hakan ba….
….
Kamar yadda suka yi zato..
A compound na dank’areren mansion ɗin suka tarar da Mommy tana jiran su, murmushi Yasira ta yi kafin ta juya ta kalli Ƙausar wadda ta haɗe rai tamau, ta ce mata
‘’Your guarding angel,
ai na san ta daina fushin dake dama, gashi har ta zo tarbarki.
Jiya da Daddy ya ce mata zai dawo yau, bakiga yadda hankalinta yayi bala’in tashi ba, saboda gudun kar ya dawo bai tadda ki ba.
Tun jiyan take tambaya ta
‘Flight ɗin naku dai 8:00am ne ko?
In tabbatar na je na dauƙo ki da wuri….
Kar Ya Yash ma ya fahimci bakya ƙasar kuma kar Daddy ya zo ya ga bakya nan’.”

Duk da yadda Ƙausar ta shirya ƙin yin murmushi sai da wata ƴar siririyar dariya ta suɓuce mata!
A chan ƙasan ranta tana mamaki da yaba tsantsar ƙaunar da Mommyn nata takeyi mata!
Amma dukda haka ba zata
bari Mommyn ta ga lagonta ba dan in ta bari ta ga sauƙinta to ta san yau sai ta sha faɗa!.
Dan haka ta sake haɗe rai sannan ta turɓune fuska kamar bata taɓa dariya ba,
tukunna ta murza handle ɗin marfin motar ta fito.

Duk yadda mommy ta so sauƙewa Ƙausar ruwan bala’i, suna haɗa ido sai ta ji fushin nata yana ɗan sauƙa!!
Tabbas ita kanta ba zata iya auna adadin ƙaunar da take yi wa Kausar ba.
Ganin yanayin fuskar Kausar ɗin kuma sai ya sanya ta ta ɗan fara d’ar-d’ar,
amman dukda haka yau kam ba zata bari Kausar ta ga lagonta ba, Ita ce uwa!
Ita ya kamata su bi, ba wai ita ta dunga binsu ba.
Tana cikin wannan tunanin kawai ta ga Kausar ta zo ta wuce ta ba tare da ta ko gaida ita ba.
A fusace Mommyn ta juya ta bita sannan ta shiga kwala mata kira….

Ɗaga mata Hannu kawai Kausar ɗin ta yi tana wani yatsine fuska kamar irin kin isheni ɗinnan, daganan ta wuce ta bi ta kan haɗaɗɗiyar Barandar da ke kewaye da main door ɗin gidan,
ta murza handle na ƙofar ta tura ta shige ciki abunta.

Ba mommy ba hatta Yasira sai da ranta ya ɗan ɓaci!
kamar zata bi Kausar ɗin ta yi mata magana
sai kuma ta tuna yadda su ke ita da mommy ‘ba’a shiga faɗan su, yanzun sai su shirya su barta tana fushinta ita kaɗqi’
Dqn haka sai ta zaɓi ta zuba musu ido kawai.

A mugun fusace, gudu-gudu, sauri-sauri mommy ta bi bayan Kausar.
A bakin stairs ta hange ta tana shirin fara hawa, dan
haka ta tafi da gudu ta finciko ta ta dawo da ita gaban stairs ɗin, tukunna ta soma faɗa! Baki da kumfa!!
‘’Ki yi laifi , kuma ki dawo mini da wannan attitude d’in? Me kike nufi kenan ?
Tou bari ki ji, wallahi zan barki da Daddyn naku wannan karan,
dan naga abun naku daga ke har Yasir ɗin fitina yake k’ok’arin zamewa mutane!!
Idan auren kuke so ku faɗa a yi muku mana kowa ma ya huta!.
Dan Wallahi na gama rufa muku asiri.
Bazai yiu ace kina bin sa kuna yawo k’asa-k’asa mu kuma muna gida a shantake ba!
In Banda iskanci wanne irin birthday celebration ne wanda ba za a iya yi miki a Nigeria ba? Har
Sai ya d’auke ki kun tafi wata uwa duniya?”.

A hankali Yasira ta ɗan matso ta taɓo ta
kafin ta ce
‘’Mommy.’’
Cikin fada mommyn
ta ture Hannun Yasirar kafin ta ci gaba da cewa
‘’Rabu da ni Yasira!
Kausar ta kaini bango Wallahi.
A gaban ki ai na ce mata ban amince su tafi ko Ina ba!
Amma da yake ta raina ni shine ta wanke ƙafa ta bi shi…..
To kuwa kamar yadda ta wanke kafa haka nima zan wanke hannayena daga rufa musu asiri da nake yi tund…’’

A karo na biyu Yasira ta sake katseta ta hanyar cewa
‘’Mommy!!!’’
Da d’an k’arfi.

Juyawa Mommyn ta yi a fusace zata rufe Yasirar da fad’a amma sai
ta ganta duk a ɗimauce tana kallon ta tana waiwayawa tana kallon ƙofar shigowa….
….Giant ne sosai mai faɗin ƙashi,
sanye cikin riga da wando (pyjamas) farare tass masu ratsin silver.

Yanayin kalar fatar jikinsa (light brown ne)…..ruwan tarwaɗa mai haske.
(Kamar na half cast)
mai tsananin kyau, sheƙi da ɗaukar idanu.

Normal lowcut da tsadadden gyaran fuska ya yi waenda suka
taimakawa baƙa ƙirin ɗin sumar kai da fuskarsa damar sake haskaka kyakkyawar fuskar tasa…..
Babu alamun sanƙo ko kaɗan a tare da shi hakan ya taimaka wajen sake fitowa da kuma ƙawata matured handsome face ɗinsa wadda ƙawataccen saje da ɗan siririn gashin Baki haɗe da ɗan guntun gemunsa da ko Hannun Yara ba zai iya kamawa ba
suka taru suka yiwa fuskar tasa k’awanya.

Yanayin yadda sumar tashi ta ɗanyi coiling dukda kankantar ta a ka da fuskarsa ke nuni da lallausar suma gare sa.

Dogayen Idanuwa gareshi, manya kamar na mai jin bacci waenda suka yi dai-dai da tsararriyar girarsa.

Hancinsa dogo ne sosai, har baka! Mai v shape ta chan ƙasa
Sai d’an mitstsin light nude lips ɗinsa mai asalin kyawu da ɗaukar hankali…
..
Ita kanta Kausar sai yanzu ta lura da YASHJUB, tsaye
a bakin k’ofar.
Wani irin sanyi take ji yana ratsa ta tun daga tsakiyar kanta har izuwa babban ɗan yatsar kafarta. Duk da yadda taga ya sake tamke fuska fiye da yadda take a kullum amma sai shauƙin da ta shiga na ganin sa ya lulluɓe fargabar tata.

A hankali ya lumshe dogayen Idanuwansa
kafin ya buɗesu ya zuba akan Kausar!
Wanda hakan da ya yi ya bawa Yasira damar silalewa ta gudu zuwa kitchen, dan ta lura zuwa wannan lokacin hankalinsa ya koma kan Kausar.
Wani ɗan mitsitsin tsaki ya jaa!
Ganin yadda take kallon sa tana wani lumlumshe idanu.
Sai da ya sake haɗe rai tukunna ya tunkaro ta cikin takun sa mai cike da ƙasaita da kamala.

Har ya k’arasa gareta Ƙausar bata cire Idanunta a cikin nasa ba,shima kuma haka, dan yana so ya ga k’arshen tsaurin idon nata.
Sai da ya matso daff da ita
tukunna da kyar ta cire kwayar Idanunta a nashi ta hanyar lumshe idanuwan nata wanda hakan ya bawa wata ƴar siririyar kwalla damar zubo mata daga ido ɗaya….

Idan akwai abunda ya ke yi masa wahalar yi
tou shine ‘magana’
Shiyasa kawai ya tsaya ya yi shiru
Har ta gama sauk’e ajiyoyin zuciyar da take (a jejjere) sannan ta sake buɗe Idanuwanta tana kallon sa.

He can’t stand her (ba ya iya jurar ta!)
ko kallon ta baya son yi.
Wallahi inda ace yarinyar ba Marainiya bace ba to
da sai ta koma gidan su dan shi da kansa zai maida ita. Babu abunda ya tsana a rayuwar sa
kamar ‘ƴa mace marar kamun kai.’
Bai yi cikakken 3 months da dawowa gidan ba amma ya fahimci sam yarinyar bata da hankali, dama tun suna Yara
( kafin ya koma Uk da zama) ya fahimci hakan dabi’ar ta ce
amma sam bai yi tunanin har yanzu bata nutsu ta shiryu ba .

Cikin kakkausa kuma dakakkiyar murya ya ce
‘’ATM’s , phones ,car keys &passport.’’

A rikice ta buɗe Idanunta a kansa tace
‘’Ya Yash pls I ….’’

Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata da har sai da
ta kai ta ga tsugunnawa a ƙasa!
‘’Bani nan!!!’’
Sannan ya d’aura da cewa
‘’Kar ki bari raina ya k’arasa b’aci’’

Taso ta ɗan ɓoye waya ko atm
amma tana ɗago handbag d’inta ya wafce.

Ba tare da ya sake kallon ta ba ya juya
tukunna ya ce ‘’Mommy ki turo min Yasir.’’
Yana gama faɗin haka ya juya
kamar walkiya, fitt! Haka ya fice daga parlourn, ya bar musu mayataccen kamshin turarensa.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*06*

Har ya fice Idanuwanta basu daina kallon inda ya bi ya fitan ba.

Cikin fushi Mommy ta kamo Hannunta ta ta juyo da ita saitinta sannan ta ce
‘’Ai ga irinta nan, yanzu kinga magana kam ta riga ta je kunnen Daddyn ku ta gama!!!
Kin janyowa kanki da kanki.’’
Chapter 11 · 0% Book details