Sashe 82
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiyasa gaba d’aya hankalinsa ya tashi, tashi d’aya ya birkice musu ita kanta mahaifiyar tasa sai da ta tsorata……abu d’aya da yayi dana saninsa shine farkawar da yayi!
Dan sai da ya yi fatan inama ace black snake a k’irji ko ciki ko kai ya harbesa!!
ya san babu kyau amma a ranar ji yayi ina ma ya wuce lahira kawai Ina ma bai tashi ba.
Tun daga ranar kuwa ya daina magana sam, maman nashi ta kasa gane kanshi…
Iyakar shi ya bud’e ido ya ci abinci, tayi mishi alwala yayi sallah ba um ba um um
Kuma Doctor ya tabbatar mata komai nasa lafiya lau.
So yake kawai a sallameshi
ya je ya nemi transfer ya yi
nesa da garin Kano first, daganan sai ya san abun yi dan a yanzu kam ya san
Manubiya ta yi masa nisa shi kuma ba zai iya jurar ganinta da kowa ba.
Amman fa in akwai abu d’aya da ya sani shine ‘zai yi duk yadda zai yi ya san yadda zai mallaketa, bai damu ba ko ya’ya goma ta haifa
yana nan dawowa dan ba’a haifi mutumin da zai barwa Manubiya ba……..’
*MANNUBIYA*
*48*
Kamar kullum, yau ma tunda Yashjub yayi sallar asubah bai
koma bacci ba, yana gama azkar da karatun Alk’urani ya hau aikin Yassir wanda yake so ya kammala a yau in sha Allah…
Yana cikin aikin Najeeb ya kira sa, dama yanata tsammanin sa tun jiya da ya ce masa za su yi waya da hajiya mama in sun gama zai kira sa amman ya ji shiruu…….
Ba k’aramin dad’i Yashjub ya ji ba da Najeeb d’in ya ce masa ‘’ai hajiya mama ta amince ɗari-bisa-ɗari, tana ta murna ma kuma ta ce ‘za ta yi magana da Daddy, shima Yash d’in ya je ya same shi su yi magana, ana gama bincike sai maganar aure in sha Allah.’
Sannan itama da kanta ta nuna bata so ma a d’au lokaci me tsayi’’.
Tashi d’aya wani kalar farin ciki ya lullub’e Yash, ya ma kasa b’oye murnar sa har sai da Najeeb d’in ya tisa shi a gaba da tsokana tukunna ya d’an sassauta yayi masa godiya suka yi sallama.
Sai da ya shirya shirin office tsaf, tukunna ya d’au waya ya kira Ya Musbah dan baya so
yayi masa kiran asubah gudun kar ya saka shi a al’ajabi, amma dukda hakan sai da Ya Musbah yayi mamakin ganin kiran Yash d’in k’arfe 7:48 na safe.
Ba maganar b’oye-b’oye dan bayan sun gaisa kanshi tsaye ya sanar da shi fa Manubiya yake so, yana so ya samu Baba yayi mishi maganar zai turo magabatansa.
Ba k’aramin shock Ya Musbah ya shiga ba, amman kawai sai ya bar Yashjub d’in akan ‘in sun tattauna da Baban, duk yadda suka yi zai sanar masa….’
Yashjub ya ji dad’in yadda Ya Musbah yayi masa, dan tun daga hakan ya silver lining (hasken a al’amarin)
dan haka ya fara shirya samun Daddy kawai
ta yadda in sun ce ya turo ba sai ya tsaya k’umbiya-k’umbiya ba, dukda ya san a tsakankanin jiya ko yau dole Daddy zai ji maganar daga wajen hajiya mama amma dukda hakan shima ya kamata ya d’an cire kunya ya same shi.
A b’angaren Ya Musbah kuwa, ya saka a ranshi kuma ya san Yashjub zai yi magana da Baba amman fa a asalin gaskiya shi ba zai yi magana da Baba ba har sai ya ji ta bakin Manubiya, sannan ya gama bincike tare da tsaida matsayar abunda ya kamata ayi tukunna. Dan a yadda Baba yake kwana biyun nan tsaf zai iya cewa Yashjub ya zo a d’aura masa auren da Manubiya ba tare da an yi wani ƙwaƙƙwaran bincike ba.
Sai da ya yi wa me sunan Baba wanka ya shirya shi shima ya yi wanka ya shirya suka karya tukunna suka fita suka nufi gida da niyyar in sun gama tattaunawa da Manubiya zai d’auki Jidda ta zo ta gyara masa gidan, dan yayi datti a cikin kwana biyu kacal kyankyamin koina yake yi.
Inna da Jidda ya samu kawai a dak’in
Jidda tana ganinsa, sai da ta fara gaida shi ya amsa tukunna tace’’dan Allah ga inna nan, bari in je nan baya in aro wani littafi da na tab’a gani a wajen su mami kwanaki gobe post utme, inaso in duba sosai.’’
‘’To’’ kawai yace da ita, daganan suka zauna shi da me sunan baba a gefen innar suka shiga gaida ita.
Ba su yi mintuna biyu da zama ba Manubiya ta shigo cikin d’akin da laida a Hannunta ta siyo omo da maggi
Kallonta ya yi ya kalli laidar kafin yace ‘’meyasa ba ki aiki Muhsin ba??’’
Sai da ta zauna ta gaida shi ya amsa tukunna ta ce ’’ai ya tafi islamiyyar safe’’
‘’oh haka fa, na manta’’
Ya Musbah ya fad’i hakan kafin ya d’aura da cewa “ke kika bawa Yashjub damar ya kirani?’’
Diriricewa ta yi, ga wata kunya da ta lullub’e ta tashi d’aya, a ranta ta ce “wato har ya kira shi?,
wai zumuɗin me Yashjub yake yi ne har haka?’’
Ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.
‘’Kin yi shiru!!’’
d’in da ya Musbah ya ce mata ne, ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, ahankali ta jinjina masa Kai alamun’’Eh!’’.
‘’Kin san akan maganar me ya kira ni?’’
Ya sake jeho mata tambayar.
Sunkuyar da kanta ta kuma yi kamar wuyanta zai karye kafin ta ce ’’Eh!!’’ a hankali.
Shiruu Ya Musbah ya yi kawai yana kallon ta kafin cikin fad’a sosai ya fara cewa ’’kuma amma shine kika bashi damar kiran nawa?
Kin shirya kenan kema ko?
So kike a aurar da ke da wuri?
Ba ki san Mutum ba, ba ki san daga ina ya fito ba, ba ayi bincike ba shine har za ki ce ya kira ni ayi maganar aure? Yaushe har kika san shi yaushe ma kuka fara soyayyar da har kuka fahimci juna wanda yasa kika samu kwarin guiwar ce masa ya kira ni akan maganar aure???
Daga ya ce miki ilove you sau d’aya zuwa biyu shikenan har kin aminta da shi??
Tou bari ki ji abunda baki sani ba!dama Baba so yake ya aurar da ku da wurwuri, tun a asibiti ya riga ya gama yankewa kuma ya fad’a mana, kinga idan kika yi wa kanki
kika bari Baba ya ji wannan zancen ba tare da an yi wani cikakken bincike akan Yashjub ba tou ina tabbatar miki ko
sati biyu ba za’a rufa ba za ki ganki a cikin gidan Yashjub a matsayin matarsa, Wallahi!
Dan haka Baba ya tsara ya ke kuma fata.’’
Motsin da ya ji ne ya sanya shi d’aga Kai ya kalli bak’in k’ofar toilet ɗin. Ba k’aramin bugawa k’irjinshi yayi ba sakamakon had’a idanu da suka yi shi da Baba wanda ya fito a wanka.
In-i-na Ya Musbah ya fara, yana shirin yin magana Baba ya kalli Manubiya ya ce ‘’ki ba sa number ta, ki ce na ce ya kirani’’.
Yana gama fad’in haka ya wuce yana d’ingishi yana tafiya da kyar, ya fice…
dan kamar gyambo haka yake jin y’an yatsunsa, ba k’aramin zugi suke yi masa ba.
Yana fita Ya Musbah ya ce ‘’innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
‘Ya san halin Baba, ya san waye Baba, ya san in ya saka kanshi abu babu wanda ya Isa ya hana shi.
Babban tashin hankalinsa shine kar aje Yashjub yana da wani mugun hali wanda ba a san da shi ba, su je su aura masa Manubiya…
Har gara Baraka da Ya Yusuf Allah ya rufa asiri
in sukayi abu za a iya hukuntasu aci ubansu,
wannan Yashjub d’in yanda yake da arzik’i Ina su Ina yin rigima da shi?….’
Ahankali Manubiya ta ce
‘’Ya Musbah cewa fa yayi kawai….’’
Wani uban tsaki ya ja, ba tare da ya kalli inda take ba ya mik’e ya fice ranshi a mugun b’ace.
Sai da Jidda ta yi da gaske bayan dawowar ta, tukunna Manubiya ta yarda ta turawa Yashjub number Baba ta ce ‘’ya kirashi, number Baba ne,’’
Already dama yanada number dan haka yace mata “ai yanada ita, dama izini kawai yake jira, dan haka ya gode’’
Haka nan ya yi ta murna kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljannah, kafin daga baya suka yi sallama gaba d’aya jikinta babu kuzari.
Saboda itama sai yanzu ta fara da na sanin basa damar ya kira ya musbahn tun farko da ta yi da wuri haka..shikenan
zai raina ta tun yanzu, dan zai ga kamar tana neman Kai ne da kanta,
ga kuma abunda Ya Musbah ya gaya mata wanda gaba d’aya ya d’aga mata hankali…..
A take a lokacin…ba b’ata lokaci, ya kira Baba.
Sai da Baba ya sake yi masa godiya tukunna suka fara tattaunawa…
Baba da so yayi su yi magana a waya kawai amman sai Yashjub d’in ya ƙi amincewa..a ranar suka zo da shi da Najeeb suka had’u a masallaci ya amsa tambayoyin Baban.
Daganan Baba ya nemi da ya tura masa da adress d’in sa, ya ce masa “inshaaAllah bayan kwana biyu, za su neme sa.”
Ba abunda ya fi b’atawa ya Musbah rai irin yadda Baba ya sake d’aura masa alhakin yin bincike akan Yash, kuma ya hura masa wuta ko d’aga Ƙafa babu
ko duba halin da suke a ciki ma bai yi ba.
A b’angren Baba kuwa babu abunda zai iya shiga tsakanin sa da maganar Yashjub da Manubiya dan har ga Allah ya yi farin ciki matuƙa da ya ji Yash d’in yana son Manu
ba wai kwad’ayi ko wani abun ba kawai dai ya san idan Manubiya ta auri Yashjub to hatta Jidda za ta samu kariya daga sharrin black snake….