← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 84

Sashe 18

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin fushi ya fincike Hannunsa a nata kafin ya ce
‘’I’m not interested in anything u have to say Mommy(ba na son jin komai daga gareki Mommy), na baki 3 hours ki nemo shi
Idan kuma ba haka ba to
nima zan bar gidan nan kamar yadda Daddy ya bari har sai kin gyara abun da kika b’ata
an d’aura mana aure da Kausar tukunna za ki ganni.’’
Yana gama fad’in haka ya juya zai fita,
da sauri ta sha gaban sa da niyyar rarrashi. Amma
tun kafin ta yi magana ma ya d’aga mata yatsunsa guda uku!
Cikin tsananin ɓacin rai wanda ya had’e masa da tashin hankali
ya ce
‘’3 hours Mommy,awanni uku kacal.’’

Bai iya jira awanni ukun sun cika ba ma tsabar maɗaukakin ɓacin rai, yana fita ko bi ta kan frnds d’in nasu bai yi ba, dan bai san ta yaya zai yi facing d’in su ba.
Hatta ɗayar wayarsa bai biya ya d’auka ba!
Allah ya so shi akwai car key a jikin sa dama dan haka ya nufi mota ya shiga ya kunna ya ja ya fice daga cikin mansion d’in.
..
Tun daga nan babu Daddy babu labarin sa
Ba kuma Yassir shima.

Ko da Abokin Daddyn ya zo ganin Yahanasu, Yashjub ne ya tsaya ya tarbi bak’on, haka ita kuma Yasira da Mommyn suka san dabarar da suka yi suka sallami frnds d’insu ƴan biki waenda Yassir ya tara……..
•••••••
Yau satin Inna biyu a asibiti, tunda ta kwanta a asibitin sau biyu kawai Mannubiya ta samu ta je makaranta.
Ita kanta ba wai lafiyar gareta ba dan zazzab’i da ciwon kai sun sakota a gaba.

Yau suna zaune da rana gaba d’ayansu sai ga Baraka! Ita da Mamanta da Abbakar da Mamansa shima.
Tun lokacin da Innar ta kwanta jinya yau ne zuwan Baraka na farko kuma shima haka nan ta taho ko ruwa bata ruk’o ba ballantana azo kan maganar yi wa marar lafiya girki…
Ƴan gidansu Manubiyan suma Siyama ce kawai Anty Umma ta turo, bayan ita babu wanda ya zo.

Abbakar, Ya Nafi’u da Al’ameen wanda yake zuwa a b’oye ne kullum sai sun zo,
Matar Ya Nafi’u itama zuwanta har hud’u…..

A nan kan k’atuwar taburmar da suka shimfid’e a tsakiyar d’akin suma ƴan dubiyar duk suka nemi waje suka zazzauna.

Cikin mutunta juna suka gaisa da Baba tare da tambayar sa “ya mai jiki” ya amsa musu da ‘’da sauk’i’’daga nan ya mik’e ya fita ya bar musu d’akin…
Haka shima Ya Musbah ya mik’e ya fita bayan sun gama gaisawa da surukan nasa.
Ɗakin ya rage saura Matan kawai da Innar sai Abbakar dan Muhsin ma Hannun Baba k’arami ya kama suka fita tare da Ya Musbah.

Gaisawa suka sake yi daga nan suka shiga tambayar su ya mai jiki da yanayin jikin nata.

Baraka bata wani dad’e a zaune ba ta mik’e ta bi bayan Ya Musbah, bayan ta gama ƙarewa ɗakin kallo.
Tana fita Abbakar ya kalli Manubiya ya ce
‘’Jiya fa sir Najeeb ya yi test’’

A firgice ta ce
‘’Wasa kake yi,Amma ko?’’

Cikin dariya ya ce
‘’A’a wallahi, da gaske nake,ya yi test jiya’’

Kamar za ta fashe da kuka ta ce
‘’Haba Abbakar, shine kuma baka gaya mini ba, na zo tun a lokacin na yi’’

Da sauri cikin katse ta ya ce
‘’in da ace kin je ɗin mai za ki iya rubutawa? Ai na san sai dai ki yi ta kukan da baya so, a ajin’’

Still yanzun ma kamar mai shirin yin kuka ta ce
‘’Still dai, ai da ko attendance ne na yi.
Yanzu shikenan bani da test d’in?’’

Cikin son sake firgitata Abbakar ya ce
‘’Kuma ya ce shine na continuous assessment’’

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Manubiya ta ce duk ta rikice.

Ganin yadda duk ta gigice ne ya sanya ya yi dariya sannan ya ce
‘’Matsoraciya kawai, na yi miki tou’

Da sauri tana mai sauk’e ajiyar Zuciya ta ce
‘’Da gaske ?
Test din ?’’

‘’Eh mana’’
ya bata amsa yana murmushi.

A hankali ta ce
‘’Allah sarki, Abbakar
Na gode sosai’’

A tare duk su ka yi dariya har Jiddah.

Mik’ewa ya yi, ya ce
‘’bara in wuce kasuwa, Allah ya k’ara sauk’i.
Mu je in baki handouts d’in da ya fitar a jiya, ya ce gobe zai kuma yin open test shima part of CA ɗinmu ne’’.

‘’Okay’’ ta ce, tana mai mik’ewa
sannan ta k’ara da cewa
‘’Mutumin nan d’an wahala ne Wallahi
Da shi da test 5&6’’.

Dariya ya yi daga nan suka saka kai suka fita a tare.

A bakin ward d’in ta hango Ya Musbah shi da Baraka a tsaye!
Kallo ɗaya za a yi wa Fuskokinsu kai tsaye a fahimci fad’a su ke yi.
Baraka ce take facing d’in ta dan haka tana ganin tahowar ta ta yi shiru, har suka zo suka wuce.

A cikin garden ta chan gefe ta hango su Muhsin da Baba a zaune……

Allah sarki Abbakar…
Duk wasu handouts d’in da aka fitar na course d’in da suke yi sai da ya siya mata, daman exams ta taho!
Duk haka ya had’a ya bata
sannan ya sake tabbatar mata
Da
‘ta zo gobe.’

Ta san saboda mamansa ne ya sanya ya ce ‘iya na sir Najeeb ya siyo mata’ dan ta lura da yadda suka yi a lokacin da ya ce ‘yayi mata test d’in’ ma.

Shiyasa itama da ta karb’i jakar ta yi godiya ta goya a bayanta,
ta ci alwashin b’oyewa……

Har ta karya kwana ta nufi inda su Ya Musbah suke sam ba su lura da ita ba!
Ranshi a tsananin b’ace yake ita kuma Baraka ta bata baya
shiiyasa duk basu lura da ita ba.
Tun kafin ta k’arasa kusa da su
ta ji Ya Musbah yana cewa
‘’Yanzu Baraka ya kike so in yi?
Ko sata kike so in je in yo?
Na fad’a miki wallahi babu kud’i a Hannuna’’

Cikin tsiwa ta ce
“Eh kam babu kud’i a Hannunka ga alama nan ai na gani!
Rashin kud’in naka ne ya sanya Innar ka take kwance a aminity
d’aki cike da kaji da lemuka!!
Ko y’an uwanku ne suka kawo? ‘’.

A zuciye ya ce
‘’Ba na son cin fuska kuma.!
Na ce miki ba ni da kud’i
hidima kuma da kika gani ba ni nake yi ba!
Ki yarda ko kar ki yarda wannan ba matsala ta bace ba.
Akwai kud’i a hannun ki na sani ba wai babu ba dan haka idan za ki yi hidimar gida dasu Bismillah…
Duk ranar da na samu zan maida miki,
Idan kuma za ki iya barin ɗan da kika haifa a cikin ki da yunwa saboda rashin sanin ciwon kai to shima Bismillah…
Sannan idan kinga ba zaki iya ci gaba da zaman ba
nan ma kin san mai za ki ce min inyi
ni kuma in sha Allahu zan yi miki yadda kike so’’

Cikin tsananin b’acin rai
ta ce
‘’Eh lalle Musbahu ka yi arziƙi, ga alama nan na gani…ai dama ku Maza haka kuke, wato kud’i sun fara zama maka shine ni Baraka yau nice abar wulakantawa ko?
Ka barmu da yunwa ni da d’anka
ka dauko Babarka ka kawo aminity kuma na yi magana ka ce za ka sakeni
Saboda yanzu ka san kana da kud’in da za ka yi wani auren idan na tafi ko …’’

Cikin katse ta ya ce
‘’Ba wai cewa na yi zan sake ki ba, cewa na yi idan kinga ba zaki iya zama ba to ki fad’i abun da yake ranki ni kuma in aiwatar.
Magana ta ta ƙarshe anan ‘ki yarda ko kar ki yarda
Ba nine nake hidimar asibitin nan ba, saboda bani da shi.
Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to,
ki je ki siyo kayan abinci ku ci da ke da mai sunan Baba
kar ki damu da cikina
In sha Allah zan samu abun da zan ci, kuma duk lokacin da Allah ya bani kud’i zan mayar miki’…’’
Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce ciki! Yana adduar Allah yasa Manubiya ba ta ji conversation d’in nasu ba dan shi sai yanzun ne ya lura da ita.

Takaici kamar ya kar Manubiya, sam bata yi niyyar kula Baraka ba, dan haka ta zo za ta wuceta da sauri ta na jin wani takaicin ta na musamman yana rufe ta!.
Ita kuma Baraka dai-dai ta juya dan haka suka yi kiciɓus!!!…

Wani tsaki Baraka ta jaaa!
Kafin ta ce
‘’Ni kam wannan aure,
a cuce ka kuma ka yi magana aji haushi!
Sannan ga ido ta ko ina…’’

Har Manubiya ta ɗan yi gaba
sai kuma ta juyo ta dawo ta sha gaban Baraka, ta tsaya.

Gyara tsayuwa kawai Baraka ta yi itama ta shiga watsa mata kallon wulaƙanci.

Cikin takaici Manubiya ta ce
‘’Wallahi kin bada Mata, ai ko kishi da rashin hankalin ma yanzu an daina yayin irin wannan.
Duk abubuwan da kike yi zuba miki ido kawai muka yi ba wai dan bamu san me kike yi ba ne
sai dan
a kullum adduar mu itace ki shiryu.
Haba Baraka
Mahaifiya fa?
Itace abar kishi?
Inda ace ma lafiyar ta ƙalau tou da da sauk’i
amman bata fa da lafiya, a kwance take, a gani na idan baki taimako ba to bai kamata ki d’agawa kowa hankali ba.
Kaico!!Wallahi Ya Musbah bai yi sa’ar Mace ba.’’

Yadda Baraka ta zazzaro Idanuwa waje duk wanda yagansu a wajen zai yi zaton daddanawa Iyayenta zagi Manubiya ta yi…

Ta san dama Manubiya bata da hak’uri amman bata tab’a tunanin zata iya gaggaya mata magana har haka ba.
Tijara da Zuciya da suka ciyota ne suka sanyata ta figo Hannun Manubiya da dukkannin k’arfin da Allah ya bata suka yi ciki tare.
Chapter 18 · 0% Book details