Sashe 35
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Innnalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ya ambata a ransa a zahiri kuma ya sake tamke fuska yana mai jin kansa yana tsananin sarawa, sanann yana da ya sanin zuwa gidan.
Da kyar ya samu ya iya bangaje ta
ya wuce ciki dan har ta nufo shi tana shirin yin magana.
..
Ransa a mugun b’ace haka ya nufi cikin parlourn, ya nemi guri ya zauna yana mamakin yadda take yawo a cikin gidan daga ita sai wannan guntuwa sannan shara sharar bathrobe d’in wadda ko pant d’inta bata gama rufewa ba sannan in dai idanuwansa ba gizo suka yi masa ba to tabbas ko bra babu a jikinta.
Sam ba ta damu da yadda ya yi mata da farko ba dan ta riga ta gama rikicewa da ganin sa.
Haka nan ta wuce kitchen ta had’o masa juice da cake.
ta fito tana rangwad’a ta zo gaban sa ta ajjiye sanann ta koma gefen sa ta zauna daff da shi.
Ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Ina Yasir??’’
Cikin sake matsowa kusa da shi ta ce
‘’Ooh,he’s a little busy at the moment (akwai aikin da ya ke yi yanzu) sai dai ka d’an jira shi kad’an, but don’t worry I’ll keep
you company(amma kar ka damu zan tayaka cinye lokacin)’’.
Ta fad’i haka tana mai d’aura hannunta akan cinyarsa ta fara shafawa tana masa tafiyar tsutsa tana yin sama da kad’an da kad’an.
Tsabar yadda ransa ya b’aci bai ma san ta ya aka yi ya mik’e tsaye ya zare belt d’in jikinsa ba dan tsintar kan sa kawai
yayi yana kimarta da belt tana ihun ceton rai…
Kafin su Yasir su fito har ya farfasa mata jiki, sai da suka yi da gaske
tukunna Yasir Abokinsa da d’ayar Yarinyar da suka fito tare daga ɗaki ɗaya su uku! suka iya kwatar budurwar nan a hannun Yashjub wadda zuwa lokacin har ta suma.
Cikin tsananin tashin hankali Yashjub ya ke yi wa Yassir wani irin kallo….daga shi sai boxers haka shima Abokin nasa sai d’ayar Yarinyar ita kuma da towel.
Wata mahaukaciyar shak’a ya kaiwa wuyan Yassir cikin hargagi da hargowa ya ce
‘’Dan ubanka gay ka zama?’’
Su kam wannan budurwa da saurayi sun ga tashin hankali, dan a still sai da suka kuma yin da gaske tukunna suka iya kwatar wuyan Yassir daga hannun Yashjub.
Dakyar Yasir ya iya cewa ‘’A’a, Wallahi ba abunda kake tunani bane ba, ka tsaya zan yi maka bayani.’’
Da kyar Yashjub ya iya danne zuciyar da take tunzura sa…
da yatsarsa manuniya ya nunawa Yasir k’ofa, kawai……
Duk hauka,iskanci da rashin kunyar Yassir yana tsananin jin tsoron Yashjub a irin wannan yanayin dan yadda ya tunzura d’in nan abun ba sauk’i ko last month da yayi irin haka a gida hatta Daddy sai da yayi shakkar sa da kyar da mugun kyar aka ci sa a Yahanasu ta samu ta iya lallab’a sa, amma duk da haka ya fi wata d’aya a kumbure.
Da kyar yana jin maganar tana harhad’e masa yana ganin dishi-dishi ya sake cewa Yasir ɗin
‘’Za ka wuce ko sai na baka mamaki?’’
A hankali Yassir yana d’an d’ari-d’ari ya ce
‘’Na san motarka babu tint, ka yi hak’uri in shiga in d’auki kayana, dan Allah’’
‘’In tsaya in jira ka kenan??’’
Yayi masa tanbayar yana sake tunkaro shi da idanuwansa waenda suka yi jajawur abun tsoro.
Da gudu wannan budurwar wadda gaba d’aya ta gama tsorata
ta wuce d’akin ta janyo akwatin Yasir ta fito da shi.
Tana fitowa Yashjub kuma ya juya ya fita dan ya fahimci in dai ya sake damƙar Yassir tou tabbas zai iya kai shi lahira, cikin fushi ya nufi gate d’in gidan ya na jin kamar ya fincike zuciyarsa ya jefar tsabar tafarfasa da azabar da take yi..
Da Sauri Yassir ya bud’e akwatin nasa ya zaro jallabiya ya bi bayan Yashjub da mugun gudu yana zuwa ya bud’e motar dan Yashjub har ya kunna yana shirin bata wuta,
dan ma ya tsaya wangale gate ne shiyasa yaci sa’ar samun shi amma da tuni ya tafi.
Ko rufe motar Yassir bai yi ba
Yashjub ya figee ta suka fice da guduu da kyar ya iya rufe motar ya zura jallabiyar shi dan mutane har sun d’an fara kallon su duk inda suka bi………
Hakanan suka k’arasa gidan da ikon Allah saboda tsananin gudun da Yashjub ya tsula Allah ne kawai ya kaisu gidan lafiya.
Tun kafin su k’arasa main door su ke jiyo hayaniya, dai-dai suna shiga suka ga Daddy ya dakawa Ummi wata mahaukaciyar tsawa sannan ya nufe ta gadon gadan kamar zai rufeta da duka……
..
Cikin fushi bayan ya isa gareta ya ce
‘’Wacce irin Mace ce ke?
Eh?
Ashe son kan naki har ya kai haka?’’
‘’Yarinya ta yi laifi k’iri-k’iri amma kina k’ok’arin b’oyewa?’’
Sai da ya kalle su tukunna ya juya ga Ummi ya ce
‘’To laifi mana, in ba haka ba lokacin da ta je ta ji ya fara yi mata maganar banza ai kamata yayi ta bar gurin ko?
A matsayin shi na wanda yayarta za ta aura’’
Yadda yake mata ihu da hargagi da kuma tuhumar Munirat akan abunda bata tab’a tunanin zai yadda ta aikata bane
ya sanya wasu zafafan hawaye zubo mata cikin d’acin zuciya ta ce ’’Daddy tuhumar ta kai ma kakeyi?
wanne kalar asiri ne zai juyar da lissafin Mutum mai
kimanin shekarunka a cikin lokaci k’ank’ani haka?’’
Cikin b’acin rai da d’acin zuciya ta share hawayenta kafin ta d’aura da cewa
‘’Maybe sai dai ko irin wanda akayi maka aka juyar da kanka daga gare ni ne kwana biyu’’.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*22*
‘’Babu irin wannan a tsarin mu,
ke kan ki kin san inda ace muna irin haka Wallahi da baki Isa shigowa ki taho har da agola cikin gidan nan ba.
Sannan duk abun da za ki yi, ya tsaya a iyaka kanmu amma kar ki kuskura ki sako Mommy’’
Cewar Ya’isha.
Cikin jaddada mata Kausar ta ce
‘’Tabbas, dan in dai kika tab’o Mommy to kuwa muma ba za mu ji shakkar rama mata ta ko wacce hanya ba…
yanzu dai a komawa maganar da ake yi tun farko dan naga alamar so kike yi a rufe lamarin Munira.”
Da mamaki Ummi take kallon Daddy wanda sam ya kasa tsawatarwa ya’yan nasa.
Su kansu su Yashjub sun d’an ji
mamakin sa.
Yusra ce ta k’arasa ta juyo da Munirat wadda take ta faman kuka ta ce
‘’Munirat tun muna shaidar juna mu da ke….’’
Cikin fushi Munirat d’in ta fincike hannunta sanann ta katse ta ta hanyar cewa
‘’Kar mu shedi juna daga yau dan Allah ki yi duk abunda kika ga dama, ki illatani ta yadda ba ke kad’ai ba kowa ma ba zai iya sheda ni ba’’
“Munirat wai ya ana k’ok’arin gyara abu kina turjewa ne?
kin fi kowa Baki da Zuciya ne? we are all the same (duk ɗinmu ɗaya ne) anan, so kar ki yi tunanin wai ko ana k’ok’arin nuna miki bambanci ne, ko waye a cikin sisters d’ina yayi irin abun da kikayi dole irin haka za a yi mata!!!!
We all love Yahanasu (duk ɗinmu muna son Yahanasu) dan haka ya kamata mu tsaya mu fahimci juna a samu a gyara abun da kike son ki b’ata’’
Yasira ta ce tana mai k’arasowa inda
Munirat d’in su ke tsaye ita da Yusra.
Ta bud’e Baki za ta yi magana kenan cikin d’an d’aga murya suka ji Yahanasu tace’’Ya isa haka’’ sanann ta k’arasa inda Yasirar ta ke ta saka Hannu ta juyo da ita tukunna ta fara magana “Da ni da ke da kowa duk an san daga ke har Kausar d’in ba ku wani damu da ni ba!
Infact har su Ya’ishan suma duk ba damuwa suka yi da ni ba!
Dan haka
na rok’e ku da girman Allah kar ku yi amfani da ni wajen baiyyana abun da yake a ranku game da su Ummi…
Alh Bashir da farko ya ce yana so na yanzu kuma ya ce ya fasa Munirat yake so!!!
Ni har ga Allah ban ga wani abun tashin hankali anan ba…
iyaka kawai mu yi musu addu’ar Allah ya basu zaman lafiya shikenan magana ta k’are!!!
Dan Allah kar wanda na sake ji yayi amfani da bak’in jini na da bad luck d’ina wajen nuna real face d’in shi!!…
ku bar ni in ji da abun da yake damu na’’
Ta fad’i hakan wani irin kuka yana sub’uce mata da mugun k’arfi.
A hankali Yashjub wanda ya k’araso yanzun ya sa Hannu ya juyar da ita ya rungume ta yana jin wani tsananin b’acin rai da takaicin senator Bashir suna taso masa.
Cikin kuka ta ce
‘’Yash dan Allah ka ce su daina maganar nan, su bar shi ya auri Munirat d’in su dena maganar bana so, suna rubbing salt a wounds d’ina (suna fama min gyambon da ke a zuciyata) ne, sanann dan
Allah kar wanda ya sake ce min in yi aure, dan Allah dan Annabi’’
Wani kalar kuka abun tausayi take yi wanda yasa gaba d’aya jikin Daddy wanda ya harzuk’a ya fusata ya yi sanyi haka ma Mommy da Ummi duk sai jikin su ya yi sanyi.
Munirat kuwa ji take kamar ta je ta chakawa senator wuk’a!
Yahanasu is the most nice calm and friendly person da zata ce ta tab’a had’uwa da a rayuwarta, gashi jinin su ya had’u matuka …..
A hankali Yashjub ya ja ta tana a rungume a jikinsa suka wuce d’akinta.
Suna wucewa Ummi ta ja hannun Munirat suka wuce sama suma.
Gaba d’aya kuma kallo sai ya koma kan Yassir wanda tun ɗazu da suka shigo ya gagara janye manyan idanuwansa daga kan Munirat.