Sashe 36
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin duk sun tsura mishi ido ne ya sanya ya d’an sunkuyar da Kai ya fara sosa k’eya kafin da kyar yace’’Daddy I’m sorry for..”
Kafin ma ya rufe Bakinsa tuni
Daddy ya zo ya wuce shi ya fice daga gidan gaba d’aya dan a wuya yake dama Ummi, bata san a cike yake da itaba kwana biyun nan dama, haka kurum yake jin takaicin ta!
yanzu kuma ji abun da ta yi,
ta wani bud’e Baki tana cewa ai itama Munirat marainiya ce
sannan har tana da Bakin cewa wani an juya mishi tunani akanta,duk irin yadda yake k’ok’arin bata kulawa amma sam ita bata gani how dare she!!!!
tunda yake da Mommy bata tab’a yi masa irin haka a gaban Yara ba amma ita ta iya bud’e Baki yana fad’a tana fad’a….
y’ar shi tana cikin wannan halin kalli yadda Mommy take tausaya mata amma ita tata y’ar kawai ta sani.
Yahanasu batayi deserving haka ba y’arshi mai hankali nutsuwa da sanin ya kamata, cikin fushi a fili ya ce
‘’Allah ya tsinewa Alhaji Bashir’’
……
Daddy yana fita Mommy ta k’arasa inda Yassir yake tsaye ta hau duddubashi kamar wani k’aramin Yaro, idanuwanta suna kaiwa kan wuyansa wanda har zuwa wannan lokacin yake nan jajir ta rikice ta hau tambayar sa abun da ya same shi.
‘’A hankali ya ce ‘’Mommy I’m fine, favorite son d’inki da kika tura ne ya je ya jiwa Abokai na ciwo ya sumar da d’aya sannan nima ya shak’eni da kyar aka kwace ni daga hannunsa, da tuni yau sai dai ki ga gawa ta.”
Kamar zai kurma ihu ya d’aura da cewa “da kika san yana da anger issue da sai ku taho tare ke da shi ta yadda ko haukar tasa ta motsa za ki iya shiga tsakanin mu, na san in kina nan
maybe ya d’an nutsu’’.
Cikin rashin jin dad’i Mommy ta ce
“Subahanallah, wallahi Yassir ban san zai yi haka ba…
I was so worried ne (na damu ne sosai) shiyasa na barshi ya je.
ga shi naga Daddynku yana neman mantawa da kai ma gaba d’aya tun da yayi aure
komai ya lalace bai damu da ni ba ma kai kam ko zancen ka baya yi,wannan Matar da ka gani auntyn ku ce ….’’
Cikin katse ta ya ce
‘’Yeah na fahimta daga shigowata da kuma scene d’in da na yi witnessing (abunda na gani)”
A hankali ya kama lips d’inshi na k’asa ya d’an ciza kafin ya d’ago idanuwansa ya sauk’e a kan k’annen nasa waenda sukayi cirko-cirko.
A hankali Baabaa Larai ta k’araso ta ce
‘’Ka ji maganar mahaifiyarka ka ji d’an albarka, duk abun da
Babba ya hango Yaro ko ya hau kan dala ba zai gani ba!
kar ka sake yunk’urin barin gidan nan.
Yanzu lokaci ne da ya kamata ace kun had’a kai da mahaifinku kun shiga jikin shi sosai, dan duk wanda ya yi gangancin yin nesa da shi to kuwa kanshi yayiwa.’’
Tana gama fad’in haka ta kama hanya ta wuce d’akin Yahanasu.
A hankali su Yadira Yusra da Yasmeen suka matso kusa da su suka ce
‘’Welcome home Ya Yassir(Sannu da zuwa Ya Yassir)’’
Sannan Yasmeen ta ce ‘’we missed u(mun yi kewarka)’’ tana d’an murmushi.
Kallon su kawai ya yi, daga nan ya maida duban sa ga Kausar wadda ta d’an tsura masa ido tana
mamakin ramar da ta ga yayi.
Yana kallo ta ya ce
‘’Mommy bara in je in watsa ruwa as usual nobody cares about me (kamar ko yaushe babu wanda ya damu da ni) na tafi kuma na dawo da kaina ba tare da an yi min abunda na buk’ata ba,a tunani na Inada loved one’s waenda za su damu da damuwata…
I guess i was wrong(inaga tunanin nawa ya bani ba dai-dai ba kenan).’’
A hankali ya d’auke dubansa daga gareta ya maida kansa k’asa ya fesar da wani numfashi
Sannan ya ce
‘’Bara in je in d’an watsa ruwa.’’
Tun kafin ya juya Yashjub wanda ya fito yanzu daga d’akin Yahanasu ya ce
‘’Yasir, wait!.’’
Lumshe idanuwansa ya yi ya d’an bud’e tukunna ya ce
‘’Wanka zan je in yi”
ya fad’i hakan yana mai kallon cikin idanunsa.
Ba tare da Yashjub d’in ya sake kallon sa ba ya juya ga Mommy ya ce
‘’A gyara masa d’aki a sama kusa da side d’inki.’’
Gaba d’ayan su a tare suka ce
‘’Whattt!!!!’’
Cikin b’acin rai Yassir ya ce
‘’Look here,Man!( ka ga Mallan kalli nan)
tura ta kai bango fa, haba mana wanne cin fuskar ya rage ba ka yi min ba???
Ka je ka ce in biyo ka na biyo ka bayan b’arnar da ka yi min sannan yanzu kuma za ka saka ni a tsakiyar Mata? To gaskiya baka isa b…..’’
Kallon da Yashjub yake yi masa ne ya sanya ya d’auke Kai ya kalli mommy
Ya ce
‘‘Mommy, ki yi min tsakani da shi fa, idan kuma ba hakaba to wallahi za mu kwashi y’an kallo.’’
A hankali Yashjub ya matsa daff da shi ya kamo kafad’unsa ya juyo da shi sannan ya ce
‘’Yassir, kar ka ga wai muna a gida kuma a gaban su Mommy ka ce za ka yi min shirme…
Raina already a b’ace yake kar ka sake provoking d’ina(fusata ni).
Ka wuce masu aiki za su gyara maka d’aki a chan sama kusa da side d’in Mommy ta yanda za ta fi saka maka ido saboda ni fita nake yi kuma yanzu zan dinga kai dare sosai, sannan ina so in yi tafiya dan haka ba zan iya kula da kai ba! Tunda ka nuna har yanzu ba ka yi hankali ba, dan haka dole za ka zauna a inda za’a saka maka ido a kuma kula da kai.
Anjima kuma za mu zauna
da ni da kai da Mommy da Daddy a yi magana akan abun da na gani a gidan da kake cewa na yi maka b’arna.
for the last time Yassir, ka wuce sama’’.
Iya k’uluwa Yassir ya k’ule, ya san tsaf Yashjub zai iya sake fad’in wata maganar da zata sanya Kausar ta d’an fahimci wani abun tunda gashi har ya fara dan haka kawai ya yanke shawarar wucewa sama
amma tabbas zuwa wannan lokacin yayi girman da zai gyarawa Yashjub zama, da sake!!!
Dan gaskiya ba zai yiu a dinga juyashi da girman sa ba.
A hankali Mommy wadda ta fara firgita da yanayin Yashjub ta kamo Hannun Yassir ta ce
‘’Son!mu je,mu je saman. anjima ba ya ce za mu zauna ba! sai mu zauna d’in, amma for now mu je ka ji ko’’.
Ta fad’i haka tana k’ok’arin janye Yassir d’in daga ruk’on da Yashjub ya yi wa kafad’unsa..
Ai kuwa da kyar sai da ta d’an tab’a Yashjub d’in ta ce mishi
‘’Cika shi za mu wuce’’
Tukunna Yashjub ya samu ya janye idanuwansa waenda su
ka yi jazir daga kan Yassir ya cika sa da kyar, daga haka kuma ya juya ya fice kamar zai tashi sama.
A hankali Kausar ta ja numfashi ta bi bayansa da kallo har ya wuce tukunna ta lumshe idanuwanta tana ji a ranta’tabbas bata da hutu bata da sukuni bata da nutsuwa muddin bata samu Yashjub ba!!!
yanzu ne wasan zai fara dan ko ta halin k’ak’a ne
wallahi sai ta mallake shi, bata ga dalilin da zai sanya ta rasa shi ba.’.
Su Mommy suna wucewa sama ita ma ta bi bayan su haka ma su Yadira.
Yasira kuma ta wuce d’akin Yahanasu…
bata damu da cewar ‘shirin aurenta ya tarwatse a karo na takwas ba’
dole ta kora mata warning, Wallahi.
..
Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya ke yi tsabar takaici!
Abun zai yi wani irin banbarakwai idan ya je ya samu senator Bashir da fad’a ko da rarrashi dan zai ga kamar yana neman kai da y’ar uwarsa ne…..
Ya jima rabon da ya shiga b’acin rai irin wannan a rayuwarsa, baya so ya dinga jin maɗaukakin ɓacin rai irin haka amma yau senator Bashir da Yassir sun kai sa bango!!
Da wannan tunanin ya k’arasa part d’in nasa yana zuwa ya fad’a bathroom ya sakarwa kan shi ruwa mai sanyi…
Sai da ya ji ya fara atishawa tukunna ya d’auro alwalla ya fito ya chanja kaya zuwa jallabiya…
ya na shiriin yanata faman tsaki
dan yana fitowa ya ji ana idar da sallah a masallaci.
A nan d’akin nasa ya yi sallarsa ya idar ya zauna zaman addu’a.
Yana zaune sai ga Kausar ta yi knocking, ta shigo da zumbulelen hijabinta.
ta zo ta zauna kusa da shi wai Mommy ta ce tunda course d’aya suka karanta ta zo ya k’ara duba mata project d’in ta gobe time zai cika
kar a sake dawo da ita wannan shekarar ma,sannan ya manta bai bata wayoyin nata ba.
A yadda ya ke jin kansa tabbas inya ce zai kula Kausar tou zai iya ji mata rauni, wacce irin mahaukaciyar Yarinya ce wannan mai shegen tsaurin ido haka.
Mik’ewa kawai yayi ba tare da ya ko kalle ta ba ya koma kan sofa ya nemi guri ya zauna.
Duk da tsoron da take ji hakan bai hana ta matsawa dai-dai wajen k’afafunsa ta zauna ba,
sannan cikin wata kalar murya
mai tsananin had’ari ta ce
‘’Ya Yash dan Allah’’
Gaba d’aya tashi d’aya sai ya ji tsigar jikinsa yayi wani iri…
Kallon ta ya yi da rinannaun idanunsa cikin b’acin rai ya ce ’’Tashi ki fita, in kuma tsaurin ido zaki gwada Bismillah ki k’ara second goma a nan za ki ga ikon Allah’’ ya riga ya san k’arya take yi ba Mommy ce ta turo ta ba.