← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka ta ga gwara ta nemawa kanta mafita!
Tun kafin kawaicin Fulanin Iyayenta ya cutar da ita.
A nata lissafin….
kamata ya yi a ce an barta da Imam ta juyo da hankalinshi zuwa gareta, tunda an san bai son ta, ba wai
a haɗata kishi da wata chan daban wadda za ta zo ta lalata komai ta kuma janye mata hankalin masoyi ba….

A chan parlour kuwa, Khadijah ta na shigewa ciki,
Abba ya ɗan gyara zama ya kalli Imam kafin ya ce
‘’Na ji Khadijah ta faɗi wani abu akan Khadijar da kake son ka auro wanda ni ban san da shi ba!
Ina fatan za ka ce mini ba dai-dai bane ba.”

Lumshe idanu Imam ya yi,
kafin ya yi amfani da tafin Hannunsa wajen shafa farar Fuskarshi wadda ta yi jaa zuwa wannan lokacin tsabar tashin hankali….
Abba ne kaɗai hope ɗinsa..ya san kuma shi kaɗai zai iya juyo da hankalin su Daddy a samu su barshi ya auri Khadija.
Abunda ya ke ta tsoro dama shine
kar su san ƙaddarar da ta afka wa Khadijan dan ya san muddin su ka sani to da wuya Abban shima ya yarda….
‘’Imam, ka yi shiru”
Muryar Abba ta katse masa lissafi.

A hankali ya sauƙe numfashi tukunna cikin sanyin jiki ya soma magana
‘’am Abba…
Kamar yadda na gaya maka
Khadija ba ta da kowa, ita da ƴar uwarta marayu za a ce musu kai tsaye, na santa ne a silar kawo mana Nono office da su ke yi talla daga ita sai ƴar uwarta na sani danginta sai kuma wani Kawunta
da ta taɓa haɗani da shi, wabda su ke zaune a gidansa.
A halin yanzu shima ya rasu
kuma dama
Matar tashi azabtar da su ta ke yi,
tun a lokacin da ya ke a raye ma.
Shiyasa ya na rasuwa ta tattara ta barsu ta yi gaba, su sun ce mini Uncle ɗin nasu da Mahaifinsu kawai su ka sani…
Ba su taɓa zuwa garinsu ba, bama su san garin ba har Mahaifin nasu ya rasu. To kuma su na saka ran zuwa da shi kawun nashi shima sai Allah ya yi masa rasuwa.
Shiyasa tun a lokacin na so in auri Khadijar saboda itama ƴaruwarta Miji ya fito mata ta auri wani mai mata uku da ƴaƴa ashirin a layin nasu amman ya ce ba zai riƙe Khadijah ba.
Na san zaman ta ita kaɗai akwai haɗari!
Shi kuma Daddy ya dage akan duk uzuri na ya jira, ko ma menene ya jira har a yi auren mu da Khadija tunda an riga an gama magana.

Ko uzurin nawa bai tsaya ya ji ba, gani kawai ya ke kamar turjiya na ke shirin yi masa, shiyasa na haƙura
a wannan lokacin kamar yadda ka buƙaci in yi haƙurin.

Itama ba yadda ban yi da ita akan ta biyo ni ba amman ta ce za ta iya zama ita kaɗai!
Ni kuma abubuwa sun sha mini Kai
a wannan lokacin
ga hidimar biki!
Ga aiki!
To a wannan tsa-kan-ka-nin ne aka samu wani Marar Imani ya je ya yi mata fyaɗe!”
Sai da ya ɗan yi shiruu, zafin abun ya na ratsashi tukunna ya ɗaura da cewa
“Sam ba laifinta bane ba Abba.
Dan sai da ma ta yi kwanaki biyu a asibiti ba tare da ta san inda kanta yake ba ma.

Tun daga lokacin ni kuma sai na ƙi amincewa ta ci gaba da zama a gidan ita kaɗai….
Laifina ɗaya shine da na kawota nan ɗin!
Na san bai kamata in kawota nan ba tunda gidan aure na ne!
Amman kuma banida wata mafitar,
tunda su Daddy ba za su bari in kai musu ita chan ba tare da sun san wacece ita ba!
Gashi cikin da ta samu ata dalilin ƙaddarar da ta afka mata
ya zo da matsala!
Ana yin sati biyu ta fara bleeding muna zuwa asibiti kuma ya zube.
Ga rashin lafiya ga rashin tsaro da wajen zama mai kyau
shiyasa na kawota nan ita da nurse, sai dai kuma tunda Khadija ta yi bincike ta gano asalin gaskiya shikenan ta fatattakesu…
Sai da na yi kwana uku tukunna na nemota da kyar.”

Shiruu ya ɗan yi kafin ya ɗaura da cewa
‘’Dan Allah Abba ka duba lamarin nan..
Mu taru ni da Kai mu ceto rayuwar baiwar Allah.”
Ya ƙarashe maganar cikin haɗe Hannuwanshi biyu waje guda kamar zai fashe da kuka.

Numfashi Abban ya fesar
bayan dogon nazari…..

Kafin ya kalli Imam ɗin ya ce
‘’Zan haɗa ka da driver gobe
ku je a yi duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata!
Allah ya sanya alkhairi
Allah ya yi maka albarka.
Zan yi wa Daddyn naku magana!
Kar ka damu zai fahimta shima, in sha Allahu.’’

Wani tsananin sanyi ne ya lulluɓe Imam ,har sai da wasu hawayen farin ciki suka wanke mishi fuska.

Murmushi kawai Abban ya yi, daga haka ya miƙe da shirin tafiya….
Tsakanin uba da ƴa sai Allah!
Ya san abunda ya yi, ya ke kuma shirin yi
tabbas shine dai-dai amma
kuma a take tausayin ƴar tashi sai ya lulluɓeshi ya hanashi jin walwala…
Saboda ya fahimci tunda har Imam ya rufe ido ya sake yi mishi zancen wata bayan ya aura masa ƴarshi ko watanni biyu ba a rufa da yin aurensu ba, to fa hakan ya na nufin ba ƙaramin so ya ke yi wa ita wachchar bafulatana mai tallan Nono ba.
Har ga Allah, da ya ji maganar ta yi shiru bayan wata ɗaya da yin auren nasa ya ɗauka Imam ɗin ya haƙura ne, ashe abun ya na nan!
Tabbas rayuwar ƴarsa Khadijah
ta na cikin garari…saboda tun shekara ɗaya da ta gabata (a lokacinda aka fara maganar aurensu) har kawo yanzu,
bai taɓa ganin ɗigon son ƴar tashi a cikin idanun Imam ba.

Daddy, babban Abokinsa ne tun yarinta, wanda ba dan albarkacin hakan ba da kuma yadda ya ga Daddyn ya nace da son ya ga ya ƙulla auratayya a tsakanin su tabbas da babu dalilin da zai sanya ya yarda da auren Khadjansa da
Imam tun farko, tunda ya san ba sonta ya ke yi ba.
Yana ta fatan su samu su ɗan sasanta, ya so ta wata rana
to kuma yanzu gashi zai auri wadda ya ke so!

Fatanshi ɗaya ‘Allah ya sa Khadijan ta yi hankali ta kwantar da hankalinta ta yi biyayya ta zauna lafiya…
Wataƙila ta samu matsugunni a zuciyar Mijinta…
In ba haka ba kuwa
Ba ya jin tana da rabo a Zuciyar Imam
……
An ɗan kai ruwa rana kafin
Daddy ya yarda aka ɗaura auren Khadija(Mai tallar nono) da Imam a cikin sati ɗaya.
Wanda a tsakankanin kwanaki bakwai ɗinna babu kalar haukar da Khadija (uwar gida) ba ta yi ba!
Har kalanzir ta zuzzuba a gidan koina lokacin yana bacci
ana i gobe ɗaurin auren!
Allah ya taimaka,
ya ji warin kalanzir ɗin cikin barci dan haka ya farka da wuri….
Yana zuwa ya tarar da ita ta na ta ƙoƙarin kyasta ashana….

Da kyar ya samu ya karɓe ashanar
ya jefar, ai kuwa ya na jefarwa ita kuma ta rarumo wuƙa.
Fahimtar da ya yi da gaske kishi ya haukatata kuma idan ya barta kashe shi za ta yi, hakan ya sanya ya fincikota zuwa parlour sannan da kyar ya fitar da ita tsakar gidan ya saka ta a mota…..

Iyayenta tamkar iyayenshi su ke,
dan zai iya cewa shi da ɗan uwansa especially ma shi ɗin kusan a hannun Mahaifiyarta ma ya girma!
To amma kuma ya kamata a takawa haukar tata burki!
Tun kafin ta yi ɓarna, shiyasa ba dan ya so ba ya kaita gidansu ya faɗawa su Abba duk abubuwan da ta ke yi masa har ƙoƙarin kashe shi ɗin da ta soma yi.
..
Sallamar Imam kawai Abba ya yi
bayan ya bashi haƙuri.. ya ce a barta a nan kar ya koma da ita.

A tunanin ta faɗa kawai
za a yi mata, daga nan a maida ita
a ranar amma sai ta ji Abba ya hana! Sannan ya hana a barta ta
fita ko da ƙofar gida ne…
Tana ji ta na gani haka nan aka ɗaura auren Imam da Amarya Khadijah…
Ba abunda ya fi ɗaga mata hankali kamar yadda ta ji Abba yace
‘’ba za ta koma gidan Imam ba kwata-kwata‘’
Gashi auren da ta yi haukar a kai an riga an ɗaura
dan haka a take ta fara da ta sani..
Hankalinta ya sake tashi sosai dan sai ta ga kamar ma ta bawa Imam damar cin amarcin shi hankali kwance kenan!.
Ko sati ɗaya ba a yi ba ta ƙara gigicewa ta fita a haiyyacinta,
kamar mahaukaciya haka ta koma.

Ba dan Baabaa Larai wadda ta zo musu ta ke bata Baki da kuma Mahaifiyarta wadda itama ta ke tausar ta tabbas da ba tuni ta zauce!!
….

Sai da ta sha wahala ta ƙara fita a haiyyacinta tukunna
da kyar su Maama Mommy da Daddy su ka takurawa
Abba ya kira Imam ya ce masa “ya zo ya ɗauki Matarsa”
A Lokacin Amaryarsa watan ta ɗaya a gidan har da ɗan cikinta.
…..
Tare da Larai suka koma gidan nata
saboda itama Laran a lokacin an ɗan samu matsala da ita a ƙauyensu, ta ƙi komawa.

Sosai Imam ya yi mamakin yadda Uwargidan tasa ta chanza lokaci guda….
Ba kishi ba hauka sannan ta ja Abokiyar zaman ta a jiki kamar za ta cinye ta domin so…
Cikin jikinta kuwa ko ita uwar iyaka yadda za ta kula da shi kenan.
Sai wani nan-nan ta ke da ita ko abu mai nauyi bata taɓa bari ta ɗauka…gashi sun hanata girki shima sun ce ta huta kawai ita Uwargidan da Larai ne su ke yin komai!
Ko ruwa in ta je tafasawa haka Uwargidan za ta amshe
Ita ko Larai a samu wani ya tafasa mata a kai mata har ɗaki.
Chapter 2 · 0% Book details