Sashe 70
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikin anty Umma kam ba sauk’i sam, sannan har gara Baba ma shi an samu an kaishi asibiti
Ita kuwa ko asibitin ma ba a samu me kaita ba.
Siyaman ce take gayawa su Jidda cewa “babu wanda ban kira a cikin manyan gidan nan ba, amman kowa sai dai yace min ba shi da ko sisi.
Uncle shi kam ma rufe ni yayi da fad’a!
wai yanzu Ya Musbah ya kira shi, ya tura masa kud’i shine nima zan kuma kira…
gaskiya shi fa an saka mishi ido!Ɗan shige da ficen da aka ga yanayi shine ake ganin kamr wani k’arfi ne da shi. Daga yau in dai na san maganar kud’i ne tou kar ma in sake kiranshi yana wajen aiki, shima bashida shi…’’
Muryarta ce ta katse ta dalilin kukan da ya taho mata.
Cikin kulawa Manubiya ta shiga rarrashinta tana bata Baki…..
duk da damuwar da su Manubiya suke a ciki basu yarda sun bar parlourn ba sai da suka d’an kwantarwa da y’ar uwar tasu hankali, suka ga ta d’an ware, tukunna suka yi wa anty umma ‘Allah ya k’ara sauk’i’
suka mik’e za su tafi.
Mik’ewa itama Siyaman ta yi ta cewa Umman nata “bari in d’an raka su’’
‘’To’’
kawai anty Umman tace daga haka ta yi musu sai da safe tace su gaida Baba.
Suna fita Siyaman ta ce
“Manu, akwai abunda nake so in gaya muku, kar ku ji a Bakin wani gara ku ji a Bakina’’.
Tsayawa su ka yi duk suna kallonta, dama sun lura kamar akwai
abunda take son fad’a!
Anty Umma kuma sai gargad’i take ta yi mata da ido.
Cikin sanyin jiki Siyaman ta sanar musu ’ashe Suraj..wanda zai aureta ne ya fasa. wai akan an zab’a masa y’ar uwarsa…
shine ma dalilin da ya sanya Anty Umma ta d’aga hankalinta har ta kwanta rashin lafiya.’
Tausayin ta ne ya lullub’e Manu
dan haka sai tama kasa cewa komai.
Jidda ce ta iya cewa ‘’Siyama dan Allah ki kwantar da hankalinki kema karki wani d’aga hankalinki.
InshaaAllah hakan shine mafi alkhairi,
Allah ya riga ya rubuta dama ba mijinki baneba, inshaaAllah shi zai baki wanda ya fi shi.”
Ajiyar zuciya Siyama ta sauk’e kafin ta ce
‘’Jidda sam ban d’aga hankalina ba wallahi ni kaina ina mamakin yadda abun bai wani dameni sosai ba, amma yadda Umma take yi ne bana so, sannan Itafa har yanzu ta ƙi ta hak’ura, shiyasa ma kika ji bata gayawa kowa ba, ni kuma na riga na san tunda har suka ce sun fasa to sun fasa d’in kenan saboda matsalar daga b’angaren mahaifinsa ne fa tun da y’ar k’anwar mahaifin nasa aka basa ashe shiyasa suke ta ja mana rai wajen kawo kaya su ce yau su ce gobe.
Amman wai duk da wannan abunda suka yi wa mutane in kika ga yadda Umma take waya da mahaifiyarsa tana wani lallab’a ta abun sai ya b’ata miki rai, sai kace irin ana neman kai da ni ɗinnan….
Da ya ke itama mahaifiyar tasa ba so take ya auri ita wachchar Yarinyar ba.’’
‘’Haka iyaye mata suke Siyama,
gani takeyi kamar za ki shiga damuwa…
Duk abunda za ki ga ta yi domin ke ne take yinsa”
cewar Manubiya wadda gaba d’aya jikinta yayi sanyi.
Cikin sanyin murya Siyama ta ce
“da wannan kam gaskiya, sannan kuma na lura kamar tana so ma ta nunawa kaka mallan iyakar sa,
a nawa tunanin kenan. saboda kin san ai ya yi wa makwaftanmu magana akan karb’ar kaya, tou yanzu duk ya je yanata yayatawa wai an fasa auren nawa…
A bakin yayata fa da take aure a illorin mukaji, wai wata makwafciyar mu anan ta kirata takanas dan ta tabbatar, kinga kuwa ai ya gama yayatawa kenan. Amma dukda haka ni ban san me yasa Umma ta ji haushi ba, dukda a yanayin da yaketa sanarwar bai dace ba amman kuma ni a ganina gara ma a sani tun wuri,
tunda dole dai za’a fasa d’in, kuma kowa zai ji.’’
Ajiyar zuciya ta sauk’e cikin son kawo k’arshen zancen ta ce
‘’ko ma dai menene…
mai faruwa ta riga ta faru.
Ni kuma Ko ba komai yanzu da na yi muku maganar na d’an samu sauƙin abun wallahi’’.
Murmushi Manu ta yi kafin ta ce
‘’Siyama ai iyayenmu ne basu gane hakan ba tun wuri,
zaman tare dole akwai sab’ani wasu lokutan ma har da rashin fahimtar juna amma muddin aka ce akwai had’in kai a tsakani to sai ki ga an dace’’
Da sauri Siyama ta ce
‘’Wallahi Manu rashin had’in kan y’an gidan nan namu nima yana damuna, har gwara ma ku ku biyu ne
Ni fa?
Wani zubin fa idan aka k’unsa mana sai dai mu zauna Umma tana kuka nima ina taya ta, babu mai rarrashinmu’’.
Murmushi Jidda ta yi daga haka ta kamo Hannun Siyama tukunna ta ce ’’rashin had’in Kai wannan zab’in iyaye da yayyen mu ne. amman mu za mu iya gyarawa, ko da a tsakanin mu ne, wanchan tsarin su ne dan haka inaga muma za mu iya shimfid’a namu tsarin!
watak’il idan suka ga ribar had’in kan a tsakanin mu suma su gyara….
kasancewarsu manya ba shine zai sanya ace
duk abunda suka yi shine daidai kuma muma sai mun bi ba’’
Murmushi Siyama ta yi kafin ta ce “tabbas Jidda maganarki hakan take.
Tun tasowata bani da burin da ya wuce inga mun had’a kai ni da y’an uwana, amma kash!
Ɓangaren Mahaifina sun fi nan gwanancewa a fannin rashin haɗin dan su kam zan iya cewa da su gara babu ma, tou nan d’in ma dande kawai muna zaune a waje d’aya ne Ina ganin ku Ina jin sauk’i amma ta fannnin had’in kai kam duk sammakal….
Na cire rai da gyaruwar al’amura a tsakanina da ɓangaren Babana amman nan kam dama Ina saka ran dacewa.
Na ji dad’in wannan goyon bayan dana samu daga gareku y’an uwana, Ina rokon Allah Ubangiji ya dafa mana ya bamu ikon gyara zumuncin mu.’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai rungumo su gaba d’aya…..
…
Siyama ta yi waec, takardarta ce dai batayi wani kyau ba, ta ji kwad’ayin inama ace itama itace zata zana post utme jibi
kamar Jidda, dan haka suka k’ara k’arfafa mata guiwa akan ‘ta sake yin waec, ta yi jamb ta koma makaranta…’
Idan Allah ya kawo aure ta yi in kuma bai zo ba ta maida hankali akan karatu da gina rayuwarta, kar ta bari wani chan Suraj dashi ya saka mata damuwa.’
Sun tab’a hira, tare da shawarwari a tsakanin su sosai. kafin suka yi mata sallama suka wuce d’akinsu itama ta koma fanninsu.
•••
K’arar zuge gate tare da parking d’in motar Yashjub ne ya katsewa kowa tunani.
A kurkusa ya yi parking d’in shiyasa har ya samu damar shigowa kafin Daddy wanda ya nufi k’ofa kamar wani zararre ya Ida fita.
A bakin k’ofar suka yi karo da shi da Daddyn wanda ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya sakamokon ganin Yashjub d’in da yayi a kan ƙafafunsa lafiya lau.
Cikin kwantar da murya Yashjub ya d’an yi kalar tausayi ya ce
‘’Daddy I’m so sorry, dan Allah ka yi hak’uri…
Tun 5 lokacin da ka kira Najeeb muka fito, to muna fitowan ne sai motar Najeeb ta lalace, shine na tsaya na ara masa battery ɗina wai dan a samu a tashi nasa ashe wata waya ce ta lalace dan haka nima sai nawa battery d’in ya samu matsala….
Da waya d’aya na fita, to da yake tun rana muke yawo ni da shi munata waya kuma akayi rashin sa’a duk ba wasu isashshen charge ne a wayoyin namu ba shiyasa duk sai suka d’auke, bamu samu mun kira kowa ba.
D’azun kuma da na fita daga meeting wani abune mai matuƙar muhimmanci ya taso, zan yi maka bayani akai anjima amma yanzun dai ka yi hak’uri akan fitar da na yi da komai ma, ka yi hak’uri pls Daddy.’’
Ya k’arashe mganar tasa yana me had’e hannuwansa guri guda alamun roƙo.
Juyawa Daddy yayi, ya kalli yadda gaba d’ayansu har Ummi da Munirat suka zuba musu idanu sannan suka yi musu cirko cirko.
A hankali ya juyo ya kalli Yashjub d’in ya ce
‘’ka je ka ɗan huta, ka ci abinci, sai ka same ni a sama.’’
Daga haka ya juya ya wuce.
Yana wucewa Yahanasu da Mommy suka taho a tare.
Fuskar Mommy kamar wadda za ta fashe da kuka har da hawaye yaga ya taru a idanunta.
Dasauri ta ɗan ture Yahanasu ita ta k’arasa, ta na zuwa ta rungume Yashjub d’in kafin ta cikashi ta shiga tattab’a fuskarshi tana dudduba jikinshi, sai da ta tabbatarwa idanunta da lafiyarsa k’alau tukunna ta ce ’’Gaba d’aya hankalin mu a tashe yake Son…’’
Wani guntun murmushi Yashjub ya yi wa Mommy, da kyar, kamar irin an saka shi dole d’innan. tukunna ya kamo hannunta wanda yake rik’e da kumatunsa a hankali ya sauk’ar mata da hannun nata daga haka ya matsa kusa da Yahanasu wadda
ta ja ta tsaya tun lokacin da aka ture ta gefe.
Murmushi yayi mata kafin ya ce ’’sorry, na d’aga muku hankali….
Am anjima inaso za mu yi magana dake,kar ki yi bacci da wuri pls’’
Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarsa da alamun kulawa tukunna ta ce ‘’tam,
I’m just glad you are okay
(Na ji daɗin da ya kasance ba abunda ya same ka).”
Ahankali ya ce ’’na gode’’ kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta turo baki ta ce ’’you owe me an apology…(gaskiya ina binka bashin ban haƙuri)…..
Ka saka na bada speech d’in da ban shirya ma ba.’’
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Ina buƙatar hutu yanzu, sai da safenku.’’
Har ya juya zai fita sai kuma ya sake juyowa ya kalli Yahanasu ya ce ’’kar fa ki yi bacci!’’
daga haka ya sa kai ya fice.
Tun lokacin da Yash ya ture hannun Mommy, ta k’ame a wajen, ta gagara motsi. Gaba d’aya kanta ya d’aure ya d’au zafi dan kwata-kwata
ta ma kasa fahimtar yanayin Yash d’in.