← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 84

Sashe 32

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta ta bud’e, ta san halin Abbakar da shegen naci, a yadda ya kafe d’innan in bata gaya masa ba to ko ruwa ba zai barta ta sha ba, bayaga haka ma in ba shi ko Jiddah ba
bata san wa zata gayawa ta samu sauk’i ba, dukda bama ta san inda damuwar tata ta dosa ba bata san ta yaya za ta fassara ko ta fasalta damuwar tata ba saboda ba lalle ta yi making sense to anyone ba(bada ma’ana a kwakwalwar kowa ba) dan ita kad’ai ta fahimci sannan ta san me take ji take kuma fuskanta dan haka ba lalle a fahimce ta ba..

‘’Manu ke nake saurare’’
Abbakar ya fad’a yana sake gyara zaman shi.
Cikin tsare gida Manubiya ta ce
‘’Ok.
zan fad’a maka amma sai ka yi min alk’awarin ba za ka yi min mummunar fahimta ba’’.
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’inshaaAllah,ina jinki’’.

Sai da ta had’iye wani abu da kyar wanda ya tokare mak’oshinta tukunna ta ce
‘’Wannan Mutumin na office d’in Sir Najeeb na ranar nan, to shine nake ganin wata Mata mai kama da shi anan gidan kuma in dai na ganta to sai in yi ta tunanin sa har mafarki fa…
Ni kuma bana so ina yawan tunanin sa, bana buk’atar abun da zai had’ani da shi sam, shi yasa nake tunanin barin aikin nan..’’
Ta k’arashe maganar cikin tsananin sanyin murya da rashin jin dad’i.

Shiruu Abbakar ya yi yana tunani, har sai da ta sake cewa
‘’Ka fahimce ni?’’

Tukunnan ya d’an yi firgigit
Ya ce
‘’Yeah, yeah na fahimceki’’.
Daganan ya yi shiruuu ya sake dulmiyawa duniyar tunani.

‘‘Shikenan tou tunda ba ka ma da abun da zaka ce, yanzu gaya min abun da yake tafe da kai’’
Ta fad’i hakan cikin d’an had’e gira alamun ta ji haushin kanta na fad’a masa ta kuma ji haushin shirun da ya yi dan in ba dakyar ba to tasan tunanin abun da bata so ɗin shi kwakwalwarsa ta bashi yake yi.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*20*

Murmushi Abbakar ya yi kafin ya ce
‘’Yi hak’uri, ban san me zan ce ba ne shiyasa kika ga na yi shiru….

abun ne ni kaina ya sakani a tunani da damuwa ballantana kuma ke, shawara d’aya
itace
‘kawai kiyi ta addu’a..Allah ya sa mu dace.’.”

A hankali ta ce ’’Ameen’’

Sai da Abbakar ya d’an sake yin nazari tukunna ya ce
‘’Am..kiran da Sir Najeeb ya yi mini ɗazu akan ki ne fa.’’

Da sauri ta zaro idanu waje, sai kuma ta ce
‘’A kan me wai???’’
Ta yi masa tambayar a d’an tsorace.

Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’kwantar da hankalinki, abun alkhairi ne.
Aiki kika samu, a wata a yadda ya ce min 30k, kuma sau d’aya kawai za ki dinga zuwa a sati
ragowar kwanakin duk ta waya za ki dinga bada rahoto.’’

Da sauri ta ce
‘’Da gaske? Tayaya? a ina kuma?’’
Ta yi masa tambayar cikin zumud’i da d’aurewar Kai.

Yana murmushi ya ce
‘’Kina cewa sir Najeeb bashi da kirki ko?
To ba haka abun yake ba, sannan kuma wataƙila ina tunanin yana da wani rauni a duk lamarin da ya shafi mahaifiya…
Dan Ce mini ya yi yana yawan ganin ki a damuwa
‘dayake kin san ranar ai kin ce
masa Inna bata da lafiya to inaga yana tunanin ko akwai wani problem d’in da ba za ki iya fad’awa kowa ba,
shiyasa ya ga ya dace ya taimaka miki ke kuma ki taimaki Inna’.’’
Abbakar ya zaiyyane mata hakan cikin son rufe duk wata k’ofar da zata sa ta fahimci wani abun.

A hankali ta ce
‘’Allah sarki Sir Najeeb,
Allah ya saka masa da gidan Aljannah.
Amma aikin nasa ne? I mean (ina nufin) a Ina ne?company ne?’’.

‘’Eh to nima ban sani ba gaskiya amma inaga kamar na Uncle d’insa ne or something like that(ko kuma wani makamancin hakan), ga dai katin wanda aka ce ki kira nan, shi zai yi miki bayanin komai’’.
Abbakar d’in ya bata amsa, yana mai mik’o mata card d’in Yashjub wanda Najeeb ya ba sa.

A hankali ta sa Hannu ta karb’i katin tana mai jin yanayinta yana chanjawa, haka kurum….

Cikin nutsuwa take kallon had’ad’d’en business card d’in mai d’auke da sunan ‘Yashjub Imam Kura’.
Shiruu ta yi tana sake kallon sunan tana sake maimaitawa…
kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta d’ago da sauri ta kalli Abbakar sannan ta ce
‘’Abbakar ko dai wannan Mutumin ne wanda muka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb ɗin wanda na gama maka maganar shi yanzu?’’

Cikin katseta ya ce
‘’A’a ba shi bane ba, in da ace shine da zai gaya mini…
wannan d’in Sir Najeeb ce min ya yi kamar Uncle d’insa ne fa, Kinga wanchan kuma ai bashi da shekarun da za’a ce masa Uncle ko?’.
sannan duba katin da kyau wannan fa landlord ne
Estates gareshi har a su Abuja da nan garin, yaushe aka haifi wanchan Mutumin wanda bana jin ya kai 30yrs da har zai gina estates haka??’’.

‘’Eh kam.’’
Manubiya ta ce. Tana mai k’ok’arin son yarda da maganar Abbakar d’in, daga nan ta saka a ranta
maybe kawai ta ji fad’uwar gaban da ta saba ji in ta yi tunanin shi ko ta had’u da Mama
By mistake ne,
Amman wannan ba wanchan Mutumin bane ba.

A hankali ta ci gaba da karanta sunan tana sake maimaitawa
dan ya yi mata dad’i sosai
A fili ta ce
‘’Yashjub’’
A hankali,sai kuma ta d’an yi murmushi.
Ba tare da ta kalli Abbakar ba
Still idanunta na akan katin
ta ce
‘’Nagode kwarai Abbakar,
Allah ya sa mu dace’’.
Sai kuma ta d’ago kyawawan idanuwanta tana kallon sa tukunna ta ce
‘’Amman ka san sai na yi shawara da su Ya Musbah da Baba, mu yi adduar Allah ya sa su yarda dan ka san halin su ba sa so su ga ni ko Jidda wani a cikin mu yana contributing (kawo gudummawa) wajen ciyar da gidan.
Ya Musbah ya dage yana k’ok’arin d’aurawa kan sa abun da ba zai iya ba, wuni yake yi yana guga da wanki A shagon Mati kullum in ka gan shi a gajiye ya ke abun tausayi.’’
Ta k’arashe maganar tata idanuwanta suna ciccikowa da kwallah.

Murmushi Abbakar ya yi kafin ya ce
‘’Ai har aiki yake yi a wajen masu ginin chan na bayan layi
ya tura suminti ya tura bulo duk dai wani aikin k’arfi yi yake,
ni fa yana burgeni Manu, Namiji da neman na kanshi aka san shi.’’

Cikin karyewar zuciya ta ce
‘’eh, hakane Abbakar,
amma shi abun nasa ya yi yawa kuma kar aje ayi biyu babu, ka duba fa ka gani saboda d’aurawa kai aikin wahala Baba ya rasa k’afarsa guda d’ayar kuma ta ji rauni,
Inna ma saboda yawan tunani kalli halin da take ciki!
Kar mu je shima Ya Musbah
abu ya yi mishi yawa shima ɗin aje ya samu wata matsalar, in hakan ta faru( Allah ya rufa asiri )
da ni da Jiddan da basa so mu wahala mu zamu zama a wahale ai ga Muhsin shima.
A rayuwa in dai ana so a ga abu ya yi perfect (dai-dai) to fa sai an had’a Hannu da Hannu k’arfi da ƙarfe tukunna.’’
Ta k’arashe maganar tata wasu siraran hawaye suna zubo mata, da sauri ta yi ƙasa da kanta.

A hankali Abbakar ya sauk’e ajiyar Zuciya kafin ya ce
‘’Manubiya k’addara kowa da irin tasa, ki daina kuka dan Allah, ki yi addu’a, ki kwantar da hankalinki.
wata rana sai labari.’’

A hankali kanta a ƙasa har yanzun ta ce
‘’Astaghfirullah! amman Abbakar k’addara ta mai zafi c…’’
Cikin katse ta ya ce ‘’shiii‘’ Sai kuma ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ya ce ’’Taki kawai kika sani.’’
Kamar zai ce wani abun sai kuma ya mik’e ya ce
‘’Bara in wuce,duk yadda kukayi kya gaya min gobe’’.

A hankali ta ce
‘’To’’.
Daganan suka yi sallama ta sake masa godiya sannan ta koma gidan Ammi shi kuma ya wuce yana tunanin Allah yasa Manubiya kar ta ji haushin sa sosai idan ta fahimci ya san Yashjub za ta yi wa aiki amma ya b’oye mata..dama bai yi niyyar gaya mata ba, ya fi so ta je ta fara aikin tukunna ta fahimci Yashjub d’in ne, ya san kafin nan ba lalle ta iya bari ba.
To kuma yanzu a yadda ya ji tana ik’irarin zata bar gidan Ammi saboda mai kama dashi ya san babu dalilin da zai sanya ta aminta da aikin in ta san shi d’in ne…
wannan dalilin ya sanya shi ninke ta ta bai-bai..

Sai dare tukunna ta samu gayawa family d’inta har Inna, duk da sun san ba iya magana zata yi ba amma za ta ji su kuma ance in ta amince ta lumshe idanuwanta za su fahimta.

Kamar yadda suka yi zato tashi d’aya Baba da Ya Musbah suka ce “A’a”, shi Ya Musbah ma cewa yayi ‘’mutumin d’an kidnapping ne ko kuma dai yanada wani mummunan nufi akanta, dan in ba hakan ba tayaya za a yi Mutumin da kullum shine yake bata tsoro a cikin Malamanta ace tashi d’aya ya bata aiki kuma aikin ma ba zuwa zata dinga yi kullum ba iyaka sau d’aya a sati kawai, sannan a wata ya d’auki dubu talatin zuwait!! Ya bata.”
cike da bin bayan ya Musbah Baba yace ‘’Tabbas maganar ka haƙƙun Musbahu, ke Manubiya ina so ki..’’
Cikin katse su su ka ji Jiddah ta ce
‘’Inna ta amince’’.
Da mamaki duk suka maida duban su gare ta, ai kuwa ta sake lumshe idanuwanta kamar yadda ta yi da farko.

Cikin rashin jin dadi Ya Musbah ya ce
‘’Inna,Manu Mace ce, nauyin
family d’in nan akaina ya ke
Pls karki…’’

Ahankali ya ji Baba ya dafa kafad’arsa,Kafin da sanyin murya ya ji ya ce
‘Shikenan’’
Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya ya ce
‘’Ki kira Mutumin.
Duk Ranar da ya baki ya ce ki je sai ku tafi tare
Ke da Musbahu’’.
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice daga d’akin.
Chapter 32 · 0% Book details