← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin zaman da ta yi sai da ta bashi dariya,
ya lura da yadda ta wani zabura lokacin da ya zauna d’in ma sannan ta kuma matsawa jikin Jidda sosai.
Murmushi kawai yayi, ya amsa gaisuwar Jidda yana mai kallon ta
a hankali ya ji tace’’Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi’’
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’ba komai, Allah ya kare gaba ya ba su lafiya’’

‘’Ameen’’ ta ce,daganan ta yunk’ura zata tashi dan ta lura kamar yana d’an bukatar space da Manubiyan amma sai ta ji Manubiyan ta yi saurin damk’ar Hannunta ta rik’eta gam.
A hankali Jiddan ta gyara ta zauna a wajen ba dan ta so ba,
itama ta sunkuyar da kanta ta shiga wasa da bakin hijab d’in jikinta…
Har ga Allah ta jinjinawa Yashjub da abunda ya yi musu,
dan tun d’azu da Manubiya ta ce mata ‘ai shine wanda take yi wa aiki’
Jiddan take ta mamaki, dan a ganinta a zamanin nan na yanzu wanne employer (Oga) ne yake damuwa da matsalar employee d’insa (ma’aikatansa) har haka, a take wata zuciyar kuma sai ta ce mata ‘’kodai!kodai!!’’ dan haka ta d’an yi murmushi ita kad’ai, ta ci gaba da lissafe lissafen ta.

Ba k’aramin burge Yash su Manubiya sukayi ba…yadda suke da kunya da kamun kai
tabbas ya san iyayen su sun yi k’ok’ari wajen tarbiyyar su,
dan ko ba a fad’a mishi ba
ya fahimci jiddda k’anwar Manubiya ce sakamokon tsananin kamanni da ya ga suna yi..
Banbancin Jidda da Manubiya
yanayin girman jiki, kalar fata da ido ne kawai..Manubiya ta fi Jidda tsayi da jiki kad’an, kalar
fatar Jidda fara ce ita tass sosai Manubiya kuma ba b’aka bace ba kuma ba fara bace sosai,
Idanuwan Jidda sun fi na Manubiya girma sosai amma na Manu sun fi na Jidda kyau da d’aukar hankali..a ransa ya ce ’’ idanuwan da suka kusan haukatani”
sai kuma ya d’an yi murmushi kad’an.

Shiruu duk suka yi kafin Yash ya katse shirun ta hanyar cewa Manubiya
‘’Sister d’inki ce ko?’’

A hankali ta d’an jinjina kanta sai kuma tace ‘’eh’’daganan shiru ya sake biyo baya.

Still shi ne ya sake kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa ‘’Baba zai samu sauk’i, inshaaAllah.
kar ki damu komai zai daidaita. inshaaAllah’’

A hankali ta ce
‘’InshaaAllah,’’itama Jidda tace’’inshaaAllah’’a cikin ranta.

A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta, tana mamakin yadda k’iri-k’iri ta gagara yi masa godiyar da take ta zumud’in son yi…
gaba d’aya duk sai ta ji ba dad’i ta inda ko ishashshiyar gaisuwa ta gagagara shiga tsakanin su..
Yo ta inama zata iya? itafa tunda ya zo ya zauna a kusa da ita shikenan ya sakawa tunani, kuzari da duk wasu lissafe-lissafenta full stop.
Ganin rashin kyautuwar abunda ta yi ne yasanya ta yi da gaske da kyar ta samu ta d’an d’ago kanta da niyyar ta kalle shi ta yi mishi godiya, suna had’a ido ta yi sauri ta fara kallon gefen kunnensa sakamokon wani irin kallo da ta ga yana yi mata gashi sai wani tsadadden murmushi yake zuba mata.
Babu yadda ba ta yi ba amma da ikon Allah sai ta gagara cewa komai, ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shiga yi…
ganin da ta yi ba zata iya bane ya sanya ta yi sauri ta sunkuyar da kanta tana tunanin ta yadda zata aro jarumta ta yi masa magana ko da ace bata kalleshin ba dan zuwa yanzu ta fahimci abun kamar da wuya,a ranta ta ce ’’wannan wanne irin abu ne haka, wanne irin feelings ne wannan?’’
ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba.

A b’angaren Yashjub kuwa kad’an ne ya rage bai fashe da dariya ba a ransa ya ce ’’.to wai menene nata na k’in kallon cikin idonshi ne?’’ yadda take yi
tana kallon gefen fuskarshi abun ba k’aramin burge shi da bashi dariya ya ke yi ba.’’

Murmushi kawai yayi yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta yana jin wani sanyi yana ratsatsi…
baisan wanne Hali zai shiga ba in da an yi rashin sa’a black snake ya tafi da ita ko yayi mata wani abun, ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya ya yi saurin kawar da tunannin cikin taushin murya ta ji yace “Allah ya ci gaba da karemin ke, tare da family d’inki a duk inda kike’’.

Dumm!! Haka ƙirjinta ya buga,a take ta runtse idanunta tana jin yadda kalaman nasa na yanzun suke ratsa zuciya da dukkkannin sassan dake a jikinta tare da sauk’ar mata da wata sabuwar kasala mai tafe da fad’uwar gaba…
cikin mutuwar jiki a chan k’asan ranta ta ce ’’Not again Yashjub,plsss
(Kar ka kuma, Yashjub, dan Allah!)”.

Tunani Yashjub ya fara yi akan ko dai ya sako maganar incidence d’in jiya da safe, dan haka
ya bud’e Baki zai yi magana kenan aka bud’e k’ofar d’akin da aka shigar da Baba da Abbakar aka fito, da sauri su Manu da Ya Musbah da sir Najeeb suka rufarwa Doctor d’in da ya fito.

Yayinda Yashjub yake nan a inda yake ko motsi ya gagara yi, bayan Manubiya wadda ta mik’e da sauri ta nufi doctor kawai ya bi da kallo yana murmushi yana jin wani nishad’i yana ratsashi…ashe haka so yake? shi fa ko wanne irin takaici yake ciki to wuyarta ya yi magana da ita ko ya ganta kai ko tunanin ta ne ya samu ya yi
to fa da yardar Allah tashi d’aya sai ya ji b’acin ran nasa ya kau.

Cikin nustuwa sir Najeeb wanda ya gama jin bayanin Likitan ya juya ya nufi inda Yash d’in yake a zaune, har ya k’arasa ya tsaya a kansa sam Yashjub bai lura ba sai da Najeeb d’in ya kyasta ƴan yatsunshi a setin fuskar Yashjub tukunna ya d’an d’ago
yana kallon sa.

Murmushi Najeeb yayi ya zauna a gefen sa tukunna ya ce “ya dai?’’

Bai da niyyar b’oyewawa dan haka tashi d’aya ya ce
‘’Najeeb! Manubiya ce rayuwata, adadin yadda nake
numfashi kullum haka k’aunarta take k’aruwa a cikin zuciyata,
ku yi sauri ku nema min aurenta tun kafin in haukace muku.’’

K’amewa Najeeb ya yi kawai yana kallonshi yana mamaki, a ransa yace “Ubangiji mai’kun fa ya kun’!’’
Kafin ya yi murmushi ya ɗan
bubbugan kafaɗan Yash d’in cikin sigar zolaya yace “Mutumina! Ai ka riga ka fara hauka, kalli yadda ni kaina ka maidani bawan students d’ina..
mun gama duk wasu abunda suka kamata amma ka hanamu tafiya, sannan ka ji yadda kake magana kuwa?..
Gaskiya kam ya kamata mu yi wani abun da sauri’’
ya k’arashe maganar yana dariya k’asa-k’asa.
Kafin ya sake cewa “yanzu dai zo mu je ka ga sirikin naka,,mu samu mu wuce, Inada aiyyuka da yawa wallahi.
Doctor yace
Abbakar d’in an cire bullet an yi komai amma bai farfad’o ba tukunna,
Sirikin ka kuma he’s well and conscious so let’s go say hi
(Ya farfaɗo yaana lafiya, dan haka mu je a gaisa),
daganan mu wuce ko?’’
Ya k’arashe maganartashi da tambaya yana mai mik’ewa tsaye.

Har ya d’an yi gaba sai kuma yaga Yashjub bai ma taso ba, dan haka ya koma ya ce “ya akayi kuma?’’
Tunda yake bai tab’a ganin Yashjub yayi kalar tausayi ba sai yau, har da wani karkata wuya…
Dan haka kawai sai Najeeb d’in ya saki baki yana kallon ikon Allah..
Muryar Yashjub d’in ce ta katse masa tunani jin yana cewa
“I’m serious (da gaske fa nake) Najeeb, ka fara yi wa Hajiya Mama magana ita kuma ta yiwa Daddy, ka san halinta yanzun sai ta birkice a kasa gane kanta, shiyasa bana so ni in yi mata magana da kaina dan na san idan ta ga na damu kuma na rikice akan maganar to ba za ta taimakamin ba, cewa za ta yi tun yanzu Ina haka ina kuma ga idan anyi auren, ni kuma na san a yadda nake ji d’innan ba zan iya yin komai a nutse ba.

Ka yi mata magana, a samu a fara maganata da Yarinyar nan
Najeeb tun kafin a samu matsala.”

Shiruu Najeeb ya yi kafin ya bud’e Baki yana shirin yin magana k’arar wayarsa ta katse shi, dan haka ya cewa Yash d’in “a minute pls
(Ina zuwa dan Allah)’’
kafin ya sanya Hannu a aljihunsa ya zaro wayar.

Yashjub ya kalla kafin ya sake maida hankalinsa ga wayar sakamokon ganin sunan Daddy da ya yi a matsayin wanda yake kiran nasa, sai kuma ya sake kallon Yash d’in tukunna ya ce ‘’Ina wayarka??’’

‘’Tana mota’’
Yash ya bashi amsa a tak’aice, yana mai ci gaba da tunane-tunanen sa…’ya riga ya k’arbi har number Baba, zai jira ya d’an warke daganan sai ya bawa Daddy number d’in tasa su yi magana a tsakanin su ya san inshaaAllah kafin nan Najeeb kuma ya tsara masa hajiya Mama ita kuma ta yi wa Daddyn magana,
daga nan ya san inshaaAllah komai zai zo masa da sauk’i,
ta b’angaren Manubiya kuwa yana addu’a tare da yak’inin inshaaAllah za ta aminta da shi da yardar Allah ba zai sha wahalar samun soyayyarta ba, shiyasa ma yake so ya je mata ta koina har ta sama ta yadda zata fi d’aukar sa serious.’….

Cikin nutsuwa da girmama Najeeb ya gaida Daddy shi kuma ya amsa masa kafin cikin fushi ya ji Daddyn ya ce ‘’kana tare da Yashjub ne??’’

Sai da Najeeb ya kalli Yash yaga sam hankalinsa bama ya gurin ya tafi ga tunanin da yake ta yi tukunna ya ce ’’eh Daddy,‘’
kafin ya d’aura da cewa’’gashinan, bara in basa’’

Da sauri cikin katseshi Daddy yace
“A’a barshi. Ka ce masa na ce dan ubansa ko me yake yi ya bari ya zo yanzunnan’’
Daga haka ya kashe wayar kit.

A d’an duburce Najeeb ya kalli Yash dan bai tab’a jin Daddy da irin wannan fushi haka ba, kafin yace’’Yash!Daddy fa a zuciye yake, mai ka aikata?’’

A hankali Yashjub ya maida kallonsa da tunaninsa ga Najeeb kafin ya yi shiruu kamar mai tunani sai kuma chan ya ce ’’kash!wallahi mantawa na yi’’
Chapter 64 · 0% Book details