Sashe 59
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dama Ya Musbah neman Ya Yusuf d’in yake yi, dan a iya bayanin da Baba ya yi masa d’azun ya fahimci Baban bai lura tarko ne Yusuf ya d’ana masa ba, amman shi yana fara yi masa bayani ya fahimci hakan…a ganin Ya Musbah duk hauka da iskancin Ya Yusuf bai kamata ya sako Baba a cikin rashin mutuncinsa ba.
Da gudu ya nufesu ya je ya fara k’ok’arin kwatar Manubiya daga Hannun Ya Yusuf, ganin ya ƙi cikata ne yasanya Ya Musbah ya fara kai masa duka, kamar jira Jidda take yi haka itama ta saka dukkannin k’arfinta ta dinga zuba masa duka a baya…
Cikin ƙanƙanin lokaci abun sai ya yiwa Ya Yusuf yawa, shiyasa bai san lokacin da ya cika wuyan Manubiya ba, yana cikata kuwa itama ta sa hannu suka had’u har ita suka rufe Ya Yusuf da duka…
duka bana wasa ba dan dukkan su su ukun a zuciye suke da shi, sai da suka kaisa har k’asa…
Duk da haushin sa da Ya Musbah yake ji, sai kuma ya ga rashin dacewar hakan, ga kuma halin y’an gidan dama! kar Babansa ko wani nashi ya gansu ya ce sun yi masa taron dangi, haka nan su je su b’ullo da wani sabon hargitsin na daban kuma…..
Dan haka ya tsayar da dukan da ya ke yi masa sannan ya fara k’ok’arin janye su Manubiya.
Amman sai akayi rashin sa’a Baba Habu ya k’araso wajen sakamokon hayaniyar su da ta fara fita harabar gidan kuma ya ji kamar muryar Yusuf d’in.
Da kyar Ya Musbah da Baba Habu suka samu suka janye su Manubiya dan rufarwa Ya Yusuf sukayi, suka yi masa
dukan mata ta koina kamar sun kama b’arawo.
Haushi da takaici ne suka sanya Baba Habu yarfawa Ya Yusuf mari bayan ya d’ago sa,
A cewarsa ta ya zai tsaya su Manubiya su dake sa.
Da kyar! dan ya jigata ko gani bayayi sosai saboda Ya Musbah ya fasa masa gefen ido..ya samu ya iya cewa Baban nasa “ai har da Musbahu..
shine ma ya fara kai masa dukan da ya kai sa k’asa.”
Cikin fushi Baba Habu ya juya ya kalli Ya Musbah, kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ja hannun Ya Yusuf suka wuce wanda gaba d’aya jikinsa! baki! hanci da gefen ido suke fitar da jini, gashi ya kasa mik’ewa ya tsaya sosai yanata faman rik’e ciki alamun sun dake sa a wajen….
*MANNUBIYA*
*35*
*BARKAN MU DA BABBAR SALLAH,UBANGIJI ALLAH YA KARB’I IBDUNMU YA MAIMAITA MANA.*
Suna wucewa Ya Musbah ya dafe kansa..
ya fi second ashirin a haka tukunna ya d’ago ya ce
‘’bari in kai Inna gidana, sai in zo mu tafi wajen Baba.
Muhsin dama tun d’azu na mik’a sa gidan Nafi’u.’’
Da sauri Jidda ta ce ‘’Ya Musbah kar ka je su ganka kai ma namiji su kamaka.
A ganina gara ka bari mu Mata mu je…dan kai ba lallai su d’aga maka k’afa ba, inaga shiyasa Baba bai nemi ka je d’in ba ya ce ‘mu gudu’!.
Ka bari za mu je na san idan suka ganmu Mata za su tausaya mana su d’aga mishi k’afa.’’
Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e yana mai kallon ta ya ce
‘’D’azu Baban ne suka sanya ya kira ni da kanshi.
Na ji tsoro tare da firgici mai tsananin a cikinnmuryarsa.
Shin wanne irin d’a zan kasance idan na gudu na barshi a wannan halin saboda ni in ceci kaina?
Jidda babu inda d’aya a cikinmu zai gudu ya je, ko da kuwa za su d’auke ni a matsayin fansar kud’in da Baba ya ci ne.
Inna ma zan kaita gidana ne saboda kar a barta ita kad’ai anan,
Dan gaba d’aya mu ukun nake so mu tafi tare.”
Cikin katseshi Manubiya ta ce
‘’Ya Musbah ka san dai Baraka ba za ta kula da ita ba ko’’.
A hankali ya ce ‘’Manu na sani.
Yanzu haka Muhsin yana wajen Matar Nafi’u, so idan na kai Inna zan tura mata shi kuma zan ce masa in Inna tana buk’atar wani abun da ya san ba zai iya ba ya je ya kira matar Nafi’u.
Ina so mu tafi mu dukan mu mu uku saboda Baba yana buk’atar mu dukkan mu, sannan kinga ni ban iya karatu ba dan haka ba zai yiu in je ni kad’ai ba…
Jidda ba zai yiu mu je da ita
kad’ai ba, kema kuma ba zai yiu in je dake ke kad’ai mu bar Jidda anan ba hankalinta ba zai kwanta ba,
Ni kuma ba zan barka ku tafi iya ku biyu ba.
Ba za mu bar Inna anan ba,
kar mu tafi Yusuf ya shiga ya yi mata wani abun dan izuwa
yanzu na gama tabbatarwa Yusuf babu abunda ba zai iya aikatawa ba….na Kira Nafi’u ya ce yana hanya, ku zo mu je mu had’a k’arfi da k’arfe mu hud’un tunda ba mu da wanda zai tsaya mana, na san Allah zai taimakemu, shi zai tsaya mana
InshaaAllah…
In ma sunk’i yarda su hak’ura ni zan bada kaina a matsayin fansar kud’in ba komai, a samu Baba ya dawo gida”.
Shiruu duk sukayi kafin
Manubiya ta yi sauri ta wuce
tana share hawayenta tana mai cewa “zan jira ku a titi’’.
Ya Nafi’u yana zuwa suka saka inna a motarshi suka kaita gidan Ya Musbah, kana ganinsu ka san suna cikin tsananin tashin hankali Jidda kam in banda hawaye ba abunda takeyi, ya Musbah ma da kyar ya ke iya rik’e kwallarsa, dan basu da tabbacin dawowar tasu…
Baraka tana kitchen ya lek’a ya ce mata ‘’za su je wani waje, ga inna nan a d’akin bak’i.’’
Bata ko kalle sa ba ballantana
yayi tunanin zata amsa shi.
Hakanan ya juya ya bar mata kitchen d’in, ya samu Muhsin yace masa “in yana buk’atar
wani abu ya je ya kira anty Aisha”
daga haka ya kama hanya ya fito ransa duk ba dad’i.
Yana zama a cikin motar, Nafi’u ya lura da yanayin shi dan haka ya ce ’’in ba zata yarda ba Musbahu kawai mu kai Inna wajen Aisha, tun d’azu da ka kirani dama na kira ta na gaya mata, dan da ni da ita duk mun d’auka a gidana ma za a ajjiye innar a wajenta…shiyasa ma har ta gyara mata d’ayan d’akin bak’in dake a tsakar gida.’’
Girgiza kai kawai ya Musbah ya yi kafin yace’’karka damu Nafi’u.
ba zai yiu ace ni da
gidana amma mahaifiyata ba zata shiga ba! ba zai yiu ba!.
Ka bar batun Baraka kawai, dan bata da lissafi da ishashshen hankali, mu yi sauri mu yi abunda yake a gaban mu kar mutanen nan su fara shirme.’’
A bakin titi suka tsaya suka d’auki Manubiya tukunna suka kama hanyar Bankin…
cikin d’aurewar Kai Ya Nafi’u
Ya ce
‘’Ni fa duk ban gane komai ba, wanne irin banki ne za su ranta kud’i iya na kwana uku
kuma su ce za su kama Mutum tashi d’aya?
Sannan na ji kace Baban ya ce maka da kansa ya je bankin to ya akayi kuma suka kamashi????’’
Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e kafin ya ce ’’wallahi nima kaina a d’aure yake da lamarin nan, na dai san sharrin Yusuf ne bani da tantama shi ne ya had’a komai.
Shi kuma Baba ya yarda da shi,
kuma ka san shi da b’oye b’oye,
sannan ya ƙi yin shawara da kowa har ta chab’e.
Bara dai mu je d’in, sai mu ji komai, Allah ya shige mana gaba.’’
‘’Ameeen’’
gaba d’ayansu suka ce, daga haka motar ta d’au shiruuu kowa yana tunani da fargaba, dan haka suka shiga jero addu’o’i a cikin ransu.
Aikuwa da suka je abun da suka yi zato d’in ne, dan ko cikin bankin ma ba su shiga ba a waje ake case d’in, saboda babu bashin banki tsakanin Baba da banki.
Bashi!
a tsakanin Baba da wani mai kud’i ne wai shi ‘Black Snake’
wanda k’asa take zarginsa dan a file d’in nashi ma har da case da efcc suna kan yi….
A jikin takardar
….Baba ya tambayi Mutumin aron miliyan d’aya, akan yana buk’ata urgent kud’insa sun d’an mak’ale amma suna fitowa nan da 2 days zai maida masa har da interest!.
Idan bai maida ba kuma to ya yarda Mutumin ya yi masa
duk abunda ya ga dama…
Su ya Yusuf su suka yi shaida suka tsaya a tsakani da shi da
wasu Abokan shi guda biyu.
Babban abun takaicin
shine yadda Mutumin ya ƙi baiyyana su gansa balle su samu su yi mishi magana!!!
an ma ce musu baya ma k’asar gaba d’aya…
Wasu mutane ya aiko su biyu
bak’ak’e murd’ad’d’u, waenda ana ganinsu kallo ɗaya an san babu d’igon Imani a tare da su.
Ana cikin haka aka ce ‘’ai case ya tashi anan, awa uku da aka bada ta cika dan haka yanzu sai dai a tafi da shi
Police station.
Kamar wani shahararren b’arawo haka aka datsa masa ankwa, aka saka shi a mota.
Gaba ɗayansu Yaran suna kuka haka aka tafi da shi.
Ba tare da b’aata lokaci ba suka bishi a motar ya Nafi’u.
Suna zuwa suka tarar da wani sabon tashin hankali ‘Wai an bada order, a yi masa horo mai tsanani,’
Gashi an k’i a basu bail d’in shi.
D’ayan police d’in ma ce musu yayi “su gudu.”
Saboda wai black snake d’in tun d’azu ya bada order a kama har family d’in Baban a had’asu waje d’aya..
Suna tsaye a reception suka fara jiyo ihu, babu yadda ba su yi ba amma aka hana su shiga….
d’ayan police d’in ne ya d’an kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu “ai ba ihun Baba baneba” sannan ya basu shawarar ‘su je su nemo kud’in, tun kafin abun ya fi haka lalacewa’
Da kyar dai aka samu suka hak’ura suka yi waje a gigice masu hawaye suna yi
masu kuka sunayi.
suna fita
Ya musbah da ya Nafi’u
kowannensu ya d’au waya suka shiga neman mafita a rikice.
Sun shafe sama da awa d’aya
suna tambayar jam’ar da suka sani bashi amma daga Ya Musbah har Ya Nafi’un kwata-kwata dubu ashirin suka had’a….