← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 84

Sashe 1

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*MANNUBIYA*
*01*

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.

Kano, Shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in….(1990)

A gefen titi sannan a hankali ya ke tuƙin motar tasa k’irar ‘Daewo Nubira’ tamkar ba ya son ƙarasawa inda ya tasarma zuwa ne.

‘Sannu-sannu bata hana zuwa’
In ji Mallan Bahaushe dan a hakan ya samu ya ƙarasa gidansa wanda ya ke a Unguwar sharaɗa. Ko da ya ƙarasa bakin gate na gidan bai yi horn ba. Alamun tsayuwar Mota da mai gadin gidan ya ji a ƙofar gidan ne ya sanya ya leƙo wanda ganin Mai gidan nashi ya na jira ya sanya ya koma da sauri ya wangale gate na Madaidaicin flat house ɗin.

Ko da ya shiga ya ƙarasa ya yi parking, kashe Motar kawai ya yi ya ɗaura kanshi a jikin sitiyarin Motar ba tare da ya fito daga cikinta ba.

Ya fi mintuna talatin a haka ya na tunani shi kaɗai kafin tashi ɗaya gabanshi ya yanke ya faɗi! Ranshi ya sake ɓaci!
Sakamokon jin fitowar ta da ya yi dan ko ba’a gaya masa ba ya riga da ya san ‘Khadijah’ ce, kasancewar
ba su da mai aiki, a gidan daga shi sai ita sai mai gadi wanda shi ke yi musu har wankin kayansu da guga.

Shiruu, kawai ya yi ya na jin ta ta rufo ƙofar parlourn tukunna ta tunkaro Motar da ya ke ciki a zaune.

Kamar yadda ya zata, ta na zuwa da rashin mutunci ta soma ta inda ta buɗe ƙofar Motar da ƙarfi kamar ta iso filin daga, sannan ko sannu da zuwa ba ta yi masa ba, cikin fushi ta soma da cewa “shine sai da ka kira Abba ko?” Ba ta jira ya bata amsa ba ta ɗaura da “ashe cin fuska da
rashin adalcin da ka kusan aikatawa bai isheka ba kenan? tunda gashi har an kashe magana an gyara komai amma ka ɗauki waya ka kira Abba, me kenan kake so
yanzu? So ka ke ya goya maka baya ko me?”

Bata jira jan numfashi ba a hassale ta ɗaura da cewa
“Tou bari ka ji, ko da ace Abba ya goya maka baya akan abinda kake so ni ba zan bari hakan ta taɓa faruwa ba wallahi…
Zan baka mamaki dan in ka na tutiyar ka na da Abba (zai tsaya maka) to nima ina Daddy (yana bayana)”
Ta ƙarashe maganar tata cikin tsananin bacin rai da takaici.

Tun lokacin da ta iso ta fara magana shima ya haɗe rai,
Fuskar nan tamau kamar bai taɓa dariya ba.
Ba tare da ya kalle ta ba
ya zare key ɗin Motar ya ɗauki abubuwan buƙatar shi tukunna ya fito daga cikin Motar.
Ko kallon inda ta ke bai yi ba
ya fara ƙoƙarin wuceta.

Da ɗan ƙarfi sannan da sauri
ta riƙo Hannunsa!
Cikin tsananin bacin rai ta ce
“IMAM ,Wallahi na fi ƙarfin ka wulaƙanta ni, ai so ba hauka bane ba, bar ganin wai Ina sonka
wallahi idan har ba ka janye maganar nan ba to zan yi maka abinda sai ka yi da ka sanin haɗuwa ma da ita kanta ‘Khadijar’, zan baka mamaki, zan sanyaka ……..”

“Sannu Uwarsa”
Su ka ji Muryar Abba daga sama
dan sam ba su san lokacin da ya shigo ba ma.

Tabbas, ta sha jinin Jikinta amman dukda hakan
kishi da baƙin cikin da ya ke kwance a kan kyakkyawar farar Fuskarta bai kau ba sannan Zuciyarta in banda turniƙi da tafarfasa ba abunda ta ke yi.

Ganin yadda har zuwa wannan lokacin Abban ya kafeta da Idanuwa yana mai ƙarasawa zuwa inda suke ne ya sanya ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa da sauri, kafin kuma ta cikawa
Imam ɗin Hannu.

Abban yana ƙarasawa
Imam ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi, bayan sun gaisa ya ɗaura da cewa
“Abba ai da ka bari mun ƙaraso,
dan yanzu dama na ke shirin in yi wanka mu karaso wajen naka.”

“kada ka damu, ai
babu nisa, kuma Ina buƙatar yin tattakin nima”
Haka kawai Abban ya ce ya na kallon Khadijah wadda ta ke gaishe shi da “ina wuni”
Cikin ɗan russunawa.
Bai amsata ba, ya juya ya bi bayan Imam wanda ya juya ya nufi ƙofar parlourn nasu da ɗan sauri yana ce wa “Bismillah Abba.”

Bayan sun shiga ciki, Abban ya zauna, Imam ɗin ne da kansa ya shiga kitchen ya kawo masa lemo mai sanyi da ruwa sai snacks a gefe, dan Khadija ba ta riga ta shiga parlourn ba ta na waje ta na ta faman lissafe-lissafe, hankalinta chaa ya tashi dan tabbas
a yadda ta ga Abba a wannan lokacin ta san ba zai bi bayan ta ba!
Sannan ba ɗaga mata ƙafa
zai yi ba, gashi ta san Abban nasu in ya ƙule sam ba ya tolerating nonsense da tirjiya…
‘Za ta iya cewa ba ta taɓa ganin soyayyar ƴa da uba mai zafi kala ta Abban da sister ɗinta ba amman tunda sistern nata ta yi masa laifi ya fita harkarta shikenan ya yafe ta
har gobe ita kanta ba ma ta san inda ƴaruwar tata take ba.’

Shiyasa hankalinta ya ke a tashi maƙura, har ba ta san lokacin da ta soma kuka ba. Tsoronta ɗaya kar ya goyawa Imam baya kuma ya kafe akan itama sai ta bi ta yarda da abunda Imam ɗin ya ke so
dan in dai hakan ta faru
tou wallahi ta shiga ukun ta.

Ita kanta ta san ta na da tsananin kishin da ko da ace ba Imam ta aura ba to fa ba ta jin za ta iya zama da kishiya, ballantana
kuma Imam ɗin ne, Mutumin da ta ke da tabbacin a yadda ta ke masifar sonshi tabbas ba za ta taɓa
iya jurar ganin wata ƴa Mace a matsayin Matarsa ba, bayan ita babu kowa kawai, sannan daɗin ɗaɗawa kishiyar ma ace wai ‘Khadija’
Yarinyar da ta san ya ba tsananin so da ƙauna!
Ko satin da ya wuce haka nan ya fito ƙiri-ƙiri
ya ce mata ‘albarkacin sunan su ya zo ɗaya ita da Khadijarsa ne ya sanya ya ke yi mata raha sannan
ya ke ɗan kulata.’
…….
Ta san rashin shigarta a kan lokaci
zai iya sake hasssala Abba, dan haka ta yi ƙoƙari da kyar ta iya tsayar da kukan nata, ta
goge hawayenta, tukunnan
ta nufi parlour itama.

Abba ya na zaune a kan kujera
Imam a gefen shi, zaune a ƙasa

A haka ta shiga ta samesu,
dan haka itama ta ƙarasa ta zauna a ƙasa ta ɗayan gefen ƙafar Abban.

Ba tare da ya kalleta ba, Abban ya ce
‘’Sai yanzu ki ka ga daman shigowa kenan “
Bai bata damar cewa komai ba
ya ɗaura da cewa
‘’Inaso ki nutsu ki ji abunda zan fada miki yanzu….
Na farko shawarace!
Na biyu ma kamar shawarar ta ke!
Sai na uku kuma umarnine daga gareni wanda ya zame miki
dole ki ji, sannan ki yi.”
Still bai ɗau lokaci ba ya ɗaura da cewa
‘’Idan Mata uku Imam ya ce zai ƙaro to baki da hurumin shiga cikin lamarin da zummar hanawa”
‘’Ki zauna a matsayin ki
sannan ki yi wa Mijinki biyayya, ki kuma bashi goyon baya.
Ni ma a matsayina na Mahaifinki
ki yi mini biyyayya ki yi abunda na ce.
Sai da ya jaa numfashi ya sauƙe tukunna ya ce
‘’Khadijah”
Wanda hakan ya sanya ta ji gabanta ya yanke ya sake faɗuwa, ba ta kai ga dawowa dai-dai ba Abban ya ɗaura da cewa
“Imam zai ƙara aure!
Ba na son in ji wata matsala ta kuma kunno kai daga gareki daga yau har a yi auren nan a gama
Idan ba haka ba kuma wallahi …..’’

Kukan da ta rushe musu da shi tamkar ana yankata ne ya sanya duk su ka zuba mata ido kawai, su na kallon ikon Allah.
Cikin kukan ta ce “Haba Abba,
ko fa wata na biyu ban gama rufawa a cikin gidan nan ba amma
ace za a yi mini kishiya!
Kuma ku ce in yi haƙuri in yi shiru?.
Shi mai ya sa ba zai yi haƙurin ba, mai ya sa ba zai haƙura ba?.
Daddy fa ya ce bai yarda ba, ya ce ba ya ma son ya sake jin maganar. “

Cikin katse ta Abban ya ce
‘’A lokacin da Daddyn bai san cewa ita wachchar Khadijar Imam ya fara so ba kenan…a lokacin da bai san itace budurwarsa tun asalin farko ba…
Bari ki ji abunda ba ki sani ba, tun kafin shi Daddyn ya fara maganarku Ke da Imam, tun a lokacin shi Imam ya yi mini maganar Khadija!.
Maganar aurenku ke da shi ce ta sanya ya ɗaga ƙafa dan haka yanzu banga dalilin da zai sanya ya fasa aurenta saboda ke a karo na biyu ba wallahi”

Cikin kuka ta ce
‘’Abba har fa ciki ta zubar, kuma
tsabar cin fuska har gidan nan ya kawo mini ita, lokacin ko sati biyu ban yi ba, a chan boys quarters ɗin aka yi jinyar ta!
Saboda bata da kowa.
Fisabilillahi ta ya za a haɗa ni kishi da wadda ta gama shigo mini gida ta san sirrina, wadda batta da iyaye,
mai yawo a titi suna tallan Nono
…..’’

‘’Ya Isa haka, Khadijah”!.
Abban ya daka mata tsawa cikin tarar numfashinta.

Kafin ya ce
‘’Tashi ki tafi ki bani guri‘’

Za ta yi magana ya kuma daka mata wata uwar tsawar dan haka ta miƙe ta wuce zuwa ɗaki tana wani irin kuka.

Ko da ta shiga ɗakin ma
ta jima ta na kukan, kafin daga karshe ta yanke shawarar neman
‘Larai’.
Saboda ta lura hatta Mahaifiyarta ita ma bayan Abban ta ke bi….
Iyayenta su na da matukar kawaici da kara, duk an san Imam ba ya son ta!
Biyayya ce ta sanya ya aureta,
shiyasa su kuma iyayen nata ba za su taɓa goyon bayan ta ba
saboda gudun kar su shiga hakƙinsa..kuma sosai su ke gudun dasa matsala tsakaninsu da ‘Family friends’ ɗin nasu, shiyasa duk wani abun da zai buɗe wannan ƙofar ba sa ƙaunarsa sam.
Chapter 1 · 0% Book details