Sashe 8
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Manu ta ce
‘’Allah ya ƙara sauƙi.’’
Kamar Muhsin zai fashe da kuka haka nan ya ɗago ya kalli Manubiyan kafin ya ce
‘’Adda Manu, sai da fa ta kuma suma da ki ka tafi makaranta ɗazu’’.
Shiruu ta yi chan kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa,
wanda hakan ya bawa hawaye damar fara gangaro mata…
Haka ita ma Jidda ta sunkuyar da kanta ƙasa
ta fara nata kukan…
Ganin hakan ne ya sanya shima Muhsin ya fara nashi kukan….
Haka nan suka tusa Baba a gaba kowa ya na hawaye.
A hankali Baba ya zaro wayarsa daga aljihu ya danna kiran Ya Musbah…
Kamar ɗazu yanzun ma wayar a kashe!
dan haka ya ɗago ya kalla Jidda bayan ya maida wayar cikin aljihun malun malun ɗin da ke a Jikinsa ya ce
‘’Maijidda kikace ɗazu ya ce miki
Mu jira shi zai zo ko?’’
Sai da ta ɗan yi shiru tukunna a hankali ta gyada masa kai sannan ta ce
‘’Eh, Baba.’’
Tsaki ya yi daga haka ya miƙe tsaye ya ce
‘’Muhsin taso mu je .’’
Da sauri Jiddan ta ce
‘’Baba ka bari ni in sake komawa, in dubo shi, ba sai ka je ba.’’
Kallon ta ya yi kamar ba zai ce wani abun ba
Sai kuma ya ce
‘’kar ki damu!
yanzu za mu je mu dawo
InshaaAllah…
Ina son ganawa da shi.’’
Daga haka ya kalli Manubiya ya nuna mata gurasarta wadda suka ajjiye mata a cikin kwano ya ce “ki tabbatar kin ɗauka kin ci.”
Sannan ya sa kai ya fice cikin tafiyarsa da ke baiyyana nakasar da ke tare da shi, dan ƙafa ɗaya gareshi yayinda ɗayar ta kasance ta roba.
Ya na fita Muhsin ya mara masa baya da hanzari, dan shi ma Yaron
hankalinsa a mugun tashe yake, Allah Allah kawai yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti, dan jikin nata ya tsorata kowa!
Babba da Yaro.
Suna fita Manubiya ta miƙe ta cire hijabin Jikinta.
Daga haka ta ƙarasa inda su Innar su ke, (ita da jidda).
Sai da ta tabbatar innar bacci ta ke yi tukunna ta kalli Jiddan ta ce
‘’Mai ya faru ɗazu da kika je gidan?
kin gan shi?’’.
A hankali Jidda ta share hawayen da su ka zubo mata.
Kafin ta shiga koro mata bayanin
yadda su ka yi….
Da yadda Ya Musbah ya ce kawai ta zo gida, su jira shi.
Gashi kuma har yanzun bai zo ba.
Shiruuuuu, duk su biyun su ka yi!
Ko wacce zuciyarta babu daɗi.
Suna kuma tunanin a ina za su je su samo kuɗi!
Dan sun san tunda Ya Musbah ya fara wasar ƴar ɓuya da su
tou shima bashi da yadda zai yi ne.
A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya, ta san zai taimake su.
………
A ƙofar gidansa su Baba su ka hango shi.
Kamar wani saurayi haka yanayi da jikinsa ya ke, sam bai yi kama da magidanci ba.
Fari ne sol kyakkyawan gaske, bai cika tsayi ba amman yana da faɗin ƙashi.
Cikin sanyin jiki Baba da Muhsin su ka ƙarasa inda Ya Musbahn ya ke
alwallar sallar Maghrib ɗin da ta gabato, shi da wani maƙwafci kuma Abokinsa mai suna ‘Nafi’u’.
Cike da girmamawa
shi da Abokin nasa
su ka gaida Baba.
Kafin Abokin ya cewa Ya Musbah
‘’Bara in wuce.
In fara karatu kafin ku kammala.’’
Jinjina kai kawai Ya Musbah ya yi, dan gaba ɗaya hankalinsa a mugun tashe ya ke, ga shi ya ga Baban sai wani irin kallo ya ke ta yi ma sa
wanda ya kasa gane ma’anarsa.
Rashin sanin abun yi da kame-kame ne su ka sanya shi cewa
‘’Bismillah Baba
Mu shiga daga ciki ko?’’
Sai da Baban ya sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya ce
‘’Naa shiga kuwa?’”
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’to ko soro ne ka shiga dan Allah.
Akwai bayanin da na ke so in yi maka ne.”
Ba dan Baba ya so ba!
Ya Kama Hannun Muhsin su ka bi bayan Ya Musbah.
Anan soron kuwa ya shimfiɗe musu tabarma…..
Dan a wannan lokacin bai isa shigar da su cikin gidan ba!
Daff da zuwan su Baban
Nafi’u ya gama yi musu shari’ah shi da Baraka!
Saboda kawai Jidda ta zo ɗazu, shikenan tunda Yarinyar ta zo ta tafi Baraka ta ke ta bambami
‘Wai ta zo har gida ta yi mata rashin kunya!!!!’
Kuma sarai ya san ƙarya ta ke yi!
Kawai ta na neman hanyar da za ta bi ta datse zuwan ƴan uwan nasa gidansa ne!
Gaba ɗaya.
Bayan a yanzu kamata ya yi ma ace shi ya ke riƙe da Jidda ko Manubiya…..
‘’Tunanin mai ka ke yi???’’
Muryar Baba ta Katse ma sa tunani.
A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya!
Ya na shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa
‘’Innar ku har yanzu ta na kwance,
babu kuɗin magani, babu na zuwa asibiti.
Musbahu!
Kai ne ka hanani aikin ƙarfi,
Sannan kai ne ka ce ƙannen ka Mata ba za su yi Aikatau ba wanda ba daban hakan ba na san da yanzu mun san yadda mu ka yi
aka kai ta asibiti.
Tun shekaran jiya mu ke ta tsammanin ka!
Ka kashe wayarka kuma
ka ƙi ka yarda ka zo inda muke.
Wanda in m kuɗaɗen ne ba su samu ba a gani na dai a ya kamata ace ka zo ka duba Mahaifiyar ka dai ko?’’
Cikin yin ƙasa da murya sannan a hankali Ya Musbah ya ce
‘’Baba, kalli fa ƙafar ka. Ba za ka iya aikin ƙarfi da ita ba!
Ina tsoron ka saka mata nauyi da yawa haka nan mu je Itama ƙwaya ɗayar wadda ta rage maka ya zamana itama ta samu matsala.
Su Manubiya kuma
ba wai girman kai bane ya sanya na ce ba za su yi aikatau ba!
Kawai a ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa ɗaya
amman ace ƙanne na Mata su ne za su na kula da iyayena, ba.
Dan Allah Baba ka yi haƙuri,
ka bar maganar dakon da ka ke so ka yi, da duk ma wani aikin ƙarfi.
In sha Allahu zan yi ƙoƙari in san yadda za a yi.
InshaaAllah zan iya kula da kowa.
Kuɗin asibitin ma na nemo, ba wai ban nemo ba!
Amman sai jikin Baba ƙarami ya ɗan mot……’’
Shiru ya yi kafin ya ci gaba da cewa
‘’Amman karka damu
Nafi’u ya yi wa ɗan uwansa magana kuma ɗan uwan ya ce
za’a san yadda za ayi…
Mu jira shi zai kawo kuɗin. Shiyasa ma ka ga ban zo ba saboda
bana so in zo muku ba tare da kuɗin ba. Shi nake ta jira na fi so in ya zo ya bani ni kuma sai in zo
a kaita asibitin‘’.
Sai a sannan
Baraka wadda ta laɓe musu tun ɗazu ta shigo cikin soron.
A hankali ta ƙarasa inda su ke ta zauna!
Cikin ladabi ta gaida Baba. Inda ya
amsa mata da Kulawa ya na mai tambayarta “Ina takwaran sa” ta ce
masa “yana ciki yana barci.”
Da ladabi Muhsin ya gaida ita
ta amsa daga nan soron ya ɗauki shiruuuuu,
kafin a hankali sautin kukan Baraka ya soma tashi.
Da sauri Baba ya ce
‘’Subahanallah,
Baraka lafiya?
Mai ya faru?”.
Cikin kukan da kyar ta ɗan tsagaita sannan ta ce
‘’Ba komai Baba, ba komai. Ku yi haƙuri, suɓuce mini ya yi.’’
Tana gama faɗin haka ta fara ƙoƙarin miƙewa.
Cikin ɗan tsare gida Baba ya ce
‘’Koma, koma
Baraka.
Koma ki zauna’’.
Ya bata umarni
ransa duk babu daɗi.
A hankali ta koma ta zauna ta na ɗan satar kallon Ya Musbah wanda ya haɗe rai!
Yana ji kamar ya rufe ta da shegen duka.
Cikin kulawa Baba ya shiga rarrashin ta….
Har sai da ta yi shiru tukunna ya nemi ta faɗa masa me ke faruwa.
Cikin yin ƙasa da murya ta fara zaiyyane masa cewa
“dama kwanakin baya ne Ya Musbah ya karɓi kuɗinta, kuma itama kuɗin ba nata bane ba
na wata ƙawar Mamanta ne
To a halin da ake ci
Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biyan rabi shine ƙawar ita Mahaifiyar tata ta ce ‘za ta je da ƴan sanda ta tafi da Mahaifiyar tata’.
Tun jiya ta ke bin Ya Musbah akan ya bata kuɗin shi kuma ya ƙi ya bata,
yanzu gashi ƴan sandan sun je za’a tafi da Mahaifiyarta.….”
Shiruuu Baba ya yi,
da jin batun Baraka.
Kafin ya miƙe tsaye ya kama Hannun Muhsin.
A hankali ya kalli Ya Musbah ya ce
‘’Musbahu, idan an kawo kuɗin da akayi maka alƙawari ka bata.’’
Da sauri Ya Musbah ya ce
‘’Amman fa Baba..’’
Cikin katse sa ya ce
‘’Bana son musu!
Sannan bana son ja-in-ja!
Ka bata kawai.
Kar ka damu, zan san abun yi ‘’.
Tukunna ya kalli Baraka
wadda ta yi kalar tausayi ya ce
‘’Kar ki damu, ba za a tafi da Mahaifiyarki ki ba.
Inada mara lafiya a gida, shiyasa ba zan iya bin ki mu je in ga komai ya lafa ba.
Yanzu ki yi sauri ki je wajen ta, Musbahu zai biyo ki da kuɗin
InshaaAllah.
In basu cika ba ma
In na san yadda nayi na haɗa kan ƴan kuɗaɗe na kashe wutar gaba na…
Ki yi mini magana sai in cika miki ‘’.
Yana gama faɗin haka ya jaa Hannun muhsin su ka fice daga soron.
Cikin ɓacin rai Ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun
sai kuma kawai ya miƙe shima ya fice!
Ya bi bayan Baba ranshi a mugun ɓace!.
Yaso ya fahimtar da Baba
a samu
ya yi haƙuri ya karɓa kuɗin ya bar batun Baraka!
Amman furr Baba ya ƙi sauraron sa, karshe ma faɗa ya rufe sa da shi!
Sannan ya ce “ya koma kar wanda zai kawo masa kuɗin ya zo bai same shi ba,
kuma Wallahi idan ya sake karɓarwa Baraka kuɗinta sanna ya hana ta tabbas ransa sai ya yi mugun ɓaci.”