Sashe 31
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana zuwa wajen ana shiga sallah, sanin halin Sir Najeeb d’in ne ya sanya sai da ya je office d’in nasa ya tabbatar da baya nan tukunna ya nufi masallacin shima.
Yana shiga ya tarar da shi a sahun gaban sa.
Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar la’asar ana idarwa shi da wasu a cikin masallacin da suka rasa raka’a suka tashi domin ramawa masu addu’a kuma suna yi.
Yana idarwa shima yayi addu’a ya shafa daganan ya zauna zaman jiran Sir Najeeb
yana mai ha’dawa da adduar ‘Allah dai yasa ba wani laifi ya kuma yi ba’
dan bayan class rep in dai ka ganka a office d’in Sir Najeeb to ba k’aramin abu bane ba.
Ko wani abun ne ma kake da buk’atar yi ko gaya masa to daman an san ka’idarshi’ka gayawa class rep shi kuma ya fad’a masa’….
Ganin fitar sa ne ya sanya
Abbakar d’in mi’kewa da sauri ya bi bayan sa.
A bakin office d’in nasa suka had’u yana k’ok’arin bud’ewa dan haka yana bud’ewa suka shiga tare Abbakar ya shiga da sallama sannan ya shiga gaida shi da ladabi.
Cikin nutsuwa ya amsa masa
yana mai neman guri ya zauna akan d’aya daga cikin
sofa d’in dake a office d’in kafin ya d’ago ya kalle sa
ya ce ‘’d’an zauna.’’
Cikin d’an d’ari-d’ari Abbakar ya nemi waje ya d’an d’osana mazaunansa ya yi shiruu,
zuciyarsa tana masa sak’e-sak’e kala-kala.
Shiruu shima Najeeb ya yi yana tunanin ta ina ma zai fara ne,
Wallahi ba dan Yashjub bane Allah da babu abunda zai sa ya yi wannan abun
haba!student d’insa fa abun ya yi wani iri da yawa, amma ya ya iya dole ya daure ko ba komai shima yana so ya ga Yashjub ya yi aure, kuma tunda har ya ga Yashjub ya zo ya same sa a kan maganarta tou kuwa ya san abun na gaske ne, wanda hakanne ya sa shima ba zai yarda ya ɗauki batun da wasa ba.
Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an yi gyaran murya
wanda hakan ya sanya Abbakar ya mik’a masa
dukkannin hankalinsa.
Cikin nutsuwa Najeeb ya ce
‘‘Akan wannan ƙawar taka na kira ka, Manubiya”
Shiruuu Abbakar d’in ya yi da farko
kafin a hankali ya ce ’’Ok,Sir.’’
Dan zuwa wannan lokacin
Kwakwalwarsa ta gama bashi
amsar dalilin kiran da aka yi masa.
‘’Tana da wata matsala ne?,as in family issue besides rashin lafiyar Mahaifiyarta?’’
..
Manubiya ƙawarsa ce da yake yi mata kallon kamar ma ta zama ƴar uwa, a ganin sa bai kamata ya kunce mata zani a kasuwa ba.
Dan haka ya ce
‘’A’a rashin lafiyar Maman nata ne kawai issue d’in ta’’.
‘’Shiyasa take kuka kusan kullum a class?’’
Sir Najeeb ya sake jeho masa wata tambayar cikin katse sa.
Shiruu ne ya d’an biyo baya kafin Sir Najeeb d’in ya ce
‘’Kamar yadda na fad’a muku the other day
Malamai kamar iyaye su ke,
a yadda na ke ganin ta so disturbed (a dame) kullum na yi tunanin tana da financial issue ne.
Am na san ba hurumin mu bane
but Aboki na wanda ka ganmu tare ne yake da offer na aiki very simple wanda Mace ko tsoho za su iya yi…”
A Ta’kaice Sir Najeeb ya yi wa Abbakar bayanin aikin da ya ga damar had’awa a kansa a take a wannan lokacin kafin ya d’aura da cewa
‘’Na yi tunanin tana da financial problem shiyasa na ce mishi akwai wadda zan nemo ta yi mishi aikin but tunda ka ce ba haka bane ba shikenan zan ce mishi ya nemi wata kawai’’.
Shiruuu Abbakar ya yi, ya hau tunani…...
‘Tabbas ya san Manubiya za ta yi farin ciki da offer d’in nan, to amma kuma….’
Cikin katse masa tunanin Sir Najeeb ya ce ’’Shikenan, u can leave, dama reason d’in kiran naka kenan’’.
Duk da b’oye-b’oye da kwana-kwanar da Sir Najeeb yayi tashi d’aya Abbakar ya fahimci inda suka dosa daga shi har Abokin nasa, hakan ya sanya ya shiga tsaka mai wuya dan on the other hand, no matter how (a ta wani fannin, duk rintsi)…ko ma menene yake ji yake kuma tunani to fa bai kamata ya yi wa Manubiya bak’in ciki ba!
Besides (baya ga haka ma) shi a rayuwa da ko da yaushe yana saka farin cikin ta ne a saman nashi..
Dan haka ya ɗan gyara zama!
Da kyar ya iya danne zuciyarsa ya d’ago manyan fararen idanuwansa waenda suka d’an fara surkuwa da kalar ja ya ce ’’za ta yi, baku da matsala za ta yi cikin farin ciki ma, in sha Allah.’’
Yana gama fad’in haka ya maida kansa k’asa.
Har cikin zuciyarsa ya yi wa Manubiya farin ciki da samun wannan aiki dan daga gani mai tsoka ne, ya san zata rage damuwa kwarai sannan za ta yi maganin matsalolinta, duk da kuwa ya riga ya san akwai wata ɓoyayyiyar manufa a bayan aikin da aka bata, amma dama tun ba yau ba ya dad’e da yankewa ‘indai rana mai kama da ta yau ta zo, to ba zai bari zuciyarsa ta rinjayi tunanin sa ba’.
Ya san ba wai Sir Najeeb d’in ne yake son ta ba amma shakka babu kamar yadda ya lura da itama ta tab’u da ganin wannan Abokin nasa haka zalika shima Abokin, tunda gashi ya fara fakewa da bata aiki…..
A hankali ya fesar da iska a ransa yana sake jaddadawa kansa cewa ‘’inshaaAllah, ba zai tab’a bari shirme da mafarkinsa su shiga tsakanin Manubiya da auren wannan Mutumin ko aikin da ta samu ba..’’
A b’angaren Najeeb shima shiruu kawai ya yi yana nazartar Abbakar d’in kafin daga baya ya ce ’’ok,ga katin friend d’in nawa, idan ta shirya sai ta kira shi ta ce masa itace Manubiya Musa wadda za ta yi masa aikin da Najeeb ya ce zai had’asa da wadda za ta yi’’.
Ya fad’i hakan yana mik’awa Abbakar katin.
A hankali kamar marar lakka a jiki Abbakar ya mik’e ya k’arasa ya je ya amsa, sannan ya ce
‘’Mun gode kwarai Sir,Allah ya k’ara d’aukaka da arzik’i, Allah ya ji k’an magabata’’.
A hankali Najeeb yayi murmushi ya ce
‘‘Ameen Abbakar, ta kira soon’’
‘‘In sha Allah’’
Abbakar d’in ya ce da murmushi kwance akan fuskarsa.
Daga nan Sir Najeeb ya sallame sa suka yi sallama ya tafi…
Tashi ɗaya!! Najeeb ya gama fahimtar komai game da Abbakar amma ko hauka ya ke yi ko da wasa bai isa ya gayawa Yash ba! dan ya san zai kunno fad’an da ba lalle ya iya kawo k’arshen sa ba ne, saboda a yadda ya ga kishi k’arara a Idanun Yashjub ɗazu ya san tabbas in ya bari ya ji wannan batu to fa sai ya raba su ko da bala’i ne. Shiyasa ya bari akan ba zai fad’a mishi ba, shi ya san
ta yadda zai bi ya taya Abokin nasa akan Abbakar da komai ma
In sha Allah komai zai tafi normal..
Abbakar kuwa abubuwa biyu ne suka had’e masa na farko damuwar sa wadda yake ta k’ok’arin b’intikewa wadda ya ji mamakin yadda ta ke shirin cin galaba akansa na biyu kuma farin cikin ta ya Manubiya murnar samun riba biyu da ta yi na aiki da masoyi in sha Allah.
A hankali yayi murmushin da ya fi kuka ciwo a chan k’asan zuciyarsa yana adduar ‘Allah yasa yadda ya tsara yake kuma tunani ya tafi yadda ya ke zato, Allah yasa yadda yake tunanin zuciyarsa zata huta zata samu nutsuwa idan Mannubiya ta yi auren ta, hakan ya kasance. sannan Allah kar yasa yayi da na sanin wannan ƙudirin nasa da ya yanke .’.
Hakanan ya na tafe yana tunani ya nufi gate dan ya san dama ta riga ta tafi gida tun ɗazu, ya san zai ga farin ciki a kan fuskarta in ta ji labarin aikin dan haka yake ta sauri domin ya je ya sanar mata saboda ba kad’an ba yake kwad’ayin ganin wannan farin cikin nata.
Duk da yadda yake fargaba amma hakan bai sanya ya ji zai fasa ba dan ya fi bid’ar ganin farin cikin ta da walwalar ta sama da komai…..
Adaidaita ya samu ta kai shi har k’ofar gidan su Manu
amma sai Jidda ta ce masa
‘’Da ta dawo jakarta kawai ta ajjiye ta yi alwallah ta nufi gidan Ammi.’’
A k’ofar makeken gate d’in ya tsaya
ya d’an buga kad’an..
Dakyar, bayan mai gadin ya ji buk’atar shi ya yadda zai je ya kira masa ita dan a cewar sa k’a’ida ne sai an fad’a a day before (ana i gobe) tukunna visitors suke zuwarma masu aikin gidan.
Ba a yi 5minutes ba
Manubiya ta d’an lek’o da fuskarta ta k’aramar k’ofar gate d’in, suna had’a ido ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
‘’Ashe da gaske kai d’in ne’’.
Ta fad’i hakan tana mai fitowa daga gidan gaba d’aya..
…..
Ahankali cikin tsananin sanyin jiki ta fito ta tsaya tukunna tace “Na yi mantuwa ne? ko handout aka bada?’’
Sai da Abbakar ya fesar da iska tukunna ya ce “yau dai na tabbatar da duk abun da yake sanya ki tunani kike ta faman b’oyemin for the past few weeks (kwanakin da su ka shuɗe) a gidan Ammi ya ke, meye ne Manu?
Akwai abun da take yi miki na cutarwa ne?’’
Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce
‘’Kawai na gaji ne, shiyasa ka ga haka.
meyafaru ance kana nema na wai ka ce it’s important,ko?’’
Ta yi mishi tambayar cike da son kaucewa tambayar ta shi dan bata san amsar da zata bashi ba.
‘’Manu yau fa ba zaki kaucemin ba wallahi sai kin fad’amin damuwar ki.’
Ya fad’i hakan yana mai zama akan tebur d’in dake anan ta gefen gate d’in Kad’an
Kafin ya sake cewa
‘’Sam ba haka mood d’in ki (yanayinki) yake ba lokacin da muka rabu da ke d’azu-ɗazun nan a school,so definitely (dole) anan gidan ne kike da damuwa.
Talk
Ki gaya min mu nemo mafita kafin ya zamana lokaci ya ƙure.
Kinga ba inda ma fa zan je har sai kin fad’a min, kin dai sanni da naci ko?’’