← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 84

Sashe 50

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nutsuwa ya d’an k’ura mata idanu kafin ya ce ‘’shine kika kasa yi mini ko da message ne?’’

D’an turo Baki ta yi tukunna ta ce ’’Ya Najeeb daga shigowata sai fad’a?
To raina ne a b’ace tun safe, da kyar na yi abunda na fita yi d’in ma’’

…Ya’isha tana yi masa abubuwa da yawa masu zafi yana kau da Kai amma na yau ya yi mishi ciwo sosai!!
Wato
ranta ne a b’ace kuma ba ma shine ya yi mata laifin ba laifin wani ne ya shafe sa shiyasa ta gagara d’aukar wayarsa!
shi yana chan yana ta tunanin ko maybe fushin da ta Saba yi da shi ta yi ashe abun ba haka bane ba wani sabon iya shege ne ta fito da shi…

Bai sake cewa komai ba haka kawai ya mik’e ya ce mata ‘’Allah bamu alkhairi’’
daga nan ya sa Kai ya fice.

Bata damu ba, kanta tsaye ko alamar nadama ko tunanin ta bashi hak’uri babu, haka nan ta ce ‘’sai anjima’’kawai,
saboda ta riga ta san ba zai ma iya kwana biyu bai neme ta ba.

Yana ficewa ta nufi sama a gigice….
direct d’akin Kausar ta nufa, tana shiga ta tarar da ita tana waya da Yasira, cikin tsananin tashin hankali ta ce ‘’she’s still here(har yanzu tana nan),
bata tafi ba har yanzu, how?(ta ya hakan ta faru?)”.

Numfashi Kausar ta fesar kafin ta ce “ba ki fi
Mu tashin hankali ba, ki nutsu ki zo ki zauna ki ji”.

Da kyar ta nemi waje ta zauna Jikinta har ɗan karkarwa yake yi, daganan Kausar ta saka wayar a hands free suka shiga magana da Yasirar har ita….

……..Thursday……..

Cikin ikon Allah
jikin Inna da sauk’i sosai, dan har zama tana iya yi idan an zaunar da ita, kuma tana iya cewa “eh” da ‘a’a’,
wanka ne dai da ragowar abubuwa har yanzu sai an yi mata.

A b’angaren Baba shima ya siyo musu buhun shinkafa, katan d’in taliya da macaroni, mai da maggi da tomato paste katon biyu.

Rabon da su Manubiya su shiga farin ciki irin haka har sun manta, sai dai kuma suna d’an fargaba dan basu san a inda Baba ya samu kud’in ba, ba kuma yadda ba su yi da shi ba amma ya ƙi gaya musu kawai dai ya ce musu “ba bashi ya ci ba!”
k’arshema da suka dame sa da tambayoyi sai ya rufe su da fad’a.. dan haka suka hak’ura suka ja bakinsu suka yi shiruu.

Ba yadda ba su yi da Ya Musbah ba akan ya d’an d’iba kayan abincin ya kai gidansa shima amman sam ya k’i yarda yak’i d’iba!
A cewar sa ‘idan bai kawo ba to bai kamata ya d’auka ba kuma ai yanada aikin yi
Alhamdulillah suna samu su ci su sha suma, yanzu kam ba laifi.’

Ba dan sun so ba haka suka hak’ura suka barshi dan ya dage akan ba zai d’iba d’in ba…
gaba d’aya tausayin d’an uwan nasu sukeji especially yanzu da matsalar kud’in haya ta sako sa a gaba,
k’iri-k’iri ya hana su gayawa Baba da Inna, dan su ce musu ya yi ya biya saboda gudun kar ya d’aga musu hankali,
su Jidda ne kawai suka san bai biya d’in ba, mai gidan ya d’aga mishi hankali a haka ma Ya Nafi’u ya bashi dubu hamsin ya bayar yanzu sauran sabain, shiyasa su Manubiya suka gama deciding ita da su jidda akan tana d’aukar albashinta za ta ba sa ya bayar, ta san dole yanzu haka yanata fafutuka dan haka wataƙila ya samu ya had’a kan 40 d’in saboda tun wachcharr shekarar da ya biya dama ya fara shirye-shiryen biyan na wannan shekarar..

Allah sarki, bawan Allah duk ya rame, farar fatarsa mai shek’i da kyan gani ta d’an yi duhu
fuskar nan hanci ya k’ara tsayi! idanuwan sun sake fitowa zurr!
Hakan ya sanya gaba d’aya suke tsananin jin tausayin shi, dauriya kawai suke yi dan ba sa so su karaya su nuna mishi ne su je su kashe mishi kwarin guiwar….

A b’angaren Ya Musbah kuwa, kud’in haya bai d’aga masa hankali ba kamar yadda Baraka ta d’aga masa hankali!
gaba d’aya ta birkice mishi musamman ma kwana biyun nan, rigimar yau daban ta gobe daban! yanzu haka ta d’aga masa hankali akan wai k’awayenta y’an unguwar su na yi mata gani-gani,
a ganin ta bai kamata ya ci gaba da wanki da guga ba saboda za ‘a raina ta, wai an yi bikin k’anwar wata k’awarsu ba a gaiyyace ta ba saboda tana a matsayin matar mai wanki da guga,
Dan haka ya nemi wata sana’ar amma gaskiya ba wannan ba!!!
ya yi low class da yawa.

Shi kuma Ya Musbah da wanki da gugan ya ke samu ya ke ciyar da iyalin nasa yake rufawa kan shi asiri, shiyasa ya k’i hak’ura, ita kuma ta dage….
hakan ya sanya kullum cikin fad’a suke ita da shi, bai san ya zai yi da ita ba dan in ya bar wanki da gugan ita ce ta farkon fara d’aga masa hankali.
Gashi yanzu ta tsiri wani salo wai tana da low bp dan haka miyar ta kullum dole sai an saka mata nama a ciki sannan sai ya siyo mata maltina,
yanzu haka ta koyawa me sunan Baba shima
Idan babu nama a abinci to ba zai ci ba sannan shima in be sha maltina ba to fa ya dinga zunduma musu ihu kenan duk makwafta sai an jiyo su.

Ya Musbah yanada guilty conscious (. )hakan ya janyo masa muddin ya
siyawa Baraka nama da maltina to hankalinsa baya tab’a kwanciya har sai ya siya ya kaiwa Inna da Baba suma ko kuma ya bawa Baba kud’i ko ya siya wani abun ya kaiwa su Manu….
Shiyasa gaba d’aya ya
sake zugewa wani lokacin ko abinci baya samu ya ci dan babu enough..
Kuma kullum idan ya fita aiki tun safe sai dare yake samu ya zauna ya d’an huta.

Tun suna Yara yake son Baraka,
ba dan ragowar birbid’in son da yake yi mata ba da kuma darajar me sunan Baba wallahi da tuni ya sallame ta, ya gaji!
har ga Allah Baraka ta kai shi bango a kwanakin nan,wayar
hannunta kad’ai abar kallo ce
amman ta siya maggi guda d’aya a gidan aiki ne babba a gareta,
ta gwammaci ta dame sa a waya idan me sunan Baba ya fara kukan yunwa.

Ba abunda ya fi sake bak’anta masa rai irin yadda ta raina iyayensa,
Kwanaki baya
Yayan Nafi’u ne ya yi hatsari
dama ba shi da Mata (gauro ne)
Dan haka
yana gida a kwance ba lafiya…
irin girkin da Matar Nafi’un Aisha ta yi ta tafi dubiya sai da ya bashi mamaki dan ranar shima har zubo masa aka yi, tun daga nan kuma bata yin sati ba ta je ta dubo sa ba, hatta Inna..Aisha bata
yin sati bata je ta duba ta ba..
amma ita Baraka ta ce su Manubiya sun raina ta kuma ba a ganin girmanta a gidan, tunda Inna ta fara rashin lafiya sau d’aya ta je ta dubata
lokacin tana asibiti kuma shima sai da yayi da na sanin zuwan nata,
k’iri k’iri ta hana k’annensa zuwa gidan kuma itama bata zuwa inda suke……

A b’angaren Jidda itama abun ba sauk’i dan hankalinta a tashe yake kwana biyun nan…
Ko waje da kyar take iya fita dan sai ta tabbatar kuma ta lura Ya Yusuf
baya gidan ko kuma in in yana wajen aiki, saboda ta tsorata da shi sosai tun ranar da suka had’u ya yi treatning dinta (ya yi mata barazana), ta inda ya sanar mata
‘…….Abunda suka yi masa ita da su Baba...disga shin da suka yi a gaban kowa, k’iri-k’iri suka ce basa so ta aure shi!
To ta sani ya ji zafin hakan sosai.
Kuma yana so ta yarda ta tabbatar sannan ta saka a ranta har abada yana sonta sannan bata da wani mijin bayan shi!
Dan haka ko dai ta haƙura ta aure shi
watak’il ya manta da rashin mutuncin da sukayi mishi a gaban su kaka mallan ya fasa d’aukar revenge d’in da ya yi niyya ko kuma ya kunnowa ahalinta bala’in da ba za su tab’a iya kashewa ba, wallahi.

Ta je ta yi tunani, yana jiran amsarta, ya bata kwana biyu, kacal!…….’

Shiyasa tun lokacin da kwana biyun ya cika take wasan y’ar b’uya da shi dan bata san me zata ce masa ba.
Duk da wata zuciyar tana bata shawarar ta hak’ura ta aure shi akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma ba wai iya bata son Ya Yusuf baneba
har ga Allah ko kallon shi wani lokacin bata son yi, sannan
Barazanar da ya yi mata ɗinnan ya sanya ta sake tabbatarwa ba mutumin kirki bane ba…
A ganinta rashin mutuncin Baraka ma ita kaɗai ya ishesu!! Sam bai kamata ace ta k’arawa su Baba da wani mugun surukin ba kuma du…..
matsalar su ma ta ishe su.

Gashi ya ce kar ta fad’awa kowa, ta san kuma idan ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah
tsoro takeji dan a yadda ta ga idanunsa a ranar sam bata ga alamun wasa a cikinsu ba.

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*30*

Duk da wata zuciyar tana bata shawarar ta hak’ura ta aure shi akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma ba wai iya bata son Ya Yusuf baneba
har ga Allah ko kallon shi wani lokacin bata son yi, sannan
Barazanar da ya yi mata ɗinnan ya sanya ta sake tabbatarwa ba mutumin kirki bane ba…
A ganinta rashin mutuncin Baraka ma Ita kaɗai ya ishesu!! Sam bai kamata ace ta k’arawa su Baba da wani mugun surukin ba kuma du…..
matsalar su ma ta ishe su.

Gashi ya ce kar ta fad’awa kowa, ta san kuma idan ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah
tsoro takeji dan a yadda ta ga idanunsa a ranar sam bata ga alamun wasa a cikinsu ba.
Chapter 50 · 0% Book details