← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita Kausar ta kalli Ya’isha ta ce “na san ni cousin d’inku ce amman a yadda muka taso
Ni kamar sister nake a wajen su Yash da Yassir, sab’anin Munirat dan haka ya kamata mu yi wa Ummi magana ta daina barin katuwar y’arta tana yi mana yawo tib’ir-tib’ir a gida, dan naga kamar ma tallar y’ar tata take yi.’’
Kausar ta k’arashe maganar cikin tsananin takaici tana addu’ar Allah yasa ba a yi
rashin sa’a Yashjub d’inta ya shigo by mistake ya ga Munirat a haka ba.

Murmushi Ya’isha ta yi cikin kamo hannun Kausar d’in tace’’
Kausar ki dena cewa ke cousin d’inmu ce saboda you are more than a sister ma to all of us, muna son ki muna k’aunar ki fiye da zaton ki,’’
cikin sake ruk’o hannunta ta ce ‘’bara in baki misali,‘’
sannan ta d’aura da cewa “in da ace wata ce ta yi breaking heart d’in Yassir a tunanin ki ya za mu yi mata?
k’iri-k’iri kika ce bakya son Yassir on top of that kika ce Yashjub kike so amma mu ka goya miki baya ɗari bisa ɗari ba tare da mun ji haushin ki ko mun tuhume ki ba dan haka dan Allah ki daina cewa ke cousin d’in mu ce,
ki yarda ki saka a ranki
You are part of this family and we love you,always &forever(kema ƴa ce kamar mu a cikin wannan Ahali n kuma har abada muna sonki).

ita kuma wachchar ki bar ni da ita, zan san maganin ta soon, in dai ina numfashi sai ta bar gidan nan da k’afarta walllahi..d’azu ai Yasira ta turo message a group akan labarin da uwar tata ta bayar, kin gani?’’

Tab’e Baki kausar ta yi sannan ta ce ’’eh!na gani,amman hakan ba zai chanja komai ba, dole sai ta bar gidan nan tunda babu gadon ubanta a ciki.’’

‘’Ita da uwarta’’
Ya’isha ta k’arashe mata maganar tata tana dariya.
Dariya duk suka yi kafin su ci gaba da cin abincinsu suna yi suna tattaunawa.

Duk yadda Munirat ta so ta hana kanta kuka sam sai ta kasa, tana fita hawaye suka fara tsiyaya daga idanuwanta.
Abun yayi mata ciwo sosai…
gashi Ummi tace kar ta sake mayar musu da magana, maimakon rikice tana so a ko da yaushe ta nemi zaman lafiya da su..tana tafe tana hawaye a haka har ta k’arasa d’akin Ummi…
bata tarar da ita a d’akin ba dama abunda take so kenan
dan haka ta zaro akwati ta je d’akinta na b’angaren su ta jido kayanta ta had’a komai tana gama had’awa ta kira sister d’inta ta ce mata “za ta zo ta yi mata kwana biyu…”
yayar tata tanata murna a haka suka yi sallama ta zauna zaman jiran Ummi ta samu ta yi mata sallama daga nan ta kama gaban ta..sai dai kuma Ummin tana zuwa tace bata san zance ba!!!

Ba yadda Munirat bata yi da ita ba amma Ummin ta hana ta tafiya, k’arshema sai ta rufe ta da fad’a, tana ji tana gani haka ta hak’ura ba dan ranta ya so ba…
….
Kamar kullum bayan sallar isha, sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta yarda ta bita suka sauk’a domin yin dinner.

Dama sun san yau su Daddy suna da meeting, dan haka shi da Yassira da Yashjub basu zauna dinner ba.
A dining d’in suka tarar da kowa har Yahanasu…

a kusa da Mommy Ummi ta ja kujera ta zauna da murmushi a fuskarta tace ‘’Barka da dare Mommy’’
ba yabo ba fallasa da d’an murmushi a kan fuskar Mommyn ta ce’’Lafiya Ummi ya gida ?’’

‘’Alhamdulillah’’ta bata amsa daga nan Munirat ma ta gaida Mommy da Baaba Larai da Yahanasu kafin ta ja kujera ta zauna…
sai da ta zauna tukunna ta lura ashe opposite d’in Yassir ta zauna,
ta so ta tashi amma kuma in ta tashi duk inda za ta koma to dole sai dai ta shiga tsakiyar su Kausar ne dan a rarrabe suka zazzauna, dan haka kawai sai ta hak’ura ta zauna.
Cikin girmamawa Yahanasu ta gaida Ummi ita kuma ta amsa mata da kulawa.

Tana shirin zuba abinci suka had’a ido da Yassir, a hankali ya d’an motsa bakinsa alamun ‘Hi’
D’auke kanta kawai ta yi ta ci gaba da zuba musu abinci itada Ummi.
Murmushi yayi kafin ya juya ya kalli Ummi ya ce “Ummi ina wuni’’

Da sauri Ya’isha da Baaba Larai suka kalle sa, sai kuma suka d’auke Kai suna mamaki.

Cikin jin dad’i da murmushi
Ummin ta ce
‘’Lafiya Alhamdulillah,Yassir.”

Wata kalar dariya Yasmeen ta yi ciki-ciki kamar irin Mutum yana k’ok’arin gimtse dariyarsa d’innan amma kuma ta yadda ta tabbatar da Ummin za ta ji.

Ta kuwa ji!
amma sai bata kulata ba, daga haka kowa ya shiga cin abincinsa.

Yassir ne ya fara mik’ewa yayi musu sai da safe yana ta satar kallon Munirat,
ita bata ma lura da shi ba amma Ya’isha da Yadira sun lura.

Yadira tana shirin mik’ewa
Ummi ta ce ‘’Yadira d’an zauna ina son magana da ku’’.
Kamar ba za ta zauna ba, sai kuma ta koma ta zauna ba tare da ta kalle ta ba, ta wani had’e rai ta d’auke Kai.

Kausar ko rabin abincinta bata ci ba bata da niyyar tashi da farko amma tana jin Ummi ta ce ‘tana son magana da su’
Kawai sai ta mik’e ta wuce sama.

Shiruu Ummin ta yi, kamar ta ce kowa ya tafi kawai sai kuma ta fesar da numfashi kafin ta ce
‘’Ya’isha in kun hau sama sai ku gayawa Kausar da Yassira abunda na ce…’’
Daga nan tiryan-tiryan
haka nan Ummi ta zaiyyano musu labarin senator da Munirat kamar yadda ta gayawa su Daddy kafin ta d’aura da cewa ‘’Munirat ba za ta tab’a auren shi ba, dan in da ace zan bari ta aure shi to da tun lokacin da ya dawo an d’aura musu aure, ballantana kuma yanzu da yake a matsayin saurayin Yahanasu.’’
cikin lallami Ummi ta ce
“Dan Allah komai ya wuce, let bygones be bygones(a bar baya ya zamto baya).”

‘’Ummi komai ya riga ya wuce,
what more do you need from us(me kuma ki
Ke sake buƙata daga garemu?)’’.
Yusra ta yi mata tambayar cikin tsare ta da Idanuwa.

Cikin rashin jin dad’i Ummi ta ce ’’Yusra zumunci da zaman lafiya nake so a tsakanina da ku, sannan a lokacin da Daddyn ku ya aure ni ya yi alk’awarin zai rik’e Munirat kamar y’ar cikinsa, ya ce za ta ji dad’i a tsakanin ku…
zaman gidan nan ba zai tab’a yi mata dad’i ba indai kuna yi mata irin haka…
Ɗazu fa tarar da ita na yi ta had’a kayanta zata bar gidan nan, kinga ai hakan bai yi dai-dai ba, pls ku zauna lafiya, dukkanmu a k’ark’ashin mutum d’aya muke…
duniyar ma duka duka nawa take?d’an zama ne fa na k’anƙanin lokaci bayaga haka ma na tabbata nan da five years ba lalle a tarar da hatta Yadira a cikin gidan nan ba..

Ya’isha ki gayawa Kausar in kin hau sama ki yi mata bayanin da na yi muku ita da Yasira tunda su ne ba….’’

Da k’arfi Ya’isha ta dire kofin juice d’in da ke Hannunta wanda hakan ya katsewa Ummi maganarta!
Allah ya so cup d’in unbreakable ne da tuni ya fashe saboda yadda ta wani buga shi.
Cikin tsananin b’acin rai ta mik’e ta kalli Munirat wadda ta d’ago itama tana kallon ta, zuciya a wuya ta ce
‘’Dan girman Allah yadda kika had’a kayanki kar ki kwance ki kwashe su ki yi gaba yau! kar in sake ganin k’afarki anan.’’
Sannan ta juya ta kalli Ummi
tace’’Ummi do you know wat your problem is?
(Ummi kin san menene matsalarki?)”
bata tsaya jin mai Ummin zata ce mata ba ta ce’’Son kai!.
son kai shine matsalar ki…
kalli yadda kika tisa mu a gaba kina mana maganar dole sai mun so y’arki!! dole sai mun yi zaman lafiya da ita, shin wai ana dolene!??.
kuma na ga ita ta janyo komai tun asalin farko tunda tun da ta zo gidan nan babu wanda ya Kyamaceta
Despite the fact that
She’s not even our class but (dukda kuwa cewar ita ɗin ba ajinmu bace ba amma) a hakan muka ja ta a jiki duk dan a zauna lafiya amma duk bataga wannan ba haka nan ta zo ta tafkawa Mutane shirme…

Kasancewar wani wai saurayintane tun farko ko ma mijinta ne tun farko hakan ba zai goge laifinta ba tunda ai dai yanzu Yahanasu ya zo zai aura
amma bataga wannan ba tsabar cin fuska haka ta biye masa..
Although (dukda)Yahanasun ta ce babu ruwanmu da case d’inta amma yadda ki ke supporting y’arki kike k’ok’arin goge laifinta k’arfi da yaji ni shine matsalata da ke!!!!!

sannan bari ki ji in gaya miki ni kam har abada i’ll never be friends with her (babu zaman lafiya tsakanina da ita) tunda na lura ba ki san mutunci,kawaici da arzik’i ba ke kawai naki kika sani, you are morethan selfish (kin fi son kai son kai) dan haka babu zaman lafiya a tsakani na da ke da y’arki har abada wallahi…
ba da irinku ake zaman lafiya ba dan naga idan aka baku fuska next time sai kun yi abunda ya fi wannan,
dan haka dole mu taka miki burki mu nuna miki matsayinki a cikin gidan nan tun yanzu,
ke ba kowa bace ba, you are just holding a place here(cike waje kawai kike yi a cikin gidan n…..)’’

Cikin tsawa Ummi ta mik’e tsaye ta ce
‘’Ya’isha!!’’

Itama Ya’ishan cikin tsawar da ta fi ta Ummi ta ce
‘’Kar ki sake d’aga mini murya!!!
gaskiya ce dole in fad’eta.

kuma naga da farko ba ku san mu ba muma bamu san ku ba amman ai mun rayu kuma kun rayu, to a kan wanne dalili ne za ki tilastamana yanzu akan dole sai mun kula y’arki?.

Sannan last warning gareki ‘kar ki sake cewa za ki tara mu da ni da siters ɗina ki yi mana fad’a ko kuma ki bamu wani useless labarinki wanda mun riga mun san shi dan an fad’a mana tun d’azu da safe…
Chapter 43 · 0% Book details