← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 84

Sashe 46

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin fushi ya juya da niyyar fita, a bakin k’ofa suka yi kicibis da Ummi wadda ta ji shigowar su ta biyo domin ta ji ya jikin Yasmeen d’in….
tunda suka fita ta ke trying numbers d’insa, saboda ita shi kuma ya saka wayoyinshi gaba d’aya a silent..

Da kyar Daddy ya iya cewa
‘’Munirat give us a moment
(Munirat bamu waje)”
ya fad’i hakan idanuwansa a kan Ummi, ba tare da ya kalli Munirat d’in ba.

Da sauri ta ajjiye parker da abun sharar ta fice daga d’akin, tana tafe tana waiwaye gaba d’aya hankalinta a tashe
tana mamakin me ya had’a su haka dan ita Ummi bata ce mata komai ba tun ɗazu, gashi
ta ga ran Daddy a mugun b’ace!!!

ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda ta ga mood d’in nasa, tsoronta kar ta je ya bugi Umminta…
tana tafe tana lissafi tana waiwaye haka ta fice a parlourn, bata yi auni ba kawai ta ji ta afka kan Mutum,
da sauri ta ce ‘‘Innalillahi’’
sai kuma ta fara k’ok’arin kwace kanta daga rikon da Yassir ya yi mata.
Tunda ta taho tana kallon baya ya ganta dan lokacin dai-dai shi kuma ya fito daga corridor na side d’in Mommy ,
ahankali ya wani lumshe ido ya bud’e saboda yauma riga da wando ke jikinta na bacci irin me bin jikin nan, rigar iya cinya wandon kuma har k’asa,dan haka a ransa ya ce ‘’lucky me’’
Ganin bata gansa ba ne ya sanya shi sake nutsuwa ya ƙi motsi gudun kar ya ankarar da ita,ai kuwa da ikon Allah ta afka jikinsa!!!
Without thinking twice shi kuwa ya rungume ta gamgam….
tana d’agowa su ka yi ido biyu da shi, cikin tsananin firgici ta ce ’’get off me, (ka cika ni) baka da hankali ne’’
Ta k’arashe maganar cikin tsawa.

Wani irin murmushi ya yi kafin ya ce
‘’Munirat yo ai ko malaikan mutuwa ne ya zo d’aukar raina
to
Sai ya d’aga min k’afa na gama appreciating moment d’innan (godewa lokacin nan)
tukunna ..’’

Wani irin kuka ta saka kafin ta fara k’ok’arin kwace kanta tana magiya tana kai masa duka, ganin tana neman cika masa kunne ne ya sanya ya fara k’ok’arin kissing d’inta…..
A gigice ta kwala wata mahaukaciyar k’ara dai-dai shima Yashjub ya ce
‘’Yassir’’
Cikin tsawa
………….
Achan d’aki kuwa, Munirat tana fita
Daddy ya cewa Ummi ‘’Ki had’a kayanki, duk wani abunda kika san naki ne, ki tartare, ki bar min gidana’’

A hankali Ummi ta ce
‘‘Daddy har me ya yi zafi haka?
Wallahi Kausar k’arya take yi, ban san Yasmeen tana da matsala a Kunne ba!
Sannan ya kamata ka tsaya ka ji abunda Yaran nan su ka yi min kafin ka yanke wannan d’anyen hukunci hak….’’

Cikin katseta Daddy ya ce
‘’Na san k’arya Kausar ta yi miki, na san basu gaya miki Yasmeen tana da matsala a kunne ba.
Kinsan abu na farko da ya fara had’ani da ke?’’.
Cikin zubar kwallah Ummi ta girgiza kanta alamun’’a’a’’
Cikin fushi Daddy ya ce
‘’Ranar da kika zo d’akina kika bamu asalin labarin Munirat da Bashir, me na ce miki ??’’

Cikin inda inda saboda duk ta rikice ta ce
‘’Cewa ka yi komai ya wuce,
amman Daddy su Kausar basu..’’

Cikin tsawa ya ce ‘’ba wannan ba!d’ayar maganar tawa ta k’arshe, me na ce miki Saddik’a?’’

A gigice ta ce
‘’Cewa ka yi zaka saka su su bani hak’uri’’

‘’Good’’
Daddy ya furta yana mai sake matsowa kusa da ita
wanda hakan ya sanya Ummi ta d’an ja baya dan ba kad’an ba ta tsorata da Daddyn, bata tab’a ganin shi a haka ba tunda su ke.

Cikin zafin zuciyar da ya ke ji tana taso masa ya ce ‘’na fad’a miki bara in sake maimita miki!
dan naga kamar kin manta,
Abu uku na fi tsana a yi min
waenda su ne suke janyowa Mutum ya ga other side d’ina;
A yi crossing d’ina
A ci Amata
na uku, a nuna min ban Isa ba!!
Duk yadda na kai ga son Mutum da ganin girman sa
muddin ya yi min haka to babu
dalilin da zai hana ni yin kacha-kacha da shi…...
da nace miki ki jira zan sanya su su baki hak’uri dan me yasa kika yi gaban kanki?
saboda kin raina ni?
saboda ban isa ba?..na ji sarai na kuma san me kika yi
Yasmeen ta gaya min yadda kika tara su a dining table
kina cewa su zauna lafiya da Munirat, kina gindaya musu sharud’a kina jera musu warning alhalin su already komai ya riga ya wuce a wajen su…..
Me kike so ki yi proving by doing that??(ki nuna ta hanyar yin hakan??)

bari kiji nan gidan ubansu Yasmeen ne, Munirat kara kawai na yi mata nake bata shelter saboda ke, and if za ki nemi ki takurawa ƴaƴana saboda ita har ta kai ga kina k’in jin maganata kina k’etare umarni na to kuwa ban ga dalilin da zai sanya in ci gaba da zama da ita a gida d’aya da ke kan ki ba!!!

Sannan yau har kina da guts d’in da za ki d’aga Hannu ki mari Yasmeen?kin tab’a gani na yi wa Munirat kallon banza???
Ko ma me Yasmeen ta yi miki ko ma menene Saddiƙa
ban ga dalilin da zai sanya ki mare ta ba’’

Cikin share hawaye Ummi ta ce
‘’ko menene?’’

Ciikin fushi Daddy ya ce
‘’Ko uwar ki ta zaga ban baki ikon ki tab’a d’aya daga cikin Ƴaƴana ba!!!

Kin tab’a ganin uwar da ta haife su ta d’ora Hannu akan su??’’.

Wani Irin kuka Ummi ta fashe da shi ta durk’ushe a wajen, dan ba wanda ya fad’o mata a rai a dai dai wannan lokacin sai
Marigayin Mijinta..

Sam bata bawa Daddy tausayi ba, dan shi wani irin haushi ma ta ci gaba da bashi, ji yake yi kamar ya yi ball da ita.

Kwanakin baya Mommy ta tuno masa da Khadija yanzu kuwa Saddik’a ce ta tuno mishi da ita..ta yadda ta nuna masa bai Isa ba, bashi da girma da daraja!!!
ta yadda ta nuna son kanta ta fifita y’arta k’iri k’iri sama da shi.

Cikin fushi ya sake cewa “ki tashi ki had’a kayan ku…”

Maganarsa ce ta mak’ale
sakamokon ihun Munirat da suka jiyo..da gudu Ummi ta nufi waje..kafin ta k’arasa ta fara jiyo na Yassir shima…..

Ummi na fita Daddy ya bi bayanta da kallo cikin takaici….
kafin kuma ya nufi wardrobe d’inta da kansa ya fara firfito mata da kayanta yana sauk’e akwatunanta sannan ya ja akwatunan ya fitar parlournta
daga nan ya wuce ya fitar dasu daga side d’inta gaba d’aya!! ya nufi chan babban parlourn da ke a saman…
ko damuwa da ife-ifen Yassir bai yi ba kawai shi a halinda ake ciki babban burinshi shine Ummi ta fitar masa daga gida, kawai shi dai ta fita, ya san in ta fita shine zai samu nutsuwa…..
…
A chan parlourn kuwa…
Yashjub yana hango su bayan ya daka masa tsawa, sai kuma ya nufe su cikin tsananin tashin hankali.
yana zuwa bai yi wata wata ba ya janyo Yassir ya kifa masa wani gigitaccen marinda har sai da ya sanya Yassir d’in ya kai k’asa yana shirin tashi ya zaro belt d’in jikin wandon shi ya rufe shi da duka yana ball da shi.

Yanayin dukan da Yashjub ya ke yi masa ba irin dukan da normal Mutum zai yi bane ba saboda k’arfin Yashjub d’in na daban ne
shiyasa duk yadda Yassir ya so daurewa sai ya kasa ga shi ya kasa tashi dan yana yunk’urawa zai tashi Yash d’in yake kuma kai masa duka da k’afa ya kwantar da shi.

Kusan a tare Mommy Kausar da Ummi suka k’araso wajen….
Kausar ce ta fara k’arasawa kusa dasu da niyyar rabawa ai kuwa itama ya zula mata belt dan dama haushin ta yake ji.

Da sauri Mommy ta matsa ta janyo Hannunta ta mayar da ita gefe, tukunna ta yi kan Yashjub d’in…

Da kyar ita da Ummi suka samu suka rik’e Hannun Yashjub wanda idanuwansa suka yi jaa sosai.

Cikin tsananin b’acin rai Mommy ta fashe da kuka ta ce ‘’haba Yash, wanne irin abu ne wannan?
Ko Yaro d’an shekaru sha takwas ai ba ka saka a gaba da duka irin wannan ba’’.

Cikin rashin jin dad’i da dauriya Ummi ma ta ce ’’Yash baka kyauta ba, ko ma me ya yi maka bai kamata ka dake shi haka ba.’’

Sai kuma suka juya ga Munirat wadda ke durk’ushe a wajen
Mommy ta ce ‘’me ya faru’’

Gaba d’aya ta tsorata ta gigita daga abun da Yassir ya yi mata ga kuma dukan da taga Yash yayi masa shiyasa da gudu ta tafi jikin Ummi ta fad’a ta fashe da kuka tukunna ta ce ’’Ummi dan Allah dan Annabi ki zo mu bar gidan nan, idan kuma ke ba za ki tafi ba ni gaskiya zan tafi’’.

Dai-dai nan Daddy wanda ya gama janyo akwati ya cillo waje
ya ce
‘’Kar ki damu, yanzun nan za ku tafi’’.

Da sauri Yashjub wanda tun ɗazu yake ta karanto sunayen Allah yana k’ok’arin daidaita kan shi, ya runtse idanuwansa da k’arfi.

Dai dai nan su Yahanasu da Baba larai suka hawo saman
sakamokon hayaniyar da suka ji.

Yahanasu ce ma ta lura da yadda gefen kan Yassir ya ke zubar da jini sai kuma taga kamar ma baya motsi da sauri ta k’arasa kansa ta shiga tattab’asa tana kiran sunan shi’’yasssir! yassir!!’’sai
kuma ta juya ta kalli
Baaba Larai a rikice ta ce ’’baya motsi fa’’.

Cikin tsananin tashin hankali Mommy ta kalli Yassir itama ta tabbatar ba ya motsin, bata san lokacin da ta juyo ta kifawa Yash wani irin gigitaccen mari ba sai kuma ta sake fashewa da kuka ta durk’ushe a kan Yassir,
cikin tashin hankali ta ce
‘’Shikenan ya kashe min Yarana, ya kashe min d’ana mafi soyuwa a gare ni, shikenan ya kashe min gudan jinina….’’
Chapter 46 · 0% Book details