← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 84

Sashe 47

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Baba Larai ta ce
‘’Haba Khadijah, ki yi shiru mana, bai mutu ba inshaaAllah’’
Sai kuma ta durk’usa ta mikar da ita, tana tittirjewa tana kuka haka suka jata ita da Kausar suka nufi b’angarenta da ita, tana kuka kamar ranta zai fita.

A hankali Daddy ya k’arasa ya dudduba sa, ba tare da ya kalli Yash ba ya ce ’’kama min shi mu kai sa d’akinsa.’’
Yana gama fad’in haka ya d’auko waya ya kira family Dr.d’insu, daga nan suka fara k’ok’arin kinkimar Yassir.

Har sun kama hanyar k’ofar d’akin Yassir d’in Daddy ya d’an tsaya ya juyo ya kalli Ummi ya ce ‘’kar ki k’ara minti biyar a cikin gidan nan’’.
Daga haka suka yi gaba suka wuce shi da Yashjub.

A hankali Munirat ta k’arasa kusa da ita ta rungume ta
cikin zubar hawaye ta ce ’’ sorry Ummi, it’s for the best
InshaaAllah( ki yi haƙuri Ummi, hakan shine mafi alkhairi, in sha Allah)”
Munirat ta fad’a hakan dan ita duk a tunaninta ita ta sake tunzura Daddy dan taga Daddy ya ji lokacin da ta ce su bar gidan……

A kan gado suka kwantar da Yassir,
Daddy ya sake zaro waya ya shiga kiran Dr domin ya ce masa ya zo da sauri, yayinda Yashjub ya faki idon shi ya juya ya fice,
ya nufi wajen su Ummi.

Bai same su a main parlourn saman ba dan haka kanshi tsaye ya wuce side d’in Ummin.

A bakin k’ofar d’akinta ya tsaya yana knocking, lokacin suna tsaye suna mamakin yadda Daddy ya watsar da gaba d’aya kayan wardrobe d’in Ummin,

ahankali Ummi ta faki idon Munirat
ta goge hawayenta ta nufi k’ofar da ta ji ana bugawa tana addu’ar Allah yasa kar Daddy ya sake creating wani scene d’in a gaban Munirat dan ita a tunanin ta shine ya sake dawowa, amma tana fita sai ta ga ashe Yashjub ne.

Dukda halin da take ciki haka ta daure ta b’oye tata damuwar ta ce
‘’Yash, dan Allah dan Annabi kar ka sake yi wa d’an uwanka irin wannan dukan,
Dan Allah’’

A hankali Yash ya had’iye wani k’ululun da ya mak’ale masa a mak’oshi yana mai mamakin kyakkyawar zuciya irin tata
tukunna ya ce
‘’Na ji Ummi, ba zan k’ara ba amma kema kar ki je koina,
I’ll speak with daddy (zan yi magana da Daddy),
In ya huce’’.

Murmushi ta yi kafin ta ce masa
‘’shigo’’

Ta fad’i hakan tana matsawa ta bashi hanya ya shigo
cikin d’akin nata da sallama a bakinsa…
da mamaki shima ya ke kallon d’akin sai kuma ya kalle ta.
Cikin karyewar zuciya ta ce
‘’Ni kaina Yash bana son barin gidan nan, banaso aurena ya mutu, amma kuma kalli abun da Daddy yayi, shiyasa na ga tunda har abun ya kai ga haka gara in fita tunda lafiyata da mutuncina..tun kafin ya zo yayi fata fata da ni kamar yadda yayi da kayana, amma Ina so ka fad’a masa ko bayan na bar gidan nan cewa ina son Y’ay’ansa kuma ba zan tab’a cutar da d’aya daga cikin ku ba.’’
Yadda Ummi take hawaye
da kuma abunda Daddy ya aikata tabbas ya san Ummi ba za ta yarda ta k’ara minti uku ba ma a cikin gidan, shiyasa a hankali ya jinjina mata kai kawai alamun fahimta,
yayi hakan yana mai kallon windunan d’akin da kuma hanyar closet d’inta har zuwa toilet ya tabbatar babu ta inda za su fita,
ya ji dad’i da balcony d’inta ya kasance a parlour ne
dan wallahi ko shi ne Daddy ya yi mishi wannan tijarar sannan ya ce ya fice mishi a gida to
sai ya fita ko ta window ne, daga baya ya dawo a sasanta…..

A hankali ya ce
‘’Na fahimci ki, Ummi.’’

Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce “ka kula da y’an uwanka, Allah yayi maka albarka’’

‘’Ameen’’ ya ce,
daga nan ya juya yana zuwa k’ofar yayi sauri ya sa Hannu ya zare makullin kafin ta k’araso ta ce wani abun har ya fice ya sak’ala key d’in ta waje tana k’arasowa jikin k’ofar ta ji ya rufe su ya zare makullin….
….
Ko da Dr ya zo, ce musu yayi “ba wani abun tashin hankali bane ya samu Yassir d’in,
kawai azaba ce ta saka shi ya suma sannan kurjewa ne kawai kan nasa ya yi ba wai dukan ne ya fasa masa kai har yasa yayi jini ba…
Dan haka su kwantar da hankalin su”
Daga nan, ya basa allurai da duk abunda ya kamata, ya tabbatar musu da “inshaaAllah he’ll be fine..”

Yashjub ne ya raka shi har mota yana dawowa ya tarar da Daddy har yanzu a tsaye a kan Yassir wanda ɗazu ya farka Dr ya yi masa allurar bacci kafin ya tafi.

K'arasawa ya yi ya tsaya shima yana kallon Yassir d'in….
tabbas
yana son d'an uwansa amma kuma halayen Yassir kullum sake tab'arb'arewa suke yi sannan shi kuma ga yanayin zuciyarsa wadda yake sake tunzura sa ga aikata wasu abubuwan….saboda Allah bayaga girman shirmen da Yassir ɗin ya yi wa Munira ai ko ba komai bai kamata ya yi mata hakan iyayensu suna cikin gidan ba!!!

Da sauri ya dakatar da tunanin gudun kar ransa ya sake ɓaci,
a hankali ya sunkuyar da kansa a ransa ya ce
''bai kamata ace na dake sa ba, inda ace Yassir ya yi aure da wuri to da yanzu maybe yana da ƴaƴa biyu ma..''

Cikin dakakkiyar murya ya ji Daddy ya ce “abun da ka yi yau was incredibly stupid(gagarumin shashanci ne), ko da wasa kar ka sake yin wannan shirmen,
Ranar da case d'in Yahanasu da Munirat ya faru cewa ka yi saboda ka ga muna wajen ne shiyasa baka hukunta su Yassira ba!
It would be nice of u(za ka fi burgeni) idan ka ci gaba da bar mini komai a Hannuna…

ban haifi ya’yana
dan wani ya ci kashi a kanku ba kuma
na san ka fi kowa sanin wannan.”
Sai da ya juyo ya kalleshi ido da ido tukunna ya ce
“Next time idan Yassir yayi laifi
U
report
To me!
(Nan gaba idan Yassir ya yi laifi, ka kawo min ƙararsa kawai)”
Yana gama fad'in haka ya juya ya fita….

Daddy yana fita daga wajen Yassir fannin Ummi ya biya…..ya je ya murza ya ji a rufe kuma bai tarar da akwatunanta ba, dan haka ya yi tunanin ta tafi ne…
a take ya ji wani irin sanyi yana ratsa shi, yayinda a chan wani b'angare na zuciyarsa kuma yana takaici da jin haushin tafiyar tata da kuma abunda ya yi mata….

Gaba d’aya Yashjub a hargitse yake, mari da maganganun Mommy sun yi mugun b’ata mishi rai!!
Ga kuma abunda Daddy ya yi masa, sannan ga yadda ya ga Yassir and yana kyautata zaton su Yasmeen ne suka shiga tsakanin Daddy da Ummi….
Ba zai yiu fa ya zuba ido ya tsaya
tarbiyyan k’annensa ya zama haka ba!!!
amma matsalar shine ta Ina zai fara tunda gashi k’iri-k’iri Daddy ya ja masa barrier(ya shata masa layi)….
ganin da yayi gaba d’aya yana neman sake b’atawa kansa rai ne yasanya kawai ya fice ya nufi side d’insa ransa a mugun b’ace.

Yana shiga parlourn shi ya tarar da Najeeb a zaune….

ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ‘’zuwa babu sanarwa?’’

Murmushi Najeeb ya yi sanann ya ce ’’inata kiran wayarka baka d’auka, driver d’inka na kira ya ce min kana nan, shine na zo,’’

‘’anything important?
(Akwai wani abu mai mahimmanci ne)’’
Kawai Yashjub ya iya cewa.

Murmushi Najeeb ya yi kafin ya ce “ko in tafi ne ?’’
Dai-dai nan Yashjub ya k’araso ya zauna kusa da shi, sai a lokacin Najeeb ya lura da yadda idanuwansa suke
wanda hakan ya basa tabbbacin ransa ne a b’ace.

‘’Me kuma ya faru ??’’
Najeeb ya yi masa tambayar.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce ‘’ba komai’’.

Tunda ya ce hakan Najeeb ya fahimci maybe family issue ne
ko kuma ba shi da niyyar gaya masa ne, dan haka ya kawar da zancen ta hanyar cewa “tun jiya Ya’isha ta k’i d’aukar wayata, ban san me ya faru ba. Yash sai ka saka baki a lamarin nan fa dan Yarinyar nan tana wahalar da ni da yawa.’’

Tsaki Yashjub ya yi tukunna ya ce ’’k’aton banza kawai.’’

Dariya Najeeb ya yo kafin ya ce “ai gara ni, I’m not living in denial sannan bana fakewa da
employing mutum..k’arara nake fitowa, speaking of which..how is she.
(Ai gara ni kai tsaye ƙarara nake fitowa in yi abuna, kuma bana fakewa da ɗaukar Mutum aiki..
Ni ka ma tuna min,
Ya take.??)”

Kamar Yashjub ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ’’she’s ok(tana dai dai)’’
Ya yi maganar yana mai jin wani sanyi yana maye gurbin b’acin ransa.

‘’Gaya min yadda kuka yi da ita, lokacin da ta je.’’
Najeeb ya fad’i hakan ya na mai gyara zamansa ya fuskanci Yash d’in sosai .

Tiryan-tiryan haka Yashjub ya bashi labarin komai, wanda kafin ya gama gaba d’aya b’acin ran da yake a ciki ya b’ace b’at!.

Shi kansa Najeeb sai da yayi mamakin yadda Yashjub ya zage ya yi doguwar magana haka.

Dan haka yana dasa aya Najeeb ya ce
‘’Yashjub Yarinyar nan ba na jin iyayenta za su barta ta k’ara shekara d’aya ma ba tare sun yi mata aure ba,
kar ka tsaya b’atawa kanka lokaci ka je garin hakan miskilanci ya cuce ka, ka san dai kana son ta ko?’’

Shiruu Yashjub ya yi a ranshi yana lissafin ‘ko dai ya cire kunya da taurin Kai ya gayawa Najeeb ne, dan yana buk’atar shawara! Saboda har ga Allah bai san ta Ina zai fara ba, kuma kamar yadda Najeeb ya fad’a tabbas tsaf iyayenta za su iya aurar da ita anytime..ya zama dole ya ajjiye komai a gefe dan Manubiya ce peace of mind d’insa(kwanciyar hankalinsa)
Strength (kuzarinsa)
Happiness (farin cikinsa)
da komai na shi’’

‘’Yash….’’
Muryar Najeeb ta katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa da ya yi cikin k’ura masa idanu.

A hankali Yash ya gyara zama yana kallon Najeeb d’in tukunna ya ce ‘’menene abun yi yanzu?’’
Chapter 47 · 0% Book details