Sashe 16
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mutsutstsuka idanunsa ya yi, ya fesar da iska kafin ya mik’e shima ya wuce saman yana tunanin ta yadda zai yi raising kud’i!!
dan ba zai yiu ace bikin su shi da Kausar amma wai babu dinner ba wani shagali ba……
…….
A bakin gado Mommy ta samu Daddy, a tsaye yana shirin shiga wanka.
Ya ji shigowar ta, dan haka ba tare da ya kalle ta ba ya ce
‘’Don’t try anything stupid (kar ki gwada yin shirme a lamarinnan) Khadijah
daga nan har gobe. Ban san wasan da kike son bugawa wannan karon ba amma ina shawartar ki da
kar ma ki fara shirin yin komai, idan kuma
ba haka ba to zan baki mamaki.’’
Ba tare da fargaba ko tantama ba ta ce
‘’Ba wai shirin wani abu sabo zan yi ba, dan na riga na gama shiri na, kawai dama naga kamatar in sanar maka abunda ya kamata ka yi ne domin ya tafi dai-dai da shirin nawa!
Dan haka ka saurara ka ji
‘Inaso ka janye maganar auren Yasir da Kausar, dan
ba mai yiuwa bane ba’.’’
Sai yanzu Daddy wanda ya gama d’aura igiyar bathrub ɗin da ke Jikinsa ya juyo gareta, ya d’an taka inda take ya tsaya
tukunna ya ce
‘’Dole, a gobe Kausar za ta fitar mini daga gida Khadijah,
It’s either ta wuce gidan Yasir ko kuma ta san inda zata je,
na yi iya yina!!.’’
Wani kalar murmushin takaici Mommy ta yi
kafin tace
‘’Ai dama na sani, na san ka gaji da rik’e ta ne shiyasa za ka yi mata auren dole.’’
Cikin fushi Daddy yace
‘’A kul d’inki Khadijah!.
Idan ke dak’ik’iya ce baki san ciwon kanki ba baki san kishin d’an da kika haifa a cikinki ba tou ni na sani.
Ki godewa Allah ma da har na yarda Yasir zai auri Kausar d’in…
Allah na tuba Maraici ai ba hauka bane ba!
Yarinyar nan fa har haihuwa ta yi sannan bata da uba!
Amma duk da haka na amince na yarda zan aurawa Yasir ita..
Shine amma har kike da bakin cewa za a yi mata auren dole?’’
Daddy bai tsaya jin amsarta ba ya d’aura da cewa ‘’Bari kiji, ba don na san Yasir yana da ikon
k’ara aure ba to da ba zan bar shi ya auri shegiya ya rayu da ita ba wallahi.’’
Kamar an kunna fanfo haka fuskar Mommy ta jik’e sharkaf da hawaye,
Cikin kuka ta ce
‘’Na gode ‘Imam’ na gode sosai.
Alk’awarin kenan ko?
Allah ya ji ƙan Abba da Daddy…
A gaban su ka amince za ka rik’e Kausar, ruk’o na amana
amma yau da kanka da Bakinka kake cewa ta fitar maka daga gida
da kanka kake kiran ta da sunan ‘shegiya’
D’an Adam butulu, walllahi Allah sai ya yi mana hisabi.’’
Cikin tsananin b’acin rai ya ce
‘’Dole in ce Kausar ta fitar mini daga gida, Khadija
‘Ƴaƴana takwas a duniya amma babu wadda a kullum take d’aga mini hankali take janyo min abun kunya da magana sai y’ar ruk’o,
ko su Mazan ba sa yin fitinar da Kausar take yi!!!.
Kalli yanzu yadda ta lalata Yassir,
shikenan ni
kullum gidana cikin case saboda ita?.
Ki duba fa ki ga yau tafiya na yi na dawo amma ko isashshen sannu da zuwa da hutawawa ban samu ba ban yi ba na fara da case din y’ar ruk’o.’’
Cikin d’aga Hannu (alamun stop )
Mommy ta ce
‘’Dakata daganan Daddy.
Maganganun ka ga Kausar sun ishe ni, sannan idan ba zaka kirata da Kausar ba to
ka yi shiru!
dan shegiya ko y’ar ruk’o ba sunanta bane ba, gorin ka da cin fuskar yayi yawa haka ya isa!!!.
kuma ta Ina kausar ta lalata Yasir?fyad’e ta yi masa?
da aka ce maka sun tafi Auckland d’in tare shi munafukin naka camera ya mak’ala musu ya ga sun yi wani abun?
Baya ga haka ba fa su kaɗai suka yi tafiyar ba??
har da Abokansu suka tafi.
Kawai kai dai ka tsani Kausar!
Na riga na sani tun ba yauba ka tsane ta shiyasa kullum burin ka ka ga ka k’untata mata.
Tayaya ma za ka ce wai Kausar ta lalata maka ɗa! haba Daddy,
ka dinga adalci mana,
ko kara babu?’’
Cikin takaici Daddy ya ce
“karar da na yi tun farko ita ta cutar da ni, gashi inaji Ina gani
Yasir zai auri Matar da sai addua kawai, kuma a matsayin uwar gida,
Idan jikokina suka tashi a gagara nuna musu dangin uban Mahaifiyar su’’.
Cikin jin-jina kai Mommy ta ce
‘’shikenan tunda kai ba Mahaifinta bane ba!
ka faɗa ka nuna kuma ka furta.
Tou nima daga yau
Inaso ka tsame Hannunka a duk lamari da rayuwar Yarinyata.
Aure kuma da Yasir tunda har kana ganin kamar za a cuce shi ne to wallahi ba za a d’aura ba!
Idan kuma ka d’aura to za a sha mamaki na.
Tunda baka son had’in
ta fi nono fari
muma bama so.
Kuma inshaaAllah daga yau
Ni zan dinga kula da ƴata,
babu ruwan ka da duk wani abun da ya shafe ta!
Zan nemo cook inn siyo kayan abinci a dinga yi mata girkinta a daban…
k’arshen wata kuma zamu dinga biyan ka kud’in haya,
ruwa da na wuta!!!
Iyakar abunda nake nema daga gareka shine ka daina takura mata, kuma ka daina yunk’urin yi mata dole.
Iyakar tsakaninka kai da ita gaisuwa.
Tunda a iya sani na babu inda Kausar za ta je muddin Ina cikin gidan nan, dan haka sai ka jira har sai ranar da Allah ya kawo mata wanda take so ta aura tukunna.’’
Tana gama fad’in haka ta juya zata fita sai kuma ta juyo ta dawo inda yake nan tsaye ranshi a mugun b’ace ta ce
‘’Allah dai ya so ba y’ar uwata kad’ai bace ta fara haifar shege!
kafin ta yi kafin Kausar ta yi sai da aka yi!!!
Ko in je in kawo maka Yahanasu?
Na san wataƙila idan ka kalli fuskarta zaka iya tuno da wadda nake nufi da kuma abubuwa da dama,
saboda kalamanka da k’iyayyar ka ga shege sun sanya na fara tunanin maybe ko dai ka yi loosing memory ne.
A yadda ka tsani Kausar kake kyamar ta inada tabbacin ta fi dubu! saboda na tabbata in dai Kausar ta auri wanda take so kuma yake son ta to ba za
ta tab’a cutar sa ba baza kuma a kamata da waninsa ba!
saboda ƴata tanada ruƙon amana kuma na san ta san darajar soyayya………..
Cikin tsananin fushi Daddy ya yunƙura da dukkannin ƙarfinsa ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari.
Dagowa ta yi da niyyar ci gaba da tsiwa amma sai yanayinsa da idanuwansa suka sanya ta had’iye maganganunta da tsiwar tata
domin a yadda ta ga yana kallon ta da jajayen idanuwansa tsaf zai iya illatata.
Da kyar ya iya cewa
‘’Fita kar in sake ganin fuskarki idan ba ni na neme ki ba.’’
Babu musu, haka nan
ta juya ta fice daga d’akin dan ta tsorata da yanayinsa.
Tana fita kuma sai ta ji wani sanyi ya lulluɓe ta, a haka ta fita daga side ɗin nasa gaba ɗaya ta sauƙo tana mai jin zuciyar ta fess!!!
Tabbas ta san dama idan ba da gaske ta yi ba to ba lalle ta iya hana auren nan ba!
Amman a yadda ta tsokalo Daddy ta tuna masa da baya to fa
ba lalle ya iya shan ruwa ba ma daga nan har Jibi, ballanta har a zo ga maganar ɗaurin aure!!
Yayinda a chan k’asan zuciyarta kuma sai ta ji kishi yana taso mata!
Sakamokon k’unci, damuwa da tsananin kishin data gani a Idanuwan Daddy kamar
jiya jiya abun ya faru…………
••••••
Kamar yadda Al’ameen ya ce,
Da yamma kusan magrib sai ga shi ya dawo da laidoji nik’i-nik’i.
Ya kuwa ci sa‘a dan Jiddah ce a wajen,
Manubiya an tafi yi mata test
saboda tunda Baba ya lura ba ta da lafiya duk sai ya damu da kyar ma
ya wuce gida shi da Muhsin ya barsu tare da Ya Musbah akan idan komai yayi settling shi sai ya dawo ya bar Jidda da Manu su kwana
washegari kuma ya koma su dawo su yi girki, idan Allah ya kaimu.
Tunda ya shigo ta diririce
gashi Inna ma bata jima da komawa bacci ba.
Dariya ta so ta ba shi dan kamar irin zai sace ta d’in nan haka yaga tana yi….
Cikin sanyin murya da sanyin jiki ta gaida shi, shi kuma
ya amsa mata da kulawa yana mai tambayar ta “ya jikin Inna?”
A hankali ta ce ‘’da sauk’i’’
Har zai zauna sai kuma ya ƙarasa gaban gadon ya ajjiye ledojin ya ce mata ‘’gashi’’
tukunna ya dawo ya zauna.
Da kyar ta ce ‘’mun gode’’
Sai kuma ta ɗan yi shiru kafin ta ce
‘’Ya Al’ameen ka daina, dan Allah’’
Wani d’an guntun Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’in daina me?’’
Ya faɗi hakan yana mai kafeta da idanuwa.
Sai da ta ɗan ɗauki lokaci tukunna da kyar ta ce ‘’ka daina kallo na sannan dan Allah ka daina zuwa, mun gode sosai, amman Ina tsoron Ammi.
kar a zo ta gane kana zuwa nan, kaga Inna bata da lafiya dan haka idan aka fara wani case na daban kuma abun ba zai yi dad’i ba’’.
A hankali ya sauk’e ajiyar Zuciya kafin ya ce
‘’Ko yanzu kafin in taho saida na gayawa Ammin inda zan je’’
Da sauri Jidda ta ɗago manyan Idanuwanta tana kallon sa!
Shima itan ya ke kallo dan haka ta yi saurin yin ƙasa da kanta.