Sashe 57
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rungumeta Yassir ya yi, kafin
a hankali ya ce
‘’Sorry Kausar, na d’auki alhakinki kwanaki, na yi tunanin gudu na kike yi, ki yi hak’uri, na fahimci komai yanzu.’’
Shiruu ya d’an yi kafin ya ce
‘’Amma ta ya Munirat za ta taimaka wajen case d’in (lamarin)Ummi?
da har kike ta k’ok’arin haɗa ni da ita, sannan shin ba kya kishina??’’.
Murmushi ta yi sannan ta ce
“Yassir Ina kishin ka,
amma bana so in zama kamar Ina
controlling d’in ka(juya ka),
sannan na san duk rintsi ni d’in dai ni ce a cikin zuciyarka.
na riga na san halinka ba wai ban saniba..
na san ko na yi haukar rabaka da ita a yanzu ba zan yi nasara ba!
Inaso mu zama d’aya ni da kai..
Shiyasa
akan ka je ka yi abu a bayan idona gara ka yi a gaban idona,
daga haka ni kuma in ci moriyar halinda ake cikin….dan
Wannan yarinyar itace lagon Uwarta!
Muddin ka kafa mata k’ahon zuk’a
lokacin da uwartata zata hak’ura ta bar gidan nan tare da ita ma ba za a sani ba…
Ba ka ji a labarin Yahanasu ba?
saboda senator ta bar garin nan ita da y’ar sai bayan
watanni tukunna suka dawo….
Tuni yanzu ita da Daddy sai dai kallo
We make sure of that
(Mun tabbatar da hakan)
fitar ta a gidan ne kawai matsala,
Wanda godiyar hakan ta tabbata ga Hajiya wadda ta hana Daddy sakin ta
in dai har ba ita ta tafi da kanta ba.
Ita ma kuma na lura idan ba sakin nata aka yi ba to ba zata tafi cikin sauƙi ba!
Shiyasa
Muke so mu sakata ta bar gidan da k’afarta daga nan
Daddy ya rakata da takardarta.’’
Wani zazzafan numfashi Yassir ya fesar kafin a hankali ya ce ’’Na fahimci komai yanzu”
daganan ya sake k’ank’ame ta
A ranshi yace
“Na gode Kausar..
ke da Mommy
ku saka Daddy ya k’ara min share(kasona)
Ni kuma zan shiga cikin dukiyar Yashjub..
In kwashi rabi
In tarwatsa rabi
Idan kuma abun ya zo da tangard’a in dagargaza komai, kowa ma ya rasa!.
Bayan na gama da shi kuma
zan dawo gareki,
sai dai kawai ki ji ana d’aura mana aure!
Saboda
duk da bayanin nan da ki
ka yi min
I still don’t trust you
(ban gama yarda da ke ba)
Dan
Inda ace da gaske kina sona to
da zan ga ko da d’an guntun kishina ne a cikin idanunki da aiyyukanki,.
Allah dai kawai yasa ba yaudarata
kike yi ba!
sannan ba ki da shirin shiga hanyata ki taremin abunda nake son cimmawa…dan cikin duk Mutane ke kad’ai ce banaso ki shiga hanyata saboda
a shirye nake in bi ta kan duk wanda ya yi k’ok’arin tare min hanyar cimma abunda nake so in cimma….’’
Tunda Kausar take a rayuwarta bata tab’a jin shakkar Yassir irin na yau ba, dan kamar yadda ya fad’a mata
tabbas ‘wannan ba shi ne Yassir d’in da ta sani a baya ba’!
Idanuwanshi sun tabbatar mata da hakan,
Hakan ya sanya ta d’an tsorata da shi dan ta san idan ya fahimci gaskiyar lamari to akwai matsala, dan ita har ga Allah baya gabanta!
asalin gaskiya ma ita so take ta yi getting rid of him (ta kawar da shi a hanyarta) cikin sauk’i, shiyasa ta zo suka shirya….
Da gaske, akwai shiri maganganun da ta gaya masa ba wai babu ba! kuma duk gaskiya ne, da batun arziƙin yash da batun yadda Daddy ya kasafta kason company ɗinsa duk gaskiya ne, amma ko su Mommyn kawai biye su take yi saboda ita a cikin zuciyarta bata da mu Yassir ya ji dad’i ko kar ya ji ba dan ba shine a gabanta ba…
ita kwata kwata babu shi a cikin tsarin ta na asalin gaskiya ma…
…shirinsu ita da su Yassira shine
su fitar da Ummi.
…shirinsu ita da Mommy da baba larai kuma
Shine
su saka a bawa Yassir kaso mai tsoka sannan
hatta Yash suna so ya janyo shi ya saka shi a cikin company d’in shi.
…Ita kuma shirinta shine ta yi wa
Yassir wayo, gudun kar ya je ya yi mata wani shirmen…
ta samu ya bata lokaci da iska
ta samu ta shiga jikin Yash shi kuma ta kwak’uma masa Munirat
daganan sai dai kawai ya ga ana d’aura mata aure da Yash.
Amma yanzu kam dole ta chanja taku!
Saboda Ta san Yassir tun suna Yara idan zuciyarsa ta motsa babu abunda ba zai iya aikatawa ba! Dan haka ya zame mata dole ta yi betraying (ci amanar) Baba larai da Mommy dan ba za ta tab’a bari
Yash ya ja Yassir a jikinsa saboda
a yadda Yassir yake a zuciyen nan tsaf zai iya cutar da Yash ko dukiyarsa.
Kuma dole ta yi sauri ta ko wachche hanya ta auri Yash
daga nan ta san yadda za ta yi ta kare kanta ita da Yash
daga sharrin Yassir.
Zuwa yanzu Ummi ba matsalarta baceba
dama so take yi ta bak’antawa Daddy rai sannan ta hana sa jin dad’i sakamokon abubuwan da yake yi mata a cikin gidan,!
Shiyasa ta had’a guiwa da su Yassira..
Ai kuwa gashi ta ci riba!
tunda gashi baya samun farin ciki da soyayyar Ummin,
kuma ba ya jin daɗi!
Dan haka ta tsame hannunta daga yanzu su ɗin
su je su yi ta fama dan tana da
abubuwan da sukafi lamarin Ummi barkatai a gabanta…
Ita kad’ai ce a kan wannan nata shirin
dan haka dole ta so kanta fiye da komai da kowa.
A hankali ta ji yanayin ruk’on da Yassir yayi mata yana sauyawa..
wani k’ululun bak’in ciki ne ya tokare ta, da kyar
ta iya danne zuciyarta ta ɓoye takaicinta tukunna ta d’ago ta kalleshi tana murmushi ta ce
‘’ba zan kwanta tare da Kai
Da sunan wata a sak’ale a saman mu ba‘’
Murmushi ya yi
kafin ya ce ’’sorry’’
daga haka ya cika ta ya je ya cire ballon d’in da suka had’a sunan Munirat ya jefar a k’asa ya dawo…..
Yana shirin rik’e ta ta ce
‘’Yassir a ganina bai kamata mu….”
‘’Shii’’ ya ce a hankali cikin katsera kafin ya d’aura da cewa
‘’Come on! dont be a grandma mana, you know i miss u, ryt?…
(Wayyo! ya kamar ba wayayyiya ba, kin san dai na yi kewarki, ko?)
Daga nan ya janyo fuskanta da Hannuwansa duk biyu ya haɗe Bakinsu waje guda…
Ba yadda ta iya dan bata so ya gano ta ko ya dasa ayar tambaya a kanta, hakanan tana ji tana gani ta hak’ura ta zuba masa idanu..
……..
A b’angaren Yash kuwa yana chan bai ma san suna yi ba..damuwa da tunani sun saka shi a gaba dan za’a iya cewa yadda ya ga rana haka ya ga dare, saboda k’iri-k’iri ya gagara yin bacci…
ganin hakan ya sanya ya tashi ya dinga jero nafila,
tukunna ya d’an ji sanyi a ranshi….
zuwa yanzu ya huce daga fushi da Najeeb dan haka ya sa a ransa inshaaAllah gobe suna fitowa daga meeting d’insu na sassafe da suke dashi, da shi da su Daddy, zai kira Najeeb,
ya san yadda zai yi da shi ya tambaya masa kwatancen k’auyen su Manubiya..
yana wannan lissafin ya sake zaro waya bai damu da cikin dare bane haka ya yanke shawarar gwada sa’ar sa sai dai tun kafin ya kai ga kara wayar a kunnensa yanzun ma ya ji an ce masa a kashe
kamar yadda tun d’azu da safe yake jin layin nata’a kashe.’
•••washegari da safe•••
A rikice Baba ya shigo cikin d’akin su, bai tadda kowa ba sai Inna dan Manubiya ta fita siyo sugar Muhsin ya je gidan Ya Musbah Jidda
kuma tana wanka
Yana shiga ya nufi wajen kayansa ya hau duddubawa….
duk wasu ragowar kud’ad’en da yake da su haka nan ya kwaso ya tara su a gabansa ya hau lissafi, dai dai nan
Jidda ta fito daga wanka tana mai gyara zaman hijabin a fuskarta.
Ganin bai ma lura da ita bane yasa ta k’arasa kusa da shi a hankali ta ce ’’Baba’’
Sai a sannan ya yi fir-gi-git ya mik’e sai kuma ya fara kalle kalle da dube dube kamar yana neman wani abun…
Sai da ya tabbatar babu kowa tukunna yace
‘’Yauwa Jidda ki kira Manu,
zan fita yanzu idan kuka ga na kai awa uku ban dawo ba to ku d’auki innarku ku je wani gidan ku b’uya.
Idan na samu na dawo zan yi muku bayanin komai.
ku kira Musbahu ki ce masa shima su b’uya shi da Baraka….”
*MANNUBIYA*
*34*

“Ba ni da ishashshen lokaci, inshaaAllah idan na samu na dawo zan yi muku bayani, ba
wani abun cutarwa ko zalinci na aikata ba..kuskure ne na yi amma da yarda Allah komai zai gyaru.”
Yana gama fad’in
haka, ya juya ya nufi k’ofa yana zuwa ya d’aga labulen d’akin ya fice, fitt!.
Da kyar Jiddah ta samu ta d’an dawo dai-dai tukunna ta juya ta bi bayan Baba da sassarfa tana mai cewa “Baba,Baba,Babaa!’’ A mugun firgice, gaba d’aya ilahirin jikinta yana karkarwa.
Tana bud’e labulen su ka yi karo da Ya Yusuf,
Murmushi ya yi mata kafin ya ce
‘’Sai mun dawo’’
daga haka ya juya ya bi bayan Baba wanda already ya riga ya yi gaba shi.