Sashe 78
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sanyin murya ya ce ‘’nima ban shiryama hakan ba…ki yi hak’uri, ba zan sake rik’e miki Hannu ba, yanzun ma mistake ne..let’s start a fresh (yanzu, mu sake farowa daga farko)
InshaaAllah ba zan sake ba.’’
Ya fad’i hakan yana kallonta, shi a karon kanshi yana mamakin yanda ya koma, dan sam bayar da hak’uri baya daga cikin tsarinshi, bai ma iya ba! Amma a iya yau a iya shigowarta cikin office d’insa kawo yanzu ya bata hak’uri ya fi a k’irga.
…….’’sam ba su yi kama da d’ayar ba dan tama fi kama da y’an china. Har gara ma d’ayar ita sun d’an yi kama wataƙila ko cousin d’inshi ce, to ita kuma d’ayar fa wacece?
Dan sarai ta lura da yadda idanuwanta suka cicciko lokacin da suka had’a ido, wacece ita? Su waye su?
Sannan wacece Mommy!?
Dan ta tabbatar inda ace wadda aka ambata da Mommy Mahaifiyar sa ce to da ba zai k’i tsayawa ya saurari abunda suka zo takanas fad’a masa akanta ba”….
Manubiya ta aiyyana hakan a cikin ranta.
Tunanin ta ne ya katse jin ya ce
‘’Mannubiya’’
A hankali
Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta d’ago ta d’an kalleshi.
Kalar tausayi ya yi mata kafin ya ce
‘‘Plsss’’
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin durk’usawa a wajen
Ita kanta ba ta san lokacin da ta ce “a’a dan Allah kar ka sunkuya’’
Ba tare da ya damu ba ya ce ’’ai ba ki ce ya wuce ba’’
Ya fad’i hakan yana me durk’usawa a gabanta.
Gaba d’aya kunya da takaicin kanta ne suka lullub’e ta, bata san lokacin da ta ce ’’ya wuce! nima sai yanzu na lura baka ma sani ba, dan Allah ka tashi’’
Murmushi ya yi kafin ya mik’e a hankali yana kallonta sannan ya ce ’’ashe dai ana so na!’’
Da sauri ta runtse idanunta a ranta ta ce ‘’Tabbas Ina sonka Yashjub!’’
Dariya ya yi kafin ya ce ’’dole ki runtse ido mana’’
A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa ta yi shiruuu, kafin chan ta ce ’’wacece Mommy?’’
Murmushi ya yi kawai…
a hankali yake kallon fuskarta yana karantarta, yana jin wani sanyi yana ratsashi….
Sai da ta sake cewa ‘’um?’’
Tukunna ya ce
‘’Sisters d’ina ne dukkan su,
Mommy kuma is my mom(mamana ce).”
Bai bata damar cewa komai ba
Ya ce “mu bar wannan maganar, yanzu mu yi maganar da ta shafe mu’’
Ahankali ya ji ta ce
‘’Kuma ita ta haife ka?’’
Lumshe idanunsa ya yi ya bud’e tukunna ya ce ’’ki bar maganar mana, um??’’
Girgiza kanta kawai ta yi
kafin ta ce ’’kawai na ga yadda ka yi ne
kamar baka wani damu ba
Wanda hakan sam bai dace ba!.
Na san bai kamata in shiga cikin abubuwanka na kashin kai ba
amman uwa ta fi k’arfin wasa..
Indai har wadda suka kira da Mommy Mahaifiyarka ce to a gaskiya abunda ka yi bai kamata ba.
Ni yanzu haka so nake ace Innata ta turo wani ya bani sak’o ko mu yi magana Baki da Baki ma ni da ita
amman ba ni da damar yin hakan.
Shawara ce nake baka
dukda na san na yi maka shishshigi amman na kasa haƙuri ne tunda naga abun ya shafi Uwa!
dan babu abunda yake ɓata mini rai kamar inga ana d’aukar Mahaifiya ba da muhimmanci ba
Dan haka
dan Allah idan zai yiu ka yi k’ok’ari ka gyara hakan,
Once again ka yi hak’uri idan na zarce iyakata.’’
Shiruuu kawai ya yi yana sauraron ta, tunda ta fara har ta dasa aya.
Jin ya yi shiru yasa ta d’an d’ago ta kalleshi…ganin kawai ita ya ke kallo ne yasa ta d’an kauda idanunta daga garesa a hankali.
A lokaci d’aya ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
‘’Thankyou! inshaaAllah na yi
miki alk’awarin zan gyara.
Kawai dama mun d’an samu rashin fahimta ne amman inshaaAllah
komai ya wuce daga yau!
Na yi miki alƙawari.
Sannan
Kar ki sake cewa kin zarce iyakar ki a cikin rayuwata ko hurumi na kashin kai na saboda Mannubiya kece rayuwar tawa ba ki da iyaka a komai nawa
duk abunda ya shafe ni to ya shafe ki….
Inaso ki yi kutse, ki shiga, ki yi duk yadda kika ga dama, dan tabbas in kikayi hakan zai sanyani farin ciki.
A yanzu amincewarki gare ni kawai nake jira, daganan idan mun zama d’aya komai nawa ya zama naki.
Na dad’e da gama tsarawa ‘matata ita ce ni
nine ita.’
Kawai ina fatan za ki bani damar da zan nuna miki how much I love you (yadda na ke son ki)…….’’
Manubiya ji take yi kamar ta ce mishi “eh, itama tana son shi. amman kuma tana buk’atar shawara da su Jidda kafin ta ce komai, dan ita kanta ta san kuma tana gani kamar Yash ya fi k’arfinta amma dukda hakan tana buk’atar shawara da wani nata
wanda zai bata izinin ta kulashin saboda itama a karon kanta abunda take so d’in kenan.
Abu na biyu kuma ko da ace zata ce masa tana son shi har ga Allah ba za ta iya kallon cikin idanunshi ayanzu dai ta fad’a mishi ba,
dan wata tsananin kunya kwarjini da girmansa take ji take kuma gani.
Abu na uku kuma abunda yayi mata yanzu ta ji zafi dukda kuwa ya bata hak’uri kuma ita kanta ta lura dagaske bai sani d’in ba amman tanaso ta sake jaddada mishi sannan su fahimci juna sosai akan
‘Ko bakin hijabinta bata yarda ya sake tab’awa ba’….’’
Dan haka kawai sai tace masa
‘’once again (Har ila yau), mun gode kwarai.
bari in wuce gida’’
Murmushi kawai ya yi kafin ya ce
‘‘Okay ranki ya daɗe! duk yadda kika ce hakan za a yi.
In kai ki? Ko in saka a maidake?’’
Yayi mata tambayar yana mai tsare ta da idanuwa.
A hankali ta girgiza Kai kafin ta ce ’’na gode’’ daga haka ta juya ta wuce
Numfashi ya fesar sannan yace
‘’Ina jiran amsata’’
Tsayawa ta yi i ta kasa gaba ta kuma kasa juyowa
Bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba sai da ta ji maganarsa a setin kunnenta
A hankali yana cewa ‘’pls dear, don’t keep me waiting‘’
Da sauri ta yi gaba ta fice daga office d’in tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya……
Shima ajiyar zuciyar ya sauk’e sannan ya fesar da iska yana wani sihirtaccen murmushi kafin ya koma ya zauna a fili ya ce ‘’Alhamdulillah’’
Kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya mik’e, ya bi bayanta da sauri…..
Sai da ya nemi adaidata sahun da ta kwanta masa ya sakata tukunna hankalinsa ya kwanta…haka nan suka rabu kamar basa so bayan ya ce mata ‘akwai ƴar uwarsa ta musamman da zata kirata, mai suna Yahanasu.’
Sai da suka k’ule ya daina ganinsu tukunna ya juya ya koma builɗing d’in, har ya isa shi kad’ai sai faman murmushi yake ta yi..
Ba drivers ba hatta securities na company d’in nashi sun sha mamaki yau, dan haka sukayi ta y’an ƙus-ƙus d’in su a tsakani shi kam Yashjub bai ma san sunayi ba.
Sai da suka yi nisa da company d’in tukunna Manubiya ta samu ta shak’a sanann ta fesar da wani bahagon numfashi, dan tun d’azu ji takeyi kamar an shak’e ta,
gaba d’aya kunya!k’auna!shauk’i!da asalin mamakin Yash sun hanata sukuni…
Yashjub yana zama a office, aikin Yassir wanda ya saka a gaba ya d’an tab’a, kafin daga baya ya fad’a duniyar tunani….
Ya kuwa dad’e yana lissafe-lissafenshi kafin ya mik’e ya fice daga company d’in gaba d’aya dan dama saboda Mannubiya ne ya zo yau…..
A b’angaren su Kausar kuwa, suna fita ta samu gaban company d’in chan da d’an nisa ta yi parking.
Kallonta kawai Yassira ta ke yi
tana mai jin wani tsananin tausayinta ya na sake lullubeta a lokaci guda kuma tana da na sanin gaiyyatar ta ɗin da ta yi akan su zo nan ɗin, dan inda ace ta san za su yi wannan mugun ganin to da ita kaɗai za ta zo abinta, su tattauna ita da Yash d’in akan Mommy su magance matsalar iyaka su biyu’ kawai! Dan ba zai yiu ace ta zuba ido tana gani yana gaba da uwar su ba’.
Ta lura da yadda Kausar d’in ta ci uban kwalliyar da ita kanta ta ma manta rabon da ta ga ta yi kwatan kwacin irinta, gashi ta zo amma ko kallonta Yash d’in ma bai yi ba, gashi kuma sun yi mugun gani…..
Yassira tana cikin wannan tunanin ta ga Kausar d’in ta zaro wayarta. Wani cleaner wanda su ke shiri kuma suka shirya akan zai ke fad’a mata shige da ficen Yash ɗin! Ta kira.
Yana zuwa ya fara sosa k’eya, bayan sun gaisa kuma yayi shiru, ya sunkuyar da kanshi k’asa dan tun a ranar da yaga Manubiya ta zo an kaita har office d’in Yash ya kamata ace ya kira Kausar ya sanar da ita a yadda suka tsara amman kawai shi baya son wannan harkar ne dan ya zama kamar munafurci da cin dunduniyar Yash kenan
Mutumin da wani lokacin in wata ya k’are har k’ari yake yi musu akan salary d’in su…..
‘’Ka san laifin ka kenan’’
Muryar Kausar ta katsewa cleaner d’in tunani
Murmushi yayi ya d’an sosa k’eya, ahankali ya ce
‘’Afuwan hajiya! na d’an yi
tafiya ne, nima yau na fara ganinta da na tambaya shine aka ce min ai ta d’an kwan biyu’’
Sarai Kausar ta fahimci k’arya ya shirga mata, shiyasa ta ce ‘’Ina da recording d’in wayoyin da muka yi ni da kai,
ba zan damu ba dan Yash ya san me nakeyi
dan haka idan baka bi min Yarinyar chan ka gano min gidansu ba
tou zan kwashe komai in tura masa.’’
Da sauri yace ‘’ki yi hak’uri dan Allah, inshaaAllah zan bi ta, yanzu ma kuwa. Tana fitowa zan bi ta.”
‘’Ka d’auko min number gidan adress d’in ta da sunanta da komai’’
Dasauri yace
‘’To to,angama…’’
Kafin ma ya gama amsawa har ta kunna motar, bata sake bi ta kansa ba ta figi motar suka wuce.