Sashe 34
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani kalar murmushin takaici
Yahanasu ta yi kafin ta ce ’’kar ki damu, sam ba laifin ki bane ba Munirat,
Idan ba ki sani ba yau ina so ki sani ‘wannan shine aure na 8 da aka so a kulla min yana warwarewa’!
sam ban ji haushin ki dan ya ce ke yake so ba, kawai dai ina kuka ne sabo da…..”
Salatin da Kausar ta rafka ne ya katse su, tashi d’aya ta figo Hannun Munirat sai da ta kai ta tsakiyar parlourn tukunna
ta ce
‘’oya oya!
20 minutes kawai zan iya baki!
Ki tartare garbage d’in (sharar) tsummokaranki ki bar gidan nan tun kafin in yi miki abun da za ki yi regretting (da na sanin) haihuwar ki da aka yi a duniya’’
Cikin tsananin b’acin rai takaici da kuma tausayin Yahanasu
waenda suka had’e waje d’aya
suka tunzura Munirat ta kalli Kausar da idanuwanta da suka jik’e da hawaye ta ce
‘’Ai ba ke kika kawo ni gidan ba,
ballantana ki ce za ki koreni’’
Kamar jira Kausar d’in take yi tashi d’aya ta d’aga Hannu ta
d’auke Munirat da mari!!!
dai-dai nan Mommy Ummi
da su Yasira suka faara firfitowa sakamokon hayaniyar da su
ke ji sama-sama tana d’an k’ara yawa.
Kallon ƙasƙanci da tsana Kausar ta yi mata kafin ta matso daff da ita
ta ce
‘’Ko Yasira kin tab’a jin ta gaya mini magana anyhow a cikin gidan nan?’’
Da sauri Ummi ta k’araso ta ce
‘’Kausar, mai ya had’aki da k’anwar taki haka?’’
Cikin rashin kunya da tantiranci
ta kalli Ummi sama da k’asa ta watsar sannan ta juya ga Mommy wadda ta k’araso garesu yanzun ta ce
‘’Mommy, senator ya ce ya fasa auren Yahanasu, Munirat zai aura!!!
All thanks to abun da ta zuba masa a cikin abinci ya ci yau’’
Kusan duk a tare Ya‘isha,
Yasira, Yusra da Yasmeen su ka ce ‘’watt!’’
Suna zaro ido
‘’Dama tun da na ga tanata faman kai kawo a kitchen da sunan tayata girki wallahi na san za a rina!!!
Idan ba haka ba tayaya tashi d’aya zai ce wani ita yake so? Kaff y’an Matan gidan nan bai ce yana son kowa ba, sai ita’’
Cewar Kausar.
‘’Ya Isa haka Kausar’’
Ummi ta fad’a cikin d’an tsare gida
‘’Ke Saddik’a bai Isa ba!!!
ko kowa ba zai yi magana ba ni zan yi magana kuma sai in da k’arfina ya k’are wallahi, sai kun warware abun da kuka yi kafin ta bar gidan nan, dan ba za mu iya ci gaba da ganin Yahanasu a wannan situation d’in ba’’.
Kausar ta ce tana kallon cikin Idanun Ummi…
Da sauri Yasira ta matso ta ce ‘’Tabbas nima zan yi magana, kuma bayaga haka ma yau in ta yi mata aka yi shiru gobe d’aya a cikin mu zata sake yi wa dan haka dole a d’auki mataki’’
Kamar yadda Kausar da Yasira suka ce ‘sai Munira ta bar gidan
After ta warware asirin da ta yi wa senator yau ba sai gobe ba’ haka ma su Ya’isha da Yasmeen da su Yusra suka yi wa Ummi da Munirat chaa!! A ka!
chin kashi Kala-kala babu kalar wanda ba su yi musu ba a wannan ranar…
Ganin rashin kunyar tasu ta yi yawa ne yasanya Ummi ta kalli Mommy da Baabaa Larai ta ce
‘’Yanzu sai na ce ku hana su tukunna za ku yi magana??’’
Dai-dai nan Daddy ya shigo cikin parlourn ransa a b’ace da alamun ya sallami Senator ya fita ta k’ofar baya sannan daga gani basu k’ark’are k’alau ba..
A hankali Mommy ta ce
‘’Saddik’a, situation d’in nan is out of my hand(al’amarin ne ya fi ƙarfina), Yaran nan sun fi ku gaskiya…
Yahanasu has sufferd a lot (Yahanasu ta sha wahala sosai) a kan irin wannan issue d’in.
a ko da yaushe idan irin hakan ta faru mu kan ji inama ace munada ikon gyarawa, yanzu kuwa muna da iko kinga kuwa ai bamu da abun yi wanda ya wuce mu gyara d’in ko?.
Idan ba ki duba komai ba to ina so ki duba maraicin Yahanasu dan Allah ki yi wa Munirat magana, a samu a daidaita komai, wallahi
Yarinyar nan tausayi ta ke bani, ba zan iya ci gana da ganinta cikin wannan pain ɗin ba.”
Wani sanyi Daddy ya ji a zuciyarsa, in akwai abunda zai iya rantsuwa akai to shine
‘tsaftatacciyar zallar ƙaunar da Mommy take yi wa Yahanasu!..’
dukda ta kasance y’ar kishiyarta kishiyar da ya fifita nesa ba kusa ba a sama da ita amma sam Mommy bata kishi ko jin takaicin Yahanasu.
Cikin kaiwa iya wuya
Ummi ta ce
‘’Haba Mommy..
Ita kuma Munirat d’in ba marainiyar bace?.
kamar yadda Yahanasu ta ke marainiya haka Munirat itama,
Hasali ma maraicin Munirat ya ma fi na Yahanasu tunda ita uba ta rasa’’.
Cikin tsananin fushi Daddy ya ce
Saddik’a……….
……..
Sai da Yashjub ya yi sallah, ya yi wanka ya d’an huta tukunna ya d’au makulli ya nufi gidan da Yasir yake.
Shi Yasir a tunaninsa ya b’oyewa kowa ne bai san tun lokacin da ya saka Ƙafa ya bar gidan idanun Yashjub yake a kansa ba..
da farko Abuja ya wuce sai last week tukunna ya dawo shi da tawagar y’an Mata da Abokansa suka
tare a guest house d’insu d’aya daga cikin Abokanayen nasa su ke cin karen su babu babbaka.
Wallahi,ba daban yana jin tausayin Mommy da halin da take ciki kwana biyu ba
sannan shi kan shi yana jin Yasir d’in a ransa tunda duk lalacewa dai d’an uwansa ne shi ɗin ciki d’aya suka fito, to da tuni ya turawa su Yasir y’an Hisbah!!!
Kuma ya cikawa y’an Hisbahn aljihu ya had’asu da manyan sojoji sun nad’e kaff d’in su ta yadda ba uban wanda ya Isa ya amsosu….
..
Yana zuwa bakin gate d’in tun kafin ya gama mik’a hancin motarsa ga gate d’in wani mutum k’ak’k’arfa sanye da gajeran wando da vest ya taho daga majalisar chan gefe da gudu yana cewa ‘’kai! Kaii!! Kaii!!’’
Sai da ya zo
Jikin glass d’in motar ta dai-dai inda yake ya d’an buga tukunna Yashjub d’in ya ma lura da shi.
Glass d’in motar tasa bullet proof ne sannan hankalinsa ya tafi ga lissafin ta yadda zai shiga gidan saboda ya san Yasir da shegen wayo da taka tsantsan ba zai tab’a zama babu security ba..
Sai da ya gama k’arewa
mutumin kallo tukunna ya zuge glass d’in motar tasa,ya zuba masa dogayen idanuwansa kawai ba tare da ya ce komai ba.
Cikin girmamawa mutumin ya ce
‘’Oga ai masu gidan basa nan,
sun yi tafiya,sannan ni ban ma sheda ka ba …’’
Dai-dai nan wasu samari guda biyu suka k’araso suka saka mutumin a tsakiya fuskarsu babu alamar wasa.
Sai da Yashjub ya d’an lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna
ya d’an matso mutumin
yana kallon cikin idonsa ya ce
‘’Ni yayan Yassir ne, na san ka san shi..
Yasir wanda ke a cikin wannan gidan yanzu haka’’
ya yi maganar yana nuni da gidan kafin ya d’aura da cewa ‘’Ban zo ba sai da aka tabbatar min da yana nan yanzu haka.
Ka bud’e min ko in kira maka sojoji da y’an Hisbah,
dan in baka barni na shiga ba hankalina ba zai kwanta ba sai na tabbatar na yi maka d’aurin goro.
Amman in ka barni na shiga
zan baka kud’i yanzu ka kama gaban ka dan kar ma su hukuntaka kuma zan hana Yasir nemo ka ya hukuntaka shi kuma Yasir na san zai yi maka tsakani da Abokansa.
Shiruu Mutumin ya yi yana
kallon Yashjub….
Suturar jikinsa, motarsa da kuma yanayinsa kad’ai sun isa su sanya a fahimci tabbas kud’i sun zauna sannan ya jik’u a naira, yana lura da yadda Abokan Yasir d’in suke yi masa fadanci saboda duk ya fi su kud’i to Ina kuma ga yayansa,kar ya je garin gadin y’an tsaki ya janyowa kan sa fad’a da giwa..
‘’Ina da abun yi ka tsaida ni’’.
Yashjub ya fad’a yana d’an kallon tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar Hannunsa.
Sai da mutumin ya kalli Mazan dake a gefe da gefen sa su ka yi masa sign da ido tukunna ya kalli Yashjub ya d’an jinjina kansa alamun amincewa.
‘’Hmmm’’kawai Yashjub ya ce
yana mai d’an girgiza kansa daga nan ya d’auko bandir biyu na kud’i ya mik’a masa.
Wani kalar murmushi Mutumin ya yi shi da samarin biyu daga nan ya sa Hannu ya amshe ya yi godiya..
A tare su duka ukun suka shiga gidan ta k’aramar k’ofa suka wangale masa gate ya shige su kuma suka d’auki ghana most go d’insu dake a d’akin mai gadi suka yi gaba abun su..
Gida ne mai kyau flat babba sosai dan compound d’in zai d’auki motoci kamar 15 haka,sai pool da pool house d’in shi a ta baya.
Flat din kuma daga gani d’akunan ba zasu wuce 5 ba da maybe 2 two parlours da kitchen haka.
Yana yin parking ba tare da b’ata lokaci ba ya bud’e motar ya d’au wayarsa ya fito ya nufi main door d’in gidan.
Tsaki yayi ganin ta a rufe dan haka ya d’an danna bell ya koma gefe ya tsaya.
Budurwar da take parlourn zaune tana kallo ce ta mik’e a ranta tana cewa’’i wonder who that could be
(Waye kuma ya zo mana?’’.
Tana zuwa bakin k’ofar ta d’an tsaya ta lek’a…
duk da ta y’ar b’ular k’ofar ta gan shi hakan bai hanata ganin tsananin kyawaun sa ba, jikinta da hannunta har rawa suke yi haka ta sa Hannu ta bud’e k’ofar cike da zumud’i.
Tana bud’ewa ta d’an saita kanta kana ta d’an karkace tana wani irin shu’umin murmushi.