Sashe 13
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun lokacin da Mommy ta turo k’ofar ta shigo Kausar ta lura da ita
amma sai ta yi kamar ma ba ta san mutum ya shigo ba, tana kwance Idanunta suna kallon sama har zuwa lokacin da Mommyn ta zauna a kusa da k’afafunta Idanunta ba su motsa ba, ta na nan a ƙame kamar farko alamun ta yi zurfi a tunani kenan, ta ke so ta ce.
A hankali Mommy ta ce
‘’Kausar’’
Jin shiru ya sanya ta d’an sake k’ura mata ido kafin ta sake cewa ‘’Kausar’’
Nan ma shiru taga Kausar d’in ta yi, babu ko gezau!
Dan haka ta kama k’afafunta ta d’an jijjiga kafin da d’an k’arfi ta sake cewa ‘’Kausar!!’’
tana me kallon fuskarta.
A firgice Kausar ta ɗan kalli Mommy, sai kuma wasu hawaye suka tsinke mata, a lokaci guda.
Aikuwa nan take Mommyn ta rikice!
Ta shiga tambayar ta “menene?” a lokaci guda ta na mai k’ok’arin zaunar da ita.
Sun jima kafin dakyar ta samu Kausar d’in ta d’an yi shiru, tukunna a hankali Mommyn ta kamo Hannayenta tace
‘’In dai akan fad’an da na yi miki ne ɗazu, ki yi hak’uri, ba zan sake ba inshaaAllah, ki daina kuka komai ya wuce.’’
Wani kalar murmushi Kausar ta yi wanda ake cewa yafi kuka ciwo,
kafin ta shiga girgiza kanta sannan a hankali ta ce
‘’Ba shine ya saka ni kuka ba, kawai dai ina tunanin ‘ina ma ace Ammina tana da rai’, ne’’.
Cika Hannuwan nata Mommy ta yi a take kafin ta ce
‘’Kar ki yi min haka Kausar’’.
Da sauri Kausar ta ruk’o Hannayen Mommy kafin ta ce
‘’Kar ki yi misunderstanding ɗina.
Mommy ko da ace Ammi tana nan na san iyakar soyayyar da kike yi mini ita ma zata min!
Maybe ma ba lalle ya kai naki ba.
Kawai ina tunain ‘ina ma ace tana raye’ saboda na san inda ace tana nan to ba lalle in zauna a gidan nan ba, babu ruwana da takurar Yasir da kuma tsangwamar Yashjub.
Har ga Allah Mommy bani da matsala dake ko su Yasira,
amman Yassir!! Shine matsalar da ya fi damuna sannan saboda Yash ne naji inason barin gidan nan gaba ɗaya, dan
akwai wani abun da yake damu na wanda in dai ba Ammi na ba to wallahi ko ke kanki ba za ki taɓa iya fahimta ta ba.’’
Ta ƙarashe maganar tata tana mai fashewa da kuka.
A hankali Mommy ta share hawayenta kafin ta ce
‘’Na fahimce ki, na fahimci dalilin furucin ki na ɗazu.
Abunda nakeso dake yanzu shine
Ki faɗa mini abu uku…
Na farko
mecece matsalar ki da Yasir
Na biyu
Meye damuwarki da Yash,
Na uku kuma
wanne irin abu ne yake damun ki wanda har kike tunanin Ammin ki ce kad’ai zata iya fahimta?’’
Ba tare da tantama ba
Kausar ta ce
‘’Mommy bana son Yasir, shi kuma naga alamun kwana biyun nan kamar wanda aka yi wa wahayi aka ce dole sai ya aure ni.’’
Duk da Mommyn ta ji ba dad’i
yadda Ƙausar ɗin ta gaya mata direct bata son Yasir, amma sai ta yi k’ok’ari ta danne ta sake riƙe hannun Kausar d’in duka biyu kafin ta ce
‘’Faɗa kukayi?
wani abun ne ya faru ?’’
Ganin kausar ta ƙi ta bata amsa ne ya sanya tace
‘’To, koma dai menene ya faru ina mai baki shawarar ki yi hak’uri ki auri Yasir domin shine rufin asirin ki, ko kina tunanin akwai namijin da zai aure ki ba tare da ya san wacece ke ba?’’
Sai da Mommy ta runtse idanuwanta ta bud’e tukunna ta kalli Kausar d’in ta ɗaura da cewa
‘’Kausar ki yi hak’uri ki rufa mana asiri, kar ki ɓata mana sunan family’’.
Da sauri ƙausar ta ce
‘’Mommy ni fa ba wani wajen na ce miki zan je in yi aure ba! A cikin gidan nan zan yi, dan haka kinga wanda zan aura ɗin already shima ya riga da ya san maganar haihuwar da na taɓa yi da kuma maganar Mahaifi da komai nawa.’’
Cikin tsananin ɓacin rai Mommy ta yi wurgi da Hannun Kausar da ke a cikin nata kafin ta mik’e tsaye ta ce
‘’Kar ki kuskura!!!!
Wallahi kar ki soma Kausar. Ba na son iskanci da yayen sabon rikici a cikin gidan nan!!!
Ba zai yiu ba.
Dan haka tun wuri ma ki farka, dama naga take-taken ki tun wanchan watan da ya shige ashe kuwa hassashen da nake yi gaskiya ne.
To bari ki ji, ki bud’e kunnuwanki da kyau!!!
Wallahi ba zan yarda ki raba mini kan ƴaƴana ba, Ina raye.’’
A hankali hawaye yana zubo mata Kausar ɗin tace
‘’Saboda ni ɗin ba ƴar ki bace ba?’’
Rikici da ɗimaucewa ne suka sanya Mommy ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari!!!
Cikin fushi ta fara magana
‘’Kar ki kuskura ki murƙushe tunanina da dabararki saboda son ranki wawuyar Yarinya kawai, doluwa.
In banda rashin tunani ma irin naki
tayaya ma
za ki bar Yasir wanda ya ke tsananin ƙaunar ki da tausayin ki
saboda
Gawurtaccen miskilin Mutum irin Yashjub???
Mutumin da na san ba zai taɓa ƙaunar ki ba ko da ace baki kasance budurwar ƙaninsa tun asalin farko ba’’.
Wannan karon mikewa tsaye Kausar ta yi!
Cikin faɗa-faɗa itama ta ce
‘’Mommy kinga ta inda ake cuta ta ko?
Ko kuma ince ta inda ni da kaina na lalata komai sannan na ɗaure kaina da jijiyoyin jikina..ta hanyar kasa cewa kowa ‘ba son Yasir nake yi ba’.
Kuma kina so ki san dalilin da ya hanani yin magana?’’
Bata jira jin amsar Mommy wadda ta kafe ta da idanuwa ba ta ɗaura da cewa
‘’Saboda kawaici da kunyar in kalli idanun ƴan gidan nan in ce musu bana son Yassir.
In banda hakan
Wallahi tallahi kin ji dai na rantse miki ni ban taɓa son Yasir ba tunda na yi wayo na san kaina….
friendship dai tun Yarinta na san akwai shi, Ina son sa a matsayin ɗan uwa kuma Aboki amma bayaga hakan babu komai kuma tsakaninshi da zuciyata.
Yashjub shine wanda na san inaso tun tasowata har kawo yanzu da soyayyarsa take neman kashe ni Mommy,
wallahi inda ace ba Yash nake so ba tou da zan
iya haƙura in auri Yasir amman matsalar shine ba zan iya auran ƙanin wanda zuciyata take ƙauna ba.”
Ta ƙarashe maganar tana mai durƙusawa ta kamo ƙafafuwan Mommy cikin kuka ta ce
‘’Mommy dan Allah ki fahimce ni na yi kara na yi kawaici amma zuwa yanzu idan na ce zan ci gaba da yin kawaicin tabbas cutuwar zata yi mini yawa, wallahi mutuwa zanyi!!!
Ki fahimce ni Mommy dan Allah.’’
Suna a hakan,
Yasira ta shigo ta same su.
Da sauri ta ƙarasa ta ɗago Kausar ɗin sannan ta shiga rarrashin ta
kafin ta kalli Mommy ta ce
‘’Daddy ya dawo, yana ta neman ki’’.
Da kyar Mommy ta iya jan ƙafafuwanta, ta fice daga balcony ɗin tukunna ta bar parlourn ba tare da ta kalle su ko ta sake ce musu uffan ba.
Tana fita Yasira ta kalli Kausar wadda har yanzu take ta faman gunjin kuka ta ce
‘’Sannu, dan naga k’ok’arin ki, amma kuma mood ɗin Mommy kaɗai ya sanya jikina yayi sanyii….
Ina matuƙar son in ga na taimaka miki game da lamarin nan Kausar (really wanted to help u) amman inaga gara kawai ki haƙura haka nan, dan gashi Mommy kanta bata baki goyon baya ba, dama na san tunda case ɗin ya shafi favorites ɗin ta to ba lalle ki yi nasara ba!
no matter yadda kuke ke da ita’’.
Shiru Yasirar ta yi kafin ta ci gaba da cewa
‘’ki yi hak’uri sis, ki hak’ura kawai.’’
A hankali cikin goge hawaye Kausar ta ce
‘’Yasira!!
Yasir da Yash and me
ne favorites ɗin Mommy ko kin manta? Za ki ce na gaya miki
Mommy tana side ɗina.’’
Da mammaki Yasira ta ke kallon ta.
With full confidence Kausar ɗin ta sake cewa ‘’yeah,
za kuma ki ce na faɗa miki.’’
Ta na gama faɗin haka ta juya ta bar wajen, ta shige toilet domin ta wanko fuskarta…..
Duk da tana fargabar yadda zata kaya tsakanin ta da Daddy, Yash da kuma Yassir amma ta san tunda yanzu Mommy ma tana bayan ta to komai zaizo mata da sauk’i.
Although Mommyn bata riga ta faɗa mata cewar tana bayan nata ba amma ta gani a yanayin ta da kuma idanunta dan haka ta san definitely tana bayan ta.
Tun kafin Yashjub ya dawo Nigeria
ta lura da yadda Mommy ta ɗaga hankalinta akan tarin dukiyarsa,
tabbas Yash bai saba da Mommy sosai ba kuma bama a gabanta ya taso ya girma ba hakan ya sanya Mommyn duk ta bi ta ɗaga hankalin ta.
Babu abunda ta lura Mommyn bata so kamar Daddy yq yi maganar auren Yash da wata!
kuma ta san ba dan komai yasanya Mommy bataso Yash ya yi auren ba sai dan saboda kar wata ta zo ta ƙarasa janye mata Yash ɗin da shi da dukiyarsa gaba ɗaya ba tare da ita Mommyn ta samu sun shaƙu da Yash ɗin ba.
Ta san Mommy kamar yunwar cikin ta!
Duk yadda ta kai ga ji da Yassir
ba zata taɓa bari ga Kausar wadda ta nuna tanaso ace wai
Kuma Yash ɗin ya je ya auri wata daban ba.! Dan ta san in dai Yash ya auri Kausar tou da shi da dukiyar sa kamar sun dawo Hannunta ne sun gama………
•••••••
Shinkafa mai kyau da kayan miya harda nama Ya Musbah ya kawo.
Babu yadda Jidda bata yi da Mannubiya ba akan ta barta za ta yi amma sai da ta saka mata Hannu a aikin.
Dama tun suna girkin suka dunga shiga one by one suna yin wanka
dan haka
Girki yana kammaluwa dai-dai nan suma sun shirya abunsu tsaf.
Babu fannin da basu shiga a gidan sun sanar musu da rashin lafiyar Inna ba,
amman Baba Habu ne kawai ya bada kuɗin lemo ragowar kuwa ba wanda ya basu ko sisi
Anty Umma ce ma ta ce “inshaaAllah zuwa anjima za ta je ta asibitin ta duba ta in Siyama ta dawo.”