← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 84

Sashe 56

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘’Na san kin san ta fita ko?
so za ki iya fitowa,
Sannan nan gaba dan Allah ki daina motsi da k’ofa
wajen yin lek’en, dan kad’an ya rage ba ki yi drawing attention d’in ta towards inda kike ɓoye ba
(ba ki ja hankalinta zuwaga inda ki ke ɓoye ba).’’
Yassir ya fad’i hakan ba
tare da ya juya ya kalli k’ofar bathroom d’in ba, kafin a hankali ya durk’usa ya fara d’auke candles d’in yana kashewa.
Dai-dai nan Kausar wadda ta fito daga toilet d’in ta k’araso kusa da shi itama ta sunkuya ta fara tayashi, suna kwashewa suna kashewa a tare.
….
Ganin ya ƙi kulata ne ya sanya ta ce
‘‘Haba dear!
wai har yanzu fushin ne?’’

Mik’ewa ya yi fuskarsa babu alamun wasa ya ce
‘’Kausar!it’s either you talk (ko dai ki faiyyace min komai) ko kuma in yi fatali da wannan plan ɗin naki gaba ɗaya wallahi!.
kin san dai yin hakan ba k’aramin aiki na bane ba ko?’’

Murmushi ta yi kafin ta ce
‘’ka tabbata?
Na fa san halinka,
Kuma take-taken ka ma akan Yarinyar na gani shiyasa na zo maka da wannan tayin, domin mu samu mu jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya.
Are you sure(ka tabbata) za ka iya yin fatali da mission d’in nan (manufar nan tamu) ba tare da ka samu abunda kake so ba?’’.

Cikin fushi ya mik’ar da ita tukunna ya ce ’’and you are not even jealous!(Kuma ba ma kya kishi!!)…

tabbas yanzu na sake tabbatarwa
raina min hankali kike son ki yi..kin ga Kausar i’m not your pet (ni ba abun wasanki bane ba)
sannan ni ba k’aramin Yaro baneba…..

Kwanakin baya da suka shuɗe kin nuna kin tsaneni, yanzu
kuma a cikin kwana biyu kawai kin dawomin!.

Idan kin san wasa za ki yi min da hankali saboda ki samu ki cimma wata manufa taki to wallahi tun wuri ki janye!!

Idan kuma ba ki janye ba to this time around (wannan karon) zan ba ki mamaki!!
bar ganin wai Ina son ki wallahi I can be your worst nightmare(wallahi zan iya zame miki babban masifarki)…

Ba wanchan Yassir d’in da kika sani baneba har yanzu,
Yanzu na chanja.

Sannan
kin ce akwai reason d’in (dalilin) da ya sa kukayi calling off auren mu ke da Mommy(da ya sa kuka janyo aka fasa aurenmu, ke da Mommy)…..
Inaaso in ji dalilin da komai, inaso ki fad’amin komai, inaso in san menene shirinku dan ba zan yi participating a game d’in (ba zan bada gudummawa a wasan) da ban san inda aka dosa ba…
Ba zai yiu ki dinga yi min abu ta bai bai ba, akwai abubuwa da dama da na ke so ki fahimtar dani
If not (idan kuma ba haka ba to)
kawai inaga gara abar……’’

Rungumeshi tayi wanda hakan ya sanya ya kasa ci gaba da magana..

sun d’an jima a haka
tukunna ta d’ago ta na kallonsa ta ce
‘’Yassir ba zan iya gaya maka dalilin mu ni da Mommy ba, ka yi haƙuri.

Na fad’a maka mun fasa ne saboda Kai da kuma farincikinka duk abunda mukayi mun yi shi ne saboda Kai!
Idan ni ba ka yarda da ni ba!
na san ka san dai Mommy ba za ta tab’a nemo bak’in cikinka da hannnunta ba dai ko?

You just need to trust us on this one
(Naka shine kawai ka yarda da mu a wannan lamarin)
Saboda ba zan iya fad’a maka ba.

Abu na biyu kuma kai nake so Yassir, Ina sonka tun farko..
fushin da ka ga Ina yi da Kai kwanakin baya kawai Ina yi ne saboda ina so ka bani space (iska) a samu a fasa auren mu da gaske.
Ba za ka tab’a samun abunda kake so ba tare da ni ba!
Dan haka ka taimakemu, ko kuma in ce ka taimakeni in samu in
fitar da Ummi daga cikin gidan nan!
In gyara tsakanin Daddy da Mommy!
ta yadda za mu samu mu yi maka gatan da muke son yi maka, daga nan in ya so sai a yi maganar aurenmu.
ka fahimceni?’’.

Kanshi tsaye ya girgiza mata Kai kafin ya matsa daga Jikinta da inda take sannan ya juya mata baya tukunna ya ce ’’ban fahimceki ba Kausar!
not untill you tell me (har sai kin gaya mini)
ko da ace d’an single hint(ƙaramar alama) ne.

Ba zan tab’a fahimtarki ba idan ba gaya min kika yi ba kuma in ban fahimceki ba
ba zan taimake ki ba.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce
“shikenan Yassir, amma kar ka bari Mommy ta san ka sani dan Allah’’

‘’I promise
(Na yi alƙawari)
kawai yace,
yana mai juyowa ya kafeta da idanuwa.

Sai da ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana
‘’Ka san tun lokacin da aka haifi su Yahanasu,
Daddy ya bawa Yashjub rabin dukiyar shi ko?’’.

‘’Continue
(Ki ci gaba)”
Yassir yace yana mai gyara tsayuwarshi

A hankali Kausar ta ci gaba da cewa
“Da wannan rabin dukiyar da kuma taimakon ƙwazo da aiki tuƙurun da Yashjub ya ke da su ne suka zamto silar da a yanzu haka hatta Daddy bai isa ya kamo k’afarsa a kud’i ba!.

Bayan estates d’in da muka sani, Yashjub yanada hannun jari a companies daban-daban da kuma gidanjen man fetur!…

Ita kanta Mommy bata san da hakan ba sai last two years ago (shekaru biyu baya da suka wuce) ne ta fahimci d’umbin arzik’in Yashjub.
Daddy ne kawai ya san komai nasa amma abunda zai baka mamaki shekarar nan da ta wuce da ya tashi raba wasiyyar masu Hannun jari a companynsa(shi Daddyn)…
Kamar haka ya raba;
share d’in Yashjub (kason yashjub)a company d’in Daddy
50%ne
(Kaso hamsin a cikin ɗari)

Na Daddyn 18%
(Sha takwas a cikin ɗari)

Su Yasira su 6 kowacce tanada 1%

masu hannun jari
dama nasu already (tuntuni) 5%
ne

Mommy bata da komai ita dama

Mama 20%

naka kai kuma 1%.”

Da k’arfi Yassir ya ce ‘’watt??’’

‘’Kwarai da gaske’’
Kausar ta ce
kafin ta d’aura da cewa
‘‘Mommy ta b’oye maka ne saboda ta san idan ka sani ba za ka ji dad’i ba.
Yassir
Idan ta ji na fad’a maka ba za ta min da sauk’i ba, ko su Yasmeen basu san da maganar nan ba!

Yasira ce kawai ta sani
Dan haka kar ka fad’awa kowa dan Allah
sannan ina so ka yi min alƙawarin ba zaka yi komai ba.

A hankali ya ce’’I promise (na yi alƙawari)
Cigaba Ina jin ki .’’

Cikin son fahimtar da shi Kausar ta ɗaura da cewa
‘’Ka san a yanayin tsarin Daddy
Idam Mutum ya yi graduating (kammala karatu) ya fara aiki ma to tsame hannunsa ya ke yi a kansa
kuma tun ba yau ba ya riga ya ce ‘a cikin ku idan kuka riga kuka yi aure to
tsakanin sa da ku sai dai ku
dinga kawowa gida, dan ya gama baku kwandalarsa,’……

Tuni, ya riga ya gama gina Yashjub ya kafa shi!
Wat about you(kai
Kuma fa)?.

Yassir idan ka kuskura ka yi aure a yanzu shikenan ka tashi da 1 percent da kuma company d’inka wanda bana jin a shekara ma yana kawo maka sama da million biyu,
Shin
ta yaya za ka iya ciyar da iyalinka?
kuma na san idan baka kawowa gida kamar yadda Daddy ya tsara ba
to kuwa ka had’u da tijarar sa kenan.

Ita Mommy abunda take so shine
‘ta samu ta san yadda zata yi ta janyo hankalin Daddy a samu ya k’ara maka wani abun, ko da a cikin share d’in Mama da nasa dana Yashjub ne! A samu ayi maka karo karo kaima ka yi sama..’
To kuma an d’an fara samun nasara sai Hannun agogon gaba ɗaya ya koma baya tun lokacin da wannan matar Saddik’a ta shigo rayuwar Daddy, shikenan komai ya tab’arb’are!

We need to get her out
(Dole mu fitar da ita)!
mu gyara tsakanin Mommy da Daddy, a k’ara mata share ka tsaya da k’afafunka kaima tukunna ayi maganar aure Yassir.

A yanzu balance d’inka na duk shekara wanda Daddy yace yana tarawa kowa nasa
Idan aka tashi baka na shekara ukun da suka wuce ba a baku ba
dai dai fa kake kai da su Yasira!
A matsayinka na ɗa Namiji!….
Daddy ya tartara komai ya damk’awa Yashjub wanda ba shi da wata kyakkyawar alaƙa da ɗaya daga cikin mu
hatta Mommy…
Iyaka Daddyn ne kawai ya san cikinsa kuma ya ke ɗan shiri da shi…
Ka ga kuwa duk ranar da aka ce ya yi aure to komai hannun matarsa zai koma!
Mu sai dai mu zama y’an kallo a gefe..
Daddy can take care of himself
(Daddy zai iya kula da kanshi)
daga nan har tsufan sa yanada kud’in da zai temaki kansa da shi da Mommy!
Kai fa?
kai da su Yasira….
Allah ya rufa asiri
Idan ba ayi wani abun ba sai dai mu zama a gefe y’an kallo, abun tausayi!
Gaba d’aya arzik’in gidan nan ya koma hannun shi shi kad’ai daga shi sai matarsa
tunda tun yanzu dama ba kulamu yake yi ba……

Amman idan kuka zamto equal (ɗaya) da kai da shi, ko ma ace ka fi shi samu to
tanan ne kad’ai komai zai tafi normal!
tunda munsan kuma muna da tabbacin kai za ka kula da su Yasira da ita kanta
Mommyn sannan ni za ka aura ba wata stranger (bare) ba dan haka arzik’inmu yana nan a wajen mu.

Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin yadda
ya yi maka duka ranar nan!
Kuma ka kasa ramawa saboda baka da power, shiyasa take so ku zama ɗaya a fannin arziƙi da samu,
bata so wani ya taka wani….
kuma tana jin tsoron kar a yi ta zalintar ka ka zo ka ce zaka rama ta hanyar da bata kamata ba…

Wannan itace gaskiyar magana
Yassir, so muke yi mu taimake ka
amma sai ka bamu hadi’in kai tukunna za mu iya.
sannan dan Allah kar ka bari Mommy ta san ka sani dan bata so kowa ya ji!
Saboda ta san ba lalle a fahimceta ba, dan za’a ga kamar ta fi sonka ne akan Yashjub’’.”
Chapter 56 · 0% Book details