← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 84

Sashe 15

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin har tsawon wani ɗan lokaci Daddy bai kai ko loma d’aya Bakinsa ba ya sanya suma duk suka tsaya!.
Shiru dining d’in ya d’auka gaba d’aya….
Kafin chan Mommy ta ce
‘’Na lek’a ta ɗazu, tun kafin ka sak’k’o, amma sai ta ce mini a k’oshe take.’’

Shiru ya yi bai tanka mata ba,
ganin hakan ya sanya ta mik’e ta nufi k’ofar wani d’aki wanda ke a nan cikin main parlourn, tana ta faman guna-guni.

Bata yi mintina hud’u da shiga ba suka fito tare ita da wata farar budurwa wadda ak’alla zata kai kimanin shekaru 29 a duniya, bata da jiki sai dai doguwa ce sosai, kallo d’aya tak za a yi mata a gano tsantsar kamanninta da Daddy wanda tun fitowar su ya kafe ƴar tashi da idanuwa yana mamakin tsantsar ramar da yaga ta sake yi.

A kusa da Yashjub Mommy ta zaunar da ita.

Daga nan ta koma mazaunin ta itama ta zauna.

A hankali suka shiga passing mata kulolin abincin zuwa gabanta..
Bata zuba ba sai da ta fara sunkuyar da kanta ta gaida Daddy cikin girmamawa tare da yi masa sannu da zuwa dan itama ba ta san ya dawo ba…
da kulawa ya amsa ta tukunna ta shiga zuba abunda ranta yake so.
Tana gamawa Daddy ya yi bismillah ya fara….
Bismillah suma duk sukayi
daga nan aka gabatar da dinner d’in cikin nutsuwa.

Sai da kowa ya kammala,
tukunna Daddy ya juya ya kalli
Yahanasu
ya ce
‘’Lafiyar ki kuwa ?
duk naga kin sake ramewa’’.

Murmushi ta yi ahankali
kafin ta ce
‘’Lafiya ta k’alau Daddy,
Alhamdulillah’’.

Ya jima yana nazartar ta kafin daga baya ya d’auke kai ya maida hankalinsa kan Mommy ya fara magana
‘’Akwai Aboki na ‘senator Bashir’!
Ba wai ya kaini shekaru bane ba, kawai dai tamu ta zo d’aya da shi ne shiyasa muka zama Abokanai.
Matar sa d’aya, ya yi min maganar yana son ya k’ara aure ne
Shine na ba sa izinin ya zo yaga Yahanasu!
Is an sun daidaita
Alhamdulillah.

Na san shi tun ba yau ba, shima haka ya sanni so banajin za’a samu matsala wannan karon, InshaaAllah.
Na bar komai a Hannunki, ku shirya tarbar sa da kyau ranar juma’ar nan zai zo.’’

A hankali mommy ta ce
‘’InshaaAllah Daddy.
sannan da yardar Allah ba za a samu matsala ba.’’
Ta yi maganar tana mai yi wa Yahanasu addu’ar dacewa a wannan karon, ko ba komai hankalin kowa zai kwanta.

A hankali yahanasu wadda gaba d’aya hankalinta ya tashi lokaci guda ta ce
‘’Daddy, Dan Allah…’’

Cikin rashin son ya saurare ta ya ce
‘’Sai magana ta ta biyu.’’

A take duk suka tattara hankulan su suka maida akan sa! Ganin yadda lokaci guda ya sake tamke fuskar sa ne
yasanya
duk suka sha jinin jikinsu.

‘’Yashjub ya sanar da ni
Irin taɓargazar da Yaran nan su ke shukawa’’
Daddy yayi maganar yana nuna Yasir da Kausar.
Kafin cikin b’acin rai ya kalli Mommy ya ce
‘’I’m really disappointed in you,
da ke da su bansan wa ya fi wani ba.
Anyways, na riga na gama yanke shawarar d’aura musu Aure gobe da safe in sha Allahu!!!
dan ban shirya d’aukar shege a karo na biyu a cikin gidana ba’’…

Tun kafin ya kai k’arshen aya Kausar ta fashe da wani irin kuka, cikin sheshshek’ar kuka ta ce
‘’Allah ba zan aur……’’

Ai kuwa a take Daddy ya mik’e da shirin isa inda take,
ganin haka ya sanya ta kwasa a guje ta yi sama.

Ya so ya bita, ya ci k’aniyar ta dan dama a mugun k’ule yake da ita, bayajin haushin Yasir kamar yadda yake jin haushin ta, sannan a ganin sa ita ta b’ata Yasir tun asalin farko shi kuma bai farga da wuri ba, shikenan garin tausayi gashi Yarinya tana neman tarwatsa masa tarbiyyar Yaro ko ma ace ta riga ta tarwatsa d’in…
Muryar Mommy ce ta katse shi
jin tana cewa
‘’Daddy u need to reconsider(ka sake tunani),
wannan abun da kake shirin yi ba dai-dai bane ba!
kuma lokacin da ka d’auka a gaskiya ya yi kad’an,
dan Allah ka sake tunani.’’

Cikin tsananin ɓacin rai ya ce
‘’Bar ganin a gaban ƴaƴanki kike, wallahi yanzun nan zan kifar da ke.
kin bar Yara suna shashanci sannan yanzu ana k’ok’arin gyara abu amma kina k’ok’arin kawo tangard’a akai ??
karfa ki bari rai na ya k’arasa b’aci da ke!
wallahi ba za ki ji dad’i na ba’’.
Yana gama fad’in haka ya juya fuuu ya wuce saman shima ya nufi side d’insa.

A zuciye Mommy itama ta mik’e ta k’arasa inda Yashjub ya ke tsabar fushi bata san lokacin da ta rufe sa da fad’a ba!
Baki da kumfa ta shiga cewa
‘’Mai yasa kake da muguwar zuciya ne? Yanzu kukan da take yi dad’i yayi maka ko mai?
ka fini sanin ciwon kaina ne?
ko kuwa ka fini sanin abun da ya fi dacewa a yi?
Tunda har ka ga na yi shiru ai ka san akwai dalili dai ko?’’

A hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba mata ba tare da yace uffan ba…..
Ganin yanayin kallon da ya ke yi mata ne ya sanya ta yin shiru a take ta kauda kanta daga gareshi ta had’iye ragowar maganganun nata.

Ya jima yana kallonta kafin ya d’auke idanuwansa daga gareta ya fesar da iska ya mik’e tsaye! daganan ya fara k’ok’arin barin wajen.

Cikin tsananin sanyin jiki ta ce
‘’Yash’’
Juyowa kawai ya yi ya tsaya yana kallon ta.
Gaba d’aya kuma sai ta diririce ta gagara cewa komai
Ta hau kame-kame
‘’am dama a ganina bai kamata ka gayawa Daddy…..”

A hankali ya ce ‘’Mommy ..’’sannan ya ɗan girgiza mata kai yana mai lumshe idanunsa ya bud’e
daga haka ya juya ga Yahanasu ya ce
‘’Allah ya tabbatar da alkhairi.’’
Yana gama faɗin haka ya sa Kai ya fice daga parlourn ko sai da safen su Yadira bai tsaya amsawa ba.

Mommy ji ta yi kamar ta d’aura Hannu a ka! Ta yi ta kurma ihu!!!
Tabbas idan akwai Yaron da bai San darajar mahaifiyarsa ba tou Yashjub ne….kalli fa bashi ma da lokacin yi mata magana ballantana a je ga sauraronta ko bata haƙuru.

Tana tsananin k’aunar Yasir amman ya zama dole ya hak’ura da Kausar Yashjub ya aura dan bata hango shak’uwar da take kwad’ayin samu daga gare sa ba muddin ya yi aure ya tare chan da wata ba Kausar ɗin ta ba!
Musamman ma idan ya samo wadda yake so!
Shikenan ta zama ƴar kallo a gefe..

Tana wannan tunanin ta dake ta cire tsoro ta nufi sashen Daddy
da niyyar tana gamawa da shi kuma zata lek’a d’akin Baba Larai saboda tabbas a yau take so a yi ta, ta k’are!!.

Ɗaya bayan ɗaya aka dinga watsewa daga dining table ɗin,
ya rage saura Yasir shi kaɗai.

Ya yi mamaki haɗe da jin zafin yadda k’iri-k’iri ya hango rashin amincewar auren nasu a kwayar idanun Mommy!
shiyasa tun lokacin ya fad’a duniyar tunani ya gagara cewa komai har izuwa yanzu da kowa ya watse ya bar sa a wajen.

A hankali ya mik’e ya nufi sama sashen Kausar
amman ko da ya je ɗin sai ya tarar da k’ofarta a rufe ruff!!
Babu kalar bugu da kiran wayar da bai yi mata ba amma sam ta ƙi yarda ta bud’e, ta ma ƙi kula shi.
Haka nan ya gaji ya kama hanya ya sauk’a ya fita daga sashen gaba d’aya ya nufi nasu, wanda yake a jikin mansion d’in amma k’ofar su ta baya take da wani makeken compound a wajen wanda ya ma fi na gaban gidan dan tsaf za a iya gina irin mansion d’in guda a wajen!
Da har da gate d’insu daban
a wajen amma saboda yawan yawon dare da Yasir ya tsira yakeyi ne
ya sanya aka rufe gate d’in Daddy ya hana fita ta nan gabad’aya.

…. Parlour ne babba sosai
sai kitchen, dining area da 2 bedrooms a k’asan
sama kuma 2 bedrooms ne ko wanne da parlourn sa sai saperate d’aki guda d’aya,
Side d’in nasu ta b’angaren mansion d’in mai hawa ɗaya ne
sab’anin na su Daddy wanda ya had’a hawa biyu….

A nan main parlourn ya tarar da Yash yana zaune yana sipping tea yana waya a hankali.
Mommy ta gaya masa yana nemansa! Sannan So yake ya tambaye sa abu dan haka ya nema waje ya zauna shima akan d’aya daga cikin kujerun parlourn.
sai da ya zauna tukunna ya fahimci ashe da Abokinsa ‘Najeeb’ yake wayar

Wani dan guntun Murmushi Yasir ya yi a ransa ya ce
‘’Haba, dama ni dai na san ba da Mace yake wayar nan ba
Mutum sai kace waliyyi …..’’

Ya fi 1 hour yana waya kafin finally ya ajjiye wayar ya d’ago ya na kallon Yasir ya ce
“Ka je kawai, maganan da za mu yi an gama ta tun ɗazu a wajen dinner, an rufe komai ai”

Murmushi Yassir ya yi ya ɗan sunkuyar da kanshi ƙasa ya ce “eh”sai kuma ya ƙi tafiya, dan haka Yashjub ɗin ya ce masa
‘’Lafiya?’’
Sai da Yassir ya ɗ’an sosa kansa tukunna ya ce
‘’Um, dama ina d’an son…’’

Tun kafin ya k’arasa Yash ya ce
‘’Kud’i,ko?’’

Murmushi ya yi kafin yace ‘’yess,a lot (masu yawa)”

A hankali Yash ya mik’e tsaye
sannan ya ce
‘’Yadda Daddy ya Zuciya da ku ɗinnan Yassir idan ka yi
dinner ko wani shirme a auren nan ka san ranka ne zai yi mummunan b’aci,therefore ba za ka samu kud’i daga gareni ba, gaskiya’’.
Yana gama fad’in haka ya wuce sama.

Yasir ji yayi kamar ya bi shi a baya ya make shi! a ransa ya ce
‘’Munafuki!!! Ai kaine ka janyo Daddyn ya ke fushin da mu, duk da dai munafurcin naka yau ya yi mini rana tunda gashi gobe za a aura min farin ciki na .’’
Chapter 15 · 0% Book details