← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 84

Sashe 71

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chaan kuma sai tashi d’aya kwakwalwarta ta d’au chargi gumi ya shiga keto mata dan in dai abubuwan da ta ji daga bakin Yasira da wanda ta fahimta yanzu a take gaskiya ne to kuwa tanada babbar matsala a gabanta!
A take k’irjinta ya shiga dukan uku uku, ta shiga add’ua a ranta akan ‘’Allah dai ya sa bata riga ta makara ba’’
A take kwakwalwarta ta fara lissafawa tana haska mata yadda abubuwanta da shirye-shiryenta na sama da shekaru za su zagwanye
a gaban idanunta, muddin bata tashi ta tsaya ta yi da gaske ba!.
A chan k’asan ranta ta ce
‘’Wacce irin shuumar Yarinyace wannan? Da zata shigo mana bagatatan haka ta tarwatsa min duk wasu taka tsantsan d’ina’’.
Tsabar rud’ani da rikici Mommy bata san lokacin da a fili a hankali kamar me mumbling ta fara cewa “ba zai yiu ba, ba zai yiu duk wasu sadaukarwar da na yi su tafi a banza ba….’’

Da sauri Baaba Larai ta matso ta rungume ta, a cikin kunnenta ta ce mata ’’ana dai kallon ki, ki zo mu je sama tukunna, sai mu yi magana’’

Jinjina Kai Mommy ta yi kamar ta fahimta sai kuma ta d’ago ta kalli Baba Larai ta ce ’’kikace Mace ce a rayuwarsa ko? kin tabbatar d….’’

‘’Innalillahi!!! Na ce ki zo mu je sama ko?!!’’
Baaba Larai d’in ta fad’a mata hakan da d’an zafi.

Sai a sannan tukunna Mommy ta samu ta ɗan dawo cikin haiyyacinta.
Ba tare da ta kalli kowa ba,
ta juya ta wuce sama jiki ba lakka..
Baaba Larai na bin ta a baya.

Anan suka bar Yahanasu wadda ta bisu da ido kawai a tsaye. “hmmm’’ kawai ta ce, kafin ta juya ta nufi d’akinta,
ba tare da ta kalli su Yassira ba.

Ummi ma bayan Mommy ta bi
dan gaba d’aya duk sai ta ji tausayinta ya lullub’e ta..
A gaskiya Yashjub bai kyauta ba,
taya za ka dinga yi wa uwar da ta haifeka irin hakan?…..
Da wannan tunanin ta haye sama ta bi bayan Mommy da Baaba Larai dan tana so ta d’an taya Baaba Laran tausar Mommyn.

Achan parlour k’asa kuwa, wata hirar su Yassira suka shiga yi gaba d’ayansu suna raha suna dariya….Yayinda Munirat ke tsaye a gefe tana mamakin yadda basu damu da damuwar mahaifiyar tasu ba, suka hau hira haka. sai da tafiya tayi tafiya tukunna ta fahimci ashe don ita da ummi suka kafa hirar dan babu komai a cikinta sai habaice habaice, tun suna habaici har suka fara sako sunayen su suna zagi suna dariyar rashin mutunci dukkansu banda Kausar wadda tun d’’azu ta yi shiruu.

Nazartar ta (kausar ɗin) kawai shi kuma Yassir yakeyi shiyasa ya ƙi tashi a wajen.

Munirat ce ta katse masa tunani ta hanyar nufar sama da wani irin sauri dan ita sai yanzun ne ma ta yi tunanin ‘to me ma ya tsayar da ita a wajen ne tun fako?’

Wani irin wawan tsaki Yassir ya jaa, dan bai riga ya gama fahimtar Kausar ba amma kuma dole ya tashi ya bi bayan Munirat.

Cikin had’e fuska ya mik’e ya bi bayanta a ransa yana aiyyana ‘’gaskiya shi fa yana gama samun abunda yake nema a wajen ta to zai yi fatali da plan d’in Kausar…
baya son damuwa, bayajin zai iya ci gaba da jurar yarinyar nan muddin ya samu buk’atarsa ta biya.’’
yana tafe yana mita a cikin ransa fuskar nan tamau haka ya haye saman….

A hankali Kausar itama ta mik’e ta nufi sama jiki ba lakka.
*MANNUBIYA*
*43*

Sai da su Mommy suka kusan shiga d’akinta tukunna suka lura da Ummi a bayansu…
Mommy ji ta yi kamar ta zurma uban ihu, dan a halinda take ciki bata buk’atar ganin kowa da yin magana da kowa in ba Baaba Larai ba….ayanzu da ya kamata ace sun keb’ance daga ita sai Baaba Larai shine wannan matar zata kama ta wani biyo su.
Da kyar kuwa ta d’an sake ta bata fuska suka shige d’akin nata gaba d’ayansu.
…..
‘’Babe!Babe!!’’
Muryar Yassir ta katsewa Munirat tunani.
Da kyar ya samu ya d’an daidata fuskarshi, dai dai nan ita kuma ta juyo…
dama ta san sai ya biyota dan haka tana juyawar ta ce ’’i’m okay,sai da safe.’’
Ruk’o hannunta ya yi, dan
haka ta juyo ranta a b’ace ta ce ‘’Yassir na ce ka daina tab’ani ko??’’

Cikata yayi yana mai d’aga hannuwansa sama kafin ya maidasu k’asa ya zura su duk biyun a cikin aljihu tukunna ya ce ’’kin tabbatar?’’

Murmushi ta yi tukunna ta ce ’’eh, i’m okay!
Ina buk’atar hutu, sai da safe’’
Bata jira jin me zai ce ba ta shige ciki ta banko k’ofar!.

Runtse idanunshi ya yi da k’arfi sosai, ya dunk’ule hannunsa, a ransa ya raya ’’ Tabbas idan burinsa ya cika akan yarinyar nan sai ya ci uban ta Wallahi’’.

Gyaran muryar da Kausar ta yi ne ya sanya shi bud’e idanuwan nasa, kafin ya juya ya zuba mata idanu yana kallon ta har ta k’araso inda yake, sai da ta kalli k’ofar da Munirat d’in ta banko tukunna ta kallesa tace “Rashin kunya fa kenan”
Sai da ya furzar da iska tukunna ya matsa kusa da ita sosai ya ce “kuma dole in jure duk wannan abun nata ba, tunda kin had’ani yin soyayyar dole da ita’’

Murmushi ta yi kafin ta ce
‘’Shiyasa k’aunarka take sake nunkuwa a cikin zuciyata…

Ammafa dukda haka Yassir ba fa ka yin yadda ya kamata da kyau, dan ni dai bana ganin wani shak’uwa a tsakaninku’’

Motse Bakinsa yayi ya d’an chuno lips d’inshi, still idonshi yana akan Kausar d’in ya ce ’’ko d’azu ma kamar za mu cinye juna a waya, kawai dai tanada attitude ne sannan bata iya danne ɓacin ranta ba ..na lura idan ranta ya b’aci a kaina take hucewa’’

Cikin katseshi ta ce
‘’Ko kuma haushi ta ji akan baka tsaya mata agaban su Yasira ba’’

Murmushi ya yi ya d’an sunkuyar da kansa tukunna ya d’ago ya ce ‘’Tabbas hakan ne ma.
Kinga,
ni yanzu mu bar maganarta haka, ke mene ya ke damu ki?’’
Yayi mata tambayar yana me tsare ta da idanuwa.

Itama idon ta zuba masa na y’an dak’ik’u..tashi d’aya ta fahimcesa tsaff dan haka ta ce
‘’Mommy ce take bani tausayi, ko kai baka lura da ita tun d’azu ba?
In nufin lokacin da taji labarin Yashjub ya bar office.’’
Sai da ta d’an sunkuyar da kanta ta fesar da iska tukunna ta d’ago ta ce ’’muna tunanin yana tare da wata ne, kuma ka san dama na gaya maka yadda take ji game da batun aure a lamarin Yashjub batare da mun samu mun karb’o dukiyar gidannan daga hannunshi ba……d’azun baka lura da yadda ta yi kuka ba kafin su hawo?’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ’’yeah na lura’’
A ranshi kuma yana jin wani sauƙi yana zuwar masa dan shi kansa baya so zargin da yake yi akan Kausar ya tabbata, saboda bai san me zai zama ba kuma.

‘’Ya akayi?’’
Muryarta ta katse masa tunani

Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’ba komai’’
Ya fad’i hakan yana d’an ruk’ota.

Dariya ta yi kafin a hankali da style da wayo ta samu ta zille tana mai cewa “ka je ka kira budurwarka ku shirya, bari in je na ji da Mommy’’ daga haka ta wuce ta barshi a nan tsaye.

Yashjub yana fitowa a wanka ko abinci bai ci ba saboda dare ya riga ya yi….
Ya d’auki waya ya kira Manubiya…dan zuwa wannan lokacin kam ya san ta kunna tunda ya ganta da ita a asibiti.

Lokacin basu wani jima da dawowa daga wajen Siyama ba, suna zaune ita da Jiddah suna shawara…
Ta inda Jiddan ta ke cewa
Manubiyan ‘ta siya masa jallabiya da Alkur'ani, ta kai masa a matsayin gift na godiyar abunda ya yi musu….’

Suna cikin lissafin ta Ina kud’in za su fito ne wayar Manubiya ta
fara k’ara, dan haka ta yi sauri ta mik’a Hannu ta d’auka daga inda take, ta yi saurin saka ta a silent, gudun kar ta tashi su Inna….
Dukda ta goge numbersa tun lokacin da ta yi fushi ta bar masa office ɗinsa amma tana ganin number kallo d’aya ta gane shi ne!
dan haka ta zubawa screen d’in idanu tana kallo kawai, yayinda k’irjinta yake bugawa a hankali a hankali.

Lek’awa Jidda ta yi, kafin ta d’an d’ago ta kalleta tana murmushi ta ce ’’shine ko?’’ sai kuma ta kalle ta ta ce ’’Adda Manu, anya kuwa mutuminnan…ko dai ko dai,
d’azu fa naga irin kallon da yake ta miki’’

Da sauri Manubiya ta d’ago ta kalleta, sai kuma ta shiga girgiza mata kai alamun ‘A’a’ kamar za ta yi kuka.

Dariya Jidda ta yi ta ce ’’to ki d’auka da wuri kar ta tsinke, in yaso sai ki je ko bakin dakalin gefen k’ofa ne, kar ki tashi su Baba.

Kamar wata Yarinya haka Manu ta d’an jinjina Kai alamun tou, sai kuma ta mik’e ta fice da sauri dan itanma tanaso ta d’auka d’in…tun d’azu take ta tunanin sa, sam bataji dad’in yadda har ya tafi bata samu ta yi masa cikakkiyar godiya ba,
kar yaga rashin kyautawarta..

Tun kafin ta Ida fita ta d’auka ɗin tukunna
a hankali ta maida k’ofar ta rufe, ta nemi waje gefen dakalin ta zauna kafin ta ce
‘’Assalama alaikom’’
A hankali.

Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e, yana jin wani sanyi yana ratsa shi tukunna ya nemi waje ya zauna a bakin gadon shima. A hankali ya fesar da iska sannan ya ce
‘‘Ameen.
Wa alaiki Assalam’’

Daganan shiru ya d’an biyo baya kafin ta ce
‘’Ina wuni.’’

‘’Alhamdulillah’’ ya ce
tukunna ya sake cewa ’’ya jikin Baba?”

Itama ‘’Alhamdulillah’’ ɗin tace,
daga nan suka sake yin shiruu.

A b’angaren Yashjub tunanin kawai yakeyi yana fatan
Inama ace tana gefen shi a yanzu haka.
Chapter 71 · 0% Book details