Sashe 4
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wannan karon ma ya kawo mata wani dalilinsa na yin hakan, inda ya ce Yaro Namiji na farko ya kamata a bashi support tunda duk ƙannensa a ƙarƙashinsa su ke sannan kuma dama ya na so ya bada kyautar saboda farin ciki dan haka gara kawai a barshi ya yi…
Sai dai ita Amaryar sam ba ta fahimci fa’idar yin hakan ba.
Tun ba ma yadda ya ware ta ita kaɗai ya gayawa ba bayan itace ma ƙarama….
A ganinta kamata ya yi ya haɗe su duk su biyun ya yi shawara da su,
Idan ma hakan ne decision ɗinsa tou ya gaya musu a tare.
Ganin da ta yi ranshi ya na sake ɓaci game da tirjiyar da ta ke ta yi ne ya sanya kawai ta haƙura ta rabu da shi…
Amman har ga Allah a chan ƙasan ranta addua ta ke yi Allah Ubangiji ya sa Uwargidan ta haifi ɗa Namijin.
Sarai ta san Matar tana fahimtar wasu abubuwa na bambanci da Imam ɗin ya ke nunawa a tsakanin su amman dukda haka ta ke kauda Kai kamar ba ta san me ke faruwa ba, but fa ta san ko zuciyar gwal gareta muddin akace yau sun haihu tare ita ta haifi ɗa Namiji an ɗauki rabin dukiya an bata tou fa ta san zaman lafiyar ta da Abokiyar zaman na ta tsaf sai ya taɓu!
Ita kuma bata son abunda zai haɗata da Abokiyar zaman nata
dan ta yi mata abunda ba za ta taɓa mantawa da ita ba..yadda ta
kula da ita da ɗan cikin ta na fari ba ko wacce kishiya ce za ta iya ba, ko ɗanuwa na jini iyakar abunda zai yi maka kenan.
…………
A kwana a tashi…..
Watan haihuwa ya kama, cikin hukuncin Ubangiji ko wacce ta sauƙa lafiya, sai dai fa abubuwa ba su tafi yadda Imam ya tsara
ya kuma yi zato ba domin Amarya Mace ta Haifa!
Uwar gidan shi kuma ta haifi ɗa Namiji…
Sam-sam Imam bai yi zaton hakan ba.
A ranar da suka haihun ma ba ya nan….
Ya yi tafiya zuwa Abuja,
A ranar da zai tafi ɗin Uwargida ta fara labour da sassafe dan haka ya bar musu duk abunda ya san za su buƙata sannan ya ce shi da Amarya za su je su ƙaro wasu kayan, basu dawo ba sai da ya biya da ita asibiti aka tabbatar masa sai nan da two weeks tukunna edd ɗinta zai cika! Inda ya ji daɗin hakan sosai saboda dama ya fi so ta haihu yana a tare da ita kuma shi sati ɗaya kawai zai yi a Abujan ya dawo…
Dan haka ya maida ita gida
cike da farin ciki, yayinda ita kuma ta ke ta faman kumbure-kumbure ta na ta yi masa wa’azin ya dai dinga adalci.
Cike da fatan alkhairi
da kuma tsananin kewar Amaryarsa ya tafi, tare da fatan
yana dawowa ita ma in sha Allahu ta haifa masa sanyin idaniyar shi.
Sai dai kuma yana tafiya itama Amaryar ta fara samun contractions, dan haka akayi asibiti da su duk su biyun.
Suna zuwa akace sai dai a yi wa Amarya cs dan ba za ta iya haihuwa da kanta ba.
Ba tare da ɓata lokaci ba Daddy da Mama su ka cike takardun amincewa aka shige ɗakin tiyata da ita.
Itace kuwa ta fara haihuwa
aka ciro mata babynta Mace ƙatuwa tubarkallah, Larai ita ta miƙawa su Mommy waenda su ke a wajen labour ɗin kowa yana ta farin ciki, fuskokinsu tamkar gonar auduga….
Basu gama murna ba!
Likitan ya fito musu da kyakkyawan Yaro mai tsananin kama da Ubansa ɗan wajen Khadijah (uwar gida.)
Kowa idan ya kalleshi sai ya ce MashaaAllah, dan tun ya na jariri kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci kyakkyawa ne.
……
A ranar Imam ya biyo flight ya dawo
a hargitse dan ɗoki
…..
Tun a chan ya gama yanke shawarar fasa bawa ɗan gidan uwar gidan ta sa rabin dukiyar sa
da tunanin neman wata mafitar tunda ba kowa ya san da zancen ba dama…..saboda shi babban dalilinsa da ya ɓoye ya ƙi gayawa kowa shine ba ya so ya riga Amaryarsa gidan gaskiya ta wulaƙanta ba ya so wani abun ya sameshi ba tare da ya kafata ta tsaya da ƙafafunta ba.
….
Imam ya na zuwa da ya ɗauki Yaron a take ya ji duk duniya ba abunda ya ke so sama da shi.
Dan har kuka ya yi tsabar asalin farin ciki.
Wata irin soyayya Allah ya dasa masa ta Yaron, mai tsayawa a rai.
Ya na son itama ɗayar Yarinyar da aka haifa masa amman ba kamar yadda ya ke son Yaron ba,
wani irin kalar so ƙauna da tausayi na Yaron ya ke ji suna ratsa dukkan ɓargo jini da tsokar da ke jikin shi.
…..
Bai yi tunanin su Maama sunsan maganar alƙawarin da ya ɗauka na raba dukiyar shi biyu ba, sai da ta yi masa maganar.
Ashe wannan karon ma uwar gidan ta sani kuma ta gaya mata
tun farkon sanin zancen da ta yi.
Wanda kai tsaye Maama ta fahimci son kai ne ya ke shirin yi
ta kuma ji haushi duba da yadda ya yanke shawarar a cikin Amaryar na farko ma ba tare da ya tuntuɓi kowa ba, shiyasa ita kuma ta cewa Uwargidan ta yi shiru ta barta da shi, za ta yi maganin shi.
Ya so ya ziille!.
Tabbas ya na son ɗanshi fiye da komai, amma kuma yana duba rayuwar Amaryarsa.
Ya so ace ita ta Haifa masa wannan Yaron da tuni ya bayar ba tare da shayi ko kokwanto ba.
Fahimtar da ya yi Uwargidan har ma da Mahaifiyarsa sun fara fahimtar dama chan ba adalci ya so yi ba, hakan ya sanya kawai ya haƙura ya bayar da rabin dukiyar tasa a ɗan nashi ba dan ya so.
…………
Wani ikon Allah..
Tun daga wannan lokacin abubuwa sai su ka sauya!
Gaba ɗaya soyayyar Imam ga Amaryarsa sai ta yi rauni.
Ita sai ta ke ganin kamar ma haushinta ya ke ji! Dan ko
kusa da shi ta fahimci ba ya so ta je.
Itama uwar gidan tashi ba wani sake mata ya ke yi ba, amma dai ya
fi tsanar amaryar akanta.
Indai ka ga yana dariya tou ya ɗauki ƴaƴansa ne!
Amman baya ga haka ba shi da wata walwala kuma.
Tashi ɗaya ya koma wani irin murɗaɗɗen Mutum mai wuyar sha’ani, lamarin nasa har abun tsoro ma.
Dan har ga Allah ita kam Amaryar zuwa wannan lokacin ya fara bata tsoro.
Ga ga hantara, kyara da tsangwama wadda ya ke gwada mata ƙiri-ƙiri.
Ga wani irin masifaffen kishinta da ya ke yi marar misali, har ya janyo zargi, wanda hakan ya sanya ta ke tunanin
ko dan ya san ya daina bata kulawa da bata dukkan hakƙinta ne shiyasa ya ke tunanin za ta je ta kula wani a waje.
Gaba ɗaya tashi ɗaya sai duniya ta yi mata zafi!.
Da ga Uwargidan sai Larai ne kawai ta ke da su, ta ke ɗan hira da su ta ji sauƙi. Sai ko ƴar jinjirar Yarinyar ta
wadda da aka ƙara ƴan kwanaki itanma sai ta lura kamar ƙiyayyar da Imam ɗin ya ke yi mata ta shafi hatta jinjirar Yarinyar wadda ba ta ji ba bata gani ba. Dan kafin ya ɗauki Yarinyar sau ɗaya to ya ɗauki ɗanuwanta sau
ashirin…..
Ba ta da yadda za ta yi,
tunda bama ta san laifinta a gareshi ba ballanta ta gyara….
Shiyasa ta duƙufa addu’a kawai
ta ke kuma ƙoƙarin wajen riƙe kanta kar ta gigice dan yadda ya ke sonta a baya itama haka ta ke son shi har gobd wanda hakan ya sanya daya juya mata baya komai nata sai ya tsaya mata chak!.
Shiyasa ko Mutum bai santa ba tun farko to da zarar ya ganta a wannan lokacin kallo ɗaya tak za a yi mata a fahimci ta na cikin tsananin tashin hankali.
……
*Bayan Shekaru Talatin*
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*02*
*Bayan shekaru talatin*
*AUCKLAND(okland)*
…..
Babban jirgin ruwa ne, na alfarma(superyatch) mai kyawun gaske, tsaye a chan tsakiyar ruwa, keɓance daga dukkannin gidaje da al’ummar garin. Kwata-kwata jirgin ruwan ba zai ɗauki sama da mutane 70 ba kasancewar ba wani girma gareshi ba….
Walwali na kalolin fitilu mabanbanta, da haskensu ke ratsowa ta cikin jirgin ke bada tabbacin party ake yi a ciki.
Tun daga nesa da su kaɗan sautin ƙiɗa ke tashi alamun an ƙure speakun sun kai ƙarshe kenan, cikin jirgin kuwa muddin Mutum ya kasance ba ma’abocin son kiɗe-kiɗe bane to ko sakanni ba zai iya ɗauka a ciki ba.
Sama da ƙasa ne da jirgin kamar girman madaidaicin gida mai bene (duplex).
A ƙasan ake gudanar da event ɗin, wanda yanayin decoration da cakes ɗin wajen zai sanya a kira hidimar da ta ‘birthday party’….
……
Ƴan Mata ne guda biyu tare da wata farar budurwa wadda ba za ta haura shekaru ashirin da bakwai a duniya, keɓance a ɗakin da ke sama su uku kawai
yayinda dukkannin al’ummar cikin jirgin ƴan Mata da Samari su ke a babban parlourn da ke a ƙasan sun cika shi taf har ma da ƴar varander da ta fita waje itama ta cika da Mutane in banda kiɗa da rawa ba abunda ake gudanarwa a wajen.
Wine rack na nan cike da kwalabe, duk kalar abunda su ke buƙata zuwa kawai su ke yi bar tender ya tsiyaya musu su kora ta maƙoshinsu.