← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 84

Sashe 53

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Yashjub ya yi mamakin yadda Manubiya ta had’e rai ta tamke fuskarta tamau!!!
Ta k’i cewa komai.
Yadda ta chuno d’an mitsitsin bakinta ne ya bashi dariya kuma ya burge sa.
A hankali ya d’an yi murmushi mai sauti wanda har sai da ta ji sa, ba tare da shakku ba ya sake cewa”
You look cute today!
breathtaking,to be precise
( kin yi kyau yau, a taƙaice irin mai tafiya da numfashin nan)”

Saboda yana so ya tabbatar da ‘shin maganar tasa ce ta ɓata mata rai har haka
kuma yana so ta sake cuno bakin dan ba kad’an ba kara mata kyau yake yi sannan har ga Allah daga cikin zuciyarsa direct maganar take fitowa.’

Shiyasa tashi d’aya Manubiya ta rikice dan har cikin gangar jiki da tsoka maganganunsa suke shigar ta..jin tana shirin bada Kai ne ya sanya ta ta mike tsaye da sauri…
ba ta yarda ta kalle sa ba kawai ta fara magana
“Sir! with all due respect, our relationship is strictly professional
(Sir! Cikin girmamawa, dangantakarmu ni da kai ta aiki ce kawai!)
ka ba ni aiki saboda Sir Najeeb yana jin tausayi na amma hakan ba wai yana nufin zan barka ka ci min fuska ta ko wacce siga ba!
Yes,
I know I’m poor (eh, na san ba ni da shi) amma hakan ba shi zai sanya in barku ku ci zarafin talaucina ba,
dan haka ko ma wanne irin tunani ne a ranka game da ni ka daina,
Banaso!..

Sau biyu kawai ka ganni ta ya har ka samu ƙarfin halin iya gaya mini kalar kyawun da na yi?.

Mu ba komai ba ne face baƙi ga juna. A gaskiya, kirana da ka ke yi cikin dare da kuma yadda kake mu’amala da ni suna sa ni jin rashin kwanciyar hankali.

Aiki ne kawai ya had’a ni da kai, babu wata alaƙa ta ƙashin Kai da ke a tsakaninmu…

Ka je gida ga Matarka! Na tabbatar tana chan ta yi maka kwalliya..ita ya kamata ka cewa she looks cute (ta yi kyau) ba wai ni ba.’’
Tana gama fad’in haka ta juya da sauri ta nufi k’ofa, ji take yi kamar ta kurma ihu a ranta ta ce ‘’ku yi hak’uri Inna, na san na yi muku bak’in cikin albashi na duk wata amman ba zan yarda yayi wasa da tunani ba’’….

Dama tun farko yanayin yadda aka bata aikin ya ɗan so ya d’aure mata kai amma kamar yadda Abbakar ya ce
‘tausayin ta Sir Najeeb ya ke ji’ ne ya sanya kawai ta kawar da duk wani tunani na rashin kyakkyawan fata,
In ba haka ba a ganin ta tsaf secretary d’insa za ta iya dan aikin sam ita ba ta ga wani dalilin hiring d’in ta (ɗaukarta) da aka yi ba.

Tun lokacin da ta mik’e ta fara zazzaga masa bala’i ya kasa cewa komai, kuma ya kasa d’auke idanunsa a kanta..dama tun ranar farko da ya fara ganinta a office d’in Najeeb! Yadda ta ƙi yin magana da kuma yadda ta saka kuka ya sanya ya fahimci tana da temper but she’s also very weak (tana da zafin rai amma kuma tanada raunin Zuciya)
tunda ga shi yanzu ma sam ta gagara jure tasirin da kallon sa gareta da maganarsa ta yau suka yi mata!!!

Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya aiyyana a ransa
‘Kawai ni fatana, Allah ya sa ta ɗan ji wani abun da ya shafi so da ƙauna a kaina, ko da ɗan kaɗan ne!
Ba wai iya ɓacin rai maganganu da kallona suka janyo mata ba’……..

Ba abunda ya fi ba sa mamaki
irin yadda sam ko sau d’aya bai ji zafin maganganunta ba!
In banda burge sa ma shi kam ba abunda ta yi kuma ta sake samun mazauni ta zauna daram a cikin zuciyarsa, tabbas Manubiya ta san darajar kanta.

Babu kuma abunda ya fi bashi dariya irin yadda ta balbale shi da masifa kamar ta samu d’an cikinta amman kuma sam ta gagara kallon idanunsa ko da sau d’aya ne.

Tana kama hanyar k’ofar, Yashjub ya danna wani abu a kan tebur d’in nashi, ya koma ya jingina da jikin kujerar yana kallon yadda take tafe tana sassarfa kamar wadda aka ce mata zai biyo ta ya kama ta ne.

Tana zuwa jikin k’ofar ta fara k’ok’arin jan glass d’in amman sai ta rasa ta ya ma za ta ja!
Saboda ɗazu k’ofar a d’an bud’e take kad’an amma yanzu kuma kamar an yi sealing (haɗe) glass d’in an manne su duka a waje d’aya dan sam babu alamar ta inda zaka ce zaka zuge ko kuma ka tura ka bud’e…
“innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Manubiya ta furta hakan a fili sai kuma wani irin tsoro ya lullub’e ta!
Tabbas Yashjub ne ya rufe k’ofar nan, ko shakka babu.
A yadda ta zuba masa rashin kunya sannan ta wuce za ta barshi a nan wurin.. to fa in dai babu mummunar nufi a cikin zuciyarsa game da ita kai tsaye yana zuwa ta san zai koreta ne bayan ya dake ta ko kuma shima ya rama bak’aken maganganun da ta zuzzuba masa!!
Waenda ita kanta sai yanzun ne take tariyo wasu maganganun da ta faffad’a masa masu zafi waenda bai kamata ace ta gayawa Babban Mutum kamar shi ba, a ranta ta ce ‘’shikenan yanzu na tonawa kaina da kaina asiri, dan shi dai ba cewa yayi yana sona ba amman na bi na tak’arkare ina ta faman cewa ‘dangantakarmu ta aiki ce kawai’.”

In dai kuma mummunan nufi ne a zuciyarsa game da ita to kuwa yadda ya rufe k’ofar nan
Yana zuwa raping d’inta zai yi shikenan tata ta k’are yau.
Ta aiyyana hakan a ranta Jikinta yana soma karkarwa.

Juyawa ta yi da niyyar ganin me ya ke yi..
ta ganshi zaune ya hard’e hannuwansa biyu a k’asan k’irjinsa ya jingina da jikin kujera ya zuba mata ido sai kuma ta ga ya taso ya nufo inda take…
Ai kuwa da sauri sannan a rikice ta juya ta fara kiciniya tana shashshafa k’ofar tana addu’ar Allah ya sauk’o da mu’ujizar da idanuwanta za su nuna mata wata tsaga ko alama a jikin glass d’in domin ta samu ta bud’e ta fice.
..
A rikice take dudduba glass d’in tana yi tana waigen sa a gigice.
ganin dai da gaske itan ya nufo ya sanya ta fara dukan glass d’in tana kwala k’arar
‘‘Help’’

Murmushi kawai Yashjub yayi,
dai-dai nan ya k’arasa inda take.

Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’...
*MANNUBIYA*
*32*

Murmushi kawai Yashjub yayi,
dai-dai nan ya k’arasa inda take.

Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’

Yashjub bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba, aikuwa ya shiga yi kalar wadda ya dad’e bai yi ba.

Ba k’aramin k’ulewa Manubiya ta yi ba kuwa, sannan ga tsoron da ya bi ya dabaibaye ta dan haka ta yi k’asa da kanta a take hawaye suka shiga wanke mata fuska.

A rikice ya ce
‘’Ooo’O!sorry,i’m so sorry’’
dan tashi d’aya sai hawayen nata suka d’aga masa hankali.

Bata kalle sa ba kuma bata daina kukan ba sai ma yawa da yaga hawayen nata sun k’ara, sannan ya lura da yadda hatta jikinta ya ke karkarwa……

A hankali ta d’aga hannunta, ta juya ta shiga k’ok’arin bud’e k’ofar a karo na biyu, wanda hakan ya ke nuni da
alamar so
take kawai ya bud’e mata ta samu ta fice.

Ba zai tab’a iya jurar ganin ta a hakan ba, dan yadda hawayen nata yake zuba akan kumatunta haka yake ji kamar ruwan zafi ne ake kora masa a cikin k’irjinsa..

So yake ya bud’e mata k’ofar, amma kuma ya san muddin ya bud’e ficewa za ta yi , ba tare da sun fahimci juna ba.

Jin kukan nata ya fara fita da sauti had’i da jan hanci ne ya sanya kawai ya d’aga hannunsa, a nan jikin glass d’in ya danna abunda ya bawa k’ofar damar bud’uwa wanda ba kowa ne ma zai fahimci za a iya bud’e k’ofar da shi ba.

Tana ganin glass d’in ya ɗan motsa ta saka hannu ta jaa ta bud’e ta yi waje da wani irin sauri…

Zai zama wani iri idan ya bita, kuma ya san ba za ma ta so hakan ba dan haka kawai sai ya juya a hankali ya koma ya zauna akan kujerarsa!
ya dafe kansa wanda har ya fara sara masa.
Sai yanzun ya fara jin haushin kansa da ya kasa fahimtar ya kamu da kaunarta ne tun a ranar farko..tun asalin farko soyayyarta ta yi wa zuciyarsa sahihin kamu, amma ya gagara fahimta bayan ga gaskiya nan k’iri-k’iri amma bai iya ya fahimta ba ya dinga wahalar da kansa da kuma ita kanta Manubiyan har da su bata aiki gashi ynzu ta tashi ta dank’ara masa matsayin boss d’inta a kwakwalwa da tunaninta… baya jin za ta yarda da shi cikin sauk’i..a yadda yaga ta
rikice ta kid’ima sannan ranta ya b’aci daga ya ce mata ta yi kyau ɗinnan, ya san idan ba yayi da gaske ba to ba k’aramar wahala zai sha ba kuma sai ta d’auki lokacin da baya so a ɗauka a lamarin nasu kafin ma ya samu matsayinsa na ‘sir’ya goge a idanunta na ‘masoyi’ ya shiga.

A hankali ya sake fesar da iska, kafin tashi d’aya ya yanke shawarar zuwa gidansu!…
Ba zai sake d’aukar lokaci ko jira ba tunda ga abunda kwana kwana da jiran ya haifar.

Sai da ya jera mata misscalls sama da biyar amma bata d’auki ko d’aya ba.
Chapter 53 · 0% Book details