← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 84

Sashe 75

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafe Kai Yassira ta yi, ta matsa gefe ta juya sannan ta d’an runtse idanunta ta yi shiru kafin ta bud’e ta ce
‘’Abin baƙin ciki ne sosai!! Ace lokaci guda gaba d’aya aikin da ku ka yi tuƙuru na shekara da shekaru ya tarwatse, ba tare da mun ci riba ko guda d’aya ba’’.

Da sauri Mommy ta ruk’o ta, ta juyo da ita sannan ta ce
‘’Yassira, ina son abu na gaba da zai fito daga Bakinki ya tafi kai tsaye zuwa ga ainihin maganar da duk mu ke son ji!
Ki fad’a min abunda ya faru tun wuri saboda raina ya fara b’aci.’’

Kallon ta Yasirar ta yi kafin ta ce ’’ai ba ki ji b’acin rai ba
Mommy sai na ce miki Yash zai yi aure!
Kuma nan da wata ɗaya na ji ya ce dan haka kinga kuwa an riga an gama komai ma kenan…ba maganar budurwa ake yi ba yanzu, maganar aure ake yi’’

Cikata Mommy ta yi da sauri, sai kuma ta k’ame, sam ta kasa sake yin motsi.

Cikin takaici Yassira ta ce
‘’Yes Mommy, Yash zai yi aure
ba tare da kun fahimci juna ke da shi ba, ba tare da mun samu damar amso uban dukiyar da Daddy ya mallaka masa ba, ba tare da ya damu ko ya had’a Kai da d’aya daga cikinmu ba
Sannan mafi muni Yash zai auri wadda bamu sani ba kuma
ga dukkan alamu yana matuk’ar sonta da k’aunarta, kinga kuwa zuwa nan da y’an shekaru kaɗan komai ya zama nata, daga ita sai ya’yan su!
mu kuma sai dai kallo!’’

Cikin fushi Mommy ta ce
‘’Yi shiru Yassira, ya Isa haka!’’

‘’Mai yasa? Saboda me zan yi shiru?
Ba kya son ji ne?
Ai gaskiya na fad’a, in ba haka ba Mommy ki duba fa ki gani aure ne Yash zai yi ko kuma in ce yake shirin yi nan da wata ɗaya fa!!! Amman kaff d’inmu nan babu wadda ya gayawa, ko kyallin zancen ma babu wadda ta taɓa ji saboda tsabar yadda kanmu da nashi yake ba’a had’e ba!….
Wannan shegiyar Yahanasun ita kad’ai ce ta sani, ita kad’ai ya gayamawa, ashe tun farko dama ta san da Yarinyar amman ta yi mana shiru..’’

Cikin fushi Yasmeen ta ce
‘’Ai ita take cin dunduniyar mu dama, ku gaya min dalilin da zai hanani cin uwar Matar nan yau a cikin gidan nan!’’
Ta fad’i haka tana shirin fita da niyyar zuwa ta sami Yahanasun.

Da sauri Baba Larai ta sha gabanta, ta rik’eta kafin ta ce
‘’Ba za ki tab’a Yahanasu ba Yasmeen, ba za ki ce mata komai ba’’

A harzuƙe Ya’isha ta ce
‘’Haba Baaaba! Ya za ki ce haka???yanzu inda ace ta gaya mana tun farko ai da mun san abun yi, da tuni ba’a kawo ga haka ba, amma yanzu kalli abunda b’oyewar da ta yi ya janyo.
saboda Allah idan mu tana ganin bata shiri da mu ai ko ke ko
Mommy ya kamata ace ta gayamawa, tunda na san ta san dole ba’a san da zancen ba.

Har ga Allah Yahanasu ta fara wuce iyakarta kwana biyun nan,
Ranar chan fa da ta gaggaya mana magana a parlour
ranar da akayi case d’in senator
da Yassira ta je d’akinta idan kika ga yadda ta yi wallahi za ki sha mamaki, Yasira tana fad’a atake itama take mayar mata k’arshema toilet ta shige ta banko mana k’ofa.

Kwata-Kwata bata shakkar uban kowa a cikin mu amma dukda haka kuna gani kun yi shiru sannan da ance za a gyara mata zama sai ku hana….yanzu kalli abunda saken da kukayi ya janyo’’.

A hankali Mommy wadda zuwa yanzu tama daina gani sosai tsabar b’acin rai ta ce ’’Ya’isha so kuke ku kasheni? Aka ce ku bari tukunna yanzu a fara sanin abun yi in ba hakaba wallahi zan tura ku d’akinku kamar Yusra da Yadira tunda kuma Yaran ne…
Ku tsaye ga matsalar da ya kamata ayi magana akai nan amman kun tsaya kuna shirme?’’
Mommy ta k’arashe maganar tata cikin d’an d’aga murya da tsananin b’acin rai.

Komawa Yasmeen ta yi ta zauna, haka itama Ya’isha, ammafa dukda haka a kumbure suke kamar za su fashe..

Shiruu d’akin ya d’auka kowa ya shiga tunani….

‘To kenan Daddy shima ya sani amma ya b’oye mata ko dai ya abun yake ne???’
Mommy ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba, a take wata zuciyar ta ce mata “da wuya idan ya sani, kuma ko da ace bai sani d’in ba ma ta san wuyarta Yashjub ya ce masa yana son aure! Ko a cikin sati d’aya ne ba abunda ya shafesa tsaf zai d’aurawa Yash aure, in dai har Hajiya Maama ta amince kuma an yi bincike’’…
Sabodahaka ta san yanzu Baaba Larai ce kad’ai za ta iya taimakon su, dan haka ta d’ago da niyyar yi mata magana kenan Idanuwanta suka sauk’a a kan Kausar wadda ta turo k’ofar d’akin a dai dai lokacin ta shigo.

Lumshe idanu Mommy ta yi ta bud’e saboda yadda ta ga hawaye shab’e-shab’e a fuskar kausar d’in ta san ta riga ta gama jin komai.

A hankali ta d’an matsa kusa da ita da niyyar yi mata magana amma sai Kausar d’in ta yi saurin d’aga mata Hannu alamun ‘stop!’ Kafin kuma ta juya da
sauri ta bar wajen……

Da sauri su Ya’isha su ka bita
da hanzari, su Mommy suma suka rufa musu baya..duk suka d’unguma side d’in Kausar inda suka ga ta shige.

Suna zuwa suka tarar har ta shige ta turo k’ofar bedroom d’inta dan haka suka tura suma, cikin ikon Allah bata rufe ba. Suna shiga suka tarar da ita ta fasa kwalba tana k’ok’arin yanka jijiyan wrist d’in ta(wuyan Hannunta).

Da sauri sannan a tsorace suka je suka rirrik’eta Mommy tana cewa ‘’Haba Kausar, ba fa auren aka ce miki an riga an d’aura ba’’

Inaa! ko jin ta Kausar bata yi ba,
in banda kuka da hauka ba abunda take musu..
Dan haka Mommy ta juyo da ita ta wanka mata wani kalar gigitaccen mari.

Wani sabon kukan Kausar ta sake fashewa da shi kafin ta fad’a jikin Mommy ta rungume ta tana kuka sosai kamar za ta shid’e ta shiga cewa
‘’Mommy kawai ki barni in mutu, all my life I’ve been unlucky (ni duk tsawon rayuwar da na yi ba ni da sa’a)
Ammina ta rasu!
Mahaifina bana jin ma ya san da ni!Daddy shima ya tsaneni!
Sannan tare muka fara karatu da su Yassira su duk har sun gama sun kama aiki
amman ni har yanzu Ina project!…

Dan Allah ku bar ni in mutu,
Idan na zauna Yash ya rayu da wata a matsayin Mata mutuwa zan yi Mommy, gara kawai in mutu….”

A hankali Mommy ta rungumota itama zuwa jikinta sannan ta ce’’Na yi miki alk’awari, Yashjub ba zai auri kowa ba sai ke.”

Cikin katseta ta ce
‘’Mommy haka kike cewa kullum, gashi yanzu har yayi budurwa yana shirin aurenta bama mu sani ba’’

A hankali Mommy ta saka Hannuwanta ta d’ago da fuskarKausar ta yi cupping a cikin tafin hannuwan nata kafin ta ce mata ‘’kin yarda da ni???’’
tayi mata tambayar tana kallonta

A hankali kausar wadda duk ta miƙa wuya ta jin jina mata kai alamun’yes’
Idanuwanta shab’e-shab’e da hawaye, har ga Allah ta karaya da yadda ta ji maganar ta taho gadan gadan dan ta san tunda akace nan da wata ɗaya to hatta su Hajiya mama sun sani kuma sun amince, ta riga ta san duk bala’i ba’a isa a chanjawa hajiya mama ra’ayi ba, shiyasa kawai ta zab’i ta mutu amma wannan alƙawarin da mommy ta yi mata ya sanya ta ɗan ga alamun haske dan haka ta zaɓi saka rai da dacewa sannan ta zaɓi ta yarda da mommyn ɗari bisa ɗari ko bayaga hakan ma yarda da mommyn dama shine zaɓinta mafi sauƙi wanda ta ke so ɗin, dan akan ta mutu ta barwa wata yash ɗinta gara a fafata su yi nasara ta hanyar raba shi da Yaroinyar, in sha Allah.

Dan haka ta sake cin ɗamara, bayan ta ɗaura gaba ɗaya yardarta akan abinda mommy ta faɗa mata ɗari bisa ɗari ta kuma aminta da momnyn za ta cika mata burinta.

Sai da Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ci gaba da cewa “ki kwantar da hankalinki,
babu wadda ta Isa ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa, ki zuba ido ki ga ikon Allah’’

Ya’isha ce ta ce
‘’Mommy me za a iya yi a cikin sati uku zuwa wata d’aya? Wataƙila ma fa an riga an kai komai.”

“Ba dai ni nace muku ku zubamin ido ba?….dan haka bana so in sake jin wata magana game da batun auren Yash a cikin gidan nan’’
Sai da ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ’’zan ga ta yadda zai yi auren, zanga ta yadda zai aureta.’’

A hankali ta kamo fuskar Kausar ta ce ’’alfarma d’aya nake so daga gareki…’ki kwantar da hankalinki!’.
Ki cire komai aranki, kar ki damu in dai kinada ‘Ni’ na dad’e da yi miki alk’awarin ba za ki yi kuka ba………..”
••••••
Washegari da sassafe Manubiya ta tashi, ta shirya tsaf, dan tun a jiyan Ya Musbah yace mata “ta shirya da wuri, za su je su dawo saboda Ya Nafi’u yana da interview by ten‘’
shiyasa take ta sauri ta shirya ɗin, sai dai bata ko fara karyawa ba sai gashi sun shigo shi da mai sunan Baba.

Bayan an gama gaggaisawa ne
Manubiya ta sanar dasu yadda sukayi da Yash d’in jiya da kuma yadda ya ce yau Likutar za ta zo ta duba Inna.

Shiruu Baba ya yi da jin bayanin nata kafin chan ya nisa ya ce ’’Manubiya daga wannan, kar ki sake gaya masa wata damuwar ki. Ɗawainiyar tayi yawa haka’’

A hankali ta sunkuyar da kanta tace ‘’to Baba,’’ saboda dama ta san za’a rina, har ga Allah ita ta ma yi tunanin zai yi mata fad’a idan ya ji.
Chapter 75 · 0% Book details