← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 84

Sashe 61

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta kawar da kanta gefe, tana wani irin kuka…dan gaba d’aya a tsorace take
ga tashin hankalin da take a ciki tun farko dama ga kuma zuwan wannan abun tsoron
shiyasa duk ta bi ta sake duburcewa,
in banda karkarwa babu abunda jikinta yake yi.

‘’Mallan kana haukane!’’
Ya Musbah wanda ya taso yanzu ya fad’a a Zuciye yana shirin yin kan black snake d’in…

A take wani a cikin bodyguards d’in nashi ya saita masa bindiga..

Da sauri Baba ya ce ’’dan Allah kar ku yi musu komai, dan Allah”
sai kuma ya fashe da Kuka.

Shi kam black snake gaba d’aya hankalinshi ya tashi
da ganin Manubiya!..
Babu k’asar da bai je ba a rayuwarshi sai dai in da ba’a rasaba, amman ba zai yi k’arya ba duk yawonsa da gane ganensa bai tab’a ganin Mace mai kyawu sannan Macen da ta d’auke hankalinshi lokaci guda kamar Manu ba.
Kallonta kawai yake yana sakewa
kamar ya samu television….
Sai da ya lashe Bakinshi tukunna ya kamo hijabinta ta k’asa bata yi auni ba kawai ta ji ya d’ago shi ya zare ya yar a gefe…

Tabbas ba k’aramin zafin tozarcin da ya aikata mata ta ji ba, dukda kuwa doguwar riga ta Abaya ce a jikinta amma ji ta yi kamar ta kurma ihu.
Tashi d’aya ta ji wani irin bak’in ciki
ya lullub’eta, bata san lokacin da ta d’aga Hannu za ta kifa mishi mari ba.
Ya Musbah da Ya Nafi’u ma duk nufar sa suka yi dukda bindigar da ke saite a kan Ya Musbah bai ma san lokacin da ya motsa ba.
Abbakar shima yana ganin haka ya yi kansu cikin fushi.

A lokaci guda black snake ya zaro pistol daga cikin aljihun wandonshi
ya saita k’afar Abbakar ya sakar mishi bullet sannan ya rik’e tattausan Hannun Manubiya da d’ayan Hannun nashi.

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
gaba d’ayansu suka ce, sai kuma suka yi kan Abbakar wanda ya fad’i a wajen, ya yi suman wucen gadi, tsabar azaba ya ma kasa kuka ya kasa magana
Yanajin azabar da tunda uwarshi ta kawoshi duniya bai tab’a ji ba tana ratsashi.

Black snake bai huce ba sai da
ya kuma harbin d’aya a cikin bodyguards d’insa a kafad’a wanda d’azu ya saitawa Ya Musbah bindiga
Cikin dakakkiyar murya ya ce ’’da ka saita masa bindiga ka ga ya motsa harbesa ya kamata ka yi, next time you should take note
(Ka ɗauki darashi saboda gaba)!’’.

Ba tare daya cika Hannun Manu wadda taketa k’ok’arin kwacewa tana kuka tana kallon Abbakar ba
Ya kalli kowa a wajen tukunna
Ya ce ‘’yanzu na samu attention d’in kowa ko?
Perfect(dai-dai kenan) bari ayi magana’’
‘’My name is black snake (suna na Black snake)
wanda ya kamata ace kuna jin tsoro amma na ga ku da Babanku kun raina ni, wanda hakan ne ya nuna min cewa ba ku san wayene ni ba ba kuma kusan what i’m capable of ba(abunda na kan aikatawa ba).”

“Baba na nan kwance’’
Ya yi maganar yana nuna Baba, Kafin ya d’aura da cewa
“ya ci kud’ina!.
Ban san ta ya aka yi this old man (wannan tsohon) ya samu guts da audacity d’in (ƙarfin guiwar) cin kud’ina ba but duk nan mun san ya ci min kud’ina, sannan a statement d’inshi ya rubuta in yi mishi duk abunda na ga dama idan har bai biyani ba.’’
Dariya ya yi kafin ya d’aura da cewa ‘’sai da na saka aka dubamin aka tabbatar min da mutumin nan ba mahaukaci baneba
Tukunna
Saboda na yi mamakin mutum mai hankalin da zai yi wannan rubutun a statement na tsakanina da shi
I’m the black snake
(Ni ne fa black snake)”
Ya fad’i hakan yana d’aga hannuwanshi biyun sama
still yana rik’e da hannun Manubiya, kafin ya ci gaba da cewa “ni mutum bai ce in azabtar da shi ba ma na azabtar ballantana kuma ya fad’a?!.
Anyways I was overseas
(Ko dai yaya ma, ina ƙasar waje)
ba na k’asar aka fara case ɗinnan.

Ni da Kabir a friend
of your nephew Yusuf (Abokin ɗan wanka Yusuf)
muka tafi and ya ji ni a waya ina magana akan hargitsin
shine ya bani labarin da na ji dad’i kuma da idanuwana suka gani na sake jin dad’i….

Da farko ya ce min
‘wannan Baban ko kashe shi zan yi ba zai biya ni kud’ina ba saboda bashi da kud’i!
Amma akwai wata hanyar da zan iya fanshewa….
Baba yanada kyakkyawar yarinya fara k’al! akwai wata rana da ya je a gidan su Yusuf d’in ya ganta ya cewa Yusuf yana sonta to ashe
wai budurwar Yusuf d’in ce’.”
Cikin yin k’asa da murya ya ce
“ban gayawa Yusuf komai ba, bai ma san na dawo Nigeria ba as we speak(yanzu haka), dan
Kawai
Ina jin maganar budurwa na hayo private jet na na taho
Na zo in yi betraying d’in shi (in ci amanar shi)’’
Ya k’arashe maganar yana mai kwashewa da dariya
haka suma guards d’in shi duk suka kwashe da dariya.
…
‘Da kyar Abbakar ya iya zaro wayarshi ya fara k’okarin kiran sir Najeeb.
…
Sai da suka gama dariyar su tukunna Black snake ya ci gaba da cewa
“da farko ina ɗan tantama but yadda na ga Kabir ya rikice yana zuzutamin kyawun Yarinyar ne ya sa na amince na bi shawarar da ya bani na zo
Akan
‘Baba ya auramin ita ni kuma in bar mishi
1 million,
na yafe har intrest d’in’!‘’.

Manubiya bata san tanada k’arfi ba sai da ta samu damar fincike hannunta daga cikin na black snake
dan ba k’aramin girgiza ta maganar sa ta k’arshe ta yi ba.

Dariya ya kwashe da ita
kafin ya ce
‘’Ai ba ki ji best part d’in ba ma
(Ai ba ki ji mafi ƙayatarwar shirin nawa ba ma),’’
Bai jira jn magana ba ya d’aura da cewa ‘’na yi zaton ke d’aya ne, to kuma da na zo sai na tarar ku biyu ne kyawawan matan, shiyasa na zo da better
plan(shirin mafi dacewa)
‘Zan auri ɗaya in ajjiye d’aya mistress(ƙwara)’.
What a smart boy am i, ko??
(Ni ɗin mai wayo ne, ko???’’)”.
Ya k’arashe maganar tasa da tambaya yana d’an rawa kad’an-kad’an sai kuma gaba d’ayansu suka sake kwashewa da dariya.

Kasa ma motsi Manubiya ta yi dan gaba d’aya kanta ya d’au zafi,
In banda ambaliyar hawaye ba abunda take yi kamar an kunna famfo.

Su Blake snake sun jima suna dariyar da su Manubiya suka kasa fahimtar abunda yake sakasu yin dariyar kafin black snake ya d’aga bindigar sa ya harbi window dan haka duk suka yi shiru suka nutsu..

su Manubiya kuwa in banda karkarwa ba abunda jikinsu yake yi,
Addu’o’i kawai su ke karantowa
dan tabbas black snake masifa ne.

A kan Baba ya k’arasa ya tsaya tukunna ya ce
‘’Okay Baba,
komai yana Hannunka yanzu, kaga dai na
harbi mutane har biyu…
But bafa wai na yi releasing gaba d’aya temper d’ina bane ba(ammafa a hakan ba wai na saki gaba ɗaya fushina bane), dan na yi iyakar k’ok’arina wajen danne Zuciyana shiyasa ka ga na harbesu a wajen da na tabbatar ba za su mutu ba!
saboda bana so in yi mugun abu a gabanka a matsayinka na father inlaw d’ina(surukina)

Amma, na yi maka alƙawarin muddin ka yi mini gardama! musu! ko taurin kai! to zan kashe maza guda ukun nan
Sannan in tafi da matana!
Ruwanka ne ka yarda ko kar ka yarda, kuma
ba za ka sake ganinsu ba
sai wataƙila bayan shekaru sha biyar in sun tsufa sai su dawo maka.

Dan haka idan ni ne kai Baba to zan yi wa black snake biyayya in aura masa mata d’aya in bar masa d’aya kamar yadda ya ke so
kowa ya tafi safe….

A rabu ba tare da wani fad’a ko grudges (riƙon haushi) ba, kaga ta hakan sai mun fi kare dangantakar da ke a tsakaninmu a samu ta zamto lafiyayyiya kuma dauwwamammiya.

Sannan wani hanzari ba gudu ba,
Inaso ku san cewa ba za ku iya sharia da black snake ba!
Dan haka idan ma kuna tunanin court ne
na wuce nan tun tun tun tuni….
I have my ways!
(Inada hanyoyi da dabaru na).’’
..
Da kyar Abbakar ya iya d’ago wayarshi ya kira sir Najeeb,
bai d’auka ba dan haka ya samu ya tura mishi message
da taimakon Ya Nafi’u wanda ya tambayeshi ‘’mai zai yi?’’ shi kuma ya ce masa ’’wanda zai taimakesu ya ke so ya kira’’
Daga nan ya gaya mishi shi kuma
ya rubuta;
‘Manubiya tana buk’atar taimakon Yash da gaggawa’
Da
Address d’in police station d’in da suke a k’asa.’

Daga haka suka tura ba tare da an gansu ba.

Kishi haushi da kuma takaicin abunda ya sake aikatawa wanda ya yi wa kansa alk’awarin ba zai kuma ba ne…suka taru suka sake zuzutamasa azabar da ya ke a ciki…dishi-dishi ya fara gani, daga haka idanuwansa suka rufe, ya sume a wajen yana mai addu’ar Allah ya sa Yash d’in ya zo, dukda kuwa kishi da takaicin sake had’ashi da Manu da yayi a karo na biyu yana ta addabar zuciya da ruhinsa amman kuma ba zai iya barin Manubiya a cikin wannan bala’in ba, bayan ya san akwai hanyar da zai bi ya cece ta.

A chan gefe kuwa, wani
a cikin guards d’in black snake ne ya tak’ark’are yana yi masa
bayanin yadda ake auren Musulmai dalla-dalla, dan bai
gama sani ba kasancewar sa Christian.

A take suka yanke shawarar za a yi na musulmai
kuma za a yi na Christian’s duk a wajen a yau!
Dan haka ya cewa d’aya a cikin guards d’in nasa ya tafi ya d’auko pastor ɗinsu na church ya zo da shi kafin a gama d’aura na musulman.
………
Kuka gaba d’ayansu suke yi,
ga Abbakar a yashe an ce za a kaishi asibiti
Amma Black snake ya ce ’babu uban wanda zai yi motsi a wajen har sai an gama aura masa Manubiya.’
Zuwa wannan lokacin su kam sun d’auka ma Abbakar d’in ya rasu ne saboda dogon suma ya yi mai nauyi, duk wanda ya ganshi ba zai yi tunanin akwai rai a jikinsa ba.
Chapter 61 · 0% Book details