Sashe 25
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ciki d’acin Zuciya ta juya ta kalli Uncle ta ce
‘’tunda na haifi Al’ameen
bai tab’a yi mini musu ba
sai da ya had’u da Yarinyar nan, Wallahi’’.
Cikin katse ta Manubiya ta ce
‘’Kar ki d’aura alhakin taurin kan d’anki akan mu, tunda ba ke kad’ai yake yi wa ba…ki tambaye shi ki ji yadda muka dinga cewa kar ya zo inda muke amma sai da ya je!!!
bayaga haka a gani na ai ke kika haifi Al’ameen dan haka idan yayi taurin kai
ko ya ƙi yi miki biyayya hakan yana nufin ke ce kika kasa sannan ke ce kika sangarta abunki …..’’
‘’Manu!!’’
Ya Musbah ya kira sunanta da kakkaurar murya yana kallonta
da idanuwansa waenda suka kad’a suka yi jaa.
Sai a sannan Ammi ta d’auke idanuwanta daga kan Manubiya ba tare da ta ce komai ba ta mik’e ta kalli Uncle ta ce
‘’Shigowar da na yi cikin d’akin nan ya ishi k’ask’anci ba sai na tsaya wannan y’ar ta gaya mini maganganu ba!
Idan ka lura ko uban su bai isheni kallo ba shiyasa na kira ka akan ka yi mana alk’alanci ni da Jidda, amma tunda basu san sulhu ba sannan basu san
banbancin da yake tsakani na da su ba, inaso ka gaya musu nace ‘duk abunda Al’ameen ya kashe musu su dawo mini da shi!!
kafin nan da awanni ashirin da hud’u, idan kuma ba haka ba to wallahi kotu ce za ta raba ni dasu’.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita fuuuuu.
Cikin rashin jin dad’i Uncle ya kalli Baba ya ce
‘’Haba Musa, yanzu ina amfanin haka? wutsiyar rak’umi fa ta riga ta yi nesa da k’asa, bayan haka ma Ina ce ita Jiddan Yusuf za ta aura, mai ya sake had’ota kuma da Al’ameen ɗin da aka raba ku da
wannan Matar kwanakin baya da kyar????’’
Cikin tsananin ɓacin rai Ya Musbah ya ce
‘’Ta je ta tafi kotun, idan bata da hankali, waye take tunanin zai kalle ta?
kud’i ai Al’ameen ne ya bayar ba ita ba’’.
Cikin katse shi Uncle ya ce
‘’Kai Yaro ne har yanzu Musbahu, kamar yadda ta ce
akwai fa bambanci mai k’arfi a tsakanin ta da ku, Allah na tuba ko police station ta kai ku ta kulle wallahi sai kun ji a jikinku!!
dan babu d’an sandan da zata zubewa kud’i ya ƙi sakawa a narkeku, barin ma idan ta ce kud’i take binku tsaf za a yi ta jibgarku, tunda an san baku da shi har sai kun biya, idan ma za a tsaya muku to fa kafin a yi wani abun kun ji jiki….
gashi yanzu kowa ta kansa yake yi ban san taya ma za a fara biyanta kud’in ba, thats in ba a yi rashin saar kullenkun ba…
Kai yanzu instead of ka ji da rashin lafiyar Matarka mai yasa
ka je kana amshe kud’in Yaro?.’’
Uncle ya Ƙarashe maganar tasa cikin b’acin rai.
A hankali
Baba ya d’ago gajiyayyun idanuwansa yana kallon Yayan nasa, bai bashi amsar tambayoyin sa ba
maimakon hakan sai shima ya jefa masa tashi tambayar ta hanyar cewa
‘’Menene yake damun Matar tawa?’’
Cikin rashin fahimta Uncle ya ce
‘’Ban gane ba’’
Cikin son fahimtar da shi
Baba ya ce
‘’Wanne kalar ciwo ne yake damun matata wanda har ta shafe sama da wata d’aya a kwance a gadon asibiti?.
Kai d’an uwana ne dan haka na san ka je ka duba ta kuma ya kamata ace ka san abubuwan da suke damun ta’’.
Cikin kame-kame
Uncle ya ce
‘’Magana za ka gaya min?
baka san yanayin tsarin aikin banki ba ko? to bari ka ji Matana ma hak’uri suke yi da ni!
Ni kaine bani da lokacin kaine
balle kuma..’’
‘’Balle kuma wani ni,ko?’’
Baba ya k’arashe masa maganar tasa cikin sanyin murya.
Cikin d’an fad’a-fad’a
Uncle ya ce
‘’Kaga Musa, ba ta wannan muke ba yanzu, kar ka zille ta wannan hanyar, ka fito ka fad’i ta yadda akayi ka karb’i kud’in yaro da kuma dalili, ni kuma in gayawa su Baba Habu daga nan mu ga abun da za mu iya’’.
Kamar Baba ba zai yi magana ba sai kuma ya yi murmushi tukunna yace
‘’Ba zillewa zan yi ba, amsar da zaka bani ita zata sa ka fahimci yadda akayi na karɓi kud’in.
Ciwon k’oda ne ya ke damun Amina wanda saida ta kai ga an cire (guda ɗaya).
sannan ta samu stroke!!
hawan jini, ga kumburin zuciya..
Iyakar allurai da magungunanta kad’ai aiki ne.
Ba daban Al’ameen ɗin ba to da ban san ya zan yi ba’’
Ya k’arashe maganar wasu zafafan hawaye suna zubo masa….
A hankali ya share hawayen kafin ya kalli Uncle ya ci gaba da cewa
‘’Waennan sune abubuwan da suke damun Matata suka sanya har na karb’i kud’in Al’ameen
Saboda ya nuna kwad’ayin yanaso ya taimakeni sannan shi kad’ai ne ya zo mini ya kuma taimakeni.
Inaso ka gayamin
In da ace kaine a matsayina
shin,
‘Ba za ka amshi kud’in ba’?”.
Uncle ya dad’e yana kallon Baba kafin ya ce
‘’Anjima za mu had’u a parlourn Kaka Mallan, a nemo mafita
tsakanin kai da Ammi!.
Sannan a tabbatar da maganar Jiddah da Yusuf dan ta hakanne kawai ja’irar Yarinyar nan ba zata sake nemo mana magana ba’’
Ya fad’i hakan yana mai kallon direction d’in da Jiddan take,
kafin ya juyo ya kalli Ya Musbah ya ce
‘’Har ga Allah ina jin tsoron Matarnan(Ammi), fad’a da mahaukaci sai sarki, ka fahimtar da su dan Allah.’’
Ya na gama fad’in haka ya kama hanya ya fice .
Sai a lokacin Manubiya ta samu ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa.
A hankali Jidda ma ta ci gaba da nata kukan.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*15*
Cikin rashin jin dad’i Baba ya ce
‘’Ban yi tunanin zan kafa miki doka ki shallaketa ba Jidda,
yaushe har kika yi wayo da girman da za’a raba ki da shi ki kasa hak’ura?
Ashe dama ziryar da yake ta yi wajen ki ya ke zuwa a b’oye? Kenan har yanzu kuna tare? Amman shine da ke da shi kuka ce mini babu komai tsakanin ku, kun rabu ko?. Ni kika yi wa k’arya Jiddah?’’.
Cikin fashewa da wani irin kuka ta ce
‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri…
Cewa yayi zai samu right time ya yi maka bayani ta yadda zaka fahimce mu’’.
Cikin fad’a sosai Baba ya ce
“Bayanin me? Ni za ku yaudara?.
yanzu shi Al’ameen ashe ba zai iya taimako na saboda Allah ba sai in da wani dalilin kenan, yaushe aka haifeku
daga ke har shi da zaku raina min wayo?’’
Ya k’arashe maganar cikin fushi.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’Baba ka yi hak’uri dan Allah, bara in fita in ga yadda za’ayi da kud’in Matar nan, gara kawai a rabu lafiya.’’
A hankali Manubiya ta share hawayenta ta ce
“Zan je mu yi lissafi da ita, ta lissafa kud’in ta zan biyata ta hanyar yi mata aiki!
A gidan ta.”
Da sauri Ya Musbah ya ce ‘’za mu san yadda za mu yi ni da Baba ki maida hankali akan karatunki ki yi shiru,kawai.’’
Murmushi ta yi kafin ta ce
‘’Ka bari nima in taimaka dan Allah, in kuka kawo naku sai a had’a ragowar da bai cika ba
In yi mata aiki na Iyaka kwanakin, kud’in suna da yawa fa ka barni inaso in taimaka nima.
Makaranta kuma ba matsala zan iya had’a aikin da makarantar karka damu.’’
A hankali Muhsin ya ce
‘’Za mu dinga zuwa tare, sai in dinga tayaki da wani abun’’.
Jinjina Kai ta yi alamun ‘to’
Tana kallon sa tana murmushin da ya fi kuka ciwo.
Kafin ta kalli Ya Musbah
Ta ce
‘’Bara in je tun da wuri mu ji ko zata amince’’
Sai a sannan Jidda tace
‘’Adda da kin bari na….’’
Cikin katse ta ta ce
‘’Ba komai Jidda, kar ki damu, zamu gyara komai, inshaaAllah’’.
A hankali Jidda ta matsa ta rungumeta ta na kuka sosai kanta fal da na sani, ba tare da Baba ya gani ba ta saka mata wayar da Al’ameen d’in ya siya mata Kafin ya tafi a Hannu, ita kuma karb’a kawai ta ɗan jinjina Kai, daganan ta d’auki hijab d’inta ta sake sakaya wayar sannan ta cewa Muhsin ya taho.
…
A gaban Baba ta je ta durk’usa tana addu’ar Allah Ubangiji yasa kar yace a’a…
cikin kwantar da murya tace’’Baba,dan Allah ka bar ni inje, kar ta zo ta tozarta Mutane ka ga inna bata da lafiya, kar a kuma d’aga mata hankali, gara mu bi ta a sannu a rabu lafiy….’’
Yafi mintuna biyu bai yi magana ba kafin chan ya had’iye wani k’ululun bak’in bak’in ciki da tashin hankali tukunna
ya jinjina mata kai alamun amincewa.
Chan k’asan ranta ta ce
‘’Alhamdulillah’’.Sannan suka mik’e da niyyar fita, har sun d’an gota ta ji yace
‘’Manu’’.
Sai da ta lumshe idanunta tukunna a hankali ta ce
‘‘Na’am Baba’’
Ahankali yace
‘’Kar ki yi ja’inja da ita sannan ki yi mata magana da tattausan lafuzza’’.
‘’InshaaAllah Baba’’ tace
Daganan ta jaa Hannun Muhsin suka wuce.
Suna fita Baba ma ya juya ya fita.
Chan bayan gidan inda ba kowa yaje, yana zuwa ya fashe da wani irin kuka, ya manta rabon da yayi feeling
helpless irin yau, ba irin wannan rayuwar ya so ƴaƴansa su yi ba,ba irin wannan uban yaso ya zamto ba amman ba yadda zai yi ba shi da yadda zai yi,ko wacce hanya ko ina ya juya a toshe yake gani..
Ya jima ya na kuka kamar wani k’aramin yaro kafin daga bisani ya share hawayen nasa yayi istighfari sannan ahankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’ tukunna ya mik’e ya koma d’akin.