← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 84

Sashe 73

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya riga ya san ba wani abun bane kawai wayar da ta ji yana yi ne ya kuma d’aga mata hankali tunda tun daga d’azun har izuwa yanzu bata d’aga k’afa na minti uku ba! kiran sa kawai take ta yi akai akai…ba ƙaƙƙautawa

Ya san yana d’auka za ta fara tambayar sa da wa yake waya kamar wani k’aramin Yaro,
ba zai iya yi mata dogon bayani ba gaskiya, gashi kuma dama a fusace yake da ita.
Zai san abunda zai fad’a mata dan har ga Allah sai komai ya kammala tukunna za ta ji, saboda bai yarda da Mommy ba akan duk wani abunda ya shafi Kausar!!!
Sarai ya ji abunda Kausar d’in take fad’a mata a ranar da ya je sama wajen Mommyn zai yi mata magana akan ‘ta daina turo masa Kausar side d’in sa’,
Shiyasa ya yanke akan ba za su ji yanzu ba sai Daddy ya amince sannan komai ya shiryu ya zama ready tukunna, sannan bayaga wannan dalilin ma yanada dalilai dayawa….

Kiran wayar ne ya sake shigowa dan haka ya kalla, kafin ya sake d’auke kai…har ga Allah bai san me zai ce mata ba idan ya d’auka, shiyasa ya bari akan in ya gama shawarar me zai ce mata ɗin da zuciyarsa sai ya saurareta amma ba yanzu ba, dan baya so ta chanja mishi yanayi na nishaɗin da yake a ciki yanzu..
Ya san abunda ya ke yi baya kyautawa amman itama Mommy bata kyauta mishi ba!
Ba zai iya yi mata dariya ko ya sake mata ba, yana jin zafin ta har yanzu.….na marin da ta yi masa a gaban k’annensa sannan ta fifita Yassir sama da shi, har gobe idan ya tuno maganganunta ji yake kamar ya yi kuka, abun yayi masa ciwo sosai, ya tsaya a ransa, ya kasa mantawa…..

Cikin son kawar da tunanin ya maida hankalin shi ga Manubiya, wadda tausayinta gaba d’aya ya mamayesa tun ɗazu, a hankali ya ce ’’Allah ya sa a dace da magani da pt ɗin doctor sofia, a samu mshaifiyarta ta warke ta fara magana’’
yana wannan tunanin text na adress d’inta ya shigo wayarsa dan haka ya turawa Dr sofia d’aga haka ya mik’e ya fice.

Wajen Daddy ya fara biyawa ya bashi hak’uri sosai tukunna yayi masa sai da safe ya wuce.

Ya san cewa uwa daban take kuma tanada daraja, shiyasa duk yadda ya so sai ya gagara wuce side d’inta ba tare da ya shiga ba dan ya san hakan bai kamata ba duba da yadda tayi ta kiranshi ma ya ƙi d’auka.

Ba dan ransa yana so ba, haka nan ya k’arasa bak’in k’ofar side d’in nata ya shige cikin parlourn ya wuce zuwa bedroom d’inta.

murd’a k’ofar yayi amman ga mamakinsa sai ya ji ta a rufe.

Yana shirin fara knocking ya ji magana k’asa-k’asa….kamar zai tsaya kuma sai ya juya kawai ya fita dan ya san ita da Baaba Larai ne kuma magana mai mahimmanci ce sukeyi tunda har ya mud’a handle amman suka gagara lura

sannan ko yaro ne shi ɗin, ya san bai kamata ya yi musu laɓe ba.

Da wannan tunanin ya fice ya nufi d’akin Yahanasu yana mamakin yadda sam baya jin Mommy a jikinshi, dan har ga Allah shi kansa abun yana damun sa….
kwata-kwata baya jin ta kamar yadda yake jin Daddy da su Yasira wanda kamata yayi ma ace ya fi jinta a zuciyarsa fiye da kowa tunda ita soyayyar uwa daban take…
Har a bakin ka’aba ya yi adduar ‘Allah ya saka masa soyayyar mahaifiyarsa a cikin zuciyar sa’
saboda wani zubin har tsoro ya ke kar ya je shi bai sani ba rashin shak’uwar su ta ja yayi wani abun da za ta ji haushi, ta ga kamar ba ya kula da ita yadda ya kamata, ya je garin hakan ya fad’a halaka.

Shiyasa ko da yaushe ya ke iyakar bakin k’ok’arin sa wajen ganin ya samu ya jata a jiki to ita kuma gashi yanzu ta zo ta kuma bak’anta masa rai akan Yasir!!!
da sauri ya kawar da tunanin saboda in ya tuna ma ransa sake dagulewa yake yi dan
maganganun da ta farfad’a a ranar sun tsaya masa a rai matuk’a…..

Cikin takunsa ya k’arasa dak’in Yahansu, bayan ya gama yankewa akan
‘sai Daddy ya gama hucewa tukunna maybe ko zuwa gobe ya same shi da maganar Manubiya.’

Ya san bashi da matsala tunda Daddy da bakinsa ya sha gaya musu cewa “ko wanene ko wacece in suka kawo zai aura musu a duk lokacin da suke so in dai tarbiyyan su yayi masa’’
Amma dukda hakan yana adduar Allah yasa ya dace, kar Daddy ya baɗa masa ƙasa a ido.

Sai da ya shiga da sallama tukunna ya ɗan sake yi mata knocking dan ya fahimci kamar ma bata san ya shigo ɗin ba…saboda a chan kan tebur ya hangeta ta barbaza takardu da alamun aiki takeyi.

Glasses d’in idonta ta zare ta mik’e ta nufesa tana murmushi.
..
A gefen gado ta zauna tukunna tace masa’’Bismillah’’ta yi maganar tana nuna masa gefenta,
ganin yadda ya tsura mata idanu.

Sai a sannan ya d’an sauk’e ajiyar zuciya yana me zama a gefen nata ya ce ’’baki gama warkewa ba amma kika zauna aiki har twelve?
ya jikin naki?’’
Yayi mata tambayar yana kallon ta.

Murmushi kawai ta yi kafin ta ce
‘’Alhamdulillah’’

Zata yi magana ya katseta ta hanyar cewa
‘’Tunani kike yi ko? shiyasa ki ke ta tulawa kan ki aiki..
har yanzu kin k’i ki kwantar da hankalinki’’

Murmushin ta sake yi sannan tace
‘’Bafa na tunanin komai Yash,
mu bar maganar nan, yanzu fad’a min meye kake so ka gaya min?”
Ta fad’i hakan da murmushi kwance akan fuskarta.

D’an k’ura mata ido yayi kafin ya ce ’’Mun fara b’oye-b’oye a tsakanin mu kenan!
Kin san dai za ki iya tattauna koma mene dani dai ko?.
ki kwantar da hankalinki dan Allah Yahanasu, ni wallahi har ga Allah ban ga wani tsufan da kikayi ba, meyemarabar ki ke da su Kausar d’in??
Kausar ta kusa 28 fa haka itama Yassira, ita kam tama rufe 28 d’in…
meye marabar ku da za ki bi ki d’aga hankalinki??’’.

A hankali ta ce
‘’Yash, ba zaka gane ba, na tare musu hanya. in ban wuce ba taya za su saki jiki su ga dacewar suma ya kamata su wuce???’’

K’ura mata idanu ya yi, wanda har sai da ya sanyata d’an sunkuyar da kanta tukunna ya ce
‘’Mommy ko Baaba Larai wani a cikinsu ne ya gaya miki haka ko? ko kuma su Kaisar d’in?’’

‘’Yash dan Allah mu bar maganar nan, ka san dai yadda nakeji idan ana irin wannan maganar ko?
ka bar maganar kawai’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e tukunna ya ce ’’tam, na ji, zan bar maganar
amman sai kin yi min alk’awarin kin daina tunani kuma kin daina ɓoye min abubuwa, idan kinada damuwa ki dinga tattaunawa da ni pls za ki ji sanyi a ranki!
zama a d’aki ke kad’ai daga ke sai matsalolinki ba abunda zai ja miki sai depression!

Ki kwantar da hankalinki,
Aure nufi ne na Ubangiji…
yanzu ne fa za ma ki fara 30s d’in ki Yahanasu sai yanzun ne ma fa kika zama lady,

kar ki biyewa al’adar Bahaushe ki kashe kanki, kalli yadda kika rame fa.’’

Hawayen da ya zubo mata ta ido d’aya ta sa Hannu ta share kafin ta ce ’’Yash,dole abun ya dameni….tun Inada shekaru 15 nake so inga na yi aure. so nayi Ina gama secondary school ace na yi aurena,
ba wai dan komai ba sai dan
kawai ni inaso in ga na yi aure na haihu na kula da family d’ina, amma kalle ni har yanzu”.

Ajiyar zuciya ya sauk’e, ya matsa kusa da ita ya kama kafad’unta tukunna
yace’’kalle ni nan Yaha’’

Sai da ta d’ago ta kalleshin tukunna ya ce
‘’Bawa, kowanne da akwai tashi kalar k’addarar,
ki d’auka ke wannan ce taki…
Ubangiji dama ya kan jarabcemu da abunda muke matukar so, za mu samu delay amma da ikon shi in mukayi hak’uri sai ki ga mun samu har ma da k’ari.
Ki godewa Allah ma ke da ya jarabceki a yanzu, ba sai kin tsufa ba, saboda a kullum Ina yi miki addua ‘InshaaAllah wannan ita kad’ai ce mummunar k’addarar ki!
kuma itama ɗin inshaaAllah kwanan nan za ki yi auren ki, komai ya daidaita.
InshaaAllah za ki samu mutum mai hankali mai tsananin k’aunar ki, ki yi aure, ki hayayyafa, hankalinki ya kwanta, ki samu kwanciyar hankalin da in kika tuna kin tab’a shiga wannan damuwar ma sai ki nemi b’acin ran da kika shiga a yanzu ki rasa, ki ji kamar bai tab’a faruwa ba.

InshaaAllah za ki samu yalwataccen farin ciki a gaba wanda zai goge duk wannan bak’in cikin da kike a ciki.’

Amma yanzun ina so ki rungumi k’addararki ki cinye jarabawarki sannan ki kwantar da hankalinki, kin ji ko?’’

A hankali ta jinjina Kai ta goge hawayenta ta ce ’’na gode Yash, Thankyou so much(na gode sosai)”.

‘’You are welcome
(Babu komai ai)”
Ya ce, yana murmushi kafin ya cikata
sannan ya ce ’’akwai Labari mai daɗi, amma ki fara yi min alƙawarin ba za ki fad’awa kowa ba a yanzu sai in gaya miki…
saboda inaso sai komai ya kankama tukunna kafin kowa ya ji’’

Tana wani faffaɗan murmushi ta d’aga mishi kai ta ce ‘’na yi alƙawari’’

Wani kalar murmushi irin kamar ya na ɗan jin kunyarta ɗinnan ta ga yana yi kafin ya ce ’’kin kusa ki yi k’anwa…
InshaaAllah inaga wani watan ko wataƙila kafin ma nan da wata ɗaya
Zan yi aure, in har Daddy ya bani haɗin kai ita kuma Yarinyar ta bani dama da”.

Yahanasu ba ta san lokacin da ta ce ‘’what!? (Da gaske!?)’’ cikin farin ciki ba.
Tana mai zaro idanunta
Kafin ta d’aura da cewa “eh lalle Manubiya ta ciri tuta,’’

A hankali ya yi murmushi ya ce ’’eh, da gaske, ki tayani da addu’a da k’ok’ari a yi auren nan kamar yadda na tsara da sauri, saboda Manubiya ta riga ta sace zuciyata’’.
Chapter 73 · 0% Book details