Sashe 60
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uncle kanshi dubu uku ya turo ta acc d’in ya Nafi’u ya ce
“su jira sa, in ya tashi a aiki zai zo ya duba Baban.”
Gefe Jidda ta koma ta fashe da wani sabon kuka, ji take kamar ta gudu…..
Saboda ita Manubiya ta yi aikatau a gidan Ammi!
sannan yanzu ma gashi saboda ita aka kama Baba!
in ba dakyar ba kuma ta san Ya Yusuf ne ya ce ayi masa horo mai tsanani, so yake ya rama dukan da suka yi mishi.
Kuka gaba d’ayansu suke yi daga ita har Manubiya…
Su ya Musbah kuma in banda waya ba abunda suke yi dan kaff
d’an kud’in hannunsu ma duk ya k’are a siyen kati.
Suna tsaye a harabar police station d’in sukaga wasu polisawa sun fito da tray da almakashi da wasu k’arafuna akai duk jini,
sun nufi fanfo suna ƙarasawa su ka hau wankewa….
Tun kafin kwakwalwar Manubiya ta gama d’aukar charjin ‘watakil jinin Baba ne wannan…’
ta kwasa a guje ta yi cikin police station d’in, da kyar ta iya tsayawa ta shiga tambayar police d’in da ya biyota da niyyar taro ta. Tana kuka ta ce “ka bar ni in ga Baba, saboda Allah da Annabi.”
Tausayi ta bashi dan haka ya nuna mata k’ofar inda Baban yake, ya juya kawai, a ransa yana mamakin ‘mai ya had’a waennan kamilallun mutanen da Black snake.’
Juyawa ta yi zata koma dan ta baro d’akin a baya, suka yi ido huɗu da su Ya Musbah, ashe sun biyota a baya suma, duk a gigice.
sai da suka je bakin k’ofar d’akin kuma duk sai suka kasa shiga,kowa yana jin tsoron abunda zai shiga ya tarar.
Da kyar Ya Musbah ya yi ta maza ya tura k’ofar ya shige!
daga haka suma suka samu kwarin guiwar mara masa baya.
Turuss! ya Musbah da ya Nafi’u suka ja suka tsaya….
Su manubiya kuma suka saki wani irin kuka.
A kwance suka sameshi daga shi sai vest da dogon wando…
In banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, da alamun bai ma san waye a kansa ba, ga jini a zuzzube a k’asa!
Sai da suka matsa kusa dashi sosai, dakyar, tukunna suka lura ashe har da faratunsa na k’afa d’aya guda d’aya da na Hannu yatsu biyu suka fara zarewa.
Da sauri suka zauna a gabanshi Jidda ta d’aura k’afafun shi akan cinyar ta Manubiya ta shiga goge masa gumi tana yi masa fifita, suna yi suna kuka a rikice.
A zuciye ya Nafi’u ya mik’e cikin fushi ya ce
‘’Wanne irin rashin imanine da dak’ik’anci wannan?
A haka zai fito musu da kud’in nasu?’’
Sai kuma ya nufi hanyar waje.
Da sauri Ya Musbah ya sha gabansa ya tare sa.
Cikin fushi ya Nafi’u yace ‘’matsa,matsamin in je in samesu”
Cikin son fahimtar da shi ya Musbah ya ce ’’Nafi’u idan rai ya b’aci hankali ba ya gushewa…
ka je ka samesu ka ce musu me?
kud’i fa aka basu aka basu order kaga kuwa dole su yi abunda aka ce, kuma baka karanta takardar bane?
mutum bai saka hannu bama ya aka k’are ballantana an saka hannu?
Dole su yi abunda aka ce!
Kuma ko Ina za mu je babu wanda zai tsaya mana, idan ka yi fad’a ko kuma ka ce zaka tada rikici yanzu sai a had’a da kai saboda baka da kud’i nima bani da kud’i shima Baba bashi da kud’i.
Ka tsaya yanzu mu nutsu mu San abunyi mu ceto Baba, dan hayaniya da rikici ba namu bane ba.’’
Da kyar dai ya Musbah ya samu ya d’an kwantarwa da ya Nafi’u hankali aka samu ya nutsu kaɗan.
Yana huci ya ce ’’na ji, ka fi ni gaskiya, ba zan je in same su ba amma wallahi tallahi
duk wanda ya shigo da niyyar sake yin wani hauka anan wajen sai na illatashi.
Ina nan ba inda zan je’’.
Lumshe ido kawai ya Musbah ya yi ya bud’e ya ce ’’ba za su sake ba, in ma bamu samu mun had’a kan kud’ad’en ba, ba komai ni sai in fanshe sa’’.
daidai nan Abbakar ya shigo wajen shima a rikice. Yana ganin Manubiya da yanayin kukan da take yi hankalinshi ya sake tashi..hankalin nashi bai gama tashi ba sai da idanuwansa suka kai ga Baba.
Da sauri ya k’arasa ya na salati
sai kuma ya kalli Manubiya, kamar jira take yi kuwa a take ta sake fashewa da wani sabon kukan.Ji yayi kamar shima ya sa kuka, da kyar ya samu ya tsugunna inda take a ahankali
ya d’aga hannu kamar zai shafa fuskarta sai kuma
ya sauk’e hannun jiki a sanyaye kafin ya runtse idonshi da k’arfi ya bud’e tukunna a hankali ya ce
‘’Ki yi hak’uri Manu, za mu san yadda za a yi inshaaAllah..
d’azu
ya Musbah ya kirani yake gaya min,
3k ne kawai a acc d’ina na tura mishi yanzu kuma ga 20 na sake nemowa…ki kwantar da hankalinki za’a samo, kin ji, dan Allah ki daina kuka’’
Da kyar ta samu ta ce
‘‘Abbakar kafin nan mukasan mai za su sake yi masa? kall …..”
K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit.
Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu…
*MANNUBIYA*
*36*

Body guards ne bak’ak’e k’irin da su sanye da bak’ak’en kaya da bak’in glass…
biyu na farkon suna rik’e da manya manyan bindigu, ragowar na bayansu kuma k’anana ne a sak’ale a gefen k’ugun ko wannensu.
Yanayin wajen suka kalla dan haka d’aya a cikin su ya juya ya fita da gudu, ya je ya kawo kujera ya ajjiye, kafin ya koma ya shiga cikin layi biyun da suka yi a jere tundaga bakin k’ofar har izuwa inda suka ajjiye kujerar a gaban Baba.
Tsayawa kawai su Manubiya suka yi gaba d’ayansu suna kallonsu..
Basu kai ga gama tunani da lissafin abun ba, tashi ɗaya suka fara jiyo wata iriyar dariya ana yinta cikin
wani kalar sauti da kuma murya marar dad’in sauraro….
Yadda ake dariyar ne zai sanya tashi d’aya a
fahimci rashin kamala da rashin sanin ciwon kan mamallakin muryar…Yana magana da turanci yana dariya sosai kamar wani tab’abb’e!.
Yadda su ke jiyo muryar tana matsosu ne ya sanya suka fahimci Mutumin nan cikin d’akin zai shigo..
Ta tsakiyar body guards d’in nashi waenda suka hau layi ya bi ya shigo…
Ƙato ne sosai, dogo, lukuti, fari sosai..farin nasa irin jaaa!! Ɗinnan.
Babu gashi ko
guda d’aya tun daga scarf d’insa (fatar kansa) har gemun sa da gashin baki duk babu gashi!
Iya kar girar sa da gashin idanunsa ne kawai masu gashi a kaf ilahirin kansa zuwa fuskarshi wanda hakan ne ya basu damar ganin asalin yanayin fuskartashi
wadda take d’auke da
k’ananan Idanu jajaye, da ɗan
guntun Hanci, yayinda Bakinsa ya kasance madaidaici.
Yadda dpo yake binsa yana russuna masa yana yi masa magana kamar zai kwanta
abun dole ya k’ular da jama’a…
dariyarsa kawai yake ta yi shi kam at the same time yana bawa dpo amsa, har ya iso inda Baba ya ke!.
Shiruu ya yi ya tsayar da dariyar tasa kafin ya kalli dpo tukunna ya ce ’’ku ka ce yana kan karb’an punishment (hukunci)
But (amma
nagani he’s still conscious,Y(har yanzu yana cikin haiyyacinsa, mai yasa?)?’’.
Yayi tambayar yana mai zubawa dpo jajaye idanuwansa.
A take dpo d’in ya rikice ya fara kame-kame ya shiga
karanto addu’o’i daban-daban a k’asan ransa yana mai neman tsari daga sharrin ‘Black Snake’!
Dan kasancewar yanzunnan ya gama raha da dariya da shi
ba shi zai hana shi sauya masa kamanni a take a wurin ba!..
kamar kuwa ya sani dan tashi d’aya black snake ya gama rayawa a ransa ‘zai sanya body guards d’in shi su yi wa dpo asalin horo, a yanzu a gaban kowa, ta yadda next time zai fahimci mai ake nufi da horo!!’
dan haka ya d’an d’ago kansa da niyyar juyawa ya kira biyu a cikin body guards d’in shi amma sai
Idanuwanshi suka sauk’a akan Manubiya
wadda gaba d’aya tashi d’aya ta rikice sannan tsoro ya lullube ta daga ganinsa!
Ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin zanen bak’in macijin da ya fito tarr!!
wanda yake nan a kwance a hannunsa na dama…tun daga kwanjinshi har kan bayan tafin hannunshi
kamar na gaske
ga wasu uban sark’ok’i a jikinsa wuya da hannu da wani burgujejen wando shima mai sark’ok’i a jiki amma kuma rigar jikinsa armless(marar Hannu).
Wata mahaukaciyar dariya ta ga ya kwashe da, ga mamakinta kawai sai ta ga ya nufota aikuwa kafin ya k’araso tuni ta shige bayan Ya Musbah ta b’uya.
Da mamaki ya kalleta ya juya ya kalli Jidda sai kuma ya juya ya kalli d’aya daga cikin bodyguards d’in nasa ya ce
‘’John!dama ita biyu ce?’’
‘’A’a ai dama Kabir d’in ya ce tanada sister, remember(ka tuna)?’’
Dariya ya yi kafin ya juya ya shiga yi wa Manubiya wadda ta b’uya a bayan ya Musbah
wani irin kallo har da lek’awa yake yi yana sakewa saboda a yadda Abokin Ya Yusuf ya yi masa bayani tabbas Yarinyar ta fi haka kyau a fili..
Ya Musbah ya kalla ya kalleta
kafin ya yi wani kalar murmushi..
Ba su gama fahimtar ma’anar murmushin nashi ba suka ga ya yi fito!.
Da sauri ɗaya a cikin body guards d’inshi ya zo ya hankad’e Ya Musbah ya fisgo Hannun Manubiya ya dawo da ita gaban black snake ya tsayar, tukunna ya juya ya koma ya je ya tsaya a wajen tsayuwarshi.
Cikin d’an d’aga murya ya Nafi’u ya ce
‘’Me ye haka wai?’’
Ba wanda ya ko kalle sa balle su bashi amsa, a hankali black snake d’in ya sa Hannu ya d’an kamo hab’ar Manubiya ya d’ago yana mai k’are mata kallo.