Sashe 23
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ya fara magana ta kafe shi da idanuwa ta kasa motsi, sai da ya sake runtse Hannunta dake cikin nasa
tukunna ta yi fir-gi-git!!!
Tabbas they saw it coming(dama sun gani), amman ba su yi tunanin kwana kusa ba!
“Innalillahiwainnailaihirrajiun”
Ta shiga ambatowa a k’asan ranta..
Ta manta rabon da ta shiga tashin hankali Irin wannan a rayuwarta, sam ta manta!!
Ta ma kasa kuka…..ji take yi kamar an tsunduma Zuciyarta a cikin talge! Saboda tsabar azabar da tsananin tashin hanakalin
ya tsunduma Zuciyar tata a ciki.
‘’Mommy!’’
Yashjub ya sake kiran sunanta.
A hankali sannan da kyar ta k’ak’alo wani murmushi wanda ya fi kuka da ife-ife ciwo!
Tabbas wannan babban tashin hankali ne da aiki ya same ta, amma
ta wata fuskar kuma dama ce ta samu na gyara tsakaninta da Yash, dan yadda ta hango tsantsar tausayinta da kulawa a gareta
A idanuwan Yashjub yau
wataki’ila wannan auren da Daddy yayi ya janyo mata kulawa da shaƙuwa a wajen d’annata. Ta lura kamar yadda kishi yake weakness d’in Daddy haka Yashjub shima…
A hankali ta ce
‘’Zan sak’k’o Yashjub, ka je k’asa kawai, zan taho.
I need some time alone(ina buƙatar kasancewa ni kaɗai, yanzun.”
Har zai mik’e sai kuma ya janyota zuwa jikinsa ya yi hugging nata ya shiga bubbuga mata baya alamun rarrashi…
kafin ahankali ya ce
‘’Ki yi hak’uri Mommy, Allah zai baki lada’’
Daganan ya cikata ya mik’e ya fita.
A bakin k’ofar d’akin suka yi kiciɓis shi da Baaba Larai alamun shiga take shirin yi shi kuma ya fito.
Murmushi kawai ta yi masa daga nan ya nufi k’asa inda su Daddy suka jiran su, ita kuma ta shige.
*Baaba Larai* cousin d’in Mommy ce, kamar yadda Mahaifiyar Mommy ta haifesu su biyu kawai (ita da Ammin kausar)
Haka itama kakarta ta haifi maman ta da maman Baaba Larai kawai, sai dai ita Baaba Larai ita kad’ai aka haifa sannan har gobe Allah bai bata Mijin aure ba!!
Tun tana budurwa dama bata da samari….
Idan k’awayenta suka yi aure
sai ta koma wajen k’annen su da k’awance!!
Hatta da niece d’in k’awarta Baaba Larai ta tab’a yin k’awance.
A lokacin da ta kai shekaru talatin a duniya sai y’an k’auyansu suka fara d’aura mata sharrin *Maita!* wataƙila ko dan sun ganta fara sol ga gashi sannan kyakkyawa amman babu Miji ne, oho.
A lokacin Mahaifiyarta ta jima da rasuwa,
shiyasa Mahaifiyar Mommy ta d’aukota daga gaban Mahaifinta da Matarsa ta ce za ta ci gaba da rik’eta, dan sharrin dama ya samo asali ne daga bakin Matar uban.
A yanzu kuwa iyayennasu duk sun rasu shiyasa suka rungumi juna su uku
Ita(Mommy), Baaba Larai da kuma y’arsu Kausar.
Badaban shi Kansa Yashjub ya san Yahanasu y’ar kishiyar Mommy ce ba to da sai ya ce
‘Maybe a wajen Baaba Larai ta gado rashin auren’
amma dukda haka a kullum adduarsa itace “Allah ya sa kar y’ar uwar tasa ta k’are kamar Baaba Larai’’
Dukda kuwa cewa
‘ita Yahanasu tanada samarin
kawai idan an zo maganar aure ne ganga-ganga da ikon Allah sai wani abun ya zo ya tarwatsa…….’
Amma still yana yi mata adduar kar ta ƙare kamar Baaba Larai, a kullum da ko da yaushe….
‘’Tana Ina?’’
Muryar Daddy ta katsewa Yashjub tunani.
‘’Tana sauk’owa’’ ya basa amsa yana me k’arasawa cikin parlourn sannan ya nemi waje ya zauna suka sake gaisawa da Anty Amarya. Dama shi ya riga ya santa dan employee d’insu ce, kawai dai bai san akwai abu tsakaninta da Mahaifin nasa ba sai yau da ya ganta a matsayin Matar ubansa.
Kafin su Mommy su sauk’o, Daddy ya kira Yadira ya ce mata ta kirawo mada kowa hatta drivers da masu gadi da Kausar….
Yassir ne kawai bai hallara a wajen ba saboda har zuwa wannan lokacin bayan sati biyun da ya shafe baya gidan bai kai ga kenan dawowa ba, ya ma kashe wayar da ya tafi da ita gaba d’aya.
Mommy bata wani b’ata lokaci ba suka sauk’o itama tare da Baaba Larai!
She looks calm amman fa ana ganin fuskarta za a fahimci ta yi kuka.
Tana zama Daddy ya umarci
Yashjub da ‘ya bud’e musu taron da addua’
Ana shafawa ba tare da b’ata lokaci ba
Ya gabatar musu da Hajiya Saddik’a a matsayin Amaryarsa, kafin ya d’aura da cewa
‘’Na san ta, wajen aikinmu ɗaya!
Shekaru sha biyar kenan muna tare da ita…
Mijinta ya rasu, shekaru ashirin da suka wuce. Tanada Ƴaƴa Mata, guda biyu.’’
Daga haka ya ce
‘Ya na so tun daga kan Yahanasu har izuwa kan Yadira
kowa ya bata girma da respect,
har masu aiki yana so duk kalar respect d’in da za su bashi to itama su bata, baya so ya ji wani case ko ya ga ana gwada mata rashin d’a’a , in kuwa hakan ta faru to zai sab’awa ko ma waye’.
Masu aiki, Yahanasu sai Yashjub ne kawai suka ce
‘’InshaaAllah Daddy’’.
Daganan masu aikin suka yi introducing kansu sannan suka sake gaisheta.
Sab’anin su Yasmeen waenda suka d’auke Kai ba tare da sun ce mishi uffan ba.
Baya son creating scene shiyasa kawai ya rabu da su!
Da niyyar cin k’aniyar su idan ya samu lokacin su.
Cikin kulawa ya juya ga Hajiya Saddiqa
Itama ya ce ‘’ta d’auki Ƴaƴan nashi kamar nata,
In sha Allah ba zata samu matsala da su ba ‘’.
A hankali ta na murmushi ta ce. ‘’InshaaAllah’’.
Sai a sannan Yasira ta daure, da mugun kyar ta ce
‘’Daddy tou me zamu dinga ce mata’’
Cikin jin dadi da sauri ya ce
‘‘Ummi.
Ƴaƴanta da Ummi suke kiranta’’
Murmushi Yasmeen ta yi,
ta ce
‘’sannu da zuwa Ummi,
We are glad to have u (Mun ji daɗin zuwanki cikinmu)‘’.
Cikin tsananin jin dad’i Hajiya Saddik’a ta ce
‘’Nagode y’ar albarka’’.
Saboda da farko gabanta har ya d’an fara fad’uwa, dan ta yi tunanin Yasira za ta amsheta fiye da yadda ta ga ta yi mata duba da yadda suka riga suka san juna tun a office, shiyasa ta yi mamakin yadda suka yi mata ita da y’an uwanta!
Gasu duk mata.
Bayan an sallami masu aikin,
hira ce sosai ta biyo baya
tsakanin Yasira,Yasmeen da Ummi!
Mommy ma tana d’an sako musu Baki sama-sama…
Kafin daga bisani Daddy ya ce “za su wuce.”
Sun yi mamaki sosai da sukaji Daddy ya ce “ba a nan za ta zauna ba!
Already an kaita ma sabon gidanshi wanda ya ke a nndc quarters.”
Tsit!! Haka parlourn yayi daga jin hakan, dan hatta Yashjub sai da ya ji ba dad’i…
Har d’aurin auren sai da ya je, jiya. Amman Daddy bai ce masa ba tare da su zata zauna ba!
Kuma shi ya ce masa kar ya gayawa kowa ya yi shiru amman gashi shi ya b’oye masa abu, bayan haka sabon gidan ai Mommy ya kamata ya kai tun da shima mansion ne kamar girman nan
‘’Okay ba damuwa,zamu
zo inshaaAllah,’’
Muryar Mommy ta dawo da gaba d’ayan su daga duniyar tunanin da suka dulmiya.
Ba yadda Ummi bata yi da
Ya’isha akan ta biyota su tafi tare ba
Saboda y’arta Munira age mate d’in Ya’ishan ce kuma jibi zata baro gidan Yayarta ta komo wajenta da zama a chan nndc d’in!
Amman Ya’ishan tak’i yarda…
Ta bata excuse ɗin ‘tanada shirye-shirye na masters d’in da ta fara recently,
so tana buk’atar time domin ta nutsu ita kad’ai ta shirya abubuwa.’
Ba dan Ummi ta so ba ta tafi bayan sun yi mata alk’awarin za su je, inshaaAllah.
Har mota suka rakasu saida suka ga fitar su, tukunna suka koma ciki.
Yadira ce ta ce
‘’Yanzu dan Allah Daddy ya ..’’
Da sauri Mommy ta kalle ta,
dan haka ta ja Bakinta ta yi tsit.
Har suka yi dinner aka tashi
babu wanda ya yi zancen
Ummi ko Daddy!
Yashjub ya yi musu sai da safe
ya wuce,
Kowa ta nufi side d’inta.
Ba abunda ya fi yiwa Kausar dad’i irin yadda ta ga babu Yassir babu dalilin sa.
Dan ita sam case d’in sabuwar kishiyar Mommy bai wani d’aga mata hankali ba!
saboda ta riga ta san k’aramar alhaki ce…….
Tunda Yashjub ya koma Ɗaki, sam sai ya kasa
tab’uka komai!
zuwa wannan lokacin tabbas ya fahimci yana buk’atar sanin more about Manubiya.
Ya riga ya tsaya akan cewa ba son ta yake yi ba saboda to tayaya ma za ayi ya so ta!? in fact idanuwanta kawai ya gani dan haka if there is anything ma (idan akwai ma abun) da yake drawing nasa towards her maybe it’s the eyes, dan ya tabbatar bai tab’a ganin kwatankwacin masu kyawun su ba, ko kuma maybe akwai wata k’addarar da take jan sa zuwa gare ta wataƙila shi ya taimake ta a wani abun ko kuma ita ta taimaka masa……
A mazaunin haka ya bar lamarin, daga nan ya d’auki wayarsa ya kira Najeeb…
Ya san zai sha tsokana
amman gwara tsokanar Najeeb akan wannan rashin kwanciyar hankalin da yake fuskanta daga zuciyarsa dan in banda azalzalar sa ba abun da takeyi….
‘’Kawai ina buƙatar sanin fiye da sunanta ne,
daganan na san shikenan!
Ba wani abun da zai sake biyo baya kuma’’
Ya fad’a hakan a fili cike da son gasgatawa kansa iyakar
abunda yake buk’ata kenan.
Sai da Najeeb ya yi murmushi yana mamakin taurin kai irin na Yash,
dan ya san yau ɗin ma in ba da kyar ba akan Manubiya ne ya sake kiran sa….
Sai da ya girgiza kai, ya ce ‘’hmm’’
tukunna ya d’au wayar ya kara a kunnensa ya ce ’’Hello Yash,how far’’
‘’Kar ka ce komai kuma kar ka tambaye ni meyasa, kawai Ina da buk’atar sanin ƙarin bayanai akan wannan Yarinyar’’
Yashjub d’in ya fad’a yana mai runtse idanu, sannan ya yamutse fuskarsa kamar irin
‘Meyasa ma na tambaye sa’
d’innan.
Tabbas sai da Najeeb ya yi da gaske
tukunna ya samu ya danne dariyarsa sannan ya ce
‘’To a gaskiya Yash ni dai bana tara bayanai akan ɗalibaina..
Iyakar abunda na gaya maka jiya shi kad’ai na sani a game da ita.
Amma y not (mai zai hana) in karb’a maka numberta in yaso kaga sai ka binciketa ka ji komai da daga Bakinta?”