← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 84

Sashe 20

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da asubah ta tashi ta shirya musu breakfast, har lunch, ta cewa Muhsin “ya d’umama miyar idan an zo kaiwa” daganan ta wuce makaranta saboda tana so su yi karatu da Abbakar yau sosai, gashi lecture ɗin Sir Najeeb gare su da sassafe shiyasa take ta sauri saboda ta san baya bari a shiga muddin ya riga ya shiga.

Duk saurinta kuwa sai da ta yi
rashin sa’a, dan ta na karya kwanar inda k’ofar tafkeken hall d’in ya ke ta hangoshi yana shiga dan haka ta k’ara sauri amma dukda hakan kafin ma ta k’arasa bakin k’ofar har ya rufe.
Haka nan ita da ragowar d’aliban da suka yi letti suka ja suka tsaya a bakin k’ofar hall d’in dan waatak’ila idan sun ci sa’ar shi
In ya fito ya karb’a sunayen su da Matrc number ɗinsu ya raba musu ko da half half maki ne.

3 hours ne lecture d’in kuma Sir Najeeb d’an ƙa’ida ne shiyasa sai da ya cike 3 hours d’in sa tsaf tukunna ya fito.
Bai yi musu kamar yadda suka yi zato ba dan kamar ma ransa a b’ace yake lokacin da ya fito d’in dan ya had’e girar sama da ta k’asa fuskar nan tamau!!! Kamar bai tab’a dariya ba,
shiyasa kowa a wajen ya sha jinin Jikinsa.

Ko da wani a cikin su ya je yana k’ok’arin gaya masa uzurin sa
ma, a take ya daka masa tsawar da ta ƙarasa ruɗa su!
Dan haka duk sai suka ƙarasa rikicewa, kowa kuma ya jaa ya yi tsit suna ganin sa ya wuce ya tunkari parking lot.

Har ya nufi inda ya yi parking motarsa, sai kuma ya juyo, dan in dai ba gizo ta yi masa ba tou Yarinyar da yake nema ya hango a cikin dandazon ƴan letti.
Ya na juyawa kuwa su ka yi ido biyu shi da ita dan itanma bayansa ta raka da harara saboda ba kad’an ba ta ji haushin tsawar da ya dakawa wannan wanda ya zo zai ba sa uzuri, sosai.
Da sauri Manubiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tana adduar Allah ya sa bai fahimci hararar sa take yi ba.

‘’Manubiya Musa, follow me’’
Ya faɗa ba tare da ya damu ta ji ko bata ji ba, haka kawai ya sa Kai ya wuce ya shiga motarsa ya jaa ya nufi building d’in da office d’insa yake, a nan cikin BUK ɗin.
Bata ji d’in ba kuwa, ragowar Mutanen da suke wajen ne suka ce mata ‘’ya ce ta bi sa’’.
Dan haka hankalinta ya gama tashi a take saboda laifi a makaranta wanda zai janyo su Baba su sake yin fushi da ita is the last thing da take tunanin za ta yi involving kanta a ciki.’’

A take ta gama yanke shawarar tana zuwa zata durk’usa ta basa hak’uri sannan ta ce masa
Itafa haka Idanuwanta suke, ya yi hak’uri ba hararar sa take yi ba.

Tana shirin barin wajen Abbakar na fitowa daga cikin hall ɗin, kana ganinta ka san a rikice take, a haka ta k’arasa kusa da Abbakar ta ce
‘’Yauwa Abbakar, dan Allah zo mu je ka yi min shaida, ka cewa Sir Najeeb tun muna Yara haka Idanuna suke, ba harara ce na yi masa ba’’.

Kallon ta sosai Abbakar ya yi kafin ya ce
‘’Cewa ya yi ki bi shi?’’

Da sauri ta ce
‘’Eh, saboda ya kama ni Ina hararar sa’’.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Abbakar ya sauk’e kafin ya ce
‘’Inaa! Ba saboda harara ya ce ki je ba, Manu! yau ni da ke kashin mu ya bushe, ni ma ya ce min in biyo sa’’.

Za ta yi magana ya ce
‘’Mu je, mu je da sauri ke dai ki yi ta addu’a kawai’’.

..Da hanzari suka ƙarasa block ɗin da office ɗin Sir Najeeb yake, ba tare da b’ata lokaci ba suka kutsa kai cikin building d’in…
Manubiya ba ta san hanyar office d’in ba Abbakar ne ya yi musu jagora.
A corridorn
office d’insa ne na farko-farko dan haka suka k’arasa da hanzari, duk saurin da su ke yi sai da suka tsaya suka yi addu’a tukunna Abbakar ya d’aga Hannu da kyar ya fara knocking a hankali kamar wanda baya son yi…

Sun fi 5 minutes a bakin k’ofar office d’in idan Abbakar ya d’an buga sai ya tsaya ya ji ko za’a basu izinin shiga,
amma shiru.
Badaban sun ga motarsa ba
Kuma yanzu haka ma da su ke knocking ɗin kamar suna d’an jin murya k’asa-k’asa, to da sai su ce ba ya nan.

Sai da suka cire rai knuckles ɗin Abbakar har sun fara ciwo,
Tukunna suka ji ya ce
‘’Come in’’.

Abbakar ne ya ɗan murza handle d’in ya fara shiga da sallama, dan Manubiya sai da ta tsaya ta karanto addu’o’in da za su saka Zuciyarta ta yi sanyi tukunna ta bi bayansa ta shiga da sallama itama,
kanta a k’asa.

A hankali ta lumshe kyawawan Idanuwanta tana me shak’ar kamshin AC, room freshner da na zafafan designer turarurrukan su waenda su ka had’e waje guda suka bada wani zazzafan ƙamshi mai tsayawa a rai!.
Dama tunda suka shigo ta fahimci kamar ba shi kad’ai bane ba,
yanzun kuwa da suka sake bawa iska ajiyar su suka ci gaba da hirar su ya sanya ta tabbatar da
ba shi kad’ai d’in baneba
duk da kuwa har yanzu bata yarda ta kalli direction ɗin da table da kujerun da su ke zaune a kai yake ba…

sam ta rasa dalilin
da ya sanya ta tsinci kanta da samun faɗuwar gaba tun farkon shigowar ta cikin office ɗin.

Abbakar kuwa ganin computer har uku a kan table ɗin nasu
gashi daga gani da shi da Abokin nasa abu mai mahimmanci su ke tattaunawa, hakan ne
ya sanya ya ja Bakinsa ya yi shiru gudun kar ya katse su ya je ya yi laifi
Dan tun ɗazu a rikice ya ke!!!
Jiya dama tunda Mamansa ta ji ‘ya yi wa Manubiya test’
shikenan take ta faman surutai kuma ta tabbatar masa “muddin ya janyowa kansa kora daga makaranta to wallahi sai dai ya koma ƙauye ya yi noma ko kuma ya yi aure!!
Dan ba zai yiu ace ta yi ta kashe kud’i akan karatunsa tun yana k’ank’ani amma yanzu ya b’arar a banza ba, saboda wata Manubiya.
Sannan a yanzun da ya kamata ace ta ji dad’in karatun nasa shine yake so ya sake zame mata liability duk saboda wata Manubiya. To ba zai yiu ba.”
Gaba d’aya ta d’aga masa hankali ta dagawa kanta, dan tun jiya take fad’a masa tana sake nanatawa akan muddin aka gano su tou kamar ya gama shiga masifa ne a cikin makarantar……

Abbakar yana tsananin son karatu gashi ba k’aramar wahala ya sha ba kafin finally ya samu gurbi ya ci gaba da karatun nasa, shiyasa ta yi nasara wajen rikita sa da kalaman ta..

A hanakali Manubiya ta shiga bin office ɗin da kallo a ranta ta ce
‘’Aljannar duniya, ina ma za a bani aron nan in kawo Inna ko shekara d’aya ne ta yi ta huta sosai, a haɗa mata tare da abinci mai kyau sannan ba hayaniya,
Na san tabbas za ta rage wata damuwar.”

Ba abunda ya fi burge ta da office d’in irin yadda aka ware wajen Hutu daban wajen aiki daban…
Inda su ke zaune shi da Abokinsa ya yi kamar office, sai kuma chan gefe wasu lumtsuma-lumtsuman sofa ga fridge, dispenser, tv da center table, kamar dai wani parlourn amarya….

‘’You Guys Are Very Stupid,
GET OUT !!!!!’’
Suka ji muryar Sir Najeeb ya daka musu tsawa..

BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*11*

Tsananin rikici da tsoro ne suka sanya Abbakar durƙushewa a wajen, ya shiga ba shi haƙuri.

Manubiya kuwa takaici da baƙin ciki ne suka sanyata fashewa da kuka….
Tun farkon zuwan su dama da ya shanyasu a waje takaici ya isheta, daurewa kawai take yi!
Yanzu kuwa abun na shi ya kaita bango gaskiya.

….Haƙuri sosai Abbakar yake badawa amma sam ya ƙi ma ya tsaya ya saurare shi, tijara kawai ya ke zuba masa da ihu kamar wani ubansa, ba abun da ya fi sake ɓatawa Manubiya rai irin yadda ya sako iyayensu a lamarin
Ta inda ya ke cewa
‘’..in da mom d’insu ko Dad d’insu suka zo suka gani a wajen ai da za su gaishe su!
amma da yake shi sun raina shi shine suka zo suka tsaya musu kyam!! A Ka, ko shirin gaida su ma basu da shi, da yake ga sa’annin su sun tarar, ko ?.
To idan basu sani ba yau su sani
Malamanka suma kamar parents su ke a wajenka, in kuma suna da ja akan maganar tashi to su kama hanya su fita, shi kuma
ya basu c.o in fact har spill ma sai sun yi wallahi!!!!
Idan sun isa su je Iyayen su uwa ko uba wani a cikin su ya basu A a course d’in sa……..’’

Kukan da Manubiya ta sake fashewa da shi sai da ya sanya Hatta Sir Najeeb d’in yin shiru.

Idan wani ya zo wucewa ta bakin office ɗin ba abun da zai hana yayi tunanin dukan ta ake yi a cikin office d’in…
Duk tsura mata idanu suka yi suna kallon ta!
Banda Yashjub wanda tun lokacin da ta fara kukan in fact
tun farkon shigowar su ma haka nan ya daina fahimtar Najeeb, yanzun kuwa kukan nata gaba d’aya ya sake dagula masa lissafi,
bai ganta ba dan bai juya ba
sai dai kuma wani abun mamaki
Iya muryarta kad’ai da ya ji lokacin da ta yi sallama da kuma sautin kukan ta wanda a wannan lokacin yake ji har cikin ransa
ne ya sanya shi jin kamr ya tashi ya je kawai ya rarrashe ta.
Chapter 20 · 0% Book details