Sashe 40
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da asubah Manubiya ta tashi, tana idar da sallah ta yi karatun Qur’ani ta idar, daga nan ta d’auki handout d’inta ta hau karatu bayan ta je ta d’aura ruwa.
Sai da garin ya d’an yi haske tukunna ta mik’e ta je ta d’an d’ebi ruwan ta watsa ta barwa su Jidda nasu.
Tunda Baba ya fita sallah bai dawo ba har ta gama shirin ta,
ta san kuma dalilin da ya hana shi dawowar! Dan haka ta hau tunani tana lissafin ‘ko dai su hak’ura da zuwa office d’in mutumin nan ko kuma su je a k’afa idan za su iya in yaso d’an kud’in motar da suka tanada sai a siyawa inna kununta su Muhsin suma su ci abinci’
dan ta san shima Ya Musbah ba lallai a samu wani abun daga wajen sa ba.
K’arfe 7 dai-dai ta fita zuwa gidan Ammi tana addu’ar Allah yasa yau d’aya dai ta samu ko da
left over d’in jiya ne.
Kamar yadda ta yi expecting (zato) kuwa
sai da suka fafata ita da Ammi…dan jiya basu had’u ba wai ta tafi sunan k’anwarta tun sassafe so manubiyan bata samu ta tambaye ta akan fitar da za ta yi yau ba!!
Sai da Mama ta saka Baki yau ma tukunna Ammin ta barta akan nan da k’arfe goma za ta zo.
Abincin da ta yi tunanin samu kuwa san bata samo ba, haka nan ta dawo hankalinta a mugun tashe dan bata san mai za su ci ba.
Da ikon Allah tana shigowa
ta tarar Ya Musbah ya zo musu da koko Jidda har tana bawa inna nata..
ba k’aramin dad’i ta ji ba kuwa dan haka ta yi wa Allah godiya, itama ta karb’a ta sha nata daga nan Baba ya yi musu addu’a su Jidda suka yi musu a dawo lafiya, su kuma suka fito ita da Ya Musbah kowa a d’akin yana musu fatan alkhairi.
Lokacin karfe 7:36.
A hanyar bakin k’ofa suka tarar da ya Yusuf yana tsaye yana daddana waya sanye cikin suite.
da murmushi Ya Musbah ya k’arasa ya mik’a masa Hannu yana mai cewa
‘’Yusuf ina ta so in lek’a in yi maka murna…
Na ji Baba yana cewa ya ji Kaka mallan a masallaci yana gayawa Abokinsa ka samu aiki a banki ko?
Allah ya sanya alkhairi’’
Ya k’arashe maganar tasa da tsananin murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarsa.
Ko kallon sa Ya Yusuf bai yi ba ballantana ya yi tunanin zai bashi Hannu su gaisa!
A hankali Ya Musbah ya janye hannunsa kafin cikin rashin kuzari ya sake cewa “Allah ya sanya alkhairi.’’
Yanzun ma bai ko kalle sa ba sai wayarsaa da ya ci gaba da dannawa.
Juyawa Ya Musbah ya yi, ya kalli Manubiya wadda ta k’ule ta zo iya wuya, ya ce mata ‘’Manu,mu je’’daga nan ya sa kai ya fice daga gidan jikinsa a mugun sanyaye.
Manubiya har zata fita itama
sai kuma ta juya ta kalli Yusuf d’in dai dai shima ya d’ago yana kallon ta, a hankali k’asa-k’asa ta ce’’Jidda ce dai,ba za mu bayar ba!
dan Allah in kaga dama ka zama sarkin gaba.’’
Tana gama fad’in haka ta fice da sauri tana mai jin takaicin yana d’an raguwa.
…..
Ƙarfe 7:56am
Adaidaita sahun su ta yi
parking a bakin ‘Yashjub Limited’.
Sunayen su kawai masu gadin suka tambaya, Manubiya tana fad’ar sunanta suka shiga yi musu sannu da zuwa, suka bud’e musu k’aramar k’ofa su kuma suka shiga.
A reception suka zauna bayan sun je sun fad’i sunayen su an ce ‘su d’an jira.’
Cikin nutsuwa Ya Musbah yake kallon gurin yana adduar ‘Ina ma ace ya samu aiki a gurin, ko da masinja ne, in dai zai samu abun da zai ciyar da Inna da Baba da y’an uwansa da kuma Baraka da d’ansa to Alhamdulilla…’
aikin gini da wanki da gugan nan da ya ke yi ba k’aramin wahala yake sha ba sannan ogannin nasa basa biyan sa sosai, ga shi kullum a gajiye ya ke!!!,
Baraka har ta fara yi masa mitar baya sauk’e mata hakkinta na aure wanda yake a kansa saboda kullum yana zuwa gida ya ke bajewa sai barci, tsabar gajiya.
A nan kam ya san ba zai dinga yin gajiyar da yake yi a wankau ba, ga gurin ko Ina AC….
‘’Ya Musbah dan Allah ka daina kula Ya Yusuf, tunda bashi da mutunci.’’
Muryar Manubiya ta katse masa tunani, murmushi kawai ya yi kafin ya kalle ta tukunna yace’’Manu,idan na biye masa ai sai zumuncin namu ya fi yanzu lalacewa…’’
‘’Miss Manubiya, pls follow me(taso mu je).’’
Wata baturiya cikin suite da skirt ta ce da su kafin ta
juya ta nufi hanyar sama.
A tare suka mik’e ita da Ya Musbah suka bi bayan matar….
a bakin lift matar ta tsaya,
sai da ta juya ta tabbatar suna bayan ta tukunna ta danna lifter ya bud’u sannan ta shige ta kallesu ta ce ’’come in,pls(ku shigo)’’
A hankali suka shiga k’irjin Manubiya yana dukan uku-uku,dan bata tab’a shiga ba, ta dai san menene amma bata tab’a shiga ba.
4th floor dama Matar ta danna wanda shine last floor dan haka suna isa lift d’in ya tsaya k’ofar ta bud’u matar ta fice suma suka bi ta a baya.
Sai da numfashi su ya kusan d’aukewa saboda tsananin had’uwa da kyawun wajen, ko ina glass! dan kana iya hango har chan waje har titi, ga wasu fitilu da suka haska wajen suka sanya yayi wani irin haske tarr….
Hijabin idi ɗinta na last year ne a jikinta brown colour,
a wanke tass a goge har k’asa, sai shek’i yake yi, dan tun sallar da ta saka bata sake sakawa ba!
Ya Musbah shi kuma yana sanye da jallabiya bak’a da hula fara (tashi ka fiye naci)….
kayan Jikin duk su biyun a goge suna shek’i amma duk da haka sai suka raina kansu saboda had’uwar wajen da kyawun shi
sai ya fito da rashin kyau da tsadar kayan nasu.
Apart from wannan baturiyar da take yi musu jagora basu ga kowa a wajen ba, a k’asa ma kwata-kwata mutum shida suka gani daga receptionists sai wani a cikin suite sai masu gadi da cleaner, da alama dai company d’in bayan kasancewar sa private to mai company d’in ma baya buk’atar mutane da hayaniya tunda gashi itama ce mata aka yi dama ’sau d’aya za ta dinga zuwa a sati’.
Suna tafe ita da Ya Musbah suna bin bayan wannan baturiyar kowa da abunda yake aiyyanawa a ransa…
wani dogon corridor suka bi kafin su k’arasa wani babban guri tsakiyarsa na ɗauke da wani abu kamar round about cikinsa duk flowers masu asalin kyau da ƙamshi..
A ta chan gefen hagu suka hango wani waje kamar d’an k’aramin parlour mai d’auke da wasu d’urma d’urman sofa, 3seaters guda uku, masu tsananin kyau da d’aukar hankali sai center table a tsakiyar su da fridge da dispenser a gefe da gefen su.
Yayin da tsakiyar wajen ke d’auke da wani makeken roundabout wanda aka cika sa da shuke shuken flowers masu tsananin kyau da kamshi, sai kuma wuta kamar na pop yana ratsowa ta k’asan flowers d’in yana k’arawa shuke-shuken asalin kyau da d’aukar hankali…
Manubiya bata gama tunanin ta ya ake bawa flowers d’in ruwa ba ta ji baturiyar ta ce
mata “this way miss(nan za mu yi’’
Kafin ta kalli Ya Musbah ta ce masa
‘’U can wait,right there(ka ɗan jira ta, a chan).’’
Ta fad’i hakan tana mai nuna masa wannan d’an mini parlour d’in da yake ata chan gefen hagu.
Kwata-Kwata k’ofofi uku ne a wajen na glass,biyu suna kallon juna d’aya kuma yana opposite wannan mini parlourn da aka ce ya Musbah ya zauna
duk da roundabout d’in flowers d’in da yake a tsakiyar su tsaf kake iya hango komai da ya ke a ciikin dukkan wajajen.
Biyun da suke facing juna, a d’ayan kana iya hango tebura
da chairs d’insu da computer a kan ko wanne tebur, yayinda wanda yake kallon sa kuma yake d’auke da k’atoton tebur (dogo) da kujeru wajen sama da arba’in zagaye da shi, sai doguwar micro a gaban ko wacce kujera a ajjiye kan tebur d’in sai projector d’insu da suka bari a kunne.
Sai last one d’in wanda yake kallon mini parlourn, a saman shi an rubuta C.E.O, kana iya hango normal tebur sai kujeru biyu a gaban tebur d’in da kuma d’aya tana kallon biyun
sai parlour mai kyau a gefe da kuma wani mutum sanye cikin white suite dogo k’ak’k’arfa giant ya juya baya yana kallon waje da waya a kare a kunnensa….
…
Da farko Ya Musbah ya so ya yi musu da aka ce kar ya shiga, sai kuma yaga ai yana iya hango komai na cikin inda aka ce Manubiyan ta shiga dan haka ya je ya nemi waje ya zauna, yana kallon su har wannan baturiyar ta shiga Manubiya ta bi bayanta suka mayar da k’ofar suka rufe ….
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*25*
Tun lokacin da suka shigo cikin company d’in ya gan su ta cctv, kuma ya fahimci ita ce dan ba shi da appointment da kowa yau sai ita…
Babban abunda ya d’aga masa hankali shine Ya Musbah, ba ya ganin fuskokin su sosai shiyasa bai fahimci fusgen kamannin da suke yi ba dan shi a tunanin sa ma Abbakar ne tunda tare ya gansu the other day(a wachchar ranar).
a ran sa ya ce ‘’to ko dai saurayin ta ne da gaske’’
A take wata zuciyar tace masa’’to idan ma saurayin nata ne ina ruwan ka, kai naka ba kawai ka san more about her ba(santa bane ba)..’’
Yadda yake jin zuciyarsa tana tafarfasa ne ya sanya ya kasa jurewa, ya rufe computer, ya mik’e ya bar gaban tebur d’in nasa ya isa jikin glass ya juya baya yana mai kallon waje.
A haka secretary d’in tasa ta shigo ta same shi ta ce masa ‘Ga Manubiya ta zo’.
Yana bata izinin ta je ta shigo da ita ya zaro waya ya hau kiran Najeeb dan ji yake yi kamar ya sanya security su fitar da wanda yake tunanin Abbakar ne….
yana so ya san alak’ar ta da shi kafin ma su shigo masa office..