← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 84

Sashe 5

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na kwance akan makeken gadon da ke a cikin ɗakin
sanye cikin wasu matsatstsun riga da wando, Rigar ko cibiyar ta bata gama rufewa ba…
Fara ce ita ɗin tass dan hasken fatarta kalar na turawa ne ma!!
Ba za a kirata da kyakkyawa ba
ba kuma mummuna bace ba, tana da doguwar fuska, madaidaitan Idanuwa dogon hanci da matsakaicin Baki! Gashin kanta shima a cike ya ke taf ga kuma tsayi dan har ya kusan kaiwa tsakiyar gadon bayanta. Doguwa ce sosai sannan siririya ce ta gaske.
‘’KAUSAR!!!!’’
Ɗaya daga cikin ƴan Matan ta kira sunanta….
A hankali ta lumshe idanuwanta ta buɗe su
kafin cikin asalin jan aji da yauƙi ta miƙe ta zauna a kan gadon.

Sun san halinta da yauƙi dama ga kuma rashin son takura, dan haka kowacce sai ta ja Bakinta ta yi shiru, ba su sake tanka ta ba.

Ta fi mintuna biyar ta na ta yamutse fuska kafin ta miƙe kawai ta faɗa toilet…..

Ta jima sosai a cikin banɗakin
tukunna ta fito.

Kallon gadon ta yi sakamokon ƙarar da ta ji wayoyinta waenda ta bari a kan gadon, su na yi .
Ko kallon wayoyin bata sake yi ba, ta nufi ledar da ta hanga wadda ke a nan gaban dressing mirrow tun ɗazu, tana zuwa ta zaro wata 3 quarter gown black! Ta jefar da ledar a ƙasa tare da ragowar abubuwan ciki.

Ba abinda ta shafawa fuskarta sai jan jambaki daga nan ta zura gown ɗin ta feshe turarurruka, ta saki gashin ta wanda ta ɗaure gudun kar ruwa ya jiƙa mata shi garin yin wanka.

Bata kalli kowa a cikin ƴan Matan da suke nan a shirye tun ɗazu suna ta jiran ta ba…
Wayarta guda ɗaya kawai ɗauka daga haka ta kama hanyar fita…
Suna ganin hakan su ka mara mata baya duk su ka fice kusan a tare….
….
Suna sauƙa ƙasan wajen ya karaɗe da ihu, masu cewa “happy birthday Kausar” ma, su na yi.
Murmushi kawai ta yi ta shiga hugging friends ɗin nasu waenda suka taru ana gaisuwar yaushe gamo…
Anayi su na bata gifts ita kuma tana miƙawa friends ɗinta da suka sakƙo tare.
…
Tunda ta saƙƙo su ka haɗa ido da shi amman sai ta ɗauke kai ta yi kamar ma bata ganshi ba, bata ma yarda ta sake kallon inda ya ke zaune shi da Abokanayen sa su biyu, ba.

Direct inda babban cake ɗinta ya ke nan ta nufa ta je ta yi cutting daganan ta yi wa kowa godiya
tare da basu uzurin ‘ta na da
important interview’
Daga haka ta yi excusing kanta ta juya ta nufi sama inda ta fito….
Party kuma ya ci gaba da gudana.

Wata mahaukaciyar Dariya ɗaya daga cikin Abokansa ya kece da ita kafin ya ce
‘’Tunda nake a rayuwata ba a taɓa
yin disgin da ya bani tausayi da dariya at the same time kalar wannan ba.”

Kallon shi ɗayan Abokin nasu ya yi kafin ya ce
“Dude!”.
Yana ɗan yi masa alamun ya yi shiru mana sannan ya nuna masa YASSIR ɗin da ido wanda ke nan zaune a tsakiyansu su biyu….
Tun lokacin da Ƙausar ta sauƙƙo ya ɗauke wuta, ta saba wulaƙanta shi dama kwana biyun nan amman tunda su ke bata taɓa yi mishi abun da ya ji haushinsa kalar wannan ba…

Dukkan Mutanen da su ke a wajen shi ya kwaso su wasu daga Nigeria wasu daga ƙasar da su ke
duk shi ya yi musu kuɗin jirgi saboda yana so ta ga friends ɗinsu na school tare a waje ɗaya ranar birthday ɗinta, a wajen da soyayyarsu shi da ita ta soma wajenda ta soma yarda dashi wato ‘Aucland’ wajen da ya san nan ne favorite wajen da ta fi so…
Amma its like ba ta yi farin ciki da surprise ɗin nasa ko kaɗan ba.
“Wats wrong with Ƙausar ne wai kwana biyu?”
Ya yi wa kanshi tambayar a cikin Zuciyarsa, ranshi yana ƙarasa dagulewa.

A hankali ɗayan Abokin nasu ya ce “Yassir, Magana ta gaskiya…
Yarinyar nan abun nata ya fara yin yawa..You are better than this, haba mana!
Pls move on, ga girls nan kala-kala amma ka nace kai sai wadda….”

Kallon da ya ga Yassir ɗin ya ɗago ya na yi masa ne ya sanya shi kasa cigaba da maganar tashi..kafin a hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi sai kuma ya juya ya bar wajen ma gaba ɗaya,
dan tabbbas yadda ya ga Idanuwan Yassir ɗin sun kaɗa sun yi jaaaa! To fa tsaf zai iya juye
haushin sa a kan shi.
Shi kanshi ɗayan Abokin nasu da ya ke ta yi mishi dariyar shaƙiyanci shiru ya yi ya kauda kai bai sake yunƙurin cewa komai ba…..

Ya jima a wajen kafin ya miƙe ya nufi sama inda Kausar ɗin take.
Yana ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin da ta ke ciki ya hango ta zaune gaban madubi ta sunkuyar da kanta sosai, kamar ma kuka ne ta ke yi…
A hankali ya ja ya tsaya a bakin ƙofar ya shiga ƙoƙarin fahimtar yanayin ta daga nan inda yake tsaye “leƙe, ba halin kwarai bane, musamman a Macen da ta keɓance kanta ta ke buƙatar space ɗinta ita kaɗai!!’’.
Ya ji muryarta cikin yanayin kuka.

Numfashi ya fesar kafin ya kutsa Kai ya ƙarasa cikin ɗakin!
Idanuwanshi a kanta, duk tsananin ɓacin ran da ya ke ciki sai ya ji yana ta raguwa a hankali a hankali…..

A gefenta ya je ya tsugunna kafin ya miƙa Hannu ya kamo nata…
Bata kula shi ba sannan bata hana shi ba, tana jin shi ya shiga murza tafin Hannun nata,
a hankali cikin kwantar da murya ya ce
‘’Kausar abinda ki ka yi mini yau banji daɗinsa ba!
Na haɗa wannan abun ne fa domin ke kawai, ga friends ɗinmu wasu na tabbatar rabon ki da su tun a Makaranta, na kawoki inda na san ki na so na haɗa miki duk abubuwan dana san ki na so amman yadda ki ka nuna kamar irin ba ki gode ɗinnan ba, kamar ma na kwaso kashi ne na zo na yaɓa miki a Jikinki!
Ko arziƙin kallo fa ban samu daga gare ki ba, ballantana in ji yadda ki ka ji daɗin surprise ɗin. Sannan na sanar miki tare za mu yanka cake amma ba ma ki tsaya kin jira ni ba, kawai ki ka je ki ka yanka ke kaɗai.
Idan wani abun na yi miki dan Allah mu yi maganar in baki haƙuri a wuce wajen dan wannan abubuwan da ki ke min barazana ne ga relationship ɗinmu, ba kya helping kwata-kwata sai ma ƙoƙarin lalatawa da ki ke yi.
Ni kaɗai na ke ta faɗi tashin ganin mun gina alaƙar nan tama, Ƙausar ina ƙoƙari fa duk domin ki….
Ko iyaka wannan birthday ɗin
da na haɗa miki kawai don in ga farin cikin ki shin kin san nawa na kashe kuwa?”

Duk maganganun da ya ke ta yi sai da ya kai nan tukunna ta fesar da Numfashi sannan ba tare da ta kalle shi ba ta miƙe ta ɗan ja hannuta wanda ke a cikin na shi da ɗan ƙarfi, ta bar wajen cikin takun ta mai jan hankali ta nufi bed.
Jakarta kawai ta ɗauko ta zaro check ta fara neman biro.

Tunda ta fara rubutun ya fahimci me ta ke shirin yi dan haka ya miƙe shima ya ƙarasa da hanzari ya wafce takardar
dai-dai nan ita kuma ta gama rubuta mishi kuɗin.

Cikin ɓacin rai ya kalli takardar sannan ya maida dubanshi gareta ya ce
‘’Cewa na yi ki biyani???’’

A hankali ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Nop! Amma Ina buƙatar space dan haka zan yi ko ma menen domin in ga na samu, dan haka ko biyanka ɗinne ma sai in yi in dai zan samu ka daina yi mini wannan jarababban nacin naka”.
Cikin takaici ta ɗaura da cewa
‘’Kuka fa ka shigo ka ga Ina yi Yassir, amman kawai kai ta matsalar ka ke yi, kanka kawai ka sani, har ga Allah ka takura ni dayawa, ina jin matsi sosai a duk lokacin da na ke tare da kai.’’

Ɗan zaro idanu ya yi, har zai yi mata magana da ƙarfi!
Sai kuma ya runtse Idanun nasa da tafin hannunshi da ƙarfi!!!…
Ya ɗan jima a haka kafin
ya buɗe Idanun ya ɗan sake matsawa inda ta ke
tukunna a hankali cikin tsananin mutuwar jiki ya ce “Kausar, ni ne na ke nacin, ni na takuraki kuma yau??”

Shirun da ya ga ta yi ta kauda Kai ne ya sanya shi sake matsawa sosai gareta a hankali ya ce
‘’har yanzu, akan abunda ya farun nan ne ki ke jin haushi na, ko?”

Sai a sannan ta ɗaago Idanuwanta ta kalleshi, a hankali itama ta ce
‘’Yassir bana son yawan magana ayanzu amman sai surutu ka ke ta sakawa Ina yi..
Bari ka ji, idan ka ga dama ka je ka nemi duk ƴan matan duniyar nan, na faɗa maka ba damuwa ta bane ba!
Sannan in dai cikinka zai iya ɗauka to dan Allah ka je ka juye masa dukkan nin giyar da ke a cikin duniyar nan shima duk ba matsalata bace ba, iyaka abunda na ke so daga gareka shi ne “space!!”
Don Allah Yassir ka ɗan ƙyaleni na wani ɗan lokaci, ba na son takura”.

Ta na gama faɗin haka
ta juya ta shige toilet da sauri
ganin ya na shirin ruƙota.
Chapter 5 · 0% Book details