Sashe 80
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
‘’Wanne tunanin nata ne ya fita akan hanya?
And what
exactly happen in here(sannan me ya faru a nan haka?)”
Yassir wanda shigowar sa kenan ya fad’i hakan yana bin parlourn da kallo.
A hankali Kausar ta ce
‘’ba komai’’
Sai kuma ta juya da sauri ta wuce d’akinta ta rufe k’ofar.
Ya jima yana kallon k’ofar d’akin nata kafin ya furzar da iska ya k’araso ciki inda Yassira take ya tsaya yana kallon ta.
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce ’’na yi tunanin ka na office, na ji Daddy ya ce ka samu contract, me ka ke yi a gida??’’
‘’Yasira yau fa Sunday, tun jiya ma kuma na gama abubuwan da na san su ne masu mahimmancin, yau kuma
P.A d’ina yana chan.
Inada buƙatar hutu kuma na san zai yi handling (yin ) komai’’
Yassir ya faiyyace mata hakan kansa tsaye.
Cikin rashin jin dad’i Yasira ta ce ’’Yassir wannan dalilin fa ya sanya Daddy ya fi bawa Yashjub jari, saboda ya san ko an baka asara ne. Saboda Allah kalli yadda ka tarwatsa company d’inka in banda ci baya ba abunda yake yi kullum!!!
Sannan ka d’an samu contract da kyar amma dubi yadda kake wasa da damarka?…
Ka yi haƙuri da abunda zan gaya maka kai tsaye kuma a gaban idonka
Amma Yassir kana da matuƙar son jiki da kasala…’’
‘’Am, Yassira! Me ya faru da Kausar??
Me kuke tattaunawa kafin na shigo?’’
Yayi mata tambayar yana mai gyara tsayuwar shi.
Fusata Yassira ta yi, ganin
yadda k’iri-k’iri ya gwale ta,
ya ma k’i sauraron ta…
dama ga takaicin Manubiya da Kausar shiyasa cikin fushi
ta ce ’’in ka matsu ka shiga ciki ka je ka tambayeta da kanka.”
Daga haka ta bangaje shi ta fice.
Ta nufi d’akin Mommy da
niyyar jiranta ta dawo daga d’akin Daddy su yi magana
amman sai ta ganta a d’akin nata a zaune ta zabga uban tagumi.
Ta d’an yi mamaki amma sai ta kawar kawai ta ce
‘’Mommy, sai kin bud’ewa Kausar ido fa!
Ina tsoron kar ta je ta yi wani shirmen, ganin
wannan Yarinyar nan da ta yi ya haukatata!!…
Ni kaina na tsorata Mommy
dan in dai wannan ce Yarinyar da ya ke so zai aura to gaskiya ba na jin
za mu iya kai labari…..
Sannan ga dukkan alamu yana tsananin santa! Dan na manta rabon da in ji Yash yana bada hak’uri amma ita in kinga yadda yake rarrashinta wallahi
sai kin yi mamaki…
Dan haka in dai har muka bari ta
shigo gidan nan
To a idanunsa da mu da kashi duk d’aya!
Dan na san ita kawai zai dinga gani….
Shiyasa ya zame mana dole mu yi wani abun amma kafin nan ya kamata ki tsawatarwa Kausar, kwata kwata wannan
shirmen nata ba shine mafi dacewar mafita ba…’’
*MANNUBIYA*
*47*
A hankali Mommy ta ce
‘’InshaaAllah zan yi mata magana,
amman Yassira ban ji dad’in yadda kika yi mata magana ba yau sam, kalaman da ki ka yi mata amfani da su sun yi tsauri da yawa’’.
Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e kafin ta nemi guri ta zauna a gefen Mommyn, ta ce
‘’zan bata hak’uri Mommy, amma
ya kamata mu fara nuna mata kuskurenta tukunna. I love her ne shiyasa kika ga na yi mata hakan.
Kinga na farko abunda take shirin yi bai kamata ba
Abu na biyu kuma Mommy ni kad’ai na san abunda na gani a kwayar Idanun Yash game da Yarinyar nan, idan Kausar ta yi gigin raba ta da duniya
wallahi ba ita ba bincike in ya biyo har ta kanmu sai mun ga tashin hankali dan kashinmu ya bushe har ke kanki kuma mu da shi har abada.
A ganina
gwara ya tsaneta da kansa cikin sauk’i, tsana ta har abada. Akan ya tsanemu tsana ta har abada saboda ita.’’
Dafe Kai Mommy ta yi tukunna ta ce ’’Kausar ba za ta yi komai ba inshaaAllah, Yash kuma na ce muku ku barni da shi,
da shi da yarinyar duk ku bar ni da su.
Yanzu ki je abunki, ina buk’atar hutu sosai, ki koma office kin ce ana jiranki.”
Shiruu Yasira ta yi tana jin wani kalar tausayin mahaifiyar tasu yana mamayeta!
Saboda Allah
ace wai d’anka ba ya kulaka,
zai yi aure bama ka saniba sai y’ar kishiyarka ya gayamawa.
Sannan yanzu ga Kausar ta sake d’aga mata hankali….shiyasa dole ta shiga damuwa….
Har Yasirar ta mik’e za ta fita sai
kuma ta koma ta rungume Mommyn, sun jima a haka tukunna ta cika ta ahankali ta ce ‘’komai zai gyaru Mommy, inshaaAllah’’
A hankali Mommyn ta ce
‘’Na gode Yassira, Allah ya miki albarka’’
Murmushi
Yassirar ta yi
tukunna ta cikata ta ce ’’ameen,sai na dawo’’ daga haka ta fita
A ranta tana adduar ‘Allah ya kawo ranar da Mommy Yash Daddy za su had’a Kai su so
juna su k’aunaci juna komai ya dawo dai-dai Family ya gyaru ya yi dad’i……’
A b’angaren Yassir kuwa,
Yassira tana fita ya k’arasa k’ofar d’akin Kausar da niyyar shiga amman sai ya ji ta a rufe,
dan haka ya sake tabbatarwa
kansa
‘Tabbas akwai abunda Kausar take b’oyewa’
Amma kuwa in ta yi masa haka to ta yi mugun janyowa kanta bala’i da masifa….
Bai bar bakin k’ofar ba sai da
ya gama tsara abunda zai yi
‘Zai jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya’
Tsuntsun farko…zai kawo k’arshen matsalarsa.
Tsuntsu na biyu kuma…zai fallasa masa Kausar…zai gano abunda take b’oyewa, dan ya san in dai har da gaske Kausar son Yashjub take yi kamar yadda ya ke zargi
to
Idan ta ji labarin mutuwar Yashjub ɗin sai ta yi haukan da zai fallasa ta b’aro-b’aro.
Ta hakan ne zai gane gaskiya,
a daina wasa da hankalinsa kamar wani wawa!
Daga nan kuma ya ci ubanta na wasa da hankalinsa ɗin da ta yi
sannan ya aureta
ba yadda ta iya……
Ko gida Manubiya ba ta kai ga k’arasawa ba Yahanasu ta kira ta…Tashi d’aya kuwa ta ji Yahanasun ta kwanta mata a rai, itama Yahanasu nutsuwa da hankalin Manubiya yasa ta ji ta k’ara sonta…
sun d’an tab’a hira daganan ta taya d’an uwanta campaign kafin suka yi wa juna sallama.
A k’ofar gidan nasu aka ajjiye ta, kamar had’in Baki! Mai adaidaita sahun yana wucewa tana shirin shiga gida ta ji an kira sunanta dan haka ta juya.
Murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta sakamokon had’a idanu da suka yi da Mama.
Sai da ta gaida ita ta amsa tukunna Maman ta ce ’’ki yi hak’uri nima kwana biyun nan ban ji dad’i ba shiyasa ban samu na shigo na duba innar taku ba.”
Murmushi Manubiya ta yi, tana mai jin k’aunar Matar tana ratsata a lokaci guda kuma tana mamakin tsananin kamanninta da Yashjub kafin cikin kwantar da murya ta ce
‘’Allah sarki! Allah ya baku lafiya gaba d’aya…
Innar ma na san bata nan, dan ba lalle sun dawo ba amman mu shiga dai mu duba’’
Daga haka suka wuce tare bayan Mama ta ce ‘’ameen’’
Sai da ta yi sallama ta shiga tukunna Maama ta bi bayanta itama ta shiga Bakinta d’auke da sallama.
Da ikon Allah kuwa har sun dawo dan ‘a cikin wata na’ura
kawai aka saka Innar aka fitar’
amman Dr Sofia ta ce ‘’ta mayar da pt d’in sau biyu a rana sannan su kwantar da hankalinsu dan babu wata matsala saboda abun nata ma ashe minor ne dan haka su tsammaci warkewarta a ko wanne lokaci muddin aka bata kulawar da ta kamata.’’
Manubiya ta yi mamakin yadda ta gansu a zaune gaba d’ayan su sun yi jugum har Ya Nafi’u, bata gama nazartar su ba aka fara gaisawa da Mama
wadda hankalinta ya tashi matuk’a daga ganin jikin Inna dan sam ba ta yi tunanin jikin nata ya yi tsanani har haka ba.
Itama ba wani k’arfi ne da ita ba balle ta taimaka musu, dan ta lura lamarin na Inna har da d’an rashi da babu.
Cikin rashin jin dad’in ganin Innar a haka ta ce ’’akwai baba mai gadi na gidan ammi, malamin tsangaya ne kafin ya dawo gadin ya barwa ya’yansa, zan ce masa ya dinga yi wa inna rubutu duk jumaah sai Musbah ya dinga karb’a mata tana anfani da shi, sadak’a saboda Allah’’
Sun ji dad’i kuwa sosai haka nan suka yi mata godiya tanata cewa ‘kar su damu ai ba komai’
daga nan suka d’an tab’a maganganu
kafin daga bisani ta yi musu sallama ta tafi.
Manu ce ta rakata har k’ofar gate na gidan Ammi, daganan ta juyo ta komo.
Tana shiga d’akin ta gansu sun koma jigum d’insu kowa kana ganinsa ka san yana cikin damuwa.
Dan haka ta shiga tambayar su ‘’me ya faru?”.
Ya Nafi’u ne ya iya bata amsa ta inda yake cewa ‘kiran da Kaka Mallan ya yiwa Baba d’azu, akan wai su Baba Habu sun kai k’arar ku ne game da dukan da kuka yi wa Yusuf…wanda duba da hakan yanzu sun yanke shawarar
Uncle zai siye nan d’akin da band’akin da d’an filin baya wanda yake mallakin ku, sai ku tashi a gidan’’
Cikin fushi
Manubiya ta ce ’’ashe kuwa da sun tabbata mahaukata, mu bamu yi magana akan abunda shi Yusuf d’in ya yi ba
sai shi me uba ??’’
Ciki fushi Baba ya ce
‘’Manubiya bana son shirme fa…
Tun farko ai kamata ya yi ace da kuka zargi ya yi wani abun ku tuntub’eni ku ji asalin bayani ba wai ku rufe shi da duka sai ka ce wasu taɓaɓɓu ba!
Yusuf d’in d’anku ne da za ku d’aga Hannu ku dakeshi??
Baya ga haka ma ai sai da na gayawa Musbahu k……’’
Cikin fad’a fad’a ya juya ya kalli Ya Musbah ya ce
‘’Lokacin da ka zo ka same su ba ka gaya musu taimakon da Yusuf d’in ya yi min ba??
shine ka biye musu kuka dake shi??.
Har yau yana asibiti
kuma Baba Habu ya ce duk mu za mu biya kud’in jinyar sa.’’