← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 84

Sashe 55

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin su k’arasa gida har sun shirya kamar basu tab’a yin fad’a ba.
Manubiya ta lura da waensu ƴan change-change daga Abbakar tun ba ma da ta ba sa labarinta da Yashjub na yau ba!
dan tashi d’aya ta ga
gaba d’aya hankalinshi ya tashi kuma ransa ya b’aci, saboda sam ya kasa danne kansa wannan karon…

ta so ta tambaye shi sai kuma kawai ta kawar ta basar da zancen ta sako wata hirar..

Da kyar Abbakar ya dinga yak’e har suka isa gida, ya yi mata sallama tare da fatan hutu mai albarka daga nan
ya wuce gida shima.

Dakyar ya iya k’arasawa ya tsaya ya gaisa da mamansa wadda take zaune a tsakar gida daganan ya koma d’akinshi da ke a soro, yana shiga ya tura k’ofa ya sak’ala sakata tukunna ya saki zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa tun a makaranta…

bai yi tunanin ba zai iya hak’ura da Manubiya ba sai yanzu, tsananin k’aunar da yakeyi mata ne yasanya ya hak’ura yayi saurin had’a ta da Yash.

A ganin sa da lissafin sa…
na farko Manubiya ta fi k’arfin sa!
sannan kusan age mates suke (shekarunsu ɗaya) shi da ita dan ko kwak’kwaran watanni biyu bai bata ba,
sannan a kalar matsin rayuwa da wahalar da Manubiya ta sha ya kamata ace ta auri mai arzik’i ta yadda zata kula da kanta da ahalinta itama ta samu ta huta ta ji dad’in rayuwa,
Waennan dalilai su suka sanya ya hak’ura da ita domin ta samu ta ji daɗin rayuwa kuma ya yi saurin had’ata da Yash dan a tunaninsa zai iya saka farin cikinta a saman nashi kuma ya zauna ƙalau sannan yana zaton idan ya had’a ta da wani ya ga tana farin ciki tou zai hak’ura ya samu zuciyarsa ta samu salama
sai dai kuma a tashi d’aya a iya yau kad’ai ya fahimci abun ba haka yake ba!!
kuma ya fahimci ya tafka babban kuskuren da in dai bai gyara ba to shine ajalin sa….

Tunda gashi tun yanzu ya fara shiga tashin hankali Ina kuma ga in soyayya ta yi nisa tsakanin ta da Yash….?..
…
Ya yi kuka ranar kamar ransa zai fita, kafin daga baya ya yi shiru ya shiga duniyar tunanin nemawa kansa mafita
dan tabbas da sake…..

*MANNUBIYA*
*33*

Manubiya Tana shiga gida ta d’auki kud’in da Baba ya bata na Ammi ta nufi gidan, dan bata samu ta tsaya sun yi magana ba d’azun.

Tana shiga ta tarar da aiki birjik!!
Ammi ta hana d’ayar mai aikin nata tab’awa, dan hadda natan ma tace duk ta haɗa ta barwa Manubiya yau duk ita za ta yi ..
Wai punishment d’in lettin da ta yi kenan..
haka nan suka zauna babu wanda ya had’a tsinke da tsinke a cikinsu, ana jiran Manubiya ta zo ta yi, dan Ammi ta fusata yau da lettin da Manubiyan ta yi ba da wasa ba, hakan ha sanya ko da Maama ma ta saka Baki wannan karon Ammi ba ta saurare ta ba dan haka itama maman sai ta kyaleta dan ta lura yau matar tijara take ji.

Ba k’aramin tashi hankalin Ammi ya yi ba, da ta ji wai su Manubiya za su bar aiki…..
babu damar ta ce bata yarda ba tunda dai ga kud’in ta an riga an bata..
dan haka ta shiga gaggaya mata maganganu, ta hakan ne ta samu ta d’an rage takaici kuma tace sai ta yi aikin yau!!

Manubiya so take su rabu lafiya dan haka ta yi aikin ta gama tsaf ta je ta yi mata sallama…
Bak’in ciki a gun Ammi kamar ta d’aura Hannu aka ta yi ta kurma uban ihu.

Har k’ofa maama ta rakota, matar ta ji dad’in aikin da Manubiyan ta bari saboda ta lura Ammi so take ta wahalar da yarinyar dan ko Muhsin k’iri k’iri ta hana sa shigar mata cikin gida idan ya zo ko Manubiya baya samu ya gani dan iyakar sa tsakar gidan, yayi shara ya tafi,a cewarta ba ta so namiji ya shigar mata cikin parlour da kitchen ba…….
•••••
Zuwa yanzu Yassir ya warke garau, dan har ya koma office ma.
Ba k’aramin tashi hankalin Mommy ya yi ba ganin yadda
Yassir ya k’ulla gaba da Yashjub!
gashi Daddy ya ƙi ya sa Baki….

Ita ta rasa wanne irin dak’ik’in Yaro ne Yassir wanda ba a isa a gaya masa ya ji ba,

sam ya k’i yarda da ita akan ‘ya hak’ura ya kula d’an uwansa..’

ta san muddin Yashjub ya tsame Yassir a lamarin shi Wallahi in ba da kyar ba
sun rabu kenan har abada.

Gashi yanzu ita kanta Yashjub d’in fushi ya d’auki yi da ita gadan-gadan tunda ta mare sa sannan ta yi waennan furucin garesa duk akan Yassir, shikenan
ko sunanta baya kira!
Iyakaci ya ce mata Ina kwana ko Ina wuni ruwanta ne ta amsa ruwanta karta amsa.

Ita kanta ta fara da na sanin marin da ta yi masa da furucin da ta yi, dan gashi sun janyo mata ya k’ullace ta!
ita gani take yi ma kamar gaba d’aya ya tsaneta….
kamar ba uwar da ta tsugunna ta haife shi ba!
Shiyasa gaba ɗaya duniyar ta yi mata zafi.
…
Tsakanin Ummi da yaran gidan ma abun ba dad’i sam, d’azu
da safe har bangajeta Kausar ta yi ..

Yassir ma ya samu gindin zama a wajen Munirat,
tun bata kula shi har ta zo ta fara kula shi sakamokon nacin da yake yi mata, sannan duk wani abunda ya san zai janyo ta so shi to shi ya ke yi tun ba ma da ya lura tanaso ta ga yayi repenting akan abunda yayi ba dan haka ya maida bata hak’uri d’abi’ar sa ba dare ba rana…

kullum sai sun had’u a wajen dining kitchen har back yard binta ya ke yi in ta fita shan iska.

ta sake da shi kuwa, dan
Munirat irin matan nan ne masu raunin zuciya ga tausayi,
kuma Yassir ya ci sa’a dan tun a ranar farko kyawunshi ya tafi da hankalinta, yanzu kuma kulawar sa da tausayin sa sun k’ara ingiza ta
zuwa gareshi.

A ranar da Ummi ta ganta ta fito daga d’akinshi, ta ja mata kunne sosai, ta kuma hanata shiga d’akin shi!
Gaisuwa ta mutunci dai tunda ya nuna yanaso a yi su yi,
amma ta tabbatar mata da ‘kar ta sake shigar mishi d’aki dan yin hakan ba dabi’a mai kyau bace ba…’

Ita kanta Munirat ta yi mamakin yadda ta kasa gayawa Ummi dalilin da ya sanya Yashjub ya daki Yassir a wannan ranar….
Wataƙila ko dan bata so Ummin ta tsani Yassir d’in ne, ko kuma ta ce za ta raba su har abada…
Ita kuma Ummi bata tambaya ba, kawai a tunanin ta fad’an su ne ya had’o su shi da Yashjub d’in.
….
Da Allah ya tashi kama Munirat kuwa, ranar Yassir ya biyo ta har d’akinta akan ta zo su je d’akinsa yanada surprise d’in da zai nuna mata..kawai sai ga Ummi ta shigo d’akin a daidai lokacin da Yassir ya janyo hannun Munirat ɗin ita kuma mistakenly ta fad’a jikinsa.

Da kyar Ummi ta ɗan danni kanta ta cewa Yassir ya basu waje, ya na fita kuwa Munirat tana shirin yin magana Ummi ta wanka mata mari sannan ta rufeta da fad’a, kuma ta ce “ta bata sati biyu, ta fito da miji a yi mata aure..”

Ba abunda ya fi b’atawa Munirat rai irin yadda Ummi ta k’i tsayawa ma ta saurareta, da kuma yadda ta yi zargin wani abun su ke yi ita da Yassir d’in…..
..
Munirat ta ci kuka kamar ranta zai fita, dan bayan Ummi ta tafi da kamar awa d’aya ta kira yayarta za ta labarta mata amman sai ta ji itama yayar tata ta rufe ta da fad’a ashe har Ummin ta kirata ta kora mata jawabi….

sai da ta yi mata fad’a sosai, tukunna ta kashe wayar ko sallama ba ta tsaya sun yi ba..

Ranar haka y’an gidan suka gabatar da dinner d’insu babu Ummi babu munirat…

Kausar kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha.
Tabbas ta fara hango silver lining(alamun nasara) ba kamar da da komai yayi musu duɗum!!!.

Sai k’arfe sha biyu na dare tukunna Munirat ta sauk’o k’asa ta d’ebi abinci ta nufi sama, wasu ma har an saka su a fridge haka ta d’auka ta yi warming a micro wave..

tana hawa saman ta nufi hanyar side d’in su kenan ta ji Yassir ya ce ’’Munirat’’

A zuciye ta juyo amma sai ya yi sauri ya rufe mata Baki da tafin hannunsa, ya karb’e plate d’in nata ya ajjiye akan centre table na parlourn saman kafin ya ja ta zuwa d’akinsa….

ko da suka shiga sai da ya sa ta yi masa alk’awarin ba za ta yi ihu ba tukunna ya cikata, ya cika mata Baki ya matsa gefe.

Duk masifar da Munirat take ji, tashi d’aya ta b’ace ɓat!!
Sakamakon abunda ta gani a gabanta……

Sosai ya yi decorating d’akin da candles, gashi an rubuta “I love you Munirat” da ballon’s, gwanin ban sha’awa…

cikin sanyin jiki ya ce mata ‘’dama surprise d’in da na ke so na nuna miki kenan…
Ina so in gabatar miki da kaina a matsayin masoyi kuma me neman aurenki, amma kuma na rasa a ina zan yi dan na san ba za ki yarda ki bi ni mu je wani wajen ba, kuma ba zai yiu na yi miki a cikin gidan ba…”

Daga nan ya durƙusa a gabanta a hankali, sannan ya yi mata sahihin proposal.

Duk yadda Munirat ta so ta d’an ja aji kasawa ta yi dan tashi d’aya ta ce masa ‘yes’ sai kuma ta juya da sauri ta fita,
dan duk sai ta ji wata kunyar shi ta lullub’eta.

Ko abinci nata bata tsaya ta d’auka ta ci ba dan tashi d’aya ta ji ta a ƙoshe…

Tana fita Yassir ya saki wani kalar murmushi a ransa ya ce
‘’Allah sarki! zuciyar Mace bata da wuyar samu.
very innocent soul(mai tsarkakakkiyar Zuciya)’’.
Chapter 55 · 0% Book details