← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 84

Sashe 3

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani Abu da Imam ya yi noticing
shine kullum fuskar Uwar gidansa
da idanunta a kumbure su ke,
ya yi tambayar duniya ta ce mishi kawai ciwon ido ne ya ke damunta….
A yadda su ka haɗe kansu gidanshi kullum cikin zaman lafiya da lumana ya sanya kawai ya kauda duk wasu shakku ya kwantar da hankalinsa ya guji tsawwala bincike sannan ya rungumi matanshi Hannu bibbiyu. Dan sosai a ta ɓangarensa ya ke iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen kwatanta adalci,
shi kan sa ya san yana Namijin ƙoƙari tabbas wajen ganin ya yi adalci a tsakanin Matan nasa
duba da yadda ya ke ji game da ko wacce a cikin zuciyarsa……
A yadda uwar gidan tasa ta ke kula masa da Amaryar ya kamata ko Albarkacin haka ne a ce ta ci itama
ta samu guri a zuciyarsa
Amman har gobe ya kasa bata
ko da kaso ɗaya ne a cikin ɗari na zuciyar sa saboda
Amaryar ta riga ta haɗe ta mamaye gaba ɗaya kaso ɗari ɗin
Itace zuciyar tashi ma gabaɗayanta.

Amman kuma dukda haka
Yana iyakar bakin ƙoƙarinsa sosai wajen boye hakan.
Abu ɗaya ya ke yi wasu lokutan ya ke tonawa kan sa asiri….
Kasancewar sa mutum mai masifaffen kishi ya sanya kishinsa ba ya ɓoyuwa akan Amaryarsa amma Uwargidan sam ba ya nunawa sosai.

Tsananin kishin sa a Amaryar ya janyo ko Abokan shi ba ya bari su gaisa da ita. Idan za a fita ya dinga gyara mata zaman hijabinta ya na rufe koina, ko gaisuwar mai gadi in ta amsa su ka ɗan gaisa sai ta haɗu da mita na ƴan kwanaki
Saɓanin yadda ya ke nunawa uwar gidan sa halin ko in kula.

Shiyasa ko ba a faɗa ba ko ya ɓoye su sun riga sun sani.
Ba tare da shi kanshi ya san sun gama ganewa ɗin ba.

Cikin Amaryar ya na watansa na biyar Imam ya tattara gaba ɗaya dukiyarshi ya damƙawa babyn da za ta haifa!
Mace ko Namiji ya ce shi bai damu ba, kawai dai shi ya san ya daɗe da gama yanke shawarar idan aka Haifa mishi baby na farko a rayuwarshi to ya bada komai nashi a babyn kenan…
Amaryar har kuka ta dinga yi akan ya janye wannan ƙudiri nashi
dan a ganinta zai janyo mata baƙin jini ne amma furr ya ƙi ji ya ƙi gani.

Daga ƙarshe dai ya tilasta ta ba yadda ta iya ta haƙura ta bi tsarin nasa sannan su ka tsayar akan ‘Maganar za ta tsaya iyaka su biyu’
Idan Allah ya sa ta haihu shi zai ci gaba da kula da dukiyar har sai Yaron ko Yarinyar ta/ya kai munzalin aure tukunna za a damƙa mishi komai…

A cewarshi sannan a yadda ya faiyyace mata wai kyauta ce kawai ya ga damar bayarwa
sabooda farin cikin samun haihuwa ne shiyasa ya shirya hakan a ɗan da zai haifa na farko kuma ko da ace uwar gidansa ce ta haifa tou hakan zai yi…
Amman a chan cikin zuciyarshi
har ga Allah ya yi hakan ne saboda tsananin so da ƙaunar da ya ke yi wa Amaryar tashi!
Dan yadda ya ke sonta ya kuma kwallafa rai a kanta haka ya ke ji da cikin jikinta shima, kamar ranshi. Ba ya fatan wani abun ya sameshi ta wulaƙanta.
Ya san su Abba ba za su bar Yaron ya wulaƙanta ba amma ita fa! Dan ta Uwargidansa ta na da nata gatan Amaryar ce abun ji…

Wani sabon abu da ya fara lokacin da cikin ya kai wata bakwai shine
rashin godewa abunda su Larai su ke yi!
Duk kalar ƙoƙarin da su ke yi waAmaryar sai ya daina gani..
Ko maganinta ne idan ba ta sha a kan lokaciba to ranar sai an ga abun mamaki! Dan rashin kara ya
dinga masifa kenan har washegari.

Kuma in dai Amaryar ta yi missing magani tou ko dai ita Uwargidan su na girka mata abinci ne sun sha’afa ko kuma wani abu makamancin haka…amma sam Imam ba ya fahimta.

Ganin rigima ta na shirin fara kunno kai hakan ya sanya ita da kanta Amaryar ta karɓi magungunan nata daga Hannun Abokiyar zaman tata ta ce za ta dinga sha da kanta.

Dan ita kanta abubuwan da Imam ɗin ya ke yi sam ba ta jin daɗinsu…
Ko dan yadda su Laran su ke sonta da gwada Namijin ƙoƙari wajen bata kulawa ita da abunda ya ke cikinta ya kamata ace ya yaba amma kamar ma ba ya gani. Shi komai kawai ita da cikin Jikinta.

Abunda Imam ya ke yi a kan cikin nan za ka ɗauka a kan shi aka fara haihuwa a duniya!
Abu ɗaya da uwar gidanshi ta yi shine kau da Kai!
Sosai ta yi ƙoƙari wajen ɗauke kanta ta rufe Idanunta, sam ta ƙi
yarda ta biye mishi, kuma
sarai ta san da maganar ‘bawa ɗan da Amaryar za ta haifa kakaf dukiyarshi da ya yi amman shima ba ta ce masa ƙala ba!
Dan ita a wannan lokacin babbar damuwarta
Ita ce yadda ta gagara ɗaukar ciki!
Dan haka ta duƙufa addu’a
sannan ta bar Imam ya na ta kinibibin shi shi ɗaya.
Ƙarƙari idan ya ce ba ta yi wa Amaryarsa abu ba
ta bashi haƙuri kawai
a wuce wajen, ko yana mita bata biyeshi.

A kwana a tashi….
edd ɗin Amarya ya cika har ya wuce
amman sam ba ta ji motsi ko alamun labour ba, dan haka su ka
nufi asibiti.

Su na zuwa tun a gwajin farko
aka fahimci
Babyn babu rai ya ma daɗe da mutuwa dan har kamar ya fara dagargajewa ma.

Sumewa Imam ya yi a wajen da jin wannan mummunan batu!
Dan tabbas bai taɓa shiga tashin hankali kwatankwacin na wannan lokacin ba.
Har aka yi aikin aka gama aka cire babyn aka mata wankin ciki bai farfaɗo ba.

A tare su ka yi jinya a asibiti ita da shi dan ba kaɗan ba jinin shi ya hau !

A bangaren Amaryar itama abun babu sauƙi sam!
Dan bayan kwana biyu da yi mata wankin ciki
Yayarta itama ta rasu!
Ta sanadiyyar haihuwa da ta zo yi
duk su biyun ita da Yaron ba wanda ya rayu.
Shiyasa abun sai ya haɗe mata biyu, gaba ɗaya ta burkice…
Ba dan ƙarfin Imani ba da tuni ta zauce tsabar yadda abubuwan su ka daketa.

Imam ma sosai ya yi fama dan kamar wani ƙaramin Yaro haka ya ke kwana ya na wuni kuka, ga rashin lafiya, sai da Mahaifiyarsa(Yahanasu)
ta tsawatar masa ta yi
masa nuni da muhimmancin karɓa da yarda da ƙaddara tukunna da kyar da taimakon Allah da addu’o’i ya ɗan dawo dai-dai.
Ko a gidan nashi ma sai da aka kwashe duk wasu kayayyaki na babyn da ya kashe uban kuɗaɗe ya yi ta siya ya na jibgewa a ɗakin da aka ware guda domin babyn tukunna
aka samu sa’ida!
Dan kafin a kwashe ɗin haka nan zai shiga ɗakin ya rungume kayan Yaron ya yi ta uban kuka kamar wani ƙaramin Yaro abun tausayi!
Dama shi tun ya na Yaro yana da masifar son ƴaƴa
Shiyasa ya kwallafa rai akan cikin jikin Amaryar tashi masoyiyar shi, sai dai kuma
Ƙaddara ta riga fata………..

*Bayan Watanni Uku*

Kamar haɗin Baki, a lokaci guda duk su biyun su ka samu ciki.
Sai dai edd na uwar gidan ya fi na amaryar
A yadda ya nuna Ita uwargidan ce za ta fara haihuwa da sati biyu daga nan amaryar itama ta haihu …

Murna wajen Imam ba a magana
amman a wannan lokacin ma duk yadda ya so ya ɓoye kowa sai da ya fahimci ya fi farin ciki da cikin jikin Amarya.

Kasancewar Uwar gidan itama ciki gareta wannan karon shiyasa aka ƙaro mai aiki, wadda ta ke zuwa da tafiya su ka haɗu ita da
Larai su ka yi ta kula da su.

Kamar yadda Imam ya yi wanchan karon haka ya yi wannan ma
Ya kwashe komai ya damƙawa ɗan cikin Amarya.

A nan ne kuwa ya ga ɓacin ranta kalar wanda bai taɓa gani ba dan burkice masa ta yi, ta ce ba zai yiu ba, in har gaskiya za a bi ai itama yayar tata ciki gareta….
Har kuka ta dinga yi masa sannan ta haɗa da nasihar kar ya yarda ya zamto cikin Maza masu zalinci babu kyau sam.
Ita Amaryar babban abunda ya sake ɗaga mata hankali ma shine tunda ta ke da Uwargidan ba ta taɓa cutar da ita ba!
Abunda ta ke yi mata ko Ƴar uwarta wadda ta rasu ba ta yi mata shi ba…dan haka ta yaya zai dinga yi mata haka saboda Allah ita kuma ta naɗe Hannu ta zauna ai ba zai ma yiu ba.
Ita kam babu ruwanta kuma idan ya matsa sai ta je ta samu su Daddy ta faɗa musu dan ba da ita za a yi wannan zalincin ba
……
Yanayin yadda cikin Amaryar ya yi tsini kamar wanchan karon na farko
hakan ya saka masa yaƙinin Namiji za ta haifa in sha Allahu saɓanin
na uwar gidan wanda ya bi jikinta sosai yasanyata ta yi ƙiba.

Shiyasa ya zauna ya yi ƴan lissafe lissafensa tukunna ya yanke shawara, ya zo ya sanarwa Amaryar cewa tunda ta ɗaga hankalinta kuma ta ce ya yi adalci shikenan zai yi…
Na farko ya fasa bada duka dukiyar
maimakon hakan zai rabata gida biyu ne ya bayar da rabi ya riƙe rabi
Sannan zai bayar a duk wadda ta haifa masa ɗa Namiji
Idan kuma duk su ka haifi maza tou sai a rabata gida biyu a bawa kowa kashi ɗaya, kuma kamar tsarin farko shi zai ci gaba da kula da ita har sai
Yaron ya kai munzalin aure ko shekaru goma sha takwas tukunna zai damƙa masa abunshi.
Chapter 3 · 0% Book details