Sashe 79
Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai a lokacin Yassira wadda tun d’azu ta kumbura sannan al’ajabi ya rufeta ga kuma tausayin Kausar ɗin
ta ce
‘’Kausar! me za mu yi da adress d’in ta?
Kin dai san duk abunda kika je kikayi mata zata gaya masa ko??
Baya ga haka ma ba ajin mu bace, sannan bai kamata ace
mun tsaya muna chachar Baki da wannan Yarinyar wadda bana jin ta kai sa’ar Yusra ma.
Kuma idan ya sani ko ya ji labari ina fatan kin san kashinki ya bushe ko?
Ki duba ki gani dai yadda duk ya burkice ya rikice yake ta faman rarrashinta
saboda kawai ya ga tana hawaye….’’
Mahaukacin burkin da Kausar ta ja wanda sai da Yassirar ta buga kanta kad’an ne ya sanya ta yi shiru, dama Yasira a zuciye take kuma ranta a mugun b’ace yake ‘na ganin Manubiya da ta yi’ dan haka rai a ɓace ta d’ago ta ce ’’Girl! Are you crazy? (Ke! Kin haukace ne?)
kallifa ya…’’
Maganar tata ce ta mak’ale sakamokon hawayen da ta gani ya fara zubowa ta cikin Idanun Kausar d’in..
Shiyasa gaba day’a sai tausayinta kuma ya lullub’e Yasirar….tabbas ko da ace itace
take da saurayi ya yi budurwa kamar wachchar Yarinyar da suka tarar a office d’in Yashjub
to fa ko dai ta hak’ura da shi ko kuma ta bi ta ko wacce hanya ta rabasu, dan ita kanta tunda ta ganta tashi d’aya sai da ta raina kanta ga wani irin kishi da ta ji ya taso mata a take duk ya bi ya lulluɓeta lokaci guda!!
To Ina kuma ga Kausar ɗin?!
Allah kad’ai ya san me take ji!
Bata riga ta samu hankalin Yashjub d’in bama, gashi har wata ta yi wuff da shi, dan a iyakar abunda ta gani a yau kawai tabbas ta san sunada aiki jaaa! A gaban su.
‘’Yassira har mu je gida kar ki sake cewa komai
Dan Allah’’
Muryar Kausar ta katsewa Yasirar tunanin.
Tana gama fad’in hakan ta ja motar da gudu suka wuce.
Suna zuwa gida ba ta ko kalli Yasira ba, ta bud’e motar ta fice ta wuce sama.
Kai tsaye fanninta ta nufa, tana tafe Zuciyarta tana wani irin tafarfasa.
Tana shiga parlournta ta yi cilli da wayarta da d’an ficicin mayafinta sai kuma ta fara kai kawo….tana safa da marwa a cikin ɗakin, kafin kuma
ta fara d’aukar abubuwa tana farfasawa!!!
Wanda hakan ya janyo hankalin Mommy, dan
haka ta nufo side d’in nata.
Tana shiga ta zaro idanu waje, sai
kuma ta k’arasa inda Kausar d’in take ta rik’eta cikin tashin hankali ta ce
‘’Lafiyar ki kuwa?’’
ta yi mata tambayar tana mai shafa fuskarta wadda ta yi jajawur idanunta suka sake k’ank’ancewa.
Tsabar tashin hankali kasa ma magana ta yi, kuma so take ta yi kuka sosai amma ta kasa dan shima hawayen ya k’afe…
Suna tsaye a haka Yasira ta iso, tun daga bakin k’ofar ta fara cewa “Kausar bani takardun nan akwai wanda ya ke jirana a office kins…’’
Maganartace ta mak’ale sakamokon kutso
kai da ta yi cikin parlourn.
Da sauri ta ce’’Ya subahanallah!’’
sai
kuma ta k’arasa inda suke tsaye su duka biyun.
Tana zuwa ta rungume Kausar d’in, sannan a hankali
cikin son kwantar mata da hankali ta ce ‘’kar ki damu, za mu nemo mafita’’
Da sauri Mommy ma ta shiga rarrashin Kausar d’in dukda kuwa bata san dalilin fashe fashen da ta tarar ta na yi ba da ɓacin ran nata amma dama tunda Yassira ɗazu ta ce mata ‘’za su je office d’in Yash itada Kausar” ta san za a rina….
Suna nan tsaye wayar Kausar ta d’au k’ara….
Dan haka ta janye Jikinta daga na Yassira a hankalia ta koma gefe ta durk’usa ta d’auki wayar tata
wadda ta duk farfashe dan tana shigowa dama da ita ta fara yin cilli.
Ganin mai kiran nata ne yasa ta d’auka a take, sannan a hankali
ta ce ‘’ina jin ka’’
Daga chan d’ayan b’angaren ya ce mata “gani nan yanzunnan aka ajjiyeta a k’ofar gidan nasu ta shiga’’
daganan ya fad’i mata adress da number gidan tukunna ya ce ‘’ban samu
sunan yarinyar ba dai amman
Ina kan bincike.’’
‘’Tam’’
kawai Kausar ta iya cewa daga haka ta zare wayar daga kunnenta ta kashe sannan ta shiga cikin contact d’inta….
Zuwa wannan lokacin Yassira ta fahimci da wa ta gama yin waya dan haka ta matsa kusa da ita ta ce mata’’Kausar me za ki yi ne??’’
Dai-dai nan ta kara wayarta a kunne ta ce ’’Hello!na’am…zan turo maka adress d’in wani gida yanzu!Inaso ku je duk wata budurwar da bata kai 25 ba a gidan ku yi resetting d’inta….’’
A zabure Yassira ta wafce wayar ta yi jifa da ita
cikin fushi ta ce ’’Eh!lalle kam zuciyarki ta kama da wuta!!
kuma ba ki da hankali!”
Cikin rashin fahimta sannan a d’an tsorace Mommy ma ta
matso ta d’an rik’e Hannun Kausar d’in sannan ta ce
‘’Kausar! Su wa kika bada order a kashe?? Yaushe kika fara harka da y’an daba ba mu sani ba????’’
Ba tare da Yassira ta kalli Mommy ba ta ce ’’Matar da Yash yake so zai aura take so a kashe saboda mahaukaciya ce ita’’ ta fad’i hakan still idanunta na akan Kausar d’in.
Sai a sannan Kausar ta d’ago ta kalleta itama tukunna ta ce ’’kina da wata idear(shawarar) ne bayaga ‘ku bani hak’uri ku ce za a san abun yi’
Bayan wannan ɗin??
Ki fad’a min idam akwai wata mafitar da ta fi wannan
yanzu, ina so in ji’’.
Cikin takaici da tsananin b’acin rai Yassira ta ce ’’ban tab’a tunanin abun naki ya kai har haka ba!
Ban tab’a tunanin za ki iya kai har izuwa wannan hatsabibin matakin ba!
Kausar kin san menene rai kuwa??..
A kan Yashjub wanda idan Ubangiji bai rubuta Mijinki bane shi ɗin ko sama da k’asa za ta had’e baki Isa ki auresa ba shine za ki d’auki jinin bama mutum d’aya ba?”
A ɗan tsorace sannan a rikice ta kalli Mommy ta ce
“Tunda bamu san y’an mata nawa ne a cikin gidan ba.’’
Sai kuma ta yi shiruuu kawaui ta runtse Idanunta ta tsaya da magana saboda tsabar yadda al’amarin Kausar ya k’ulle mata kai ya bata tsoro gaba d’aya yasa kanta har wani jujjuyawa yakeyi.
Sai da ta d’an dawo dai-dai tukunna ta bud’e Idanunta ta kalli Kausar ido cikin ido ta ce
’’ki saurara ki kasa kunne ki jini da kyau!
Ina mai shawartar ki!
had’e da gargadi!
mai tafe da zazzafan warning(jan kunne)! Da kuma threat(barazana!)…
Na rantse da Allah idan wani abun ya sami Yarinyar nan to
da Bakina zan fad’awa Yash komai sannan babu ni babu ke har abada!Dan ban shirya zama a k’ark’ashin inuwa d’aya da murderer (masheƙiya) ba.
Idan ba ki nutsu kin dawo cikin hankalinki ba to za ki rasa komai kuma za ki rasa kowa…duk tak’amar ki da kuma isar ki baki kai Yash ba dan haka inaso ki saka a ranki cewa ‘idan kika kashe ta da shi za ki yi shari’ah!’.
Kar ki lalata rayuwarki da Hannunki!
wannan zafin da kika d’auka babu inda zai kai ki sai garin da na sani, mu d’in da muke ce miki ‘ki yi haƙuri, ki bi komai a hankali za a nemo mafita’ mu ne
masoyanki, kuma mun fi ki gaskiya.
Ki nutsu ki yi lissafi ki ga yadda duk iyakar k’ok’ari muna yi
amma sai da yayi budurwa, gashi yanzu har ana maganar aure!
Ba ki san menene a k’asa ba ba ki san me Ubangiji ya binne ba dan haka mu bi komai a hankali, a samu a nemo mafita
amman kashe ran d’an Adam sam ba namu baneba Kausar!.
Tun Yarinta ina tsaya miki tsayin daka akan dukkan al’amura amma wallahi Kausar idan kika zarce iyaka na fad’a miki na sake maimaitawa
Ni da ke pam!pam!!pam!!!.”
Ta fad’i hakan tana mai karkad’e tafukan hannayenta duk biyun.
Jinjina kai Kausar ta yi cikin b’acin rai ta ce
‘’Tabbas a yau Yassira na san cewa blood is thick(Jini ba ya ruwa)”
Cikin tarar numfashinta Yasira tace‘’this isn’t about blood Kausar
(Wannan ba akan batun ƴan uwantaka bane ba Kausar)’’
Cikin fushi Kausar ta ce
‘’To dan mai yasa kike komawa ɓangarensa?
Ba ma fa ki san wannan Yarinyar ba amman a yadda ki ke yi ɗinnan ya sa na ji kamar har kin so ta, kuma na tabbatar farin cikin da kika gani a fuskar d’an uwanki ne ya sanya kika fara sonta da har kike tunanin kareta.
Na san banida kowa Yassira amman ban yi tunanin kaɗaicin nawa ya kai har haka ba
sai yau’’
Matsowa Yassira ta yi ta kama kafad’unta tukunna ta ce
‘’Kausar, wallahi yadda kika tsani Yarinyar nan nima haka na tsaneta, abu d’aya da nake so ki gane shine
Duk rintsi ba zan tab’a goya miki baya ki yi abunda kike shirin yi ba, kuma idan har ma kika aikata hakan ke a karan kanki kin san me hakan ya ke nufi???’’
Bata jira jin amsar Kausar d’in ba ta ce
‘’yana nufin kin tsorata,
kin ji tsoronta! Kin bada Kai
kin san ta fi ki da komai,
kin yarda babu ta yadda za a yi ki iya kwace shi daga hannunta
Shiyasa har ki ka yi mata mai kan-kat!’’
A hankali Mommy wadda tun d’azu ta yi shiruuu kawai tana kallonsu ta ce ’’bari in je kiran Daddyn ku, shi ne ya kira ni na
na fito. Ina zuwa yanzu zan dawo’’
‘’Tam’’
kawai Yasira ta ce mata daganan ta ci gaba da cewa Kausar
“ita Mace ce! Kema Mace ce dan haka ki yaƙe ta! A yi duk kalar yaƙi da kissa da faɗan da za a yi har mu samu mu yi galaba a kanta..
Wannan na yi miki alƙawarin zan tsaya miki akai duk rintsi Kausar amman batun kisan kai kam ya fita daga tsari da lissafi dan haka a barshi, dan gaba ɗaya tunanin naki Kausar ya fita a kan hanya”
Ta k’arashe maganar tata a hankali.