← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 84

Sashe 21

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun a lokacin da ta fara kukan
Abbakar ya fahimci takaici da kuma tuno Inna ne suka saka ta kuka.
Sir Najeeb kuwa takaicin ta ne ya sake lullub’e sa, ya lura da yadda bata ma yi attempting ta ba shi hak’uri ba tun farko, yanzu kuma ta cika masa office da koke-koke, abun da yace ta daina yi masa a aji shine yau ta kwaso ta kawo masa har office, dan haka a fusace ya zagaye tebur d’in da ke a gaban sa ya wuce Yashjub da niyyar nufar inda take kamar wanda zai dake ta.

Cikin hanzari Yashjub ya tashi tsaye, ba tare da ya juyo ba ya ruk’o Hannun Najeeb da sauri dan already har ya gota sa
‘’Wait pls!’’
Kawai ya iya cewa.
Daga haka ya cika masa Hannu tukunna ya juyo ya nufi inda Abbakar ya ke a durk’ushe ya ce masa
‘’Stand up!.’’
Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya ce ‘’ki yi shiru ko ki fita’’ yayi mata maganar ba tare da ya kalle ta ba.

Da kyar Manubiya ta samu ta haɗiye sannan ta share hawayenta ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere itama har yanzu bata bari sun yi ido biyu ba.
Da sauri Abbakar ya mik’e ya na cewa
‘’Wallahi , I don’t want to interrupt you ne, thats y (wallahi bana so in katse ku ne, shiyasa) muka yi shiru, dan Allah ku yi hak’uri’’.

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma kawai ya juya ya ce
‘’Sir Najeeb a yi musu afuwa mana’’

Shiruu kawai Najeeb ya yi ya ƙurawa Yashjub ido yana mamakin shi, tun da ya san shi
bai tab’a gani yayi irin hakan ba…
lamari wanda ya shafe sa ma
barin wajen yake yi ballantana wannan da bai shafe sa ba.
Shi har gq Allah da ya ji ya ce masa ‘wait pls’ yayi tunanin so yake ya mik’e ya fita inyaso daga nan sa cigaba da hayaniyar tasu …..

Sai da Najeeb d’in yaga Yashjub ya d’an yi masa murmushi tukunna ya kawar da nazarin da ya soma ya d’aga masa kai kawai ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna,
Ya zubawa Abbakar Idanu.

Chan kan sofa Yashjub ya koma ya zauna ya tsurawa tV ɗin da ba a jone take ba ido.

Da sauri Abbakar gudun kar su sake yin wani laifin ya ce
‘’Morning !
Sir,ka ce mu biyo ka shine..’’

Cikin katse shi Najeeb ya kalli Manubiya ya ce
‘’Discuss on Email and Linguistics’’

Dibi-dibi ta hau yi kafin kawai ta yi bismillah ta rufe idanunta
tukunna a hankali ta ce
‘’Ban iya ba’’.

Cikin fushi ya ce
‘’Ko kuma dai kin manta,ko?
Saboda a takardarki in da ace ban gano yi miki akayi ba!
Da tsaf zan baki A.’’

A hankali gaban ta yana fad’uwa ga b’acin rai ta ce
‘’Ka yi hak’uri Sir, Mahaifiyata ce bata da lafiya, tana kwance a asibiti ma yanzu haka!
Shiyasa ya yi mini, ka yi punishing d’ina amman dan Allah ka kyale Abbakar,
tausaya min yayi, bashi da laifi.
dan Allah.’’

Tabbas ya tausaya mata, dan ko ba a bashi tabbaci ba ya yarda da gaske take duba da yadda yanayin kalar idanunta suka chanza da kuma zafafan hawayen da ya ga sun zubo mata, kaɗai, sun isa tabbatar masa gaskiya take fad’a.

Tun yana k’ank’ani mahaifiyarsa ta rasu bayan doguwar jinya amma sam bai manta zafi da raɗaɗin rashin lafiyar mahifiya da kuma rasuwar ta ba!
Hakan ya sanya ya d’an sauk’o, zuciyarsa ta d’an yi sanyi.

Tsit office d’in ya yi, baka a jin k’arar komai sai na Ac yayin da Manubiya take ta faman sauk’e ajiyar Zuciya a jejjere, ahankali.
Yashjub yana nan a yadda ya ke tun ɗazu ya k’urawa waje d’aya ido, k’arar wayarsa ce ta katsewa kowa tunani….
A hankali ya zaro wayar daga cikin aljihu ganin sunan Daddy ne ya sanya shi mik’ewa ya amsa wayar ya kara a kunnensa kafin ya nufi k’ofa da ɗan hanzari cike da k’asaita.

Tun lokacin da Manubiya ta shigo dama take tsaye a bakin k’ofar har kawo wannan lokacin, ganin da tayi ya mik’e kuma ya nufo ta ne ya sanya gaba d’aya ta diririce….
d’azu ta ji k’arar waya amma a zaton ta bai amsa ba ko kuma ma maybe ta Sir Najeeb ce ya bari akan in sun fita ya amsa, sam
Bata lura da wayar da ke kare a kunnensa ba dan ba shi take kallo ba directly kawai dai tana iya ganin Motsin sa ne.

Ganin da ta yi dai da gaske itan ya nufo hakan ya sanya ta yi sauri a k’ok’arin kaucewa dai-dai shima ya kauce da niyyar zagaye ta ya bi ta bayanta ya fice!
A tare suka sauk’e ajiyar zuciya sakamakon d’an kusancin da suka sake samu wanda ya sake dilmiya su a wani yanayi na daban.
Sai da Yashjub ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya sake k’ok’arin kaucewa domin ya samu ya wuce ta inda take da farko, ba tare da ya kalle ta ba yanzun ma,
amman sai akai rashin sa a dan a dai-dai wannan lokacin ne itama ta kauce da niyyar ta bashi hanya a karo na biyu!.
Ɗan taku ɗayan da ya yi da niyyar kaucewa kuma sai ya sanya suka matso daff da juna kamar za su yi gware.
Zuwa wannan lokacin Manubiya ta tabbatar fad’uwar gaban da take samu da yadda bugun zuciyarta ya sauya tun farkon shigowar ta office d’in a
ta dalilin wannan bawan Allahn ne
Saboda
The more yana kusanto ta
The more bugun zuciyarta yake k’aruwa…..
Haka kurum sai ta tsinci kanta da son kallon fuskarsa dan haka ta d’ago kyawawan idanuwanta waenda ruwan hawaye,takaici, bak’in ciki, damuwa da k’unci
Suka cikasu taff..

Ganin sun kusan yin gware a karo na biyu ne ya sanya Yashjub saita kwayar idanunsa a fuskarta da niyyar ce mata
‘Ta tsaya shi zai matsa, ya wuce,ya fita’…
Karaff!idanuwansu suka sark’e a cikin na juna.

Sai da numfashin Manubiya ya d’auke na y’an sakannni
tukunna da kyar ta samu ta nemo shi ta daidaita shi ya dawo mata dai-dai,
A Chan ƙasan zuciyarta ta ce
‘’Ma shaa Allah!!!!’’

Duk yadda Yashjub ya so ya d’auke idanuwansa daga kanta kasawa yayi, a lokacin in da za a tambaye shi yanayin Bakinta ko hanci hatta ma da kalar fatar ta to ba lalle ya iya fad’a ba! Saboda
tsabar yadda zuciyarsa da ruhinsa suka karkata sannan suka dulmiya a cikin kwayar idanunta……
…….
Kamar irin idan Mutum yana bacci ɗinnan ya dinga jiyo muryar Mutum daga chan nesa ana tashin sa, haka Yashjub ya fara jiyo muryar Daddy a chan nesa yana cewa
‘’Hello,Yash!Yash!!Yashh!!!!are u with me, kana jina kuwa?’’

Wani bagwaren numfashi ya fesar sannan ya yi saurin lumshe idanunsa, a hankali ya sake runtse idanuwan nasa waenda bai riga da ya bud’e su ba har kawo wannan lokacin…
da kyar ya had’iye wani abu wanda ya tokare masa mak’oshi!!!
Kafin ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce
‘’Yes!,Daddy’’
Daga nan ya zagaye ta tukunna ya bud’e idanunsa ya kama handle d’in ƙofar da sauri ya murza ya fita..

Sai da Abbakar ya ce ’’Manu!’’
tukunna Manubiya ta dawo office d’in, a take kunya da takaici suka lullub’e ta dan ta san tabbas sun lura da irin kallon da ta yiwa wannan bawan Allah da kuma yanda ta k’ame k’am! Ko bayan fitar sa.

‘’Hmm’’
Kawai Sir Najeeb ya ce, kafin ya fara magana
‘’Dole zan yi cancelling test d’in ku both of you, sai ku dage a exams. Bai kamata a ce na d’aga muku k’afa har haka ba bayan gashi na kama ku dumu-dumu!!!
Amman uzurin ki shi ya taimake ku, ku dage a exams sannan ko da wasa karku k’ara yi mini wannan shirmen a test ko assignment, idan mom d’inki bata da lafiya ki zo ki yi reporting’’.

Da sauri suka had’a Baki suka ce
‘‘In sha Allah, mun gode Sir,
Sosai.’’

A hankali ya jawo computersa ya fara latsawa
kafin ya ce
‘’U can leave’’
Ba tare da ya kalle su ba.
………………………
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*12*

Tun lokacin da Yashjub ya baro office d’in Najeeb, gaba ɗaya ya rasa nutsuwar sa. Har ya k’arasa gida ya yi wanka ya yi sallah ya nufi side d’in Mommy domin ya Isar mata da sak’on Daddy gaba d’aya hankalinsa yana kan Yarinyar da ya gani ɗazu a office d’in Najeeb.

Sai da ya yi addu’a sosai tukunna ya samu tunanin ta ya bar shi ya yi sallah a nutse.

Bai samu Mommy a parlour ɗinta ba dan haka ya wuce d’aki sai dai nan ɗin ma bata nan….

Har ga Allah Kansa har ya fara ciwo shiyasa ya bi gadonta ya kwanta shi kad’ai ya yi shiruu.
So yake ya lumshe idanuwansa ya d’an huta amma ba ya son yin hakan saboda ya san yana lumshe su idanuwan wannan Yarinyar zai ke gani.

Abun takaicin shine ko sunanta bai sani ba sannan ya san idan za’a jere masa mata blindfolded(a rufe musu Idanuwa da kyalle) ace masa ya nuna ta a cikin su sam ba zai iya gano ta ba.
Ya san
bashi da wata alak’a da ita amman kuma sam muryarta da idanuwanta sun addabi zaman lafiyar sa ya rasa nutsuwa ya kasa yakiceta sam ya rasa sukuni, tun ɗazu da ya ganta har kawo yanzu babu daƙiƙar da ta wuce wadda bai yi tunaninta ba.
Sai da ya yi da gaske ya had’a da addu’o’i tukunna ɗazu ta ɗan lafa a ransa ya samu ya yi sallah cikin nutsuwa…..

Wani bahagon tsaki ya jaa ya miƙe ya zauna a kan gadon,
kafin ya zaro waya ya danna kiran Najeeb….
Chapter 21 · 0% Book details