← Book details Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 84

Sashe 72

Mannubiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manu kuwa ta lumshe idanunta ne kawai, ta jingina da jikin bango
dan zuwa wannan lokacin tabbas zuciyarta ta yi galaba akanta…
wani farinciki da nutsuwa kawai ta tsinci kanta a ciki.
Bata san meyesa yake son kiran ta ba amma kuma kiran nata da yakeyi ɗin da kulawar sa
gareta da kuma taimakon su dayayi ayau
tabbas sun k’ara bada gudunmawa wajen tsundumata cikin tafkin k’aunarsa.
Ta san ba lalle ta sameshi ba,
ta san za ta sha wahala, ta san ya kamata ta yaƙi zuciyarta amman kuma ta san ta makaroo
dan ta san ko ta yi yunk’urin hana kanta ba za ta hanuba!
she can’t help it…
saboda ta riga ta kamu.
sannan abunda take ji a duk lokacin da ta yi tunanin shi ko kuma take tare da shi
‘aljannar duniya ne’ haka za ta fasalta abun, dan ya ƙunshi duk wani nishaɗi, farin ciki, annashuwa d.d.s…..
Dan haka bata son ta rasa wannan abun da ta ke jin ko da na second d’aya!
Ita kaɗai ta san me take ji….shiyasa a take tausayin kanta sai ya lullubeta.

‘’Na yi tunanin za ki kirani’’
Muryarsa ta katse mata tunani.

A hankali ta ce ‘’tun d’azu ban zauna ba, sai yanzu’’

‘’Yeah, nima haka…
Na san ai ko da ace kin zauna d’in ma, ba kiran nawa za ki yi ba.’’

‘’Saboda me’’
Ta yi saurin tambayar sa.

‘’Saboda na lura kamar tsoron kulani kike yi, bakya so mu fahimci juna alaƙarmu kuma ta bunƙasa.
idan kuma na yi making move (wani yunƙurin da zai bunƙasa alaƙar tamu) sai a balbaleni da fad’a, a yi fushi a bar min office d’ina”

Wata iriyar kunya ce ta lullub’eta, kamar tana gabansa haka ta rufe fuskarta da tafin Hannunta d’ayan,
saboda gaba d’aya kunyarsa da kunyar abunda ta yi masa jiya da safen take ji…
Sai kuma ta yi saurin dafe k’irjinta, dan sai yanzu ne kwakwalwarta ta gama mata lissafin abunda ya ke nufi
‘Making move (Bunƙasa alaƙa) kamar yaya?
Ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.

Shiruu ne ya biyo baya kafin
da mugun k’arfi kirjinta ya buga jin a hankali cikin wata kalar murya ya ce
‘’Mannubiya’’

Bata san lokacin da ta kashe wayar da wani irin sauri ba,
tana hak’i kamar wadda ta yi y’ar tsere!
Sai kuma ta lumshe idanuwanta, ta sake kishingiɗewa a jikin bangon kamar mai shirin shigewa cikinsa, a lokaci guda kuma ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere.

Ta d’an d’auki lokaci a hakan, kafin ta ji kira ya sake shigowa wayar. ta riga ta san shi ne shiyasa ta yanke shawarar k’in d’auka, amman kuma sai zuciyarta ta ƙi bata goyon bayan yin hakan,
dan haka ta amsa kiran…

Tana d’auka ta ce masa “zan duba inna yanzu, sannan za mu zo da ni da su Ya Musbah mu yi maka godiya,
a office. ban sani ba ko kana nan gobe sunday’’
ta so daga haka kawai ta kashe amma kuma sam sai ta gagara.

Shiruu ya d’an yi kafin ya ce
‘’Ba za a abar godiyar nan ba kuwa? zaku sa in yi ta jin kunya fa’’

A hankali ta ce ‘’ba komai ai, da har da Baba ma zamuzo’’

Da sauri yace ‘’Innalillahi. dan Allah ku rufa min asiri….
In Baba ya zo yi min godiya da kanshi ai sai in b’ace. d’azu ma duk sai da na ji wani iri da ya min a waya Wallahi.’’

Murmushi ta yi kafin ta ce
‘’Eh muma mun lallab’a shi ya hak’ura, amma dai ka bari mu d’in mu zo saboda ba zai yarda ba, ko na ce masa ka ce ba sai mun zo ba! bazai bari ba.
kuma nima ina son in yi maka godiyar, dan ban samu na yi maka a asibiti ba’’

Shiruuu ya d’an yi, har sai da ta zare wayar daga kunnenta ta kalla taga still yana kan layin
kafin ta ji ya ce ’’Ni kam ba godiya na ke buk’ata daga wajen ki ba..
Akwai abunda nake da buk’ata amman sai ido da ido tukunna zan gaya miki.
Allah ya kaimu goben.
inanan.

Akwai aiki dama, kinga goben sai ki nuna min, daganan idan mun kammala ni kuma sai in gaya miki tukuicin da nake so a bani,’’

Shiruu ta yi har sai da yace ‘’Mannubiya’’
Tukunna ta ce ‘’to.
amma fa babu aiki mutum d’aya ne kawai, sannan ya akayi ka sani?’’.

Murmushi yayi yace ‘’aikin nasa yana da matuƙar muhimmanci.”

Shiruu ta kuma yi kafin ta ce
‘’Ai be kamata ka tambayi tukuici da kanka ba, ni ce zan ga dama in bayar kuma bai ma gama zama ready ba (bai ma gama kammaluwa ba).”

Dariya ya yi, yana jiyo wauta a cikin maganar tata kafin ya ce ’’banaso ki siyamin komai…
In ma wani abun kike shirin siya, dukda kuwa na ji daɗi kuma na gode
amman da gaske ba na son ki siya min komai.
Ni a ɗaɓi’ata idan na yi abu aka yaba to ni zan fad’i tukuicin da nake so a bani.”

Sai da ta ɗan juya maganar a Bakinta tukunna ta ce masa
“Iyakar maidamin zuwan nawa sau biyu da ka yi a wannan satin, a ganina ai ya ishi tukuici to”

‘’Um um bai Isa ba, sannan ai ba iya wannan satin nace ba, zuwan ki gaba ɗaya ya dawo sau biyu kenan Friday and Sunday’’ yace hakan yana murmushi.

Turo Baki ta yi gaba kamar tana gaban sa, sai kuma ta yi shiruu tana tunani kafin ta samu tayi kokawa da zuciyarta wadda take ta faman d’aurata akan tunanin abunda zai fad’a mata goben…..
ahankali tace ‘’bara in duba Inna, sai da safe’’

Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya ce “dare bai yi sosai ba ko?
in ba damuwa inaso za mu gaisa’’

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ’’ai bata da lafiya’’.

‘’Eh, Najeeb ya fad’a min kuwa…Allah ya bata lafiya. ki
kai mata wayar in yi mata ya jiki’’
Ya sake nanata mata batun gaisawar, a karo na biyu.

Sai da Manubiya ta d’an lumshe idanuwanta ta bud’e tukunna ta ce ‘’ai bata magana, bata iya yin komai’’

Da sauri ya ce ‘’subahanallah,
Stroke?’’
Ya yi mata tambayar a d’an rikice.

A hankali ta ce masa “eh’’

Shiruu ya yi yana nazari kafin ya ce ‘’wanne physiotherapist d’in take gani?’’

A hankali ba dan ta so ba tace mishi ‘’in mun kaita tana ganin normal Dr’’

Zuwa wannan lokacin ya fara fahimtar wani abun dan haka a hankali ya ce ‘’wanne asibiti take zuwa, da magungunan da take sha?’’

Sai da ta sauk’e y’ar siririyar ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’asibitin murtala’’.

Ahankali ya lumshe idanuwan shi, yana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsa shi….ji yake yi kamar yayi mata kuka.

Sai da ta ce bara in je, sai da safe. tukunna dakyar ya ce
‘’Ok’’
sai kuma ya sake cewa ‘’zan iya kiran ki nan da 3O minutes haka, dare bai yi ba?’’

A hankali ta ce ‘’tam, ba damuwa’’
daganan suka yi sallama..
A ranta tana mamakin tsantsar tausayin ta itada ahalinta tare da kulawa da ta jiyo ƙarara a cikin muryarsa.

Ba a cikata mintuna ashirin ba ya kirata, ya sanar mata ‘’gobe su shirya around 8, akwai babbar likitar da ya yi booking, za ta zo ta duba Innar. Idan ta zo ɗin za ta tafi da ita asibitinta a goben, in suka gama aka maido Innar gida kuma Matar za ta dinga zuwa gida kullum (ko ita ko wakilliyarta) ana duba Innar ‘’
Daganan ya ce ‘’ta tura masa adress d’in gidan nasu zai turawa Likitar’’

Shiruu Manu ta yi, dan ita har ga Allah batayi tunanin Likita zai kira a daren nan ba, bayaga hakan ba ma ta yi tunanin abun zai damesa har haka ba…

ta ji dad’i matuk’a da ya damu da damuwarta, kuma ta ji dad’i da innar tasu za ta samu kulawar lafiya ta musamman dan ta san InshaaAllah da taimakon ubangiji za ta warke in ta samu kulawa ta musamman, wanda hakan shine babban burinta ita da y’an uwanta a halin yanzu(inna ta warke)
To amma kuma sai take gani kamar ɗawainiyar da Yashjub ɗin yake yi da su ta yi yawa, ba wai ko dan tana tunanin za ta d’aura masa nauyi ko kuma aljihunsa zai yi k’asa ba dan ta san hakan ba zai tab’a aljihunsa ta koina ba tunda ya riga ya tara, kawai dai tana ganin kamar in hakan ta faru su d’in za’a ga kamar sun zira jiki sun sakankance da shi dayawa, kar kuma aga kamar ko kwaɗa’…..’’

Muryarsa ce ta katse ta jin yana cewa “Likitan Babba ce ta kware sosai a aikinta. kar ki damu inshaaAllah innarmu ta kusan warkewa’’

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin a hankali ta ce ‘’bansan ta Ina zan fara yi maka godiya ba’’

Cikin katseta ya ce ’’Mannubiya, tsakani na da ke babu godiya’’
Sai kuma ya d’an yi murmushi tukunna ya ce ’’kawai dai tukuicin da na ke da shirin tambayar ki gobe ne nake addu’ar Allah yasa kar ki ce A’a’’

Ahankali ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
‘’good 9te, sweet dreams’’

A hankali kamar itama bataso ya ji tace masa “good nyt’’…

Murmushi kawai ta ji yayi daganan suka yanke kiran a tare kowannen su yana yi kamar bayaso.

Yana katse wayar ya koma ya kwanta rigingine akan gadon
yana wani kalar murmushi….

Ƙarar wayarsa ce ta katse shi…

yana d’auka da ya kalla kawai sai ya maida kanshi ya kwanta ba tare da ya amsa ba!
Yana mai jin yanayin rai da zuciyarsa suna chanjawa….tun d’azu Mommy take kiran sa, tun yana wayar da Manubiya har yayi da Doctor ya koma ya sake yi da Manubiya….
Shi da farko ma bai san ita bace ba dan bai duba mai kiran nashi ba, sai da ya gama shirya appointment da Doctor tukunna ya ga ashe ita ce.
Chapter 72 · 0% Book details