← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 95

Sashe 93

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka Gama Wayar Manal ta Mike ta shiga bedroom sannan ta Kira shi,ai Kuwa tana dagawa sai masifa ke in kin fada min bazan barki ba sai kin hadani da Hajiya,sau nawa Ina rokonka ka barni kaki yarda din sabo da ban Isa ba amma Hajiya na magana ai ka yarda,idan na Kamaki ko tam.. kici gaba Zaki dawo ne,ae din naji Haba Dan Allah yau ka tuna gwaurantarka ka rungumi pillow,Ina Baby na? tana can ta gama rigimarta tayi bacci Hajiya ta goyata,Hajiya ce ta goyata? ae Mana ai tunda Muka zo tafi son Hajiyan ma,Yace tunda Hajiya ta goya min Minal Dina ai Dole ma na barki kuyi 3days,ai na zaci ma Kara min zaka Yi 1week, sai kace Ana hauka,Belloti ne ya shigo gidan shi da Afrah Masatura kenan sun dawo daga Shopping,da kayan makulashe iri iri,Su Hajiya ai suna zuge Dadi a gidan Belloti ko yaushe cikin tande tande suke Baya gajiya,Hajiya murna ta isheta Farida tana hutawa,Tace lallai a baya munyi hauka da shirme,abin zuciya ne Ashe ba kudin ba,yaro me zuciyar Yi Haka Amma a nace sai me kudi,ba a son me rufin asiri sai Naira kawai Yan Mata da Iyaye Ido ya rufe,Farida tace wallahi dai Kinga duk abinda Hamshakin me kudi yaci Ina cinsa a gidan Nan duk da shima Allah ya bashi aikinyi me kyau Alhmdllh.
Belloti kowa ya tambayeshi ya Jariri sai yace Yana can dakin duhu,akan Likita sunce Kar a kunna Masa haske sai Nan gaba.
Farida ta samu Gift daban daban,Jariri yaci sunan Baban Belloti Umar suna ce Masa Musaddiq,kwana Uku na cika su Manal suka bi flight sai gida.

Prince da Kansa yaje airport dakko Manal dinsa,Yana hango ta da Baby Minal sun dau wanka harda sa takalmi me tsini,Ga jaka katuwa da kyar take tafiya,Suna Fitowa Fuzail ya rungumesu da ita da Baby din duka Yana Yana cewa I really miss you,Miss you too ta furta,Fuskarta ya shafa yace I need you Badly Sunshine let's go,Dariya tayi tace Dan Allah ka dinga Hakuri,au 3days banyi Hakuri ba? Kina can kullum sai su Tanko ne ke tayani Hira mu zauna suyi ta bani dariya,Wai Tanko wanne aikin zaiyi maka ne? Fuzail yace gidan fa gona na Bude katon gaske a Nan na zuba ma'aikata Tanko shine na bawa gidan gonar yake karkashinsa, zai dinga lura da komai sabo da a baya ya Dade Yana kula da gidan gonar Maimartaba Yana da Ilimi akan abin,Salary dinsa Kuma ya ninka na gidan Sarki Wajen sau Uku ko hudu ma,Sannan Kinga ko Bama Gari suna gidan Nan zasu dinga kula da gidan Bai kamata a bar gida ba kowa ba shi yasa na kawo Tanko,Sani Kuma driver na sai mata masu aikinki ai sun Isa ko? Manal tace hakane Yayi kyau kayi tunani,Minal ce take Miko Masa Hannu ya dauketa gashinta yasha gyara gata Fara tas kyakyawa kowa yaga Baby Manal sai ta shiga ransa sai yaji Dama yarsa ce,gata Yar gidan Yan gayu,Daya Hannun Yarinyar tana hannunsa Daya Kuma yana Jan akwatin Manal ya saka a mota sannan ta shiga gaba Suka tafi,Yace ga ciki ga Minal ga takalmi me tsini ga Akwati duk ke Daya ai da nasan da takalman Nan kika tafi sai na kwashe su tas ga flat Nan baza ki saka ba,to ai nafi Jin dadinsu ne shi yasa,Zaki daina sawa ne ai Bari cikin ya girma da yawa.

Dariya Manal tayi Tace prince kasan su Farida da Hajiya mamaki Suka dinga Yi ciki Wai har ta fito,Ni kunya ma naji wlh yanzu fa kusan lokaci Daya zamu Haihu da Badi'at din Ameer,ciki ne da matar Ameer din? Baka sani ba to ya girma sosai ma ku fara shiri,Allah ya raba lafiya Ameen.
Bayan sun karasa gida Yan aikin Manal suka Zo Yi Mata Sannu da zuwa,gidan yasha gyara ko Ina sunyi abinda Tace,Minal Suka karba a Hannun Prince suka tafi part dinsu da ita,shi Kuwa Fuzail yace Bai San zance ba ya fara hucewa akan Manal,ya fara Sarrafata yanda yake so,itama tayashi ta shiga Yi tana Jin dadi tana Nishi kamar me.

Islaha Kuwa sai da cikinta ya wuce wata hudu sannan ma ta tsorata ta rafka Salati Tanko Yana kwance a kujera yace lafiya? Tace ciki nane naji Yana ta tauri Kuma Yana kumburowa sannan Na Dade da daina period Kai ba lafiya ba t&k Ina Jin na harbu kawai,tashi muje Asibiti kinji dake Fuzail ya bawa Tanko mota me kyau ,Tanko anyi motar Hawa sabo da zuwa gidan gona,a Nan ya dauki Islaha Suka je asibiti ai Kuwa ciki,Islaha sai murna tace Mum nake sak,Tanko yayi Dariya yace Ni Kuma Abba ba,gida suka dawo abinsu suna ta murna Tanko yace yau Yau Dole naci farfesu da yawa.
Manal Basu Dade ba suka chale England sabo da business din Fuzail sai da suka kwashe wata biyu daga can suka wuce Saudiyya,sai Brazil, Suka kwashe 2weeks sannan Suka dawo sabo da makarantar Manal,shima Kuma ya Gama abinda zaiyi sai in ta Kama yake zuwa kula da harkokinsa na business ya dawo,Watarana ya tafi da Manal Watarana Kuma shi Daya,Yazed ma da matarsa Fuzail ya biya musu aikin Hajji.

Belloti mota ya siyawa Farida me kyau sannan ya siyar da tasa ya cika ya siyi dalleliyar babbarta,gidan da suke ciki shima sai da ya sake kawata shi aka canja furniture Yan kasar waje baya an canja paint da komai sun Faso Gari,Alhaji Kasim Yana Jin dadin aikin Belloti Sabo da Haka ya bashi takardun gidan gaba Daya ya mallaka Masa gidan ya Zama na Belloti Halak malak,Dangin Belloti Basu Kara son Farida ba sai da Suka Zo gidan yanda Farida ta kula da su ya sa musu kaunarta a ransu,ko da Suka koma sai Waya suke bugo Mata Ana gaisawa, Belloti yafi kowa murna.
Tun kafin Farida tayi Arba'in Belloti yake damunta Yaya Injin Dap ya samu lafiya kuwa? Ina Injin Dap? Farida Tace da saura,ga Jariri Musaddiq yayi wayo kubulbul da shi Dan Fulani sak,Ranar da Farida tace ai Inji ya samu lafiya Belloti yace till down yau wlh ba bacci,Farida ma an shirya anyi gyara ranar raba dare Suka Yi suna farantawa juna Rai,Haka Belloti da Abokinsa Uche suna gaisawa sosai har Uche yayi Aure shima.

Haka rayuwa ta kasance musu cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali har cikin Manal ya cika wata Tara,Lokacin Kuma Badi'at ta Haifi twins Yan biyu duka maza manya manya,ansha shagali lokacin Yara suka ci suna Fuzail da Fu'ad,su Manal sune Yan Gaban gadon me jego Abokin Miji Guda.

Bayan suna Suka koma Abuja har su Tanko ,suna komawa da kwana biyar Manal ta fara Nakuda,Allah yasa Ogan Yana gida Suka tafi asibiti da masu aikin Manal,suna zuwa ta Haifo Danta Namiji katon gaske kyakyawan gaske me Kama da Fuzail,wannan Haihuwar Manal sunsha Baki,kannen Fuzail su Na'ima Wanda an saka ranar aurensu su Biyar za a Aurar da maza Uku cikin Yaran me martaba duk Rana Daya za a daura musu aure,Tunda Suka ga mugun Haduwar gidan da Fuzail ya tsara har Basu so ma komawa gida ba.

Su Farida ma da su Hajiya da Suka ga gidan mamaki ne ya kashe su, Raheela me Yaron ciki da Yazed tare Suka Zo Suka koma,Ameer kwanansa biyar da matarsa daki Guda aka Basu a gidan abokinsa,ranar Suna yaro Kawai yaci sunan Ameer Kamar yanda Fuzail yace ,bayan Baki sun tafi komai ya dawo normal Ummi tazo a nutse tayi sati Daya ta tafi,su Annatu da Yan uwa duk sun Zo.
Rumaisa ma ta Haifi mace,Shukhra Namiji ta Haifa itama.
Manal tana yin Arba'in dole taje asibiti ta fara planning sabo da gudun kwanika.
Fuzail da matarsa da Yayansa ya dauke su Ukraine sun tafi hutawa duk Hutu in Manal ta samu sai sun tafi wata kasar hutu da yaransa.

Watansu biyu a can Islaha ta Haifo Danta Namiji me Kama da ita fari da shi Amma yayi hancin Tanko siriri me tsayi da tsini,har matan Sarki sai da Suka Zo Barka har Abuja,Bayan suna su Manal sun dawo Suka ga Jariri Kato da shi mashaallah,ga bikin su Na'ima yazo Saura 3days har su Tanko da Sani Suka tafi gaba Daya Gidan Maimartaba kowa part dinsa ya shiga.
Sai da akayi biki aka Gama lafiya Ranar da Fuzail zasu koma Abuja Minal tana jikinsa a zaune tana Wasa sabo da tana gudunta ko Ina tana magana Tace Dad a shiya min iscream,Dariya Suka Yi yace Ice cream ake cewa fa Baby,Manal ce ta shigo Tace ke Zo muje ayi wanka tafiya zamuyi,kafada ta makale
Daddy ne zai min,wlh Zan Miki duka idan Baki taho ba,Fuzail ne ya harari Manal yace karki Dake ta wlh daga tayi Abu kice Zaki duketa Rannan ma haka Kika mareta akan ta zubar da madara,Manal Tace to lalatata ta sangarce wannan yarinya r za a dinga kyalewa kana gani Bata da kunya ta rainani,Hajiya Babba tayi Dariya tace ai yarinya ce sai hakuri Kuma me tayi ma,Minal ta murgudawa Manal baki,Manal tace Zaki sani sai na zaneki,tazo ta fisgota muje marar kunya ,Fuzail yace Kar dai ki sake naji kukanta,Minal tana Jin Haka sai ta fashe da kuka tayiwa manal sharri,Hajiya Babba tace kaga yarinya da sharri ai sai ki kashe aure,Fuzail yace uwarta ta gado itama Haka take min sharri ban Mata komai ba tace na Mata abu.
Chapter 93 · 0% Book details