← Book details Mafarkin Farida Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 95

Sashe 73

Mafarkin Farida Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana zuwa Suka je da Fuzail tare da gaisar da Iyayen Belloti,Lokacin Farida tana Sallah Manal Tace Bari na jira ta idar Ina Yayan Nawa Bamu gaisa ba,Fuzail sai ya hade girar sama data kasa Kar Manal ta gaisa da Belloti,Sai Kuwa ga Belloti ya shigo Dan saurayi da wankansa na Shadda ta Masa kyau matuka,Manal tayi Murmushi tana kallonsa Suka gaisa da Fuzail,Manal tana Dariya daga kallon Belloti shike Nan Fuzail ya fice waje Yana ta bacin rai,Manal ita Kuma mamakin wayewar Belloti takeyi a ranta tace yo dama Yana Zaune da ogar Daukan wanka ko Bai iya ba ai sai Farida ta gogar da shi bare Kuma Dama a gogensa ta sanshi,Belloti ya fita daban a garin yayi kyau sosai dama gashi ba laifi Yana da kyau,Manal tace Belloti lallai kana hutawa,Belloti Yana dariya yace Hutu ai sai ku kune manya,Farida itama kishi taji ta tuna Belloti yanda yace Yana kaunar Manal ga Manal yanda take da Arnen kyau gashi wani kyau data Kara taci gayu Haka Kawai Belloti yazo yaga muninta gwara Manal ta tafi sai tayi wayo tace Kai Manal kin Shiga uku wallah ki tashi ki tafi kin San dai mijinki Bai son jira ki tafi Yana mota mu ba ruwanmu idan yayi Fushi da ke,Manal zata Yi magana Farida ta katse ta da kin fiye surutu dare fa zai Muku a hanya,Ai cikin garin Bauchi zamu kwana sai gobe zamu bi Flight,to ku tafi sabo da yanzu rayuwa ba yarda duniya ta canja Ana fama da Yan ta'adda.

Mikewa Manal tayi Belloti yace muje na rakaki,Farida tace karfa ka jawo Mata mijinta Yana da kishi,to na Riga na aureki wanne kishi zaiyi yasan dai ai bazan dawo na so Manal ba,Farida Tace zuciya Kashi ne da ita? Belloti Fuska ya Bata Kawai sai Farida ta Shiga hankalinta Kar suyi fada tsoron Belloti take ji,da Manal Suka fita a soro Manal ta bashi 20k tace gashi a kular min da Aunty,Fafur Belloti yaki karba Kuma baida kudi Amma ya rantse bazai karba ba,Manal Tace to shike Nan ka bawa Aunty na,Yace wannan Kuwa Zan Bata kawo ya karba yasa aljihu yace tana godiya.

Ai Fuzail Yana ganin Manal dinsa da tsohon saurayinta sun jero ji yayi Kamar ya hadiyi zuciya ya mutu ya huta,danne bacin ransa yayi Bai Bari Belloti ya Gane ba sukayi Sallama,Belloti ya sake zagawa ta saitin window Manal yace mun gode Allah ya kaiku lafiya kinje gidan Khaltum Kuwa kawarki? Manal tace sai na sake dawowa dai,Okay to ya juya zai tafi Manal ta sauke glass tace ka gaisar min da su Lawi Dan Allah idan na dawo Duk zan neme su,Belloti yace kin tuna cin gyadar ku kenan Manal ta fara Dariya Fuzail Yana gefenta Kamar ya masgeta Haka yake ji,driver ya yiwa magana muje Yana Jan Tsaki,Driver Yaja Suka tafi Belloti ma ya tafi gida Farida gabanta sai faduwa yake Kar Belloti yaga kyan Manal yaji ya tsaneta ita,sai gani tayi ya dawo Yana ma Yi Mata wani kallon kauna,Farida dukkan Yan gidan su Belloti kaunarta sukeyi sunga Yar gayu,gashi wani mutunci da ladabi da biyayya take musu,20k din Belloti ya bawa Farida yace gashi inji Kanwarki,Farida Tace Uche ya bani 10k ta isheni ka rike wannan,Belloti yace a'a bana son gorinku na Mata duk ranar da fada ya hada mu sai kin tuno da kudin Nan naki ba ruwana ki rike abinki kayan Mata kayan gori,mace ta taimaki Miji Amma ba dama yayi katabus sai Gori da cin mutunci bada Ni ba Kar Azo ace Belloti ai na baka 20k kyauta ka biyani abata,Farida ta dinga dariya Tace Allah bazan Yi ba,yace sai dai in ban tashi Kara aure ba duk sai kin Fadi abarki ba ruwana,au zaka iya Kara min kishiya? Ni na Isa Ina Zan Kai matan misali na Baki fa,Indai ba Hali kika canja ba ko wata kaddara ba abinda zanyi da wata Engine Nan naki ya isheni,Farida Tace karka sa na tashi na Fara taka rawa,Belloti Yana dariya yace surukarki zata ganki dakin Nan namu ba sirri gareshi ba,Haka suke hirarsu.

Da Yamma Goggon su Belloti tazo zata fara girkin dare,Belloti yace ki fita ki Taya Goggo Aiki kin San dai Dangin miji,Farida tana Dariya tace to ba musu, aikin da ko uwarta Bata tayawa amma ta yo waje ta dauki tsintsiya goggo tana ki barshi Farida Yara zasuyi daga zuwanki sai Aiki Dan Allah ki huta Haka,Farida tayi murmushi sanye da Hijab dinta Tace barni Goggo na motsa jinina ai Ni na Saba da Aiki dama tun a gida,Goggo tana Murna tace to madalla,Haka Farida duk girman gidan Nan ta share ko Ina ta gyara komai har Ledar tsakar daki ta ko wanne daki sai da ta goge,bayinsu yasha Siminti Nan ma ta sake wanke shi fes ta dawo ta karbi garrin Dawa tana tankadewa Ashe Farida ta iya Iskanci ne yasa basa Yi a gida gashi anzo Ana bautawa Uwar miji.

Manal Kuwa tunda Suka tafi tana kallo Fuzail Yana Fushi Bata taba ganin fushinsa Haka ba,tunawa tayi ko Dan ta kula Belloti ne,a ranta tace Wai wannan wanne irin kishi ne haka mutumin da ya auri Yayarta mene Kuma ai sunyi zaman gari daya tana so ta Masa Magana amma ba fuska,Tsoronsa ma ta shiga Yana can gefen daya Kofar itama tana gefen Daya Kofar,Satar kallonsa takeyi Kawai ya zurawa Hanya Ido fuskar Nan ba Rahma,a tsorace ta dinga lallabo da hannunta Daya sai kace wani wahainiya a hankali ta sa Yatsanta tare da dungurar hannunsa sai kace wani Zaki ta gani,ko kallonta baiyi ba,ta sake Dora Hannunta a cinyarsa tare da girgizawa ko kulata baiyi ba,lafiya My prince? Wani kallo ya watsa Mata kawai tayi Shuru,ganin Haka sai ta ja gefe itama tayi shuru,Har suka je garin Bauchi Bai saurareta ba Kawai wani katafaren Hotel yayi musu Booking,Sauran Securities yace Kawai su tafi da Motocin can gida zasu taho gobe ko jibi,ya sallamesu Suka wuce Manal ta dauki jakar kayansu wacce Guda Daya ce dama Suka hada kayansu ciki,Gaba yayi ya barta ta bishi da sauri,Sama Suka hau aka Basu key din room dinsu,Wani Room and Palo ya Kama musu katon gaske sanyi da kamshi Kawai ke tashi,Toilet ya fara Shiga yayi wanka da brushi ya fito ya shirya a gurguje ya wuce masallacin Hotel din,Manal ma Haka ta shiga tayi wanka da Brush ta fito sai da tayi Sallar Magriba da Isha tayi Azkhar sannan ta shafa lotion dinta ta nemi rigar baccinta ta saka wata maroon me kyau.

Knocking taji anyi ta manta Bata taba shiga Hotel ba Kawai ta tabbatar Fuzail ne ko mayafi Bata yafa ba ga rigar baccin sharara ta Bude kofa Allah yasa Fuzail din ne ransa ya sake mugun baci yanzu da ma'aikacin Hotel ne Haka zai kalle Masa jikinta shike Nan ya kalli banza,a tsorace tace Sannu da zuwa Tsaki Yaja ya hada da ita ya hankadeta gefe yayi gaba,Sharrin Manal sai ta tafi wani luuuuuu ta Fadi Tim a kasa ta fashe da kuka Tace ka dukeni? Fuzail ya tuna da cikinsa ya wani rude yaje ya tashe ta yace I'm sorry ban San Zaki Fadi ba na Dan tureki ban San Baki da karfi ba ne Haka,Manal tana kuka Tace dama kana sani Kuma ai dukana kayi,Ni din na dakeki? Kiji Tsoron Allah Manal Taya Zan daki matata Ni,Gashi Nan akan kana Jin Haushina ka dukeni,Tashinta yayi yace tashi to ya Dagata Tace Ni jiri nake ji wayyo marata Bari zanyi,Cikina ne zai zube,Bari zanyi,Fuzail yace daga Dan wannan faduwar sai ciki ya zube wallahi idan Mala'iku Suka amsa bakinki cikin Nan ya zube bani ba ke,Dan Iskanci sai kice ciki zai zube idan kika fada a dai dai fa,Ana so a furta alkhairi.

Tashi tayi da kyar ta haura saman lafiyayyen bed din sannan ta lullube jikinta,Baza kici abinci ba? Manal tace ae na koshi,Baki da hankali Haka Babyna zai kwana da yunwa,Manal zata Yi magana ya lullube ta da masifa dama haushinta yake ji kadan yake jira,yace dama haushinki nake ji na hanaki Abu kinki ji ko? Ke me taurin KAI ko? Sabo da Ina lallabaki ko? Sabo da Ina Wasa dake ban Isa in fada Miki magana kiji ba?Manal jikinta yayi sanyi tace to kayi Hakuri na daina amma kasan zaman gari Daya ba Wasa ba,Kuma Muna mutunci ne Bai kamata ba sai yace wulakanci ne Dan na auri me kudi,Kuma ma ai yanzu ya rigada ya auri Farida mutunci ya sake kulluwa a tsakani ba yanda zanyi Indai ba zargina kake Yi ba mene abin damuwa sai idan Zarg....karki lalata min aure ya katse ta,Zaki ce Wani abu Nifa nasan soyayyar maza Haka Kawai Kuna Hira Yana Jin Dadi idan Kun gaisa ba shike Nan ba Mene na wani Hira har kina Masa dariya Ina kallo fa kina Kallonsa ko ban ganki bane?
Chapter 73 · 0% Book details